Daudar Gora Book 2 page 41

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (41).........Da ƙyar ta iya danne zuciyarta cikin rumtse idanu ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga. Kamar jiya ɗakin diff babu yawaitar haske sai wani ni'imtaccen ƙamshi mai saka zuciya nutsuwa da sanyin ac. A hankali ta saki ajiyar zuciya tana mai bin ko'ina da kallo. Babu alamar akwai mutum a ciki kam duk da ita dai tana ji a jikinta yana nan. Tafiya ta cigaba da yi kamar wadda ta shigo sata da sanɗa tana ɗan lalleƙawa.

 

         “Bani shayi..”

     Cak ta tsaya ƙirjinta na wani irin dif-dif, sai kuma ta juyo da sauri domin tabbatarwa. Shi ɗin ne dai zaune cikin ƙyaƙyƙyawar kujerarsa mai ƙyawun gaske da laushi, a yanda yay zaman ƙafa harɗe bayansa kwance a kujerar sai ka ɗauka ma idanunsa a lumshe suke. Sanye yake da ga shi sai bathrobe da tausasan slippers alama wanka ya fito, cikin sauri ta sake juyawa tana rumtse idanu duk ta daburce. Sai da ta ɓata minti guda tsayen kafin tayi dauriyar jan ƙafa da ƙyar zuwa centre table na tsakkiyar kujerun da ke gefe kaɗan inda taga butar shayin. Mita take tayi a zuciyarta harta kammala zubawa ta zabga zuma a cikin ɗan kawai neman magana. Murmushi ta saki na mugunta ta ɗauka cup☕ ɗin da shayi keta turiri ta nufesa. Sai dai idanunta a rissine dan kunyar kallonsa take a haka duk da bawai jikinsa a buɗe bane. Tana ƙoƙarin ajiyewa a ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙa mata hannu alamar ta bashi. Miƙa masan tai har yanzu idanunta a ƙasa. 

     “Thanks”.

  Ya faɗa a hankali yana kai kofin kan lips ɗinsa. Da sauri ya janye jin zaƙin zuman ya wani ratsa masa harshe zau-zau. Dai-dai kuwa da ɗaga ƙafar Iffah zata bar wajen. A hankali ya riƙo hanunta cikin nashi, ta rumtse ido da ƙarfi batare da ta juyo ba. Matsota yay jikinsa, a bazata ta jita zaune ɗare-ɗare a cinyarsa. Da sauri ta zabura zata miƙe ya maidata ya zaunar. (Ya ALLAHU wannan mutumin yana lafiya kuwa?) ta faɗa a ranta kamar zata saki kuka. 

      “Haka ake haɗa shayi dama?”.

   Wani irin yamutsawa tsigar jikinta tayi saboda yanda yay maganar a saitin kunnenta da sassanyar muryar nan tasa da a yau gaba ɗaya yinin take jinta a shaƙe. Kasa cewa komai tayi, sai mutsu-mutsun son tashi shiko yaƙi yarda ya bata damar hakan. Sai ma hannunsa da ya saƙalo takan cikinta ya ɗaura kan nata da ke wajen tana ƙanƙame jiki. Tare da sake matsota jikinsa bayanta ya manne da ƙirjinsa. Ɗayan hannun kuwa shayin ya ɗauka ya kawosa bakinta.

      “Hhaah!”.

   Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. A shagwaɓe ta ce, “Ni bance zan sha shayi ba fa”. 

         “Ko?”.

    Ya faɗa cikin sigar tambaya yana ɗage gira sama. Sai kuma ya shiga yin sama da hannunsa zuwa saman jikinta, kansa kuwa na'a kan kafaɗarta yana wani irin kalan shinshinar ƙamshinta. Daburcewa tai duk da sautin fitar numfashinsa kawai take iya ji a kunnenta veil ɗin data naɗa ya lulluɓe wuyanta. Hannun tai saurin riƙowa ta damƙe, cike da in ina ta furta, “Za..zan sha kayi haƙuri”.

        Ɗan murmushi ya saki a karo na farko, batare da ya ce komai ba ya sake kai kofin bakinta. Ita kanta sai da ta ɗan rumtse ido jin yanda zaƙin ya ratsa mata harshe. Dan abu mai zaƙi bai cika damun Iffah ba. Baifi kurɓa uku ba tai ƙoƙarin kauda kanta gefe. Hannun ya sake ƙoƙarin kaiwa sama, da sauri ta riƙe kamar zata saki kuka ta ce, “Zan sha fa”. Nan ma ƙin tanka mata yay ya sake kai kofin lips ɗinta. Babu yanda ta iya dole sai da ta shanyeshi tas.

          “Ai na shanye”.

     Ta faɗa a marairaice tana ƙoƙarin janye hannunsa da ga jikinta. Amma sam yaƙi bata damar hakan. Sai ma kofin da ya ajiye ɗayan hannun ma ya kawo shi kan ƙugunta sai tin inda taji ciwon ya ɗan murza. Zabura tayi dan wajen har yanzu akwai zafi mai raɗaɗi saboda ya tsuma bata bari an murza ba. Sake maidata yay ya zaunar, yanda zafin ke ratsata sai batama san sanda ta maƙalƙalesa ba har ƙafafunta ta naɗe a jikinsa, hannayenta duka biyu kam ta saƙalosu a wuyansa tare da cusa kanta a ƙirjinsa da bathrobe ce kawai. 

          “Karyani kike son yi ne?”.

    Yay maganar acan ƙasan maƙoshi kamar mai mura da son danne abinda ke ratsashi. Baki ta ɗan tura gaba tana ƙara cusa fuskarta ta gefen wuyansa, saukar numfashita a wajen gaba ɗaya ya ƙara hargitse masa lissafi har jikinsa na wani irin yamutsawa. Amma sai ya dake kamar yanda ya saba. Sai dai tambaya da ya sake jeho mata da muryarsa dake ƙara shaƙewa. “Kinyi salla?”. 

     “Uhm”.

  Ta faɗa itama kamar wadda aka shaƙe. “Zaki tayani tawa?”. Ya sake faɗa shima a ƙasan maƙoshin yana ƙoƙarin dai-daita fuskarta da ke a kan kafaɗarsa da tashi. Bata da zaɓin da ya wuce ɗaga masa kai jikinta na tsumar da har yana ji. Tausayi da dariya take bashi, a ransa kam faɗi yake (Stubborn girl matsoraciya). A zahiri kam cak ya miƙe tsaye da ita a hannunsa, sake ɓoye fuskarta tai da cusa kai a ƙirjinsa jinta take kamar ta saki ihu dan kunya. Har cikin bayin ya kaita ya dire gaban tap, yana tsaye a bayanta ya kai hannu ya kunna mata.....


       Da kallo ya bita lokacin da suke fitowa ganin tana ɗan ɗingisa ƙafarta. Da alama dai faɗuwar da tai ɗin har yanzu na damunta. Baice komai ba kamar yanda itama taƙi yarda su haɗa ido. “Ina zuwa”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa yana raɓata ya wuce, cikin closed room ɗin sa ya nufa, ta bisa da kallo ta gefen ido har sai da ya ɓacema ganinta ta saki ajiyar zuciya da kaiwa zaune a table ɗin gaban gadon mai laushin tsiya. Bata gama dai-daita ba ya sake fitowa cikin jallabiya kalar ash sai ɗaukar idanu take ga wani sirrintaccen ƙamshi. Shi da kansa ya shimfiɗa musu sallaya. 

        “Mi zaki roƙa mana?”.

    Ya faɗa yana ɗan juyowa shanyayyun idanunsa a kanta. Fuska ta ɗan yamutse batare data kallesa ba kanta tsaye ta furta “Naga iyayena”. “Nifa?”. Ya sake tambaya har yanzu idanun dai na kanta. Sai da ta ɓata fuska da tura baki gaba sannan ta furta, “Kai mi kake buƙata kuma a duniya?”.

      (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai ya murmusa kaɗan da ɗan ƙara matsawa kusa da ita gab ya kai yatsunsa biyu kan haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau. Lumshe idanunta tayi. Bai damu ba ya cigaba da kallonta sosai. “K! Mana”. Idanu ta waro waje da sauri. Sai ya waske, ya cigaba da faɗin, “K! Nake buƙata ki haifamin yara masu kama da ke?”. Baki ta laɓe da kauda kanta gefe ta ce, “Hu'um ALLAH ya kiyaye”.

      “Sai dai kuma na gaba”.

   Ya faɗa yana sakin mata fuska ya gyara tsaiwarsa. Itama gyarawar tai tana ƙara takwaf-takwaf da fuska, dan badan tana tsoron karya maimaita mata na jiya ba da tuni ta fece a binta. Sun gabatar da salla raka'a hudu da bibbiyu, ya kwararo addu'oin da suka sata jin nutsuwa a ranta harda ƴan ƙwallarta da bata san na minene ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota. Bata da yanda zatai dole ta koma ta zauna a tunaninta wata maganar zai mata. Sai taga ya ɗaura farin hannunsa sol da ke ɗauke da dogayen farce ƙal-ƙal a saman ƙafarta, a hankali ya janyo ƙafar a saman tafin hannunsa ya ɗan riƙe yatsun, ɗayan kuma ya tallafo diddigen ya ɗagota gaba ɗaya ya ɗaura saman ƙafarsa da ya tanƙwashe. Kaɗan ya rage numfashin Iffah ya ɗauke dan mamakinsa, Shiko ko'a jikinsa ya shiga murza ƙafar a hankali cikin salon kulawa. Da sauri ta ɗan ɗaura hanunta a kan nasa tana narai-narai da fuska. 

       “What?”.

    Ya faɗa yana tsareta da idanunsa da suka wani ƙanƙance sosai a kanta. Kamar zata saki kuka ta ce, “Zafi”. Komai bai sake ce mata ba ya ɗauke kansa cike da basarwa ya cigaba da murza mata ƙafar. Tsahon minti biyu kafin ya ajiye ƙafar ya miƙe. Itama miƙewar tai ƙoƙarin yi taji kawai anyi cak da ita an dire saman gado shima ya kai zaune gefenta. Man zafi ya ɗauka a side drawer ya sake kamo ƙafar ya shafa mata, ita dai tayi kurum yanzu sai binsa kawai take da kallo dan ƙafar ya fara sakin mata. Hannunsa ya janye yana ƙoƙarin rufe kwalban suka haɗa ido. Da sauri ta maida nata ta risinar da faɗin, “Thanks”. Yanzun ma komai baice ba ya miƙe, ita kuma ta zubama ƙafar ido tana sauke ajiyar zuciya. Bayan kamar minti biyu tana kan ƙulla shawarar barin ɗakin ya dawo inda ya tashi hannunsa ɗauke da lap-top da kofin shayi.

       Laptop ɗin ya ajiye a table ɗin gabansu tare da juya mata fuskanta batare da yace komai ba. Zamansa ya gyara cike da ƙasaita ƙafa ɗaya ƙan ɗaya ya ɗauka cup ɗin shayinsa ya kai baki yana wani ɗan lumshe idanunsa da ke mata kallon nan dai dake hanata sukuni... Itama ta gefen ido take kallonsa yanzu, a zahiri kam tayi wani irin gefe da fuska ita a dole ba kallonsa take ba...

        “Autah!”.

    Wata sassanyar murya da ko a cikin tsakkiyar barci ta jita a kunenta bazata taɓa manta mai ita ba. Ƙirjinta ne yay wata irin yankewa ya faɗi, sai kuma ta juyo da sauri jin an sake kiran sunan nata. Idanu huɗu sukai da Ummu, Babiy a gefen damarta, Hanash gefen haggunta. Kamar wadda ta firgita ta miƙe a zabure jikinta na rawa. Sai kuma ta dubi Tajwar Eshaan da ke zaunensa kamar baima san mike faruwa ba. Dan shayinsa yake sha a hankali cike da nutsuwa idanunsan nan a lumshe. Kai ta fara girgizawa, sai kuma ta dubi fuskar laptop ɗin. Still dai Ummu ɗin ta ce, da Hanash da Babiy data gama yarda ta rabu da su har abada. Sai Kaka da Iyyani da suka ƙaru. Sai kawai ta diro a gadon ta durƙushe gaban laptop ɗin ta fashe da kuka. “Dan ALLAH gaskiya ne ko mafarki nake? Gizo kuke mun ko video recording ne aka ɗauka?”.

       “Live ne auta. Video call ba mafarki kike ba”.

    Hanash ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da murmushi. Yi tai kamar wadda tai suman wucin gadi, sai kuma ta dubi Tajwar Eshaan baki sake. Idonsa shima a kanta suke, ya sakar mata wani shegen murmushin da kanne mata ido ɗaya ya ɗauke kai..........✍️


No comments

Powered by Blogger.