Daudar Gora Book 2 page 46

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (46)



.......Shiru Malikat Haseenat tai kawai tana kallon Iffah da ta koma ta kwanta, hanunta ta riƙo cike da lallashi ta ce, “To ya isa haka kukan kinji yarinyar albarka. ALLAH yay miki albarka. Ya jaddada rahama a gareki da yalwataccen farin ciki na har abada. ALLAH ya sa ki cigaba da zama haske mai haskaka wannan zuri'a”.

        A saman lips ya amsa da Amin. Yayinda Malikat Haseenat tai amfani da wayarta tai kiran Daneen Ammarah. Wani irin yamm ya dinga ji a jikinsa jin Mammah na bada umarnin Daneen Ammarah ta shigo. Sai yaji kamar kasancewar su a waje guda yau wani abu ne mai girman gaske. Da ƙyar ya iya dauriyar cigaba da tsaiwa a inda yake har ta shigo ɗakin. Itama yanda take yi ɗin kamar wadda ta daburce. Sam taƙi yarda ta dubi inda yake kamar yau ne rana na farko da suka kasance ƙarƙashin inuwa ɗaya. Koda ya gaisheta kamar yanda ya saba cike da jarumtar danne nasa yanayin shima a hankali ta amsa masa batare da ta dubesa ba. 

      Ita dai Mammah hankalinta nakan Iffah ne bata san mima sukeyi ba. Sai da taji tsaiwar Daneen Ammarah kusa da ita ne ta ɗago. Daneen Ammarah da idanunta ke akan Iffah wani irin tashin hankaline ke ƙoƙarin mamaye fuskarta amma tana dannesa. Muryarta a ɗan sassauce ta furta, “Mike damunta haka?”. 

             “Ɗanki ne”.

       Malikat Haseenat ta bata amsa a dunƙule. Ta fahimta dan haka bata sake magana ba sai da Malikat Haseenat ta ce, “Kamamun ita ta tashi zaune da ƙyau. Sai ki sake haɗamun ruwan ɗumi da waɗan nan turarrukan”. Kai kawai Daneen Ammarah ta jinjina ma Mammah, ta matsa ta kama Iffah ta tayar, kuka take sosai tana rirriƙeta amma Malikat Haseenat ta ce mata ta barta so take ta zauna ɗin sosai. Ba yanda zatai haka ta zaunar da ita ta zame jikinta batare da ta sake yarda ta kalla sashen da Tajwar Eshaan ya ke ba ta wuce bathroom abinta. Shima sai kawai yaji zaman ɗakin bazai yiwu masa ba. Dan haka ya fito abinsa yana mai satar kallon Iffah da ke kuka da mutsu-mutsun kasa zama da ƙyau. Kai tsaye Gym ɗinsa ya nufa. Jallabiyar jikinsa ya zame ya canja da sport wears ya shiga motsa jiki da zafi-zafi kamar wanda ake tunzurawa.....


      

    ★Da ƙyar Iffah ta iya kai kanta bayi da taimakon Daneen Ammarah. Ashe ɗazu ba ƙaramin taimako yake mata ba da yake ɗaukar ta a komai. Sosai hankalin Malikat Haseenat da ita kanta Daneen Ammarah ɗin ya sake tashi da yanda tafiya ma ta gagari Iffah. A bayin ma duk yanda taso ganin ta nutsu a cikin ruwan ta kasa zama. Sai faman rirriƙeta take da magiyar “Mamy dan ALLAH ki fiddani, wlhy da ciwo sosai”.

       Kwantar da kanta Mamy tai akan ƙafarta tana shafa kanta cike da lallashi dan tana zaune ne a bakin kwamin. “Yi haƙuri to ba'a magana a bayi zai daina”.

          “Mamy bazai daina ba ƙarawa yakeyi”. 

      Dauriya kawai Daneen Ammarah keyi, amma ji take kamar tai kuka. Ta fahimci dole Iffah taji ciwo ne, ciwo kuma bawai ƙarami ba. Ita kam takan rasa miyasa maza basu da tausayine sam. A shekarun Iffah bai kamata namiji yay mata irin wannan zuwan na lokaci guda ba. Duk da tasan su waye mazan ahalin nan nasu akan mace, balle kuma shi da ya kasance tsahon shekaru ma babu macen, ko da ya samesu kuma ita dai Iffah'r ce ta farko dama take hasashen ya kusanta kenan ko yaya. Tunda kaf yaran randa aka kawosu garesa washe gari ake zuwa a ɗauki gawarsu sun rasa ransu. Ɗaga Iffah tai da ga ruwan, ta ɗaure fuska sosai babu alamar wasa tattare da ita, “Ki tsaya a duba ko kinji ciwo ne a wajen, dan wannan zafin da kike ta ambata dole zai kasance akwai damuwa Ibnati. Idan kuma aka bar mace da irin matsalar nan yana lalatata koma ya taɓa mata brain. Ko kina so ki samu matsala a brain ɗin ki?”.

        Da sauri Iffah ta jinjina mata kai alamar a'a tana hawaye. Daneen Ammarah ta haɗiye murmushin da ke taso mata dan ta mata hakane dan ta tsoratar da ita dama kawai. Ai ko sai gashi ta yarda ta duba cikin sauƙi amma fa ta ɓoye fuska cikin tafukan hanunnta, wani irin matsanancin kunyar Mamyn na ratsa ɓargo da jinin jikinta. Amma sai take jin inba itan ba bazata taɓa iya nunama wani ba sai ko Ummu ko su Arfa da suna raye. 

      Rasama abin cewa Daneen Ammarah tayi, sai kawai ta miƙe jiki a saɓule cike da tausayin Iffah. Tabbas dolene ta dinga kuka, a hakan ma sai taga dauriyarta, dan in har watace tofa sai duk masarautar nan sun fahimci halin da ake ciki. Fitowa tai ta samu Malikat Haseenat da ke zaman jiran fitowarsu. “Mammah akwai matsala fa gaskiya, dole a nema likita dan yarinyar nan taji ciwo bana wasa ba”.

       Idanu Malikat Haseenat ta ɗan lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Dama ita ta fahimci hakan ai tun sanda tasa Iffah zama, ta kuma yi hakanne dama danta fahimta. Amma saboda ta sake tabbatarwar tasa Daneen Ammarah ɗin sake taimaka mata, turarrukan data bada a saka mata in har Iffahn taji ciwo mai yawa to bazata iya zama ba daman. “Ammarah wannan sirrine mai girma na shugaban daular ruman. Bazai yiwu ya fita ba kema kin san bama zai yarda ba. Dole ke zaki bata kulawar da ta dace”.

          “Hakane Mammah, amma ni na ɗauka shekaru rabona da yin wani abu a matsayin likita. Kar'a samu kuskure”.

     “Baza'a samu ba insha ALLAHU Ammarah. Na sanki akan komai shiyyasa nake alfahari da ke”.

           Da ƙyar Daneen Ammarah ta iya haɗiye kukan da ke taso mata. Dan in har aka tuna mata ita ɗin ƙwararriyar likitace a baya yakan sosa mata wani ɓangare na rayuwarta data shuɗe da bata son tinawa. Dan tamkar fami akan gyanbon da tasan har gaban abada bazai taɓa ya warke ba a zuciyarta ne. Muryarta na ɗan rawa ta ce, “Zanje clinic na samo kayan aiki”. Da ga haka ta fice. Da kallo Malikat Haseenat ta bita zuciyarta itama na raunana. Tana son Ammarah, matuƙar so da duk a cikin ƴaƴanta sai dai a biyo bayanta. Sai dai tana dannewa da nuna iya tausayinta kawai gudun karta raba kan zuri'arta da kanta....


   ★....


        Tsaf Daneen Ammarah taima Iffah da ke kuka na fitar hankali ɗinkin, wai dan ma ta mata allurar kashe raɗaɗi fa kafin ma ta taɓata. Ana kammalawa ta dinga rawar sanyi na zazzaɓi kanta kam ai kamar zai fashe da ciwo. Malikat Haseenat ta tafi domin basu waje, sai dai ta aiko da lafiyayyen farfesu na musamman da wani irin kunun madara mai zafi shima na musamman. Sai tarin wasu sirrika da Iffah zata dinga amfani da su yayin sit bath da zai taimaka mata warkewa da wuri da kuma wanda zata sha dan tasan in dai wannan yaƙinne kam Iffah yanzu ta farashi. Dan in ma fitinar ce shi kam kamar yacema kowa bai iyaba a ahalin nasa. Gashi yana ɗage-ɗagen waɗan nan shegunan ƙarafunan abu goma da goma.

        Daneen Ammarah sai da ta tabbatar ta gyara toilet ɗin ɗakin tsaf duk da bawani datti tunda ba'a nan suka kwana ba. Bata canja mata rigar Tajwar Eshaan ɗin da har yau take jikinta ba duk da ta mata girma da tsaho, dan ko'a wajen gashin dama sakata tai ta nannaɗe kawai. Zaunar da ita tai kan filos masu taushi amma ta kasa zama da ƙyau sai da ta karkace. Bata hanata ba ta zuba mata madarar da ke ta turiri tare da farfesun naman tsuntsayen da ke ta tashin kamshi. 

       “Mamy na ƙoshi bakina ɗaci barci zanyi”.

    “A'a Ibnati daure kinji, idan kika sha madaran nan kikaci wannan naman sai na ƙarasa miki ɗayan alluran ki kwanta barci har sai sanda kukaso tashi kinji. Bakiji jikinki yayi zafi ba sosai. Haba ɗiyar albarka haihuwar alkairi”.

        Da wannan lallaɓawar Iffah ta fara shan madarar a hankali, Daneen Ammarah na bata farfesun da kanta cike da kulawa. A haka Tajwar Eshaan ya shigo ɗakin da sallama ya samesu. A cikin kwalliya ya ke tsaf ta alfarma ga uban ƙamshinsa da ya cika ko'ina na ɗakin, a taƙaice dai a Shahan-shan ɗin sa yake. Cikin dakewar nan tasa mai ɓoye duk wani sirrin zuciyarsa da ainahinsa yake. Idanunsa sakaye da eyeglasses. Ya wani ƙara ƙyau da cikar kamala ga wani kwarjini mai ƙara yalwata haibarsa ga mai kallo. Daka gansa kasan shi ɗinne dai ɗaya tilo Shahan-shan ɗin ƙasar ruman mai rumawa da ƙasar ruman. Sai wani shining yake da ke tabbatar da yau ɗin ranarsa ce ta musamman mai ɗunbin daraja da tarihin da bazai taɓa goguwa a garesa ba.

      Tun a kallo ɗaya da Iffah tai masa lokacin da yake sallamar shigowa ƙasa-ƙasa bata sake gigin hakan ba. Daneen Ammarah ma dai da ga kallo ɗaya bata sake wani ba, dan gaba ɗaya kwarjininsa ya cika ɗakin, ga wani kunyarsa da ke ɗawainiya da ita kamar itace ta aikata tsiyar ba shi ba. Koda yake shima ɗin dai ji yake Mamyn nasa a yau ta musamman ce a garesa, dan kasancewar ta a sashen nema ya sashi jin gara ya fita zuwa fada, sai kuma ga kira ya samu da ga Malikat Haseenat bayan fitowarsa Gym an wayi gari Ammien sa babu lafiya, yana shirin fitowar nan ma Jasrah tai kiran shi itama tana kuka dan tun ɗazun take kiransa ba'a ɗaga ba.

       Cike da dakewa ya sake gaida Daneen Ammarah idanunsa kan Iffah da ke kai kofin madara bakinta tana sha kaɗan-kaɗan. Miƙewa Daneen Ammarah tai cikin hikima ta ce ta cigaba da shan madarar da nama bara ta amso saƙon sauran magungunan ta data bada a siyo....


        Shiru ɗakin ya ɗauka sai sassanyan ƙamshin da ya gaurayesa ke tashi. Taƙi yarda ta kallesa koda da kuskure duk da yanda take jin ɗakin yay mata tsukuku saboda kasancewar sa. Idanu ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kanta sannan ya ɗan taka gaban gadon gab, zaune ya kai inda Daneen Ammarah ta tashi a gefen gadon kusa da ita sosai. Sai kuma ya kai hannu ya zare eyeglasses ɗin da ya sakaya launin idanunsa.

         “Good morning Mrs Eshaan Qutb”.

      Ya faɗa da wata irin shaƙaƙƙiyar murya mai sanyi matuƙa yana kai yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau. Har tsakkiyar kai muryar da yay amfani da itan ta ratsa Iffah, ga wata matsananciyar kunya da shakkarsa da ke ratsata. Idanun ta da hawaye ke cikosu ta lumshe da sauri.  

       “Please open your eyes my life”. Ya faɗa fuskarsa gab-gab da ita batare data san lokacin da ya matsota haka ba.........✍️


No comments

Powered by Blogger.