Daudar Gora Book 2 page 48

 


Book two(48)


....Sam kalamansa babu abinda suke kara mata sai suka a zuciya, Amma sai ta dake ta daga masa kai kawai tana dan murmushin karfin hali. Tare da kai hanunta saman fuskarsa ta shafa da fadin, "ALLAI yay maka albarka". A hankali.

Murmushi ya mata shima a karo na biyu yana mai lumshe idanunsa da budewa lokaci guda ya ce, "Amin nagode Ammie, ALLAH ya kara miki lafiya da tsohon rai mai albarka" akan lips dinsa. Da ga haka ya dauka shayin da ya samu Jasrah a bata ya cigaba da bata da kanshi. Sha take tana kallonsa tare da kara tabbatar da zancen uwa. Dan kuwa babu abinda kake gani a tattare da shi sai nutsuwa da tarin cikar kamala. Fuskarsa kam sai shining take da daukar idon tabbatar da shi ango ga duk mai iya kallonsa. Ga wani kamshi da take i can kasa-kasa a cikin nasa da ke bata tabbacin na mace ne. Hawayen da ke sake taso mata take dannewa, dan yanzu kam tama fi bukatar kowa ya fice a barta ita daya saboda tana bukatar ganawa da wa. Dole ta samu mafia, dan bazata taba barin yaronta daya tilo ya sake kusantar mafi zama makivarta kololuwa ba. Ko zatai vawo tsirara sai taga bayan yarinyar nan, sai taga banda ya tsaya mata, sai taga yar ban wacece ita, mita taka ne haka da zata zamewa cikar burinta barazana, burin data dauka tsahon shekaru tana ginawa da kauda duk wanda ya nema shiga gabanta koda a kuskure ne.

Itace fa ki gudu sa maze gudu TA-KURYA sa maza kurya. Wutar gobara kasheki koda taro sai an dace.

Matar Shahan-shan din RUMAN war Shahan-shan.

Never for ever ta fadi kasa a dalilin var cikinta da da'ace dan cikinta auren wuri yayi babu abinda zai hana ya haifeta".

Ganin kamar ta dan saki jikinta har tasha magani bayan tea din da tasha Jasrah ta hada mata ruwan wanka sai kawai yay musu sallama dan sallar la'asar na gabatowa. A can kasan ransa kam hankalinsa ya rabu biyu ne. Wani na nan wani nakan Iftah da itama ya baro cikin halin da ya jefata. Sosai Jasrah taji dadin zamansa tare da su gain yanda yar war tata ta dan sake, hakama Malikat Bushirat din ta nuna jin dadinta a zahiri, amma ita kadai tasan kunci da dacin da ke zagaye da ruhinta... Barci tayi sosa dan har akai sallar azhar bata farka ba. Daneen Ammarah da ke a sashen zaune takan lekata lokaci zuwa lokaci. Sai kusan 3 ta farka. Yanda ta danvi dama-dama fuskar ta sabe sosai da kumburin ido ya sata in sanyi a zucivarta, Ga zazzabin ma ya sauka da ciwon kan. Ta rage rakin zafi-zafin sai dai idan ta motsa da dan karfi takan aije lips. Ruwa mai dumi sosai Daneen Ammarah ta hada mata. Da taimakonta ta kara sit bath sannan ta barta tai wanka da karasa kimtsa jikita. Kafin ta fito an sake gyara dakin da kunna masa turarruka komai ya dauki haramin kamshi. Kayan da aka kawo da ga sashen Malikat Haseenat masu kyau da daukar idanu ta alive mata ta fice da dan mata short not ta ajive.

Cikin dabara ta fito tana cizar lips. Jinta take sakayau kamar iska zata iya daukarta. Ga bakinta daci sosai, Hatta tsamin da jikinta yay dazun yanzu duk ya saki sal can da idan ta motsa take in ciwon kadan-kadan. Yanzu ko data shiga ruwan zafi da sake gasa ikinta ma sai ta kara in dadi ko'ina ya mike mata. Ta dan ji dadin rashin gain Mammy, dan kunyarta take ji

ALLAH dauriva kawai take vi. Da kanta ta dan daddogara ta shirya cikin kyakykyawar abayar baka da tasha adon duwatsu sai walkiya take. Harda b8p a cikin kayan. Salla ta fara gabatarwa a daddafe, tai achar tai la'asar da taga lokacinta vayi. Tana sallar

Daneen Ammarah ta sake shigowa har sau biyu. Sai da ta idar ta lura da kyawawan kwanikan dake ajiye.

Tana kan sellayar zahe Daneen Ammeran ta sake dawowa. Zama tai a kusa da ita tana tambayarta yaya ilkin. A shanwabe ta amsa mata cewar da sauki.

Daneen Ammarah tai murmushi kawai batare data sake cewa komai ba. Sai ma abinci da tai kokarin zuba mata da talmakonta kuma ta dan ci dan girki ne na musamman da ga Mammah. Ta dadin vanda taga tari ganoshen naman da dan Rirk, ta bata magunguna sannan tai zaman busar mata gashi da dazum balar ba. Tsaf ta gyana mata shi ta daure sannan ta gyara mata fuska da kara saka mata was turarruka masu masifar kamshi da bata san da su ba.

Ta kuma sakata yin tsugunno kan was turarrukan dai bavan wanda tai wanka da su a bavi lokacin da zatayi.

Daneen Ammarah ta sauke duk wans neuvin da taken tai zaman ima Iffah nasiha da bata shawarwarin da

Jaav taimaka mata a matsayin da take a yanzun mai banbanci da na baya. Sosai nasihar ke shigarta vanda ya kamata, da da karshe ta sanya mata albarka tari-tari sannan ta dore mata wayar Tajwar Eshaan da ta gani akan side drawer ta rike dan ta debe mata kewa kalm ya dalo, ta Kuma icunna mate television dir dakin ma ta aive mata remote kusa da ita da barpusm da Mammiali duk ta aiko mata elkin kavan abincin lunch.

Ji Iffah tai kamar tai kuka, dan toro take ji a sake barinta da ga dasal shi a vanza. lla kadar lasan abinda ta fuskanta a daren jiya a hannun bawan. ALLAHn nan. Ita kanta Daneen Ammarah tausavin barin nata take. Amma yaya zatayi sai kawai ta zabi

binta da addu'a dan bata so ya davo ya sake taddata

a sashen.. Ajiyar zucia ta dan sauke da hadiye

hawayen da suka ciko mata idanu, wani irin kewar

yan uwanta take ji fiye da ko yaushe a yau din nan.

Ganin zata saka kanta a damuwa tai musu addu'ar

samun rahamar UBANGIJI ta dauka remote di da

Mammy ta ajiye mata ta kunna tv. Searching channels ta faravi a hankali harta samu inda wani film mai kvau

ya dauka hankalinta, sai dai film din akwai abun tsoro

a ciki. A kan lips cikin disashiyar muryarta ta furta,

"Bari muga kozan iva". Tana gara zamanta ta jingina da fuskar gadon tare da daukar popcorn din ta tasa a

cinya tana kaiwa baki da daddaya....

Koda wasa bataji shigowarsa ba, dan hankalinta gaba daya ta maida shi ga kallon film dinne, duk da

atsorace take kuma, wani gun ma har sai ta boye

fuska an dan wuce take iva cigaba da kallon.

Zamansa kusa da ita da saukar numfashinsa a gefen wuyanta ya sata yar zabura harda shirin fasa kara.

Guntun murmushinsa din nan kamar na dole ya saki yana rikota. "Hy relax". Ya fada cikin rada kamar mai tsoron aji su.

Idanunta ta rumtse da karfi ta sake budewa zuciyarta na wani irin gudu da sauri-sauri dan ta toratan fa da gaske. Cikin tura baki ta juya idanunta da har yanzu basu gama bajewa gaba daya ba tai masa yar hararar data nema tsarga masa zuciya. A hankali ta ce, "ALLAH kaban tsoro ka nema afuwa na".

Yanzun ma murmushi ya sake yi, batare da yace komal ba ya gara zamansa yana daura kansa a kafadarta idanunsa akan television da take kallo. Cikin rada-dara da kamo hanunta da ke cikin popcorn din ya kai wanda ta dakko guda daya bakinsa yana fadin,

"Babu tayi ne?" ya kare maganar da kallonta. Da sauri ta kauda idanunta da ga kallon da take masa ta maida ga tv cike da basarwa, a shagwabe ta ce, "Gashi kaci ba'a baka ba. Ina vini".

Idanunsa va dan lumshe da budewa va tashi da kyau yana matsota jikinsa sosai kanta da bayanta suka koma saman kirjinsa, yayinda take a tsakkiyar kafafunsa. Ita duk jitai zaman ma ya bata kunya, amma ya ta iya dole ta dake dan Mamy ta mata nasiha sosai akan ta saki tiki da milinta karta bada wata kofa da zai y dana sani kan auranta ko tunanin mallakar wata mace saboda gazawarta. Kafarsa daya ya ajive a dan dogare yanda ta sake samun jin dadin zaman. Kusan mintuna biyar bai sake cewa komai ba itama bata sake ba idanunsu duk suna a tv. Yayinda yake kamo hanunta da take dibo popcorn din yana kaiwa bakinsa. Cikin maganar nan tasa kamar ta dole ya ce, "Kinci abinci?".

Kanta ta daga masa tsigar jikinta na tashi saboda yanda yay maganar cikin kunnenta. Hannunsa na dama ya sakalo saman cikinta yana shinshinar wuyanta. "Ban yarda ba, mi kika ci?".

Cikin yar in ina da son janye jikinta amma ya hana hakan ta ce, "Mammy ta bani gasashen jan nama da madara"

"Uhm yar gatan Mammynta. Shine baki rage mun ba kuma? Gashi ina jin yunwa sosai banci komai ba tun wanda kika tsammin".

Ita gaba daya jitake kamar an canja mata shi da wani ba Shahan-shan din nan miskili mai shariva da magana ma sai ya jinjina ta ba kafin yayi, duk da a yanzun ma daddaya yake yinta kamar abun dole.

Kasa cemasa komai tai, dan gaba daya ita yamasa ta daina fahimtar film din ma. Shi kansa baima san mi yake ba, abinda kawai ya sani ta gama mamayesa da komansa. Tsananin begenta yake da jin kishin sake kasancewa da ita. Amma zai daure bazai aikata ba kodan tausayinta, ballema dinki da akai mala. Da. kyar ya dan dai-daita kansa, itama cikin dan rawar murya ta ajiye popcorn din zata mike. Riketa yay kamar mai tsoron ta gudar masa (g . A shagwabe tana narke fuska ta dubesa, sai kuma ta risinar da idanun da take kyakykyaftawa, "Zan samo ma abincin ne fa". A hankali ya saki hanun nata yana lunshe idanu da sake budewa a kanta gaba daya laurun idanuma ya canja Yanda take tafiya kaman a hahharde kuma a hankali yabi da kallo, tausayinta duk sai ya sake mamayesa.

Yaso ya dakatar da ita, amma sai maganar kuma ta masa wahala dan yunwar kuma yakeji da gaske. Tan madarar da ya sha a wajenta da dan naman nan bai sake cin komai ba. Koda ya shigo bayan sallar la'asar kuwa baiko kalla dining room din ba ya shilge. Wanka kawai yay ya canja kayansa ya taho dubata tuna vasan a vanda ya barta sharban da safen nan....


No comments

Powered by Blogger.