Daudar Gora Book 2 page 51
DAUDAR GORA…
Chapter: 51
Sake kankameta Iffah tai, cikin diddishe dan ta fita tsayi ta kai bakinta saitin kunenta tana
wani kuka kuka. "Hhhhh da dina dake akwai daukar haske Mather in-law. Why ki sallamemu
mu tafi naje mijina ya rungumeni dan ban gama dawowa hayyacina da ga faffarkanin da yay ba".
A zahiri kam raba jikinta tai dana Malikat din tana share hawaye da jera godiya. Sai kuma ta
kashe mata ido dan ta fahimci yanzu ma fa ta sake kamewa ne ta juya ta kalli Tajwar Eshaan
da ke kallonsu da alamar nuna jin dadin canjawar komai akan fuskarsa. "Ka tayani godiya *_My Asad_* (Zakina), Ammie ta
fahimceni, na sanar mata komai kamar yanda na fada maka".
A hankali ya wani lumshe idanu da takowa gabansu. Gaban Malikat Bushirat ya tsaya tare
da kamo hannayenta cikin nasa. Firgigit ta dawo hankalinta kamar wadda aka kodama mari a
cikin barci. Cikin kamewar nan tasa dake boye dukkan sirrikan fuskarsa yake dubanta a nutse.
"Ammie nagode sosai, Nagode da kika fahimci abinda naketa son ki fahimta tun tuni.Fhareedah yarinyar kirki ce mai cike da tarin alkairai daban-daban, kuma nasan zaki sake
tabbatar da hakan anan gaba. Na miki alkawarin aiki tare da ita har sai duk wani markiyinmu ya bayyana batare da shi kansa ye sani ba. Ki cigaba da mun addu'a ke dai,gaskiyar danki na gab da fitowa zahiri ga kowa.Dan yanzu haka dukkan wasu bincike akan cases din nan suna'a hannuna, hatta wanda yay tushen bada madaran, da wanda ya sakata a ruwa duk sunzo hanun hukuma. Kallonsa tai da wani irin sauri, sai kuma ta hadiye tana mai kankame hanunnsa a cikin nata. Idanunta ta lumshe hawaye sukai wani irin zubowa. "Ashe zanga wannan ranar, wanna ranar zatazo gareni haka Saiful-malik?". Ta fada cikin subutar baki.
Ko kadan Tajwar Eshaan bai fahimci kalaman nata ba, ya fassarasu ne akan nuna farin cikinta na zataga wannan raar da za'ai walkiya halin wanda batai zato ba ya fito. Sai kawai ya saki murmushi da kai hannu yana share mata hawaye. "Zaki gani Ammie. Ai dama komai yay farko zakiga karshensa na zuwa. Ki cigaba da mun addu'a ke dai indai nasarorin ne yanzu kika
fara gani. Sai kin zama mafi kololiwar uwa da zatai alfahari da haihuwar da daya tilo tamkar da
dubu insha ALLAHU"
"Na yarda da hakan Bin Haysam Abdul-majeed, tabbas na yarda, ALLAH ya makaalbarka kuje dare nayi ku huta ma karasa dasafe".
15:44
Godiya a sake mata da dan lallashi, hakama harda durkusawarta. Kafin ta wani kananna de ma Malikat Bushirat ido a kaikaice ta sakar mata gwalo. Tajwar Eshaan na juyiwa ta fuske kalar tausayi. Hannunta ya kama a hankali yana mai kallon fuskarta ya sakar mata murmushin nan nasa mai narke zuciyarta. Murtani ta maida masa da dan saka hannu ta kare fuskarta ita a dole taji kunya ne. Duk Malikat Bushirat na kallonsu. Suna ficewa ta zube kasa yarafff wani irin mahaukacin jiri na dibar idanunta. Sai kawai ta fashe da kuka tana kiran sunan Uwa.
Tantabaru biyu iyayen soyayya da alkawarin kam suna fita ya duke kasa ya bata bayansa alamar ta hau. Idanu ta waro masa waje alamar mamaki. Ya dan juyo yana kada mata kai da lumshe idanu. Babu yanda ta iya ta tattare rigarta kadan ta hau tare da makalkale masa wuya dan sam bata iya gardama ba. Takun nan nasa yake a hankali cikin izza da kasaita har zuwa sashensa tana a bayansa kwance luff mamakinsa na neman kasheta, duk wanda yasanshi a Shahan-shan din sa bazai taba mafarkin abinda yake mata yanzu zai iya ba.Koda suka shiga elevator ma bai sauketa ba sai boye fuskarta da tai a wuyansa. Aiko gaba daya numfashin da take busa masa ya nema birkita masa lissafi.Maimakon ajiyeta a daki da ya shiga sai kawai ya wuce da ita bathroom ya direta ta bude idanunta. Da sauri ta kallesa a dan rude gain inda ya kawosu. Sai kawai yay wani luuu da idanunsa cike da basarwa ya danne makunnan shower ya sakar musu ruwa a kansu mai dumi. Babu shiri ta zabura ya rikota a hankali, jikinsa ya matsota ya rungume ruwan na cigaba da sauka a kansu.
Kusan mintuna uku suna a hakan kafin ya bude idanunsa ya sauke a kanta yana mai kai hannunsa saman veil din ta ya shiga warwarewa a hankali. Tanaji tana gani ya raba jikinta da kayan da suka gama jikewa sharkaf shi ma ya cire nashi. Jikinsa ta fada kawai nata na rawa ga wata matsananciyar kunyarsa na ratsata. Sosai hakan da tai yay masa dadi, dan ya samu damar sake gain tawadan ALLAH din nan ta bayanta yanda ya kamata, yanda har sai da ya haddace ta. Ita kam har aka kammala wankan bata yarda ta bude idanunta da ta rufeba..
"Nagode"
Ya fada a hankali lokacin da yake goge mata laimar ruwan fuskarta da towel zuwa wuya da bayan keyarta. Dan dago idanunta tai ta dubesa, itama a hankalin ta ce, "Akan mi?".
“Ammie"
Ya bata amsa a takaice. Baki ta dan tura masa tana narke fuska, a dan shagwabe ta ce,
"Saboda Ammien ka ce kai daya?".
Murmushi ya dan yi da lakace mata hanci. "K ta musamman ce".
Baya ta juya masa tana murmushi, hannunta ya kamo ya sake juyo da ita. Ya dago fuskarta da kyau ta hanyar dago da habarta. "Baki yarda ke ta musamman ba ce?"
Tana dan danne murmushin ta ta ce, "Ka dan dai", Yanda ta fada da yin kamar zata dan kashe ido daya sai kuma ta jujyasu wani luuuu hakan nan zuwa gefe ya sashi jin jikinsa duk ya saki,amma sai ya kanne yayi dan murmushi kawai da sake rankwafawa suka zama dai-dai tsaho. "Zan tabbatar miki k ta musamman ce Mrs Eshaan.Dan bazaki sake rayuwa babu Eshaan a gefenki ba har abada insha ALLAHU"
Cikin dan waro idanunta kadan ta ce, "Har a kurkuku idan na koma".
"'Koda a tandun mai ne Babie. Hukunci na gama yankuwa zamu tafi can abunmu muyi zamanmu har sai kin haihu".
Takwaf-takwaf tayi da fuska kamar zata sakar masa kuka. "Wai da gaske kake sai ka maidani kurkukun?".
*kyar ya iya danne dariyarsa, a zahiri ya dan Kara tsuke fuska da daga mata gira. "Way,miki ko Mrs Eshaan zata tsira da ga hukuncin Shahan-shan ne. Ai sai munje kurkuku dole, irin wanna laifi haka da muka rakitowa kammu".
Baki ta bude a hankali zata sake magana ya manne lips dinsu waje guda, dole ta hadiye. Duk da a tsorace take da shi batai yunkurin hanashi ba, sai dai kuma bata bashi kowane irin gudunmawa ba har yay kidansa yay rawarsa ya barta. Da ga haka bakin ya mutu suka hau shirin barci, dama da biyu yay hakan dan ya gaji da maganar. Ya fara kula yarinyar nan so take tamaidashi parrot na karfi da yaji su Jaddah su sami abin masa gori. Wasu shegun kayan barci da bata san ina ya samo su ba ya dakko zai sakamata. Tako zaro ido zatai magana dan bakin faya fara dawowa (lols 😂)). Yatsansa ya daura saman bakinta ya ce, "Shill!!!". Dole ta hadiye abin cewar tanaji tana gani ya saka mata su. Ina kasa Iffah ta shige ta buya kota huta da kunyar da bawan ALLAHn nan ke dawainiyar jefata ciki itakam. Shiko gogan naku ko'a jikinsa. Sai ma nasa shirin da yay cikin pyjamas dinsa shima marasa nauyi ya jata suka fito. Zaunar da ita yaya daya daga kujerun dakin shima ya zauna kusa da ita. Idanunsa da basu ko kyaftawa a kanta ya motsa a kasalance. "Zaki sha madara?". Bawani tana jin yunwa bane, dan haka ta daga masa kai batare da ta yarda ta kallesa ba ita. Dan harga AllaH tsoron ma kallon jikin nan nasa take a tsaye, ga shi ya sa kaya marasa nauyi da gaba daya suka bayyana ainahinsa. Shi da kansa ya zuba madarar ya bata, ta amsa tana fadin, "Nagode". Shi dai nasa kawai kallonta. Yanda take shan tata a takure harya kammala ita bata gama ba, dan haka suka dan jima wajen a zaune har ta fara hammar barci.
Koda suka kammala brush suka sake yowa ya ce mata ta kwanta dan ya fahimci barci takeji sosai. A darare ta kwanta har fuskarta na bayyana tsoronsa. Yi yay kamar bai lura da ita ba, yama koma cikin sofar da ya tashi ya zauna.Itako luff tai zuciyarta cike da toro da kuma mamakin abubuwan da tai yau a sashen Malikat Bushirat. Ta jima da sanin akwai wasu lokuta da take ganin abu baro-baro a zahiri bayan ta gansa a mafarkinta, amma fa yau ita kam kawai jitai tana zano zantuka ga Malikat Bushirat din wanda itafa kamar ana nuna mata su ne cikin idanunta a lokacin, sannan tana jin wani karfin iko da izzar fadar tasu babu o dar tattare da ita. Ta dafe kanta da ke dan mata ciwo kasa-kasa, ga wani barci da ke rinjayar idanunta mai nauyi. Dole ta tattara tunanin da tsoron ta hakura tai addu'a sai ko barci.
Shima da ke zaman kallonta duk dahankalinsa nakan waya ne a zahiri sai ya shirya tattarawa ya bar dakin, dan ya tabbata idan fingilar rigar barcinta ya dagata sama kadan cikin sa'a ya iya ganin abinda yake son ga Hoton wajen ya dauka da waya ya maida mara rigar a yanda take ya mike yana sauke ajiyar zuciya. Dan ya tabbata ido biyu bazata yarda yay hakan ba cikin sauki, maybe ma tafassarashi da wani abu daban...
Maimakon shiga wani dakin barcin ya kwanta karamin falonsa na hutawa dake rukunin dakun barcin ya shiga, agogo ya kalla, ganin sha biyu ta dan gota kadan ya dauke kai. Wayar dake gefensa ta landline ya dan daddana, batare daya dauka yakai kunne ba harta shiga ta yanke.Cikin abinda baifi mintuna biyar ba sai ga amintaccensa da butar shayi. A saman lips ya amsa sallamarsa batare daya dago ko motsa daga abinda yake ba. Koda ya gaisheshi ma bai ko amsa ba, ya dai daga masa hannu kawai, shiko bai damuba ya ajiye komai yanda ya dace ya zuba masa a karamin cup yasa yar zuma kadan dan yasan baima cika shan wannan shayin da komai a ciki ba. Bayan ya kammala cikin girmamawa kansa a risine ya ce, "Ko akwai abinda shugabana ke bukata?". Yaja kusan minti daya da rabi sannan ya daga masa hannu. Duk wani yaren jiki da Tajwar Eshaan zai yi magana da shi hadimin nan ya haddacesa, dan haka cikin risinar da kai ya furta, "A huta lafiya, ALLAH ya kareka da kariyarsa". Daga haka ya fice...
Leave a Comment