Daudar Gora Book 2 page 44

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (44)

........Bai fahimci gagarumar ɓarnar da ya aikata ba sai da ya dawo jayyacinsa. Tun-tuni azaba tasa Iffah ta sume masa batare da ya farga ba. Ba ita da dama ya zama dole ta jigatun ba, hatta da shi kansa a jigacen yake kasancewar wannan shine lokaci na farko a tarihin rayuwarsa. A kallo ɗaya zaka fahimci tabbas maza sunyi laushi, laushi bana

faɗuwa ko gazawa ba, laushi na jin-jina girman UBANGIJI da godiya a garesa dan shine mai azurta bawa da ni'imomin kala-kala iri-iri daban-daban da kai kanka baka fahimtar girman wannan ni'imar sai randa ta isa gareka. Babu ɗan gata a ma'aurata mace ko namiji sai mafi ƙololuwar iya riƙe kansa da nisanta kansa da ga ZINA har sai randa ALLAH ya azurtaka da halal ɗinka. Ya shaida yau kam ya shaida. Bayan uwa da uba da kakarsa bayajin ya taɓa jin ƙauna da soyayyar wani mai tsananin ƙarfi a zuciyarsa kamar yarinyar nan. Ƙololuwa yake jinta, ƙololuwar da in har akace yay fassara ba lallai masu jinsa su iya yarda ba ko zaman saurarensa har ya kai inda yake buƙatar gamsar da su. Badan kar ace ya bada maza ba da shimafa kukan zai fashe da shi kawai a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya ɗagota yana ɗan bubbuga fuskarta da kiran sunanta cikin sarƙaƙaƙƙiyar muryar sa. A baɗini a birkice yake, amma a zahiri da zaka iya ganinsa a nutse yake komai tamkar ma koman da mai kallo zai kalla komai bai zama komai ba. Iya jijjiga da kiran sunanta da yayi babu alamar rai tare da ita. Ya rumtse ido da ƙarfi tare da kai hannunsa saman goshinsa yana murzawa tsabar baima san miya kamata ace yayi ba. Shifa ɗan gata ne, ɗan hutu ne, ɗan lele ne, tunda ya tashi bai san komai ba sai ai masa cikin bada umarni, a inda ya rayu zagaye yake da masu hidima daban-daban da ko abinci inda zai yiwu tauna masa za'ai a zuba masa a cikinsa. Sai da yay matuƙar yaƙi da iyayensa kafin ya samu wasu damammaki na dogaro da kai dan shi yafi son tsayawa a kan ƙafafunsa koda ace shine mafi zama ƙololuwar gata a wannan rayuwar. Bai taɓa ƙyamatar rayuwar talakansa ba sai ma birgesa da basa tausayi yake. Shiyyasa ya zaɓi shiga cikinsu ta hanyar ɓadda kama, ya kuma ƙir ƙiri wasu hanyoyin tsaya musu a duk lokacin da ya fahimci ana zaluntar su. 

          Bashi da zaɓin da ya wuce sake maidata a jikinsa kawai ya rungume tsam-tsam ya shiga bata wasu irin manya-manyan sumbata masu daraja da ba'aima macen data ɓarar da darajar a wajen marasa daraja. “Kiyi haƙuri, kiyi haƙuri na tuba my Ashna”. Ya faɗa cikin kunnenta yana ɗan hura mata isaka a sautin muryar nan tasa da ta sake disashewa matuƙa cikin maƙoshi kai kace zata iya jinsa. Kamar ko wani siddabaru sai kawai tai wani irin zaburowa da jan numfashi a fisge. Da sauri ya janye hannunsa da ke saman goshi ya dubeta, sai kuma ya sake riƙota da ƙyau cikin jikinsa da take neman kufcewa yana ambaton sunan ALLAH a daburce. Wani irin siririn kuka data sake birkita masa lissafinsa ta sake sakar masa tana ƙanƙamesa da jera masa magiyar roƙon ya barta, ya barta zata mutu, dan a rayuwar Iffah bata taɓa cin karo da azaba makamanciyar ta wannan gaɓa ba.

        “Am sorry relax, cool down babie” ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta cikin jikinsa da tura yatsun hanunsa cikin birkitacciyar sumar kanta da ya gama harmutsawa. Har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahi bai daina lallashin da bai san taya zai mata magana mai tsahon da zata fahimcesa ba. Shi gaba ɗaya ma ya wani mance kansa a matsayin Shahan-shan, duk ta gama harmutse masa ɗan sauran lissafin da ya rage masa da rikicinta. Yasan zai fiskanci ma fiye da haka in dai yarinyar nan ce, ba'ace mata kule ba ma tace cas inaga yau shi ya taro fitinarta da karan kansa, ai yasan a darunta ma bata fara komai ba kam dan har yanzu bata gama dawowa a hayyacinta ba ballema ta fara. A hankali yay ƙoƙarin kwantar da ita domin sauka ya samu mafita amma ta ƙanƙamesa ta na sake sakar masa wani sabon kukan da ko muryarta ma ba'a iya ji tsabar yanda ta gama galabaita. Ji yay kawai murmushi mai sanyi ya suɓuce masa, sake riƙota yay yasa a cikin jikinsa yana hura mata iska a kunne cike da soyayya da ƙaunarta da ke neman fallasa kansu a zahirinsa. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa jikinta na saki kaɗan-kaɗan, da ga haka wani wahallen barci yay awon gaba da ita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da ita a hankali sannan ya sauka a gadon.

        Cikin ƴar sassarfar da a zahiri bazaka taɓa gani ba, dan babu abinda ya canja a salon tafiyarsa ta ƙasaita ya nufi bathroom, ƙarƙashin shower kawai ya shiga, babbar gaba ɗaya ya kunna ma kansa tare da dafe bangon glass ɗin da aka zagaye wajen shower ɗin kamar wani ɗan ɗaki. Duk da sanyin da garin ya ɗauka na hadarin da aka haɗa ya ƙare da isaka da ɗan yayyafi ya baje dana ruwan baya jinsa ma. Cikin ƙanƙanin lokaci ruwan yay masa sharkaf, tattausan yalwataccen gashin kansa duk sun kwanta masa a goshi har wasu na ɗan taɓa saman idonsa saboda ɗan tsayin da suke da shi. (She's my everything. Ta daban acikin daban ƙololuwa!....) Kawai yake iya maimaitawa a zuciyarsa hakwaransa cije da lips ɗinsa kamar zai hudasu kawai ya huta. Sai da ya kwashe kusan mintuna bakwai a ƙarƙashin shower ɗin sannan yasa hannu ya danne makunar yana sauke numfashi a jajjere. Har lokacin hannunsa ɗaya dafe da bangon glass ɗin. Jin atshawa na taso masa sannan ya buɗe idanunsa da sukai wani irin jajir da ƙanƙancewa. Sanin in har ya fita da wannan sanyin a jiki zazzaɓi salamu alaikum ya sashi sake kunna shower ɗin, sai dai yanzu ruwan ɗumi ne saɓanin ɗazun. Sumar kansa ya shiga yamutsawa a kasalance ruwan ɗumin na ratsashi da ƙyau, da ace zai iya kuwwar tattaro hankalin mutanen duniya baki ɗaya zai faɗa musu itace komansa, idan yace komai, komai da komai yake nufi akan komai. Sake jin kiran salla ya sashi ƙarasa komai a gurguje ya fito..

         Yana fitowa a kanta ya fara sauke birkitattun idanunsa da launinsu ya zama abin firgitarwa ga mai kallo. Tuni barcin da ya ɗauke ta ya ƙara nisa, barcin da shi a karan kansa yasan na wahala ne kawai. Janyewa yay ya cigaba da takowa cikin ɗakin sannu a hankali kamar mai sanɗa, dan gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi kona sisin kwabo. Sai dai jarumtarsa ta ɓoye komai bayan canjawar launin idanunsa baka isa fassara yanayinsa ba. A gurguje ya busar da kansa domin rage laimar cikinsa ya shirya cikin jallabiya mai taushi fara tas, ya ɗaura baƙar alƙyabba irin ta sarakunan Saudiya da mayafi a kansa tare da daɗaɗan ƙamshi kamar ba sallar asubahi zai fita ba. Gaban gadon ya tako a hankali, barcin kam da nauyi ya ɗauketa, sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci a matuƙar wahalce takeyinsa, dan sai yamutsa fuskarta da yake ɗan gani a hasken ɗakin da yake dimmm take ga ajiyar zuciya da take ta faman saki a jajjere. Idanunsa ya ɗan lumshe ya sake buɗewa a kanta yana sakin guntun murmushi da jan jikinsa baya a hankali ya fice fara gabatar da salla kafin ya dawo su ɗora daga inda suka tsaya dan yasan sabon daru kam zai fuskanta. Shi kuma ko a yanzu badan yana jin tausayinta ba sake zuwa mata zai a yanda yake jin kansan nan.


      ★Ana idar da salla ya baro massalin, dan gaba ɗaya hankalinsa na gareta saboda yasan tana matuƙar buƙatarsa kusa da ita da taimakonsa a wannan gaɓar. Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta. Yanzun ma baiyi wani motsin da zata farka ba har ya kammala zame kayan jikinsa ya canja da ƙananu. Bathroom ya nufa ya haɗa ruwa na musamman sannan ya dawo gareta. Kai tsaye ya kunna wutar ɗakin da ta haske ko'ina ko allura kuwa ka yarda kaga abunka. A hankali yake bin ɗakin da kallo tamkar yau ne karo na farko da ya fara kasancewa a cikinsa. Ya ɗan saki murmushi yana mai lumshe idanunsa da sake buɗewa. Shi kansa ɗakin ya ƙara zama mai wata irin daraja da kima ta musamman a garesa, dan ya zamar masa ɗaki mafi zama ƙololuwar sirri sama da duk sauran sirrikansa. Dubansa ya kai ga gadon inda Iffah ke ƙudindine sai faman sauke ajiyar zuciya take yi cikin barcin wahalar da take yi. Magiya roƙo neman agajin da ta dinga jera masa na dawo masa daki-daki, da'ace gilashin ɗakin nan ba mai hana fitar sauti bane babu abinda zai hana a daren na jiya gaba ɗaya daular ruman su jiye masa sirrinsa, dan bakinta bai mutu ba sai da ta sume masa. Ya ɗan sake murmusawa da takawa sannu-sannu kamar wanda baya so zuwa gaban gadon ya zauna gefenta. Fuskarta da tai luɓu-luɓu na kukan data sha ya shafa yana kaima lips ɗinta da sukai bushewar wahala sumbata. A firgice ta farka tamkar ɗazun, ta saki wani irin wahallen kuka da jujjuya kanta tana mai jero masa roƙon ya barta, dan ALLAH ya barta karya kasheta bazata iyaba. Yanda take yi ɗin dole ne ya baka tausayi, dan a kallo ɗaya zaka fahimci har yanzu bata cikin hayyacinta. Shi baima san ta ina zai fara ba duk da ya jima da shiryama irin wannan ranar ba tun yau ba, amma a yanda yaje mata shi kansa yasan ya jigata ta, irin jigatawar da da'ace wani ne ya aikata aka kawo masa ƙara sai ya hukunta mutum. Sai gashi shi da kansa ne, shi da kansa ya kasa control ɗin kansa yay ma ƙaramar yarinya kamarta zuwa har uku a dare ɗaya duk da ta kasance tamkar jaririya a hannun uwa garesa.      

         “Shiiii!!” ya faɗa a hankali yatsansa kan lips ɗinta. Riƙeta yay da ƙyau tare da manna mata wata sumbar a goshi kafin ya miƙe cak ya ɗagata zuwa bathroom. Wata gigitacciyar ƙara ta saki jinta a ruwan zafi tana rirriƙesa azaba na ratsata, jikinta sai rawa yake shi kansa har abin ya bashi tsoro. Dole ya shiga cikin ruwan shima ya rungumeta a jikinsa. Kuka take matsananci da ƙoƙarin ganin tabar jikin nasa amma ya hanata damar hakan. Kansa ya dafe yana riƙota jikinsa da ƙyau cike da takaicin kansa, sai dai kuma shima ba laifinsa bane, gaba ɗaya idanunsa ne suka rufe, duk wani haƙurinsa da jarumtar da yake dannewa a tsahon shekaru sai da suka amayar da kansu. Tunfa yana da shekarun da basu haura ashirin ba yake dakon wannan matsalar, taya ma zai iya tuna abinda ya dace yayi a wannan gaɓar, ta yaya, ta yaya ake son ya tuna.......✍️



     _🚴🚴🥱Bazaka tunaba kam mai Rumawa._


No comments

Powered by Blogger.