Daudar Gora Book 2 page 73


 Chapter: 73



…...…..Kallon da Iffah ta musu shi ya kara girgiza zukatansu, sun kuma tabbatar akwai abinda shegiyar ke kullawa. Sannan recording din nan da akai musu

batare da sanin su ba in fa har aka budeshi kowa yaji anan akwai matsala. Dan basa raba dayan biyu zama a iya kashesu a cikin kotun nan kuwa. Saboda basa

tantamar duk abinda suka yi na tsiyatakunsu a cikin masarautar za'a samesa a ciki. Miran Jasim da yasan kwabarsa sai tafi ta kowa ruwa ya fashe da kuka yana

girgiza kai. Ya fahimci idan har ya mika wuya da kansa zai iya samun tausayawar mutane ma. llai kuwa tsitt kotun tayi, yayinda Shahan-shan ya dan jin jinama

Sayeed Hanifud-Din kai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka yay saurin dakatar da shugaban jami'ai da ke shirin playing recording din. Dakatawar kuwa yay cikin nuna girmamawa. Kotun tai shiru aka zubama Miran Jasim idanu. Shi kansa Miran Arshaan sakare yay kawai yana kallonsa dan ya kasa fahimtar ma'anar

kukan. Iffah kam wani shegen murmushi ta saki da har sai da ya bayyana farare hakwaranta.


   Ganin kukan Miran Jasim bana karewa bane ga lokaci nata tafiya Sayeed Hanifud-Din ya gyara tsaiwarsa da fuskantarsa. "Shin ko Jasim na da wani abin cewa ne haka?". Kuka Miran Jasim ya sake fashewa da shi da fadin, "Tabbas nine mai abin cewa, na kumayi alkawarin fadin duk abinda ake bukatar jiNda ga gareni, domin nayi nadama, nayi nadama matuka akan biyema Arshaan da mahaifiyarsa da tawa, Dan komai ya faro asaline da ga su...."


 Ba Arshaan kawai ba, hatta Malikat Haseenat zura masa ido kawai tai, dan kowa yasan wacece mahaifiyar Arshaan. Mace ce mai kirki da kyawawan halaye. Haka kuma mahaifiyar shi Miran Jasim din. Mace ce mai mugun hali da son kanta, duk wanda ya kwana ya tashi a masarautar kuma ya san mahaifiyar Jasim din da ta Arshaan basa ma zama inuwa daya. Amma dai bara aji mi jasim din yazo da shi. Kuka ya cigaba da yi wiwi kafin ya nisa da cigaba da fadin, "Nasan a zahirance kowa zai ce iyayenmu mata basa shiri da juna ne, sai dai abin ba haka bane. A boye su din aminai ne matuka, dan mahaifiyar Arshaan ta shiga jikin Mammah (Malikat Haseenat) ne kawai danta dinga zakulo musu sirrikanta tana kawo musu. Burinsu shine muyi mulki, tare da mallake dukiyar Abbu (Tajwar Abdul-majeed) gaba daya, dan sun san Haysam ne zai gaje komai tunda shine babba. Sunta kulla-kullar gain mun halaka Haysam tun ma muna yara amma hakan bai kasance ba, dan haka suka yanke shawarar uwa ta kashe Abbu da Haysam tun a wancan lokacin.


    "Why karya kake matsiyaci makiri!!!".


   Miran Arshaan ya fada cikin karaji da fashewa da kuka yana kaima Miran Jasim duka. Dan fa shi duk lalacewarsa yana son uwarsa, kuma yasan sam bata taba saka kanta a cikin wanna al'amarin ba, koshi bai fito da maitarsa a fili ta son mulki ba sai bayan mutuwarta. Da kyar aka rabasu, har Miran Arshaan ya jima Miran Jasim ciwo da farce a fuska. Rumtse idoNkawai Shahan-shan yayi cikin kunar zuciya. Sai da kotun ta lafa da kananun magana da ta dauka sannan aka sake bama Miran Jasim damar ci gaba da magana. Kafin yace komai Miran Arshaan ya tare da fadin, "Ba gaskiya ya shirya fada ba, dan haka ni wihy zan fadi komai, na kuma bada damar bayan duk na gama fada a bibiyi recording din nan namu dan baiyi dai-dai da abinda zan fada ba amun duk hukuncin da ya dace. Dan da ya tozarta mahaifiyata da ke kwance a cikin kabari da mata kazafi akan abinda bata aikata ba gara na fadi gaskiya koda ace itace karshena. Abinda ya fara fada ya faru amma a iya shi da mahaifiyarsa ne banda Ummi na, shi da kansa ya bani wanna labarin a randa muka yarda zamu hade kai domin yakar dan uwanmu Haysam. Dunkulewar tamu kuma ta samo asaline kan ima diyar Hifzur-rahaman fade da mukai ta mutu, muka bizne gawarta a cikin masarautar nan batare da sanin kowa ba ranar bikin al'ada. Tabbas mune muka aikata ni da shi, kuma duk neman da akai taima yarinyar har zuwa wannan shekarun da kowa ke tunanin saceta akai ko bata tai a bikin al'ada ba haka bane ba. Bayan mun dunkule mun shiga yakin gain bayan Haysam tako ina amma bamuci nasara ba. Muna a cikin wannan yakinne kuma yazo mana da zancen yin murabus ya daura dansa. Hankalinmu ya tashi matuka, a lokacin muka bazama neman bokaye kwararru da suka iya aiki, har muka had da boka Barbushi. Boka Barbushi ya mana alkawarin taimaka mana, da kuma tabbatar mana kashe Haysam da dansa. Munji dadi matuka tare da kasancewa cikin farin ciki mara musaltuwa, dan haka muka ware akai bikin nadinsa kamar babu komai a ranmu. Sai dai kuma mi, a randa Barbushi ya bamu gubar da zamu zubama Haysam sai muka iske Haysam ba'a cikin hayyacinsa ba. Shi kadai a daki yana ta aman jini da kiran sunan Eshaan da Mammah. Ganinmu yasa ya fara kiranmu akan mu taimakesa mu kira masa su, amma sai mukai fitowarmu mamaki fal zukatanmu, duk da ta wani bangaren murna muke zai mutu. Mun garzaya wajen boka Barbushi muka sanar masa komai, nan fa take shima ya shiga mamaki jin bama mukai da basa tamu gubarba. Gubar ya amsa ya ce mana muje mu dawo washe gari zai bincika, dan tabbas bayan mu akwai mai farautar rayuwar Haysam din. Gabanin asubahi muka dawo cikin masarauta, sai muka iske ALLAH yay masa rasuwa ma. Muni farin ciki, sai dai zukatanmu sun karkata da son gano wanene keda irin burinmu, domin mu a ganinmu dole ne shima mu kaudashi dan karya zame mana matsala idan shima burinsa yin mulkinne. Abinda fa zai baku mamaki a duk hadin kan nan namu muma bawai muna kaunar juna bane. Mu dikanmu burinmu shine muga bayan juna idan mun kauda Haysam da dansa. Abinda ya kara rikita lissafinmu mutuwar matan Eshaan guda biyu a washe garin mutuwar Haysam, babufa shiri muka koma wajen Barbushi. 

 

  Boka Barbushi ya tabbatar mana da lallai akwai matsala, sannan bayan mu akwai wasu masu kudirirrika sosai a cikin masarautar zagaye da rayuwar Eshaan. A yanzu hakama bayan wadan nan matan nasa biyu da suka rasu wasu zasu sake. mutuwa da shima bai san adadi ba. Sai dai akwai gabar da abubuwa zasu canja kansu dalilin auro wata yarinya da bata cika ashirin ba. Wannan yarinya akwai al'amari mai girman gaske tare da ita, sannan tana tare da manyan sirrika, a cikinsu ma harda babba daya kasance sirrin wanna masarauta. Idan kuma har ta shigo gidan burinmu bazai taba cika ba na mulkar kasar ruman. Mun tashi hankalinmu amma sai ya dakatar da mu da cewar mu kwantar da hankalinmu, munada hanya daya ta bullewa. Hanyar itace bibiyar duk matan da Eshaan zai aura, zamu gano wanna yarinya ne kawai ta hanyar auren yara biyu da ga gidansu itace cikon ta uku, biyun zasu mutu bayan suma sun shigo masarautar. Sai muyi kokarin shafe ahalin wanna yarinya gaba daya ita kuma muyi amfani da ita ta karasa halaka mana Eshaan shike nan zata kare rayuwarta a kurkuku koma a tsireta Jasim ya hau karagar mulki ni kuma na zama magajinsa batare da wancan sirrin ya bude ba. Komai ya mana, sai dai mu burinmu sanin wanene zai dinga kashe matan nasa? Ya sanar mana shima bai iya gano su wanene ba gaskiya. Amma sunada hadari sosai, kuma a cikin gidan nan suke suma, bai kuma kamata mu damu da abinda zasu aikata ba dan zasu mana aikinmu ne cikin sauki muma, Eshaan bazai samu soyayyar mutane ba a dalilin wanna kashe-kashen, dan kowa zai kallesa a mai kashe matansa.

Shi kuma zai maida hankalinsa ne a neman wanda ke kashe masa mata mu kuma muna aikinmu a kansa cikin sauki, Mun gamsu mun kuma dawo gida cikin farin ciki. Tun daga nan abubuwa suka cigaba da gudana, muma muka dage, bama sanya waien kokarin shiga da fita da gain an aurama Eshaan mace bayan mutuwar wasu. Ga kuma abinda duk boka Barbushi ya fada yanata faruwa daki-daki, tako ina zaginsa ake da la'antar mulkinsa har mutane na kiransa da Fir'auna. Hakan a mana dad, shiyyasa ma muka baza yaranmu tako ina suna gano mana kyawawan matan da za'a aurama masa, da munzo muka kalame Mammah da zance musamman ni sai ta amine da fatan ALLAH yasa karshen al'amarin kenan. A haka har lissafinmu ya kai ga wasu yara da mahaifinsu ke kawo zuma masarautar nan. Wani kuma yaronmu dake mana aikine ya kawo mana zindensu ashe abokinsa ne. Mun tabbatar da auren ta farko kamar yanda aka saba itama ta mutu, kasancewar munga biyu bayanta muka sake shigewa gaba aka auro ta biyu. Itama dai ta rasun, dan haka muka dira akan ta uku. Shekarun yarinyar da wanda Barbushi ya fada ne ya samu farin cikin da fahimtar itace wadda muke nema, dan haka bayan an aurota muka fara shirya yanda zamu tarwatsa ahalinta. A wanna ranarce wanda yay mana hanyar sanin gidan yaji hirarmu (abokin nasa kenan), bamu nuna masa mun sani ba, sai muka bibiyi rayuwarsa ta hanyar matarsa. Kudi muka bata mai uban yawa da firgita mata rayuwa, harma Jasim yay amtan da ita sannan muka bata gubar data bama mijin nata sannan muka wuce. Washe gari bamu san miya faru ba ta kiramu a rikice wai mijinta ya tafi sanarma iyayen yarinyar nan komal amma ta bashi gubar da muka bata. Hankalinmu ya tashi, babu sanya muka samar da yan sanda suka je gareta da ga nan tai musu jagora zuwan gidan. Anan ne muka saka aka kama mai gidan da babban dansa. (Nasan dal baku manta kama babiy da Hanash ba?)".


   Arshaan yaja numfashi ya fesar cikin kunar zuciya, sai kuma ya cigaba da fadin, "Makwafcinsa da wani tsoho da akace mahaifin matarsa ne sun cigaba da fadi tashin gain sun san inda suke, sai dai hakan ya gagaresu, a da burinmu kawai mu kashesu a lokaci daya, sai dai yanda Barrister Abdallah Aas ya shiga zance sai mukai sha'awar cigaba da buga wasan. Dan haka muka cigaba da wasa da hankalinsu, mun shirya kawo karshen rayuwarsu a gabar da muka gama shirya kawo karshen rayuwar Eshaan. Sai dai su bamu maida hankali kansu ba sosai dan a ranar muka damka madara mai duke da gubar dafin macizai ga yarsu, dan haka tunaninmu ya karkata kan yarsu gaba daya da kuma aikin da muka sakata. Da ga baya aka sanar mana suma an kashe mana su.…..✍️


No comments

Powered by Blogger.