Daudar Gora Book 2 page 75

 


Da kyar da kyar aka samu kotun ta lafa, yayinda kalaman Daneen Ammarah dake kuka sukai matukar daukar hankalin kowa. Fadi take, "Wlhy Mammah shine, shine wanda suka cutar da mu a tare. Bazan taba yafe musu ba, wlhy bazan yafe musu ba, sun haddasa bakin ciki mai ciwo a zuciyata. Sun nisanta ni da shi bayan sun alakanta mu".


   Sosai hankalin Malikat Haseenat dama duk wanda ke'a kotun ya tashi, dan yanda take kuka haka Babiy make kuka sai dai shi kansa duke yake a kasa. Ummu ma dai tasan komai da ya faru, dan a lokacin bai boye mata ba. Hakama lyyani. Iffah nason tashi taje garesu amma babu dama, dan ita Zawjata-almilk komai nata nada ka'ida da son nutsuwa. Dole ta hakura ta zuba musu ido kawai musamman Babiy da Ummu da Daneen Ammarah.


  Tajwar Eshaan ya nisa tare da motsa lips dinsa a hankali, "Wannan kotu na bukatar Daneen Ammarah a gabanta, da son jin fassarar kalamanta".


   Sayeed Hanifud-Din ne ya maimaita abinda Tajwar Eshaan din ya fada, dan haka Daneen Ammarah ta fito da taimakon Daneen Waheada,dan da alama abubuwan kanta ma neman sukeyi, idanunta har sun kada.


   "Ko zamu iya sanin abinda kike nufi da kalamanki Daneen Ammarah. Sannan ko kinada alaka ne da wanna shari'ar?"


  "Bani da alaka da wannan shari'ar face a farkon ta mai bada kariya ga Zawjata-almilk. Sai dai inada alaka shudaddiya da wannan bawan ALLAHn". Ta nuna Babiy.


  '"'Ko zamu iya sanin alakar taku?"


  "Mun taba kasancewa mata da miji kusan shekaru ashirin da daya da suka shude".


   Ba Iffah kawai ba, mafi yawan wanda ke'a cikin kotun sai da suka waro idanu saboda razana.


Sayeed Hanifud-Din ya ce,

"Ta yaya?".


   Shiru kamar batace komai ba, sai kuma ta nisa da share hawayenta. "Komai ya faru ne a cikin littafin kaddara ta. Na san duk wanda yake anan in har ya kai shekara talatin da biyar zuwa sama yason tabon da ke a jikin bangon littafin labarina da duka shafukan cikinsa. Bazan kirasa abin kaico ba, amma zan kirasa zalunci mai ciwo a gareni dama duk wanda yake cikin wannan masarautar. Faruwarsa kuma ta fara ne a bisa son zuciyar dan uwana Jasim dake a gaban shari’a a yanzu. Sun kulla min aure da wan nan bawan ALLAH bisa umarnin wata mushirika da ta shude ita da labarinta a wannan masarauta. Sai dai aure ne na kwanaki goma sha uku kacal suka saka ya sakeni. Bisa kudirar UBANGIJI kuma ya samar da haihu a tsakaninmu batare da shi ya sani ba ma, dan ban sake ganinsa ba tun wannan ranar sai a yau, sai dai ALLAH yayma yarinyar rasuwa a kwana uku da haihuwarta...

 

"BATA MUTU BA!!".


   Kalmomi uku masu razanarwa da ga bakin kaka. Wani irin zabura Babiy da Daneen Ammarah, da Malikat Haseenat, da Iffah, da Ummu, da Daneen Waheeda, da Malikat Bushirat, da Miran Jasim sukai a lokaci guda kuma a tare kamar wanda aka saita da camara.Su dukansu kuma suka zubama Kaka da yay maganar idanu kowanne da irin kalar luguden dakan da zuciyarsa ke masa a zahirance da badini. Cikin karfin hali Malikat Haseenat ta furta, "Taya wadda naima wanka, na shirya a cikin likafani, aka sallaceta a gaban kowa, aka gina kabari aka sakata za'ace bata mutu ba. Kai wanene? Ya akai kuma kasan hakan?".


  "ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai albarka. Nine mutumin da ya kora waccan bokanyar mushirikar a waccan raar dai da nasan bazaki manta ba".


   Ya arrahaman! Bawan ALLAH dama kana raye? Amma ka sakani a rudani.


   "Nasan zan saka kowama a rudani, sai dai wannan ranar ita naita rokon UBANGIJI zuwanta gareni kafin ya dauki rayuwata dan na cika wasiyyar mahaifina. Duk da burina ya cika na dawowar Fhareedah cikin zuri'ar mahaifiyarta a dalilin aure".

   

   Kowa zubama Iffah idanu yayi, kamar yanda itama take kallon Kaka jikinta na dan rawa. Malikat Bushirat ma wani irin bugawa kirjinta keyi, hakama Daneen Ammarah da Babiy. Cikin rawar baki data harshe Babiy ya ce, "Baba na kasa fahimtar komai".


   "Yanzu zan fahimtar da kai dama duk wanda ke anan. Kamar yanda Daneen Ammarah ta fada an aura mata miji kuma an saka ya saketa a sati biyu bisa umarnin mushirikar dake katantanwa da ikon wanna gida. Ba kowa bane wanda aka aura matan nan face Zayyan in Abbas. Zayyan dai da ne ga wani aminina da zan iya cewa ma ya zama jinina. Dan tunda muka taso babu abinda ke rabani da Abbas. Hatta aure an mana a rana guda ne, hakama haihuwar yaranmu tana zuwane a kusa da kusa. Sai dai shi nashi basa zama sai akan Zayyan. Sana'ar gidan su Abbas dinka kayan doki ne, dan haka ita ya gada ita kuma yake yi tunda yasan kansa, wannan dalilinne ya sani koyo a wajensa, danni gidanmu abinda na tashi naga anayi bana ra'ayinsa. Mahaifina babban mutumne mai bada magani sannan yana cire kowadanne irin aljanu a jikin mutum duk taurarin kansu. Ni kuma sai nake ganin kamar wani abun akwai kauce hanya, dan haka naki yarda na dingayi duk da tunda na taso yanayi a gabana na kuma san magunguna da sirrika kala-kala. Mukan dinka kayan doki ni da Abbas mu kawosu cikin Dahab City, anan ne muka hadu da wani bawan ALLAH da yay sanadin fara kawo wadan nan kaya namu cikin masarautar nan. A duk sanda muka kawo akan bamu kudinmu ne gaba daya, sai ma yazamindai mun dinka din nan kawai muke kawowa. A haka muka cigaba da rayuwa har shekarun yayanmu suka kawo girma, iyayrnmu suka bamu shawarar hada yaranmu aure. Munko yi farin ciki da shawarar, babu bata lokaci aka sha bikin Jumayma da Zayyan. ALLAH ya azurtasu da haihuwar fari da wuri, ta biyu ma haka, hakama ta uku. Zuwa sannan idan mun dinka kayan doki duk wanda zai o kawowa yakan taho ne da Zayyan da shine kadai keda sha'awar irin sana'ar tamu. Sauran yarana biyu maza kuwa suna nasu aikinne da sukafi so suma. A wata rana data kasance nine zan kawokayan da muka dinka masarautar a cikin azi sai na tashi da ciwo na zazzabi, dan haka Abbas ya amsa suka tafi kaiwa tare da Zayyan. Basufi awa takwas da tafiya ba sai gashi ya dawo min yana kuka. Hankalina tashe na tarbesa da tambayar lafiya. Bai boyen komai ba ya sanar min wai amma Zayyan aure da diyar Shahan- shan, cikin mamaki nace aure kuma? Wane irin aurene haka kamar auren kaza? Kuma da yar Shahan-shan guda anya kuwa?. Ya tabbatar min hakane, amma yanaji a jikinsa akwai dalili mai karfi nayin hakan dan yaji wasu yan samari da basu wuce sa'an Zayyan din ba na labari. Nan ya zayyane min komai dake faruwa ni da baba. Na lallashesa da kwantar masa da hankali na shirya a boye naje masarautar bisa umarnin mahaifina. Anan nake jiyo komai dama asalin dalilin hadin auren. Hankalina ya tashi dan na fahimci babban al'amari ne kam gashi ance Shahan-shan ma baya kasar shi da uwargidansa da Miran mai jiran gado. Kannensa ne da wannan aika-aikar. Na koma gida cikin damuwa mukai zaman jiran tsammani, tun muna irga kwanaki harya koma sati har sati biyu. anar kwatsam sai ga Zayyan ya dawo mana. Duk mun tarbesa da tambayoyin yaya akai ya kubuta. A take ya zayyane mana komai yana hawaye. Murmushi mahaifina dake kwance yana jiyya yayi, sai dai baice komai ba, sai daga baya 22:58

¡kirani yake sanarmin ya fahimci Zayyan ya kamu da soyayyar matar aurensa ta sati biyu dan haka a karo na farko yana son nayi wani abu, ya kuma tabbatar min ba shirka bace kamar yanda nake dauka dan shi ba mushiriki bane. Komai sai da ya zayyane mun, dan haka na dauka alwashin bibiyar al'amarinta har sanda zata haihu kamar yanda mahaifina ya bani umarni. Shi kuma ya sakashi baro cikin Jumna dan yace ya tabbata za'a iva zuwa nemansa, za kuma a nemesa a ko'ina dan haka yace yaje cikin Dahab City din inda bazasu taba tsammanin zasu samesa a kusa da su din ba, wannan ne dalilin dawowar Zayyan wanna gari, su kuma su Abbas ya sakasu dawowa cikin gidanmu yanda mutane zasuyi tunanin suma sun gudu. Haka kuwa akayi, bayan tafiyarsa da kwana biyu shi da matarsa da yaransu uku sai gashi anzo nemansa. Sai dai iya bulayi basu samesan ba, da ga baya dole suka hakura. A wannan dan tsakanin Abbas ya kamu da rashin lafiya ta kwana hudu kacal ALLAH yay masa rasuwa. Wannan mutuwa ta gigitamu matuka,hakama matarsa da Zayyan. A wajen zaman gaisuwar Abbas da Zayyan ke zuwa a sirrance ya hadu da Abu Musa, wanda shine silar masa hanyar kai zuma cikin masarauta dama abokinsa ne na yarinta. A tsorace yazo ya sanarma mahaifina abinda Abu Musa yazo masa da shi. Sai yay murmushi tare da kwantar masa da hankali tare da bashi kwarin  gwiwa saboda wani hasashe da yace yayi akan hikimar cigaba da zuwan nasa masarautar. Duk da shima yana da mai kawomasa duk wani rahoton da yake so na cikin masarautar, a haka nema muka san samuwar cikin Fhareedatu, wanda kuma yay dai-dai da samuwar ciki na hudu ga diyata matar Zayyan itama. Abubuwa sun cigaba da kai da kawo har zuwa ranar haihuwa, a lokacinne kuma mahaifina yasa na shirya yin abinda ban taba yi ba. Wato aiki da kayansa. Alhamdullah sai kafin ma nai wani yunkuri sai ga kiran mahaifina da ga masarauta wai zasuyi aiki. Da farko banyi niyyar zuwa ba dan shi mahaifina bazai iyaba saboda ciwo, amma sai ya zaunar dani yay min bayanin komai dama ban hasaso ba. Tunda dama ni nayi shirin shiga masarautar ne kawai na dakko abinda za'a haifa na fito kamar yanda ya sani sai a yanzu kuma labari ya canja. Bani da ikon bijirema umarninsa, kamar yanda shima bashi da ikon bijirema kiran masarauta dan haka na shirya zuwa kamar yanda ya umarceni tunda a duk abinda ya sanin banga shirka ko wani tsafi a ciki ba. Ina cikin shirin tafiya masarautar a dai-dai lokacin sai ga labarin haihuwar Fhareedatu da ga bakin amintaccen mahaifina. Wannan shine ya zaburar dani zuwa a gaggauce. Lokacin dana iso bokanyar ta riga ta gama shirya komai da su basuyi zato da tsammani ba ma, amma duk da haka nai iya kokarin da zan iya na mata kiranye da hadata ita da yan kayanta na Koreta a cikin masarautar kamar yanda mahaifina duk yace nayi. Ni nasan a korar da mahaifina yasa nai mata bazata iya ta dawo ba, amma kuma sai zuciyata keta faman mini kikawo. Idan uwar masu gida bata mantaba, nine na fadi cewar yarinyar ta rasu a lokacin da nasa a kawota gareni na dubata".


"Tabbas anyi haka".


  Cewar Malikat Haseenat. Murmushin Kaka yayi, da cigaba da fadin a lokacin amintaccen mahaifina ya bani gawar wata jaririyar dana canji jaririyar da ita ya fito da wadda aka haifa. Bakowa bane kuma sai wanda a yanzu kuke kira da Baba mai magani a gonar yaro, shugaban masu magajin gargajiya na wanna masarautar, saboda shi din yaron mahaifina ne"…..✍️


No comments

Powered by Blogger.