Daudar Gora Book 2 page 59

 


Chapter: 59


."Labarin ya fara ne tun zamanin iyaye da kakanni da ya kasance akwai karancin ilimin addini. Ba a daular ruman kawai ba hatta da sauran dauloli da ma talakawan kasar RUMAN kowa yasan ani matukar imani da tsafe-tsafe a karnikan da suka shude. Zaki

samu duk talaucin mutum duk yawan arzikinsa yanada wani boka da ke fada masa motsinsa ko wani abu dake tunkarosa, ko bashi Sa'a a abinda zai yi ko yake yi. A lokacin da addinin musulunci ya fara kutsowa cikin wanna kasa tamu idan akaji ka amsa sai an halaka ka, dan kuma kai shugaba ne to fa za'a tubeka a koreka kai da duk ahalinka. ALLAH sarki, masu shiga musulunci da masu hidimar gain an shiga sunsha matukar wahala a wancan karnin. Komai ya canja da cajawar labarin wanna kasa dalilin wani fari da akai na tashin hankali, ruwan dake zagaye da wannan tsuburi da kasar RUMAN take ya zagaye komai hadda gidaje da dukiyiyi har ma da rayuka. Ba kasar ruman ce kawai ta girgiza ba, Africa da ma duniya baki daya wannan al'amari ya matukar girgizasu, inda aka shiga kawo mana dauki ta kowane bangare. Wannan shine mafarin fara samun canji, domin a cikin wanna yanayin ne tarin bayin ALLAH mabiya addinai daban-daban suka fara yakin ganin sunja ra'ayoyin mutane da dukiyoyi da wasu abubuwan kyale-kyale na duniya, harda masu yimusu tayin binsu kasashensu suyi rayuwa.

Babu mai son yabar kasarsa tushensa dan haka mutane suka fara bijirewa, sai ko wani bawan

ALLAH ya basu goyon baya mai suna SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO da ga kasar NIGERIA.

shine ya tabbatar musu kasarsu itace yancinsu, itace gatansu, itace martabarsu, su tashi da

karfin kwanji su gyarata yayi alkawarin tallafa musu da karfin jiki da ga tawagarsa. Zantukansa

sun kayatar da kowa sun saka karsashi a jikin mutane, musamman yarima mai jiran gado Miran Aliy Qutb. Ganinfa Miran Aliy Qutb ya amshi wannan tunatarwa tun ya samu mabiya.

Abu mafi daukar hankalin mutane SHEHU UTHMAN DAN-FODIYO ya kasance MUSULMI

ne, hakama almajuransa da sukayi masa rakkiya, amma sai bai taba cema wani dole sai

ya shiga addininsa ba ko masa tayi da wata dukiyar da zai shigan, ya dage dai tukuri da

taimakonsu yana ibadarsa. Hakan sai ya shiga birge mutane tuni suka fara karbar musulinci.

Sai kuma cikin kankanin lokaci kasashen musulunci manya irinsu Saudi Arabia suma suka

fara yunkurowa, mabiya addinin islam suka hada karfi da karfe wajen hidimtawa wanna kasa ta

RUMAN ta sake ginuwa ta komawa kan kafafunta. A cikin abinda bai wuce shekaru

kalilan ba abubuwa suka cigaba da canjawa acewar munada tarin tattalin arziki ka davan-daban. An dauki babban mataki akar

ruwan dake zagaye da mu, aka kuma kara fadada kasar ilimin addini ya yawaita, kafirci ya

fara nisa a cikin al'ummar mu. Masu bautar gumaka da yin imani da bokaye duk suka fara

janye jiki, wasu bokayen ma da kansu suka dinga ajiye kayan tsafe-tsafen suma suka koma

ga ALLAH. Masu taurin kan cikinsu kuwa sai suka bijire da jan tunga, wasun su suka koma

dazuka wasu kuma suka koma yi a boye."


    Ta dan ja ajiyar zuciya da daukar ruwa takai bakinta. Kafin ta cigaba da fadin, "Uwa diyar

wata bokanya ce babba a wannan masarautar,bayan mahaifiyarta da ake kira bokanya Ta-bunu ta mutu itace ta gajeta. Shekaru masu yawan gaske da suka shude itake tafiya da jan

zaren yi da hani na wannan gida harta mutu yarta ta gajetan (wato Uwa). Ta kuma gajeta ne

ana gab da samun wannan iftila'i da ya faru,lokacin da abun ya faru tana farkon fara jin

dadin kar fin ikonta dan tafi mahaifiyarta hatsabibanci. Domin kuwa komi za'ayi sai an

sanar mata tace ayisa, idan ko ta hana akan dakata koda ana sonshi. Hatsabibiya ce matuka.

Dan duk da mahaifin Miran Aliy ya yarda yan kasarsa suyi addinin da suke so shi ya kasa

rabuwa da Uwa har ALLAH ya masa rasuwa Miran Aliy Qutb ya zama Shahan-shan. Shi dai

men hirans da farbn amma hahmands yaso bijirewa da farko, amma babu wanda yasan miya faru hakan ta gagara ya cigaba

mata biyayya akan abinda ta shardanta kota hana. Na takaice miki zance fa ikon Uwa sai da

ya kasance itake kamar mulkar kasar ruman dan har shi Shahan-shan din sai da cewarta yake

cewa ga talakawansa. Haka yay mulkinsa ya shude Miran Abdul-majeed dansa, mijina ya

karbi kasar ruman. Muma mun cigaba da kasancewa a karkashin say na UWA, sai dai abun na matukar damuna kasancewar nayi ilimin addini mai zurfi. A lokuta da dama idan tace ai abu nakan kalubalanta har sai na

fahimtar da Tajwar Abdul-majeed illarsa. Duk bayan wata uku takan saka ayi yanka na bakaken shanu da karnuka da rakuma wai tsarine na wannan daula. Takan tilasta daya daga cikin yayan Shahan-shan a aura mata wani talakan kasa ko bawa ta samu ciki ta hainu,da zaran ta samu cikin dole kuma ya saketa. Shi

kuma abinda aka haifa zai cigaba da rayuwa a cikin masarautar bashi da wani karfin iko da shi.

Sai dai kin san wani abun mamaki da ya fara jan ra'ayina harna bijirema wanna al'amarin?".


      Jiki a sanyaye Iffah ta girgiza mata kai. Nisawa Malikat Haseenat tayi da cigaba da fadin, "Duk wadan nan yaran da aka haifa ta wannan hanyar basa zarce shekaru bakwai a duniya suke rasa ransu. Na fahimci hakane ta hanyar bibiyar

tarinhin wanna masarautar kasancewa mutum mai son

 sanin tarihi. Lokacin dana fara

kalubalantar yankan da akeyi duk bayan wata uku na bakaken shanu da karnuka ne tasa

Abdull-Majeed ya auro mahaifiyar su Jasim. Ban

damuba dan wannan bashine gabana ba, ban kuma canja daga bijirewata ba da cigaba da

nusar da su akan sanin ma'anar yankan nan.Alhamdullah naci nasara, naci nasarar dawowar

hankalin wasu jikinsu akan hakan aka fara ja"injar a daina a canja da wani abu na sadaka bakwai sai yankan ba. Yayinda wasu kuma ke fadin ai yankan ma sadaka ne tunda raba naman

ake wa talakawa da hadimai. A cikin tsaka da wannan dambarwa na haifi Haysam. Mahaifin

mijinki kenan. Haysam yaci wahala sosai da cututtukan da aka gagara gane kansu, sai dai

ALLAH ya kaddara kwanakinsa basu kare yana yaro ba. Bayansa na haifi Ammarah, Ammarah

ta zo da wasu abubuwan ban mamaki a rayuwarta tun tanada karancin shekaru. Sai

Waheeda, auta Nayyar, zuwa lokacin matan Abdul-majeed mu hudu ne, kowacce kuma ta

haihu da shi, akwai maza kuma akwai mata. Bari na sake dawo miki akan yanka, bijirewata da

mabiya dana samu yasa aka daina a zahirance,ashe a boye ana cigaba da yi batare da sanin

Tajwar Abdul-majeed da ni ba. Sai da wata ranar juma'a da yamma fadan yara ya hada Jasim da Haysam shi da yan uwansa suka masa taron dangi Ammarah ta shiga dukan,mata kai da akai ta yanke jiki ta fadi ,abinka da yaro sai duk suka hadu kanta suna ihu ganin jini ta hancinta. An kinkimota an kawomin tana zubda wanna jini, cikin ikon ALLAH sai ban rude ba na fahimci habo ne. An bata taimakon gaggawa jini ya tsaya har tai barci, sai dai lokacin da take farkawa bayan sallar magriba sai ta tashi a firgice. Koda na tambayeta bayan na mata addu'a ta samu nutsuwa sai ta sanar min mafarki tayi ana yanka shanaye da yawa bakake da karnuka da rakuma. Ga mahaifinsu cikin bacin rai an dauresa da rufe masa baki. Da farko ban dauki wanna mafarki nata a komai ba, sai kawai nace tai addu'a mafarkine kawai. A'a bayan kwana biyu da hakan tai wata faduwa nan ma sai habo, akai mata magani dai ta kwanta sanda zata farka a firgice, nan mana tambaya ta maimaita min wancan dai mafarki da tayi. Abin ya dan fara damuna sai dai ban maida hankali ba. Da ga ranar kuma bata karayi ba har ta cika shekaru kusan goma sha biyar a duniya.Da ga lokacin kwanaki dai-dai ne bazaki samu Ammarah ta tashi a firgice a barci ba, idan ka tambayeta tace ba komai. Ban taba matsa mata ba duk da abun na dan damuna, sai dai ina binta da addu'oi akoda yaushe ita da sauran yan uwanta. Abu ya cigaba da faruwa daban-daban daga Ammarah naban mamaki, bamu fara sarguwa da ita ba sai a randa aka samu gawar Nayyar a cikin ruwa. Abubuwan data dingayi sai da ya tada hankalin duk wani mai numfashi a cikin masarautar nan, inda ta dinga ihu da jadada sai ta dauka fansar jinin dan uwanta. Anyi-anyi kuma ta fada miya faru take irin wannan magana taki cewa komai, harma abin ya ban haushi na tattarata na kyale, a kuma lokacinne ita kuma ta tattara ta tafi makarantar koyan aikin likitanci a kasar America, Sai lokaci-lokaci take zuwa mana hutu ta koma. Ta maida hankali sosai saboda tana so, gashi kuma makarantar da aka sakata makarantace ta musamman. A shekarar da take kammalawa a shekarar yayansu Haysam yay aure, hakama kanwarta Waheeda, anyi-anyi ta fidda miji itama tace a barta ba yanzu ba, ita akwai wanda take jira. Sam bamu takurata ba, dan tanada karamin jiki sosai, shekarun nata ma dai ba wasu bane masu yawa, in bama mun fada ba zaka dauka Waheeda ce babba gareta. Anyi bikin Haysam da Waheeda Ammarah ta cigaba da aikinta a cikin clinic din masarautar nan da kuma karatunsa a cikin wannan kasa ta ruman, a sati kuma takan zagaya jahohi biyu sau biyu domin bada gudunmawarta ita da wat kungiya da suka hada. Tsahon shekaru hudu babu haihuwa da ga matar Haysam, tadai samu ciki sau daya ya lalace bama ya haura wattani uku ba, harma Waheeda itama acan bata haihu ba. Nata bai damu kowa ba, amma na Haysam an fara kanan magana akan sai ya kara aure kasancewar shine Miran mai jiran gado. Bai son kara aure, amma mahaifinsa ya takura masa, ya nema damar a basa lokaci zai nemo da kansa. Anan kam sai ya bashi dama. Ba'a rufa watanni uku ba kuwa ya kawo sunan Bushirat, ta kasance kanwa ga wani abokinsa da sukai karatu, amma suma yan nan kasar ruman din ne, sannan kuma manyan mutanene dan mahaifinta babban malami ne masani sosai. Kyakykyawar nasabarta yasa bamu wani tsananta bincike ba akai biki. Sai dai me itama shiru, dan garama Ashwaq ta taba bari sau daya. Shekarar Bushirat biyu a masarautar nan itama babu labari sai ma Ashwag din ce dai ta kara bari, dan haka aka sashi ya kara auro Danish-Ara, cikin ikon ALLAH Danish-Ara bata rufa wata guda ba sai ga ciki da ga Bushirat. Kowa yayi farin ciki sosai musamman ma shi da ita da mu kammu, hakama Ammarah kai kacema ita keda cikin, dan gaba daya ta tattara ta koma sashen dan uwanta tana kula da Bushirat. Bamu hanata ba, duk da rashin aurenta na damunmu, sai dai mun fahimci akwai matsalar junnu tattare da ita, dan haka muka dage da addu'a gareta kawai"………..✍️


No comments

Powered by Blogger.