Daudar Gora Book 2 page 72

 


 .....Cike Iffah ta samu sashen Malikat Bushirat da danginta da sukazo mata Barka da salla. Hakan ya mata dadi, dan duk wani wanda ke da alaka da Tajwar Eshaan a rayuwa tana ganinsa da kima da mutunci. Cikin mutuntawa suka tarbeta, dan sakonta da na Tajwar Eshaan yaje garesu har gida a jiya. Duk da suma sun kasance mafi yawansu basu nema komai na rayuwa sun rasaba. Amma alheri dadine da shi, musamman da ya kasance wani abu bai taba zuwa garesu ba ace daga dan yar war tasu kuma Shugabansu. Abinda ya basu mamaki da tabbatar da an samu sauyi yar uwar tasu ma sai da suka zo yanzu duk suke mata godiya har tasan Tajwar Eshaan din wai ya musu aike suma. Murmushin yake kawai ta musu, dan tun jiya dama a tunzure take da abinda Iffah'r tayi. Koda Iffah'r ma ta gaisheta cikin yake ta amsa gain yan uwanta duk sun zuba mata ido.Amma zuciyarta tafasa take da yanda suke ta sanya albarka da yaba abinda Iffah'r tayi, tare da tabbatar da shugabansu kuma dansu yayi dace da mace ta gari mai buda masa hanyar alkairi. Sukam suna farin cikin shigowarta cikin ahalinsu. Wasunsu harda kiranta gagara badau wadda tafi karfin duk wani shedanci a azzaluman masarautar.


  Iffah da mur mushi kawal ta dingayi kasa-kasa. Tayi zaman kamar awa guda sannan tai musu sallama akan zuwa anjima zata aiko azo da su su gashe da Shahan-shan. Wannan zance nata na karshe ta sakasu sake shiga jin dadi, dan a cikinsu ma akwai wanda rabonsu da Tajwar Eshaan din tun kan a bar kasar da shi, Kuma uwa daya uba daya suke da Malikat Bushirat din, Sun baje babin hira da sanya albarka ga Iffah Jasrah ha kara basu labarinta. Babbar yayar su Malikat, Bushirat din da suke kira Akia Badiha cikin nuna jin dad) ta furta, "Al ni babban abinda ma ya sakani farin ciki fiye da komai wannan cikin na jikinta, dan zamu samu tsatson alkairi a zuri'armu, ALLAH dai ya raba lafiya".


  Kusan a tare duk suka dubeta. Malikat Bushirat da ke kishingide tana shakar iska da fesarwa harda zabura. Jasrah ce tai karfin halin fadin, "Akia wal waye mai cikin? Kin samu a rudan!" Baki ta Kara washewa, cikin barkwanci ta ce, "Aw to tunda baku ramfo ba ku bada goron albishir tukkanna. Kudi sabbi kal-kal Jasrah ta sauke cikin tafin hannun Akia Badiha, cike da zumudi ta ce, "Muna saurarenki".


 "Uhm wadan nan din ma babu laifi, sai dai da kanku ma zaku karo idan kunji. Insha ALLAHU muna gab da samun Miran, ko Daneen a wannan masarautar. Dan da alama Zawjata-almilk tana tare da shigar ciki".

 

"Whattt!!!!!!".


Suka fada cikin hada baki da hun murna. ALLAH ma ya sosu hadimai yau an basu freedom din kansu sai dai-daiku dakan dan shigo dan an bukaci ganinsu. To su sunama a falon Malikat Bushirat din nacan ciki ne iya su dan yau ranar baje kolin hirar zuminci ce. Wani irin diff-diff kirjin Malikat Bushirat keyi, zuciyarta kamar zata faso ta fito. Ga kanta da yay wani irin azababben sarawa, sai ta fara ganin falon na juya mata da su da ke ciki. Tashi tai da sauri ta nufi daki ta kulle kanta. Tana gama sakama kotar key ta daura goshinta jikin kofar tai wani irin fashewa da kuka mai tahowa irin gaba dayan nan mutum yaji kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa..


  Bama su fahimci halin da take cikiba su balle tashinta, sunata murnarsu, sai da mai bima Malikat Bushirat din ta juyo tana magana idonta ya sauka a wajen zamanta wayam. Bata kawo komai a ranta ba a tunaninta duk murnarce ta kebe yin abunta dan sun san yar war tasu da shegen kasaitar son mulki kamar itace Shahan-shan din ba matarsa ko uwa ba…..







*A bangaren Iffah kam tana sashan Malikat Haseenat, taso ta samu Iftihal dan yau tayo mata tanaji sai dai aka samu rashin sa'a wai ta fita ita da Husam babban dan Miran Jasim. Anan ma Iffah ta jima sai bayan sallar la'asar ta baro, sunata shan hirarsu ita da Mammah da Mammy. Daneen Waheeda dai bata saka baki sai lokaci-lokaci...








Tattauna zancen cikin Iffah ga zuri' ar Malikat Bushirat ya sa ya fito har ya fara yawo a cikin masarautar. Dan danan fa aka fara wani karamin bikin murna da sam Iffah da Tajwar Eshaan da sai da akai sallar la'asar ya samu kansa basu sani ba. Hasalima suna can manne da juna abinsu hankalinsu kwance da jin tamkar suma kadaine a cikin duniyar (Su bily duk an mutu ashe 😏🤔👹). A kankanin lokaci zancen ya cigaba da shiga lungu da sako. Da ga masu shiga farin ciki sai masu shiga rudani da tashin hankali dan abune da basuyi zato ba...










"Aiko lokaci yayi da zaki bijiro da zancen auren nan Waheeda".


    Malikat Ashwag ta fada cikin tashin hankali bayan gama sauraren Daneen Waheeda. Daneen Waheeda da gaba daya ita tasan kunar da zuciyarta ke mata ga rikicin Iftihal taja numfashi mai matukar zafi. "Hakane Ashwaq, amma kin san kafiyar Mammah, ga shi Ammarah sam nunawa ma take tafi son yarinyar nan sama da Iftihal din, taya kike ganin hakan zai yiwu cikin sauki?".


"Yuwuwarsa daya ce, mu nema su Sayeed Tasaddug-Husain da zancen shi da su Sayeed Hifzur-rahaman, da Sayeed Fayzul-haq tunda sune dai iyaye a gidan nan, duk da yake shugaba suma ai sama suke da shi, kuma dama a duk aure-auren nasa ai sune dai Mammah ke sakawa gaba ko da su Jasim".


  "Eh hakane, kema kin kawo shawara mai kyau.Yaushe kike gain zamu samesu?".


  "Ko zuwa anjima dan ba'a bori da sanyin jiki. Bara na kiga mu nema ganawar sirri da su, da ani ishan'i insha ALLAHU sai kawai mu zauna"...





    (To koyaya zata kasance,Iffah'r mu ga Abar nan na tunkaro ki ki hira 😝😢)





Su Malikat Ashwaq sun gana dasu Sayeed Fayzul. haq, sun kuma tattauna sosai da sauraren abinda Daneen Waheeda tazo da shi, shi dai Sayeed Fayzul- haq ma baice komal ba. Garama Sayeed Hifzur- rahaman yace su basu lokaci zasuyi magana da Mammah a kuma jira Sayeed Tasaddug-Husain ya dawo daga Umrah gobe insha ALLAHU. Daga haka suka rabu.


   A lokacin da suke tasu tattaunawar Iffah na can taima yan wan Malikat Bushirat rakkiya ga Shahan- shan da ya sakko hawa na biyu. Ya nuna farin cikin ganinsu shima, dan bai taba zama irin wanna dasu  ba tunda yasan kansa, ballema yanzu da yake a shugaba. Suma duk wanda ka kalla zaka fahimci tsantsar farin ciki a tare da shi. Sun kuma ji dadin yanda ya dan sake dasu yay hira duk da maganar daya biyu ce dai. Sai dai abu mafi kayatar da su yanda ya girmamasu ya mutunta su. Sai kuma komi yake idonsa aka matarsa Iffah. Kusan zaman awa daya da rabi sannan sukai masa sallama...




   Bikin sallah ya cigaba da gudana masu ziyara nata zuwa gaishe da Shahan-shan. Yayinda Malikat Bushirat ke a birkice, gaba daya Jasrah tama kasa gane kanta. Tayi kiranyen uwa har ta gaji amma taki zuwa. Sai taji komai ya karasa kwace mata. A kwana na uku da salla sai da doctor ya dubata. Jasrah dai tai

shiru da bakinta babu wanda ya sani gudun kananun maganganu. A washe garin cikar sallar kwana hudu Maganar komawa zaman kotu taje kunnen kowa, dan haka wasu suka kasance cikin zullumi da tsoron karfa garin tone-tone ga su Miran Jasim suma tasu allurar ta tone galma..







* KOTU*








A yanda zaman shari'ar ma ya cika yau sai ya baka maraki. Dan tarin matasan nan a yanzu da Iffah ta dunkule waje daya bisa jagorancin Sayeed Fayzul- haq kaf dinsu sai da sukazo. Abinda basu taba yi ba tunda ake zaman shari'ar. Hakama wasu a mata da mazan masarautar sun karu. Kotu dai ta cika tai hani'an masha ALLAH.


   Tsabar yau Iffah da jin kai ta shigo da yafi na kullum ma Shahan-shan ya rigata zuwa. Dan kusan itacema karshen shigowa da hadimanta. Nana kowa ya zuba mata ido harda uban gayyar ta cikin glasses din da ya boye idanunsa. A ransa kam kara jinjina fitinar yarinyar nan yake. Tafa rigashi kammala shiryawa amma tsabar taso neman magana sai ta gudu sashenta har sai da ya rigata zuwa kotun. Yau ma sai da taje ta gaida Malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Hakama Malikat Bushirat da tai wani irin ramar fita hayyaci da mai lurane kawai zai fahimta, dan abin dariya yau harda eyeglasses a idonta itama, da alama akwai abinda take boyewa. Hannu kawai ta dagama Iffah a maimakon amsa mata gaisuwa, ko a kwalar jikin Iffah tama mike abinta tana takun nan nata na neman magana.


  Bayan nutsuwa kotu yanda ya kamata aka shigo da su Miran Arshaan. Sunyi duhu sosai sun rame. Ba duka ba zagi babu harara zaman duhun nan kawai da suka saka Iffah ciki a wancan karon da bakin cikin kamar su a cikin kurkuku ya maida su haka. Yan kananan magana ne suka fara tashi a kotun har sai da aka tsawatar. Ameera Haifah dai sai faman rufe fuska take da mayafi, gashi yau kuma harda iyayenta itama a kotun dan habanta yazo akan maganarta tun washe garin rufesu amma bai samu gain Tajwar Eshaan ba.


  Bayan kotu ta sake nutsuwa Sayeed Hanifud-Din ya karanto karar haka. "Har yanzu dai muna kan zaman shari'a ne akan Miran Jasim da ya bada madara mai dafi ga Zawjata-almilk ta shayar da wanda suke son halakawa. A wancan zaman kotu ta bada damar kawo bokansu a zama na gaba, sai kuma aka samu wani al'amarin akan Miran Arshaan da Ameera Haitah, wanda yay dalilin kaisu kurkuku suma, zaman makwaftakar Miran Jasim da Miran Arshaan ta zakulo wasu sabbin abubuwa masu ban mamaki da ya karata ace an fara saurare a wannan shari'a kafin a cigaba  da yinta. Idan adalin shugabanmu ya bada damar hakan to".


 Hannu Shahan-shan ya daga a hankali da yin alamar an baka dama. Godiya Sayeed Hanifud-Din yayi sannan ya kalla shugaban jami' an tsaron. Mikewa shugaban jami 'an tsaro yayi, yayinda Miran Arshaan da Miran Jasim ke kallon juna a rikice, dan sun dai san karn kalar tabargazar da sukaira juna da tone-tonen tsiyatakunsu a cikin kurkukun. A hankali Iffah ta

saki wan irin sassanyan murmushi. Cikin Sa'a kuwa sai a idon su Miran Jasim din kamar an kirawosu su dubeta........✍️


No comments

Powered by Blogger.