Daudar Gora Book 2 page 49

 


DAUDAR GORA....!!

Chapter: 49

Kyakykyawan bowl din data dauro saman

tray mai kyau shima da tambulan din madara

yabi da kallo. Ta ajiye a saman dan table din

data janyo kusa da gadon kasancewar a baki-

baki ya ke zaune shi ta daura. Bowl din ta bude

tana dan kallonsa kasa-kasa kamar yanda yake

binta da shegen kallon nan nasa. A saman lips

ta furta "Kana son shi?". Gasashen naman da ke

ta tashin kamshi mai tada kwadayi ya dan kalla.

Batare da yace komai ba ya kamo hanunta da ke

rike da murfin ya zaresa ya ajiye. Rikota yay ya

zaunar a kusa da shi. "Sai dai in zaki bani da

kanki. Hannuna ciwo suke min". Yanda yay

maganar acan kasan makoshi matuka ya sata

kallonsa da sauri, ido daya ya kashe mata da

sakar mata wani lalataccen murmushi daya

nema raba jikinta na numfashinta. Da sauri ta

maida kan ta risinar zuciyarta na wani masifar

harbawa da sauri-sauri.

Hannunta ya riko cikin nasa ya dan murza

yana kara narkar da idanunsa kan fuskarta

Cikin sake tausasa harshe da cigaba da murza

hannun ya ce, "A duk lokacin da kike tare da15:37

hannun ya ce, "A duk lokacin da kike tare da

<

an ki kallesa abokin ki, amininki, yaya

A

kal harma kaninki idan ya kama, sannan farin

cikin ki. Ina son gidana da iyalina su kasance

aljannar duniyata da duk inda naje na dawo da

damuwa za'a goge min shi da farin ciki, duk

sanda kaina ya dauka zafi za'a sanyaya min shi

da nishadi. Duk sanda na shigo da farin ciki za'a

tayani yi har ma a ninka min shi da wani da yafi

wanda nake tare da shi. Anan Eshaan sunansa

Eshaan Ion Haysam Abdul-majeed MIJIN

Fhareedah (Iffah) bint Zayyan ba Tajwar Eshaan

ko Shahan-shan ba. Ki raineni kamar jariri a

fadarki, Ni kuma mai sallamawa ne gareki duk

rintsi TAURARUWA TA".

Wata irin nutsuwa ce ke ratsa mata zuciya,

tabbas tana jin dadin kasancewa da shi, amma

har yanzu bata san mi takeji game da shi ba. Ita

dai kawai yana burgeta, a cikin ado ko sabanin

hakan. Sannan duk da taji ciwo da a jikinta da

jigatuwa a jiya batajin haushinsa ko jin bai

kyauta ba, dan koba komai tayi ilimin addini,

tasan hakkokin mace aka mijinta, tasan

hakkokin miji akan matarsa, tasan muhimmancin

aure da fa'idarsa. Ta kuma san Shahan-shan

bazai taba sakinta ba koda ace zata bukaci

haka. Mammy ta sake tisa mata fiye da abinda

ta sani, har ma da wanda zatayi domin tabbatar

da kanta a matsayin diya MACE a gabansa ko gaban wanin sa

"Wayyo!".

A

ada yana matse ciki, da sauri ta kalles

yamutse fuska kamar gaske shi adole yunwa

yake ji.

Cike da nuna damuwa ta ce, "Sorry". Sai

kuma ta dakko tray din saman cinyarta. Cokali ta

dauka zata diba naman ya rike hannun. Kallonsa

ta sakeyi da mamaki. Cikin dan dage gira ya ce,

"Nikam da hannu nake so". Komai batace ba ta

ajiye cokalin kawai, tare da ajiye trayn ta mike,

bai ta nufa bata wani jima ba ta dawo da alama

hannu ta wanko. Tray din ta sake maidawa

saman kafarta bayan ta koma inda ta tashi ta

zauna ta debo naman ta kai bakinsa. Hannun ya

riko da kyau ya karasa da naman bakinsa yana

lumshe idanunsa, harda sakin siririyar ajiyar

zuciya. Ita sai ma abin ya bata dariya harda

murmusawa.

Wani irin sanyi da nutsuwa yaji har cikin ranta

ganin tayi murmushin. Dan gaba daya yau bakin

ya mutu kamar ba ita ba, shi kuma yafi son yaga

ta saki jiki da shi tana kiriniyarta da surutu

kamar da. Sosai yaci naman har hakan ya bata

mamaki, hakama madaran. A hankali ta rumtse

idanunta sanda yake tsotse yatsun hannun abin

kamar da gayya. Da gayyar kuwa yake yi, dan

yana kallon yanda take faman matse ido yana murmushi a zuciyarsa

 Bai bar dakin ba sai da ana kiran sallar magariba

<

. Yace ta shirya kafin ya dawo zata

rakasa wani waje. Da to ta amsa masa kanta a

kasa, dan duk wannan abun da ake bata yarda

su hada ido sai da kuskure. Bayan fitowarsa

alwala a bathroom har ya wuceta ya dawo da

baya, kama ta yay ya mikar tsaye da ga zaunen

da take. Fuskarta ya dago dan taki yarda ta

kallesa, shima bai matsa da sai ta kallesan ba ya

manna ma goshinta sumba mai lafiyar da har sai

da ta sanya jikinta motsawa. Idanunta a rufe har

sai da ya fice sannan ta bude tana sauke

nannauyar ajiyar zuciya, ita har yanzu ta kasa

sabawa da salon nasa sam.

Sai da ta dan kara gasa kanta kamar yanda

Mammy tace ta dinga yi akai-akai sannan tayo

alwala ta fito gabatar da sallar magriba. Bayan

ta idar zama tai tunani mai zurfi akan Tajwar

Eshaan, mutum nan nada abubuwan ban

mamaki boyayyu, tabbas ta yarda hatsabibin

kansa ne kamar yanda su Miran Arshaan ke

fada. Gaskiya tana bukatar sanin yanda akai su

Baby suka kasance a wata kasa bayan su Miran

Jasim sun mata karyar ya kashesu. Kenan video

din data gani jabu ne ko mi?. Rashin amsa da

bukatar samunta ya sata mikewa ta gabatar da

sallar isha'i da ake kira. Bayan ta idar ta shiga

gyara jikinta dan haka kawai take dokin fitar duk

da bata san ina suka nufa ba. Tsaf take cikin bakar doguwar rigar abayar datai mata kyau,sai Ver din nan da in aka nada yake yi kamar baoy

hijab fari. Fitowa tai tsabar zumudin son fitar ta

su. Dakin da suka kwana ta nufa duk da bata

zaton ya isa dawowa salla.

Kusan a tare suka aura hannayensu kan

handle din kofar, ita ta tura shi kuma ya ja batare

da kowanne yasan da dan uwansa ba. Cak ta

tsaya kanta a kasa tana mai rumtse idanunta

dan wata irin kunyarsa takeji har cikin kashinta.

Ga kwarjini mai irin mamaye waje din nan da ya

kara mata. Kusan minti daya suka kwashe a

wajen ita bata tanka ba shima bai ce ba. Tasan

in zasu kwana ma zai iya, dan haka ta dan saci

kallonsa ta gefen ido. A hankali ta janye idanun

nata gain yanda ya kafeta da shegen kallon

nan nasa mai hanata sukuni. Sai ta samu kanta

da in inar fadin, "Barka da dawowa". Karamar

ajiyar zuciyar da bata ji ba ya yayi a ciki, batare

da ya amsa gaisuwar tata ba ya karasa fitowa,

fuskar babu fara'a sam kamar ko yau she, sai

wani irin kwarjini mai cika idon mai kallo, a fisge

ya furta, "Muje" yana rabata ya wuce cike da

takun nan nasa daddaya. A hankali ta dan sauke

numfashi dan jinta take kamar an daureta a

wajen, sai kuma ta bisa da kallo kasa-kasa tana

mai tsarkake sunan UBANGIJI mahaliccin

wannan kyakykyawar halitta. (Kyau dai kam ALLAH ya bashi, sai dai miskilancin nan da jin

 nan da ke zagaye da shi) ta dan nal

fuska kamar zatai magana, sai kuma ta fasa

ranta fal tunanin ina ma zasu je a daren nan?

rashin mai bata amsa ya sata dan zabura tabi

bayansan. Ganin ya nufi lift.. taji duk ta tsure. Ita

dai harga ALLAH abin nan baya wani birgeta.

Dan indai ta shiga sai tayi hajijiya. Shiyyasa ya

zamto sai ta rike wani dan batama taba gigin

shiga ita kadai ba. Jiki a sabule ta shiga, jin

kofar ta rufe kanta ta rumtse idanu da sauri, sai

kuma ta bude akan yatsansa da ke kokarin

danna inda yake bukatar suje. "ALLAH ina jin

toro" ta fada kamar zatai kuka. Sarai ya jita,

amma sai bai nuna yaji ba ya gyara tsaiwarsa

bayan ya danna 2 floor. Iffah da ke jin kamar ta

fasa kuka a hankali tai yunkurin zamewa dan

gara ta zauna zai fi mata sauki. Babu zato taji an

riko mata hannu, kafin ta iya ko bude idanunta

tajita cikin jikinsa da ke fidda wani irin

sirrintaccen kamshi mai ratsa zuciya da bargo

da bazata taba iya mantawa ba. Da sauri ta

bude idanunta sai ko cikin nasa da ke kallonta,

dole ta maida nata ta rufe da sauri zuciyarta na

wani irin bugawa da sauri-sauri, tabbas bazata

mance wannan turaren ba, dan turarene da ta

dinga fafitikar nema a washe grin da aka

dakkota da ga sashenta cikin dare aka maidata

nashi. Kenan da gaske shi dinne ya je ya

dakkota kokuwa yaya akai? Dan wannan Kamshin dai shine. Tsaf ya fahimci inda ta nura,

kuma a randa ta dinga neman turaren ya sani

sarai, abinda bata sani ba ya ajiye abinsa ne

kawai inda bataima zaton ganinsa ba o kawowa

a ranta zai ajiye din.

"Zamu kwana anan ne?". Ya fada a kasan

makoshi yana kallon kyakykyawar fuskarta da

ke kwance a kan kirjinsa. Idanun ta bude, sai

kuma taja jikinta baya kunya na wani mamayeta.

Dauke idanunsa yay da ga kallonta ya fice,

itama sai ta bisa tana sauke ajiyar zuciya a

jajere, sai kuma ta saki murmushi dan ita da

kanta kunyar kanta taji. Wata hanyar da batama

san da ita a wajen ba suka nufa, koda yake

bawai ta taba shiga wani waje a floor 2 din nan

bane bayan falo, shima a randa Malikat

Haseenat ce ta kawota da suka biyo komai daki-

daki ba kamar yanda yay ba yanzu

Inda suka shigo dinne ya sakata tsayawa

turus tana kallonsa. Sai kuma ta dan waiga ta

kalli hanyar da suka fito, ita fa gaba daya notikan

kanta sun kwace, ta ma rasa ta yanda zata

misalta ta inda wannan hanyar take a zahirin

cikin gidan, dan ita shaidace tsakanin sashensa

da na Malikat Bushirat akwai nisa. Duk da sunyi

yar tafiya suma amma sai gasu cikin sauki.

Kallonsa tai fuska a marairaice kamar ba Iffah'r

nan matsiwaciya ba da ya sani ta ce, "ALLAH toro nake ji". Kallonta yake da shanyayyun

idanun nan nasa masu kaifi kamar bazaice

komai ba, sai kuma jitai a hankali kamar mai

rada ya furta, "Nima tsoron nake ji ai". Idanu ta

dan waro alamar mamaki tace, "Kai din?". Kansa

ya dan kada mata da lumshe idanunsa ya bude

duk a lokaci daya. Sai kuma ya kai hannunsa kan

nata ya matsota jikinsa. "Ki karamin karfi". Ya

fada yana rungumeta cikin jikin nasa.

Daburcewa tai ma ita gaba daya. Tai kokarin

dagowa ya hana hakan. Dole ta hakura tai luff

tana mai shakar kamshin da jikinsa ke fitarwa

mai azabar dadi. Kusan minti biyu suka kwashe

a wajen kafin ya dagota a hankali, kin yarda tai

su hada ido sam, shima sai bai matsa ba ya ja

hanunta kawai yana dan murmushin da iyakarsa

makoshi suka shige.

No comments

Powered by Blogger.