Daudar Gora Book 2 page 70

 


70

....Sai da tai sallar la'asar a sashen Malikat Haseenat sannan ta baro, fuskarta dauke da murmushin abinda take kullama Iftihal. Dan ta dau alwashin sai tayi dana sanin zamanta a masarautar nan duk da gidan kakanninta ne. Da ga nan sashen Malikat Bushirat ta nufa, sai dai ta samu wai bata nan tana a

sashen Shahan-shan. Hakan bai bata mamaki ba, ba kuma ta nuna ya dameta ba ta koma sashenta ita da tawagarta. Sai kusan karfe biyar ta nufi sashen Tajwar Eshaan..


A lokacin da Iffah ke nufar sashensa a lokacin shi kuma yake fita ta kofar sirrinsa zuwa sashen Malikat Haseenat. Cikin sa'a kuwa ya sameta ita daya a dakin. Kyawawan idanunta na tsufa ta zuba masa har ya kammala sakama kofar key ya cigaba da takowa gareta a nutse. A hankali ya kai zaune gabanta ya tankwashe kafafunsa.


"Barka da yamma Jaddah".


Ya tada a kan lips a dan fisge kamar baya so.Murmushin ta sakar masa cikin yar tsokana ta amsa da "Barkan ka dai Abbien unborn". Idanunsa ya dan waro mata na alamar mamaki, sai dai kuma bai iya cewa komai ba dan yama rasa bin fadar. Dariya Malikat Haseenat tayi mai kayatarwa, tace, "Ni dai bana fata ko mace ko namiji da za'a haifa su gado min wanna miskilancin naka Hafidi. Ace magana a bakin mutum amma furta ta ta zama aiki", Kasa ya dan yi da kansa kawai yana murmushi. Kafin cikin son kauda maganar ya ce, "Amm Jaddah! Kamar yanda kika bada shawara nayi amfani da ita. Ani musu gwaji ta wasu abubuwan hallitar jikinsu kamar gashi da yawu jini batare ma da sun san duk muni hakan ba. Ita na bada nata, Sayeed Tasadduq-Husain kuma ya samomin na iyayen nata dan kamar yanda na fada miki dama tunda na saka a kaudasu a kasar shine yay aikin kuma shi kadai suka sani ya kuma san inda suke a yanzu haka ma".


  Cike da zumudi Mammah tace, "Ya ake ciki? Mi result din ya nuna kuma?"


    Sai da ya dan ja iska kusan minti daya kafin ya nisa. "Al'amarin gaskiya yazo da rudani zance ne koba haka ba oho. Result din sun nuna shi Mahaifinta ne,amma macen ba itace ta haifeta ba".

 

"What! Kamar yaya kenan?".


   "Shine na kasa fahimta why Jaddah. Tun a Saudiyya a rikice lissafina yake. A daidaiton kwanakin watan haihuwarta da na yarinyar Mamy dake rubuce kwana uku ne, sannan tambarin da ke nan a ajiye iri dayane da na jikinta, ita waccan ta mutu a randa aka haifi ita Fhareedahn. Sai nake ji kamar akwai abinda ya kamata mu sani, amma idan na auna yiwuwarsa ni a karan kaina sai naji abin yazo ba daidai ba".


 "Kai mi kake tunani akan hakan?".


    Nan ma sai da yay jima kafin ya bata amsa. "Itama Mammy a mata gwajin halitta tare da ita. Kinga muma sai mu samu nutsuwar yarda ba ita bace, ko itance. To amma ya akai ta samu tambarin zuri'armu bayan mahaifinta bashi da alaka da wanna masarautar? Sosai nakejin kaina a rikice a duka abinda nake tunani da fatan ya tabbata".


     "Tabbas al'amarin akwai rudanin, rudanin kuma suna da yawa, dan inhar babu alaka tsakanin wannan yarinya da Arnmarah to tabbas tana da alaka da wani a wannan masarautar kuma dole ne mu sani. Sai dai dabi'un yarinyar na rikita mun lissafi Eshaan. Dan babu abinda ya banbanta da na Ammarah tana a irin shekarunta. Sai dai ni nasan diyar Ammarah ta rasu tunda da hannuna na mata wanka da hadata aka kuma kai ta aka bizne".


   "Kamar yanda na fada miki Jaddah akwai abinda ke boye. Dan da gaske yarinyar nan akwai aljanu a kanta wilhy. Naga alamominsu da yawa tattare da ita, dan a wan lokacin ita kanta aljanar ma nake kallonta".


  Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat tayi, amma a ranta fal yake da rudani... Sun cigaba da tattaunawa har zuwa gabanin magriba sannan ya baro sashen domin zuwa yay shirin massalaci…..






A bangaren Iffah kam data nufi sashensa kai tsaye kitchen ta nufa, inda masu kula da abincinsa ke ta kaikawon lissafin abinda zasu shirya masa na buda baki. Tana shigowa duk suka zube kasa suna kwasar gaisuwa. Hannu kawai ta daga musu, kafin tai zaran bibiyar duk abinda suke shirin yin da kallo. Duk lissafinsu sal da ta wargaza ta shimfida nata, karshe ma ita ta koma shirya abincin da taimakonsu. Wannan al'amari ya matukar basu mamaki kam, dan ko'a tarihin masarautar basu taba jin a inda wata Zawjata- almilk ta shiga kitchen girka abinci ba koda na Shahan-shan ne kuwa. Sai gashi a yau Itfah ta ajye tarihin,


   A matukar gajiye suka kammala aikin, tayi tibis da ita saboda a yanayin da take, duk da dama cikin nata nada saukin laulayi da tsurfan abinci. Sannan ita dai bazatace ga wani waje na mata ciwo ba mai jigatarwa. A dining room din ma tana tsaye suka shirya komai, aka kara turaren wuta ko ina ya dauka harami. Bayan duk wucewarsu bedroom nashi ta nufa, ta dinga binsu daya bayan daya tana lekawa har sai da ta shiga a inda ya kwana. Kamar ko yanda tai hasashe ba'a gyarashi ba, tunda ita da kanta ta hutar da amintaccensa tun kan su wuce. Duk da yanda take jin kanta haka tai dauriyar gyarawa, sannan ta shiga toilet din tayo wanka shima bayan ta tsaftacesa Bata da matsalar kaya anan kam tunda tasan tabarsu tunkan su tafi ba, tako shirya cikin wandon jeans 3quater blue da karama roga mara nauyi fara tas, sai hoton heart da akayi babba a gaban rigar. Kayan sun mata kyau. Tana barbaza gashinta da haushi na rashin son a taba mata shi ya shigo dakin da sallama. Dan turus yayi yana kallonta irin na rashin tsammani. Dan a yanzu haka da yake shigowarnan da ita a ransa ya shigo, kewarta yake ji sosai, dan duk yau bai ganta ba, rabonsa da ita tun daren jiya da ya kai mata ziyarar sirri sashenta.


    A hankali ya cigaba da takawa cikin dakin yaje gabanta ya tsaya. Jitai kawai an tura mata yatsu cikin gashi. A firgice ta dago dan ko kadan bayaji motsin shigowar tasa ba. Cikin juna idanunsu suka shige, kowanne cike da kewar dan uwansa kamar sun hada watanni basu hadu ba. Itace ta fara janye nata a slowlv. kamar mai in kunvarsa ta maida kanta kasa ta dukar. Numfashi ya dan furzar kadan, tare da dukowa

ya zare ribbon din hanunta ya saka cikin tsintsiyar nasa hannun kamar maisa bangles, sai kuma ya maida duk hannayen biyu saman kanta ya tattaro gashin a tsakkiya ya dare mata.


"Thanks you".


 Ta fada cikin siririyar muryarta da ke ratsa masa jiki, yasan tsaiwarsa a wajen bazata hafar masa da da mai ido ba. Dan haka ya rabata ya wuce cikin tafiyar tasan nan daddaya dan azuminsa ya isa lafiya. Da kallo ta bisa har ya shige bayi, sai kuma ta saki sassanyar ajiyar zuciya ta mike. Closet dinsa ta nufa kasancewar akwai finger print dinta yanzu akai itama. Lallausar jallabiya kalar maroon ta zaba masa, tare da alkyabba irin ta sarakan saudiyya. Fitowarta dal-dai  da tashi. Kallo daya ta masa ta dauke kai dan har yanzu ta kasa sakewa da kalion wanna jikin nasa. Kanta a kasa ta karaso gabansa, karamin towel da ke hannunsa ta amsa, babu musu ya sakar mata, sai da ta lumshe idanunta sannan ta fara tsane masa jikin. Dan garetan murmushi ya saki idanunsa kan kyakykyawar fuskarta harta kammala. Man da yake amfani da shi ta ajiye zata gudu ya rikota a slowly yaNmaidota baya. Sai da ya gama kare mata kallo da gaNsama har kasa sannan ya dire kan fuskarta da idanun ke lumshe. A can kasan makoshi ya furta, "Shi man wazai shafa?". Batare data bude idon ba ta ce, "Ka tayani".


"Naki wayon".


 Ya bata amsa yana maidota gabansa da kyau. Dan murmushi tai zatai magana ya ce mata, "Shilli!!!" Shiru tai ta hadiye abunta. Shi kuma ya daura mata man a kan hannu. "Oya zan makara sallar magrib". Babu yanda ta iya dole ta shafa masa. Kirjinta sai bugawa yake da sauri-sauri dan da gaske jikin nan nasa toro yake bata. Ta rasa mike birge maza suke maida kansu haka ita kam. Rashin mafita ya sa dole har shiryawa sai da ta taimaka masa wajen yi. Tana kammala saka masa turare ya kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa ya sumbaci goshinta da idanunta da karan hancinta, sai kan habarta. Sassanyar ajiyar zuciya ta dan saki. Bata ankara ba kawai ta gansa duke gabanta ya dan daga rigarta ya sumbaci cikinta. Da ga haka ya wuce abinsa cikin dakewa kamar bai aikata komai ba. Da kyar ta iya bude ido ta bisa da kallo, dai-dai zai fice ya dan tsaya a jikin kofar tare da juyowa suka hada ido. Kauda nata tai da sauri, shi kuma ya dan sakin murmushi a iya lips da fadin, "Idan kika bar sashen nan kafin na dawo sai na hukuntaki". Da ga haka ya fice ya barta da murmushi a fuska..


Bai shigo gida ba sai da aka idar da har sallar isha'in da asham, dan bayan idar da sallar magrib ya sha ruwa da dabino a can. Da ga haka yay zaman karatun Alkur'ani. Kowa yasan hakan yake yi a duk shekara, dan baya shigewa sai bayan an kammala salla baki daya kamar yanda yake yi idan ba'a azumi sai ani har sallar isha'i. Bisa rakkiyar su Sayeed Fayzul-haq ya dawo sashensa. Hadiminsa kam tun da yaji a bakin masu girki Zawjata-almilk tazo itamace taima Shahan-shan girki da kanta baiyi gigin biyosa har nan ba sai ya lake a 3 floor din. Babu kowa a faion sai sanyin ac da kamshi mai dad ba irin wanda ya bari ba. Bedroom ya nufa domin rage kaya, zuciyarsa na raya masa tama gudu kenan bataji gargadinsa ba. Sai dai yana murda handle din kofa itama tana budewa, kusan cin karo sukal da juna ALLAH dai ya kiyaye taja baya da sauri, sai kuma ta kusan faduwa sai da ya rikota jikinsa. A jiyar zuciya ta sauke cike da shagwaba ta ce, "Thanks you"


 Maimakon amsa. mata godiyar cak ya dagata bisa kasa suka koma dakin. Tana watsal-watsal da kafafu da rokon ya sauketa ita yunwa takejl bai ma saurareta ba sai da ya direta inda yake bukata ya rufe bakin tsiwar dan iya yaren da zuciyarsa da kwakwalwar ke bukata kenan kawai…….✍️


No comments

Powered by Blogger.