Daudar Gora Book 2 page 47

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (47)

........Hawayen da take riƙewa ne suka ziraro, ta girgiza masa kai alamar bazata iya ba. Komai bai sake cewa ba, sai riƙo hanunta mai riƙe da kofin madarar yay cikin nasa tare da kofin, bakinsa ya kai ya sha madarar. Ta

masa matuƙar daɗi fiye da duk madarar da yake sha. Still dai hanunsa nakan nata da kofin ya sake kaiwa ya sha. Sai da ya sha kusan sau biyar sannan ya kai bakinta itama. 

      “Hhah”.

  Ya faɗa a narke yana wani irin busa mata iskar bakinsa kan idanunta da suke mar-mar, gaba ɗaya neman daburcewa take.

          “Kina so na buɗe da kaina?”.

    Da sauri ta girgiza kai da buɗe bakin kaɗan ya ɗaura mata kofin. Kaɗan tasha ta janye, sake ɗaura mata yay. Babu yanda ta iya dole ta cigaba da sha. Bai barta ba har sai da ta shanye duka sannan ya ajiye kofin. Naman ya ɗauka shima ya shiga bata yana ci har suka cinye tare da shanye romon ma duka a tare. 

    “Sai mi kuma?”.

Ya faɗa yana riƙo hanunta a nashi. Fuska a shagwaɓe ta ce, “Barci”. Murmushi yayi tausayinta da ƙaunarta na sake mamaye shi, sannu-sannu ya kai hanunta kan lips ɗinsa, babu zato taji saukar kiss a tsakkiyar tafin hannun. Idanunta ta rumtse da ƙarfi tana matse jikinta dan har cikin ɓargo sumbar ta shigeta. A tare suka sauke ajiyar zuciya, tai ƙoƙarin zamewa zata kwanta ya riƙota jikinsa. Tsam-tsam ya rungumeta yana shinshinar wuyanta da busa mata numfashinsa da ke saka tsigar jikinta yamutsawa. 

       Luf tayi tana mai shaƙar daddaɗan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaƙa nutsuwa, yanda yake hura mata iska a cikin kunne da murza yatsun hannunta dake cikin nashi tuni barcin da keta rinjayar idanunta ya fara tasiri kanta. Jin jikinta ya saki gaba ɗaya ya sashi ɗan sakin murmushin ta sake gyarata ta kwanta da ƙyau, cikin abinda bai wuce mintuna biyu ba numfashinta ya fara sauka a hankali alamar barcinta yay nisa. Numfashi ya ɗan furzar da gyara filos ɗin gadon ya kwantar da ita. Lumsassun idanunsa ya zuba mata batare da ya ɗago da ga ranƙwafawar da yay a kanta ba. Wasu kalamanta ne na jiya suka shiga dawo masa a rai, wani lallausan murmushi ne ya suɓuce masa ba shiri, ƙoƙarin haɗiye kayansa yay da sake matsawa da ƙyau jikinta ya sumbaci goshinta da hancinta da lips ɗin da sai da ya ɗan juya su a cikin nasa sannan ya saki. Bargo yaja ya lulluɓe ta da ƙyau ya miƙe...


      Koda ya fito falon bai saurari abincin breakfast da aka shirya masa ba. Hakama Daneen Ammarah bata falon, sai amintaccensa kawai da ke dakon fitowarsa. Gaisuwar amintaccen hadimin nasa ya ke amsawa yana nufar lift.. yayinda shima yake biye da shi da hanzarinsa.

      Fada ya fara nufa cikin takun nan nasa ɗaɗɗaya na izza da ƙasaita. Shigowarsa da aka sanar tun kafin ya iso ya sa duk wanda ke a wajen miƙewa kai a ƙasa har sai da ya kai zaune. Suma duk zaman sukai cike da girmamawa suka shiga miƙa gaisuwa suna satar kallonsa dan yay musu wani fayau da sake cikar kamala kamar wanda akaima wankan inji. Saɓanin ko yaushe kuma yau fuskar da ɗan sassauci duk da bawai dariya yake ba ko murmushi. Tana nan dai kadaran kadahan bata tsuke sosai ba bai kuma saketa ba. Kamar ko yaushe amintaccensa ne ya amsa da yawunsa. Da ga haka aka ɗanyi zaman fadanci masu ƙorafe-ƙorafe suka kawo yana saurarensu. Hakama masu shawara akan masarautar ko wani abu da ya faru harma da wajenta. Na masarautar dai duk sun samu rinjaye ne akan abinda ya faru tsakanin Miran Jasim da iyalansa.

         Komai baice akai ba, yana dai jinsu da kunne bisa ra'ayinsu har gardama ma ta ɗan nema sarƙewa sai da Sayeed Anwarus-sadat ya tsawatar. Baice komai game da rashin ganin Miran Arshaan ba, shima kuma Miran Jasim ɗin da aka sanar masa ya matsa an sallamesa tun a daren jiya baice komai ba a kai. Zaman gaba ɗaya bai wuce na awa biyu ba lokacin sallar zuhur yayi....


       Bayan an idar da salla ya samu rakkiyar manyan masarautar duba mahaifiyarsa. Duk da amota suke duk inda motocin suka gitta hadimai ƙasa kawai suke zubewa kawuna a sunkuye har suka ƙarisa ƙofar sashen. Motar da yake ciki ma har cikin barandar gaban falonta ta tsaya. Amintaccensa da yay saurin fitowa da ga gaban motar ne ya buɗe masa. Shiru babu alamar zai motsa balle ya fito har sai da minti ɗaya da sakkani ya shuɗe. A hankali ya ziro ƙafarsa dake cikin takalman masu tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo farare tas heif cover, sai da ya sake jan wasu sakkanin kafin ya zuro ɗayar, nan ma ya sake jinkirtawa sannan ya fito gaba ɗayansa. Tuni mayataccen ƙamshinsa ya mamaye sashen tunkan ma ya shiga. Hadimai kam rige-rigen shigewa suke dan mai RUMAN ne fa da kansa ba aike ba. A waje kam jami'an tsaro sun zagaye sashen tamkar ba'a cikin gida ba. Ameera Danish-Ara da ke zaune a falon tare da Ameera Haifah da wasu a cikin matan masarautar masu faɗa aji da suka shigo duba Malikat Bushirat ɗin tuni sun miƙe kawunansu a ƙasa. Takun sawayensa kam tuni ya saka kowa nutsuwa kowa na satar kallon hanyar da zai shigo da kallo. Yayinda ƙafarsa ke taka cikin falon babu wanda bai ja numfashi ba, dan a wajen ado kam kowa shaidane Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed ɗawusu ne. Ƙamshi kam ba'a magana idan yana waje kowane turare disashewa yake duk ƙarfinsa. Ko sau ɗaya bai kalli kowa ba, takunsa yake a nutse cikin izza da ƙasaita da ka gansa kaga gwarzon gwaraza mai gwara kawunan gwarzo mai son nuna gwarzantaka. Gaisuwar da suke ta faman masa Sayeed Fayzul-haq ne dake take masa baya kawai ke amsawa. Dan sauran jama'ar da ke a tare da shi duk a farkon shigowa falon suka ja birki.

        Sayeed ɗin ma a ƙofar ɗaki ya dakata bayan ya buɗe masa ƙofar ɗakin da akai musu iso Malikat Bushirat na ciki. Isar ƙamshinsa ciki kafin shi ya saka Jasrah da ke kusa da ita tana bata shayi miƙewa da sauri. Malikat Bushirat kam idanunta dake matuƙar jazur ta zubawa ƙofar zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Tunda ya shigo shima kaifafan idanunsa dake sakeye cikin gilashi na kanta. Nata dake cikowa da hawaye ta rintse da sauri tana kauda kanta, wani irin zafi takeji, zafi mai amsa suna zafi na gaske a ƙirjinta har tana jin turirinsa a maƙoshi. A maimakon zama a kujerar da Jasrah ta gyara masa bakin gadon ya kai zaune. Hannun Ammien tasa ya kamo a hankali cikin nasa ya sumbata. Maimakon murmushi da take sakar masa a da idan yay mata hakan yanzu hawaye ne masu zafin gaske da ta kasa riƙewa suka ziraro da gudun tsiya kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da duk ta dame kamar ba Malikat Bushirat ɗin nan ba ƴar gaye, hamshaƙiya ƴar ƙwalisa. Idanunsa ya rumtse a hankali hawayen na ratsa har tsakkiyar zuciyarsa. Ya jima a haka kafin ya buɗesu ya sauke a kanta. Handkherciff ɗin jikinsa ya zaro ya miƙa mata, tare da motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, *“لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .*

     _La ba'asa tahoorun in sha'al-lah._

(Ba komai, tsarkaka ce in ALLAH ya yarda).

أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ *.(سبع مرات)*

_Asalul-lahal-'azeem rabbal-'arshil-'azeem an yashfeek._

    (Ina rokon ALLAH mai girma, UBANGIJIN Al'arshi mai girma, ya warkar da kai)”. 

    

    _(MANZON ALLAH, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya faɗi wannan (addu'a) sau bakwai face ya sami lafiya".)_ (ALLAH ya azurta marasa lafiyar mu da lafiya, ya basu ikon cinye jarabawa, yasa ta zama kaffara garesu. Masu ita ALLAH ya ƙara musu, ya karemu daga cutukan zamani masu haɗari da hana nutsuwar zukata😭🙏). 

     Damƙe handkherciff ɗin kawai tai taƙi share hawayen da suka gagara tsayawa. Sai Jasrah ce ke faman amsa addu'oin sa da sannu. Cikin damuwa ya kalli Jasrahn batare da yace komai ba. Ta fahimcesa, dan haka ta fara bayani tana sharar hawaye itama. “Nima ban san ainahin abinda ke faruwa ba wlhy. Amma dama kwana biyun nan duk bata cikin walwala. Na kuma tambayeta amma tace min babu komai yanayine kawai, sai jiya dai da ƙyar ta ce min akan matarka ne, tace ka saketa amma ka share ko zancen baka sake tadawa ba, ta nema iso gareka ance ka shige ciki a jiya after isha'i. Ni dai na bata haƙuri da nuna mata abi komai dai a sannu kodan abubuwan da suka faru na rasa matanka da kai idan kuma akace ka saki wannan haka ɓakatatan ba'a kai ƙarshen case ɗin nan ba maimakon ita da bata da gaskiya sai a koma zarginka kai. Ta nuna kamar taji ma wuce, amma sai banyi barci cikin nutsuwa ba dan nasanta da saka abu a rai, shine ana idar da sallar asuba nazo dan gaisheta na sameta a ƙasa babu alamar rai tattare da ita. Na nemeka amma baka ɗaga ba, dole nai kiran amintacciyarta dan ta sanar da Mammah. Sai da ma sukazo ne muka iya ɗagata a ƙasan ni da Nina Ammarah da ƙyar, kafin a kira Doctors sukazo kanta har dai ALLAH yasa ta farfaɗo suka sake maidata barci dan tanata zabura kamar wadda ke a firgice. Sun tabbatar jininta ya hau ƙololuwa har yanama zuciyarta barazana ma. Amma dai yanzu data farka Alhamdullah Dr Aliyah tace jinin ya ɗan sauka bakamar ɗazun ba”.

        Idanu ya kafe Malikat Bushirat ɗin kawai da su na wani tsawon lokaci, kafin ya furzar da iska cikin damuwa ya furta, “Why Ammie? Why zaki jefa kanki irin wannan haɗarin saboda ni. Kina tunanin idan wani abu ya sameki zan iya yafema kaina? Haba Ammien na, ki tausaya mun karki maidani maraya gaba ɗayana babu uwa babu uba mana. Yayin da na rasa Abbie sai nake kallon fuskarsa tare da taki a waje ɗaya, hakanne ke samun nutsuwa na share hawayen da suka kwaranyo min kafin su zubo a kowane lokaci saboda kewarsa. Banƙi biyayya gareki ba, sai dai ina son kareki da ga abinda zai iya zuwa ya dawo game da umarninki gareni. Yarinyar nan tabbas mai laifi ce, laifin data ambata da bakinta ta aikata. Sai dai kuma ni shugaba ne, tanada hakkin da zan bata kariya a yayin da akai yunƙurin cutar da ita itama akan dalilai biyu. Ita ɗin MATATA ce....” wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi, kalmar matata ce ɗin na mata wani irin sukar mashi a ƙirji, ya cigaba da faɗin, “Akwai haƙƙoƙinta a kaina dolen dole. Sannan ni Shugaba ne, banda hurumin yanke hukunci cikin fushi ga talakawana har sai nayi bincike. Sannan ma abu na ƙarshe da kike zargin ta aikata ba'ita bace ba. Zaki tabbatar da hakan kuma a zaman shari'a na uku gobe insha ALLAHU. Nayi miki alƙawarin gaggauto da sake zaman shari'ar gobe kodan mukai inda kike buƙata. Fatana dai yanzu ki kwantar da hankalinki, ki sama ranki haƙuri Eshaan ɗin ki na tare da ke ɗari bisa ɗari, mai kuma bin umarninki ne a duk sanda kika bashi, bazan taɓa zama mai bijirewa ba in har ba'a taɓa hurumin UBANGIJINA ba”.........✍️


No comments

Powered by Blogger.