Daudar Gora Book 2 page 40


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (40)

..........A bala'i bala'in matsanancin tashin hankali Miran Arshaan ya nufi clinic, yaji daɗin samun Miran Jasim da ke tambayarsa lafiya ganinsa a firgice shi kaɗai. Maimakon amsa masa sai ca yay, “Kasa a sallameka da ga clinic ɗin nan a daren nan”. Cikin kallo

mamaki Miran Jasim ya ce, “Kamar ya nasa a sallameni, kai bakaga yanda shegen yaron nan nawa ya fasan kai ba. Ga wuyana tsabar yanda ya nema karyashi sai da aka samun wannan abun”. Ya kare maganar da nuni da abin wuyansa. Tsaki Miran Arshaan yayi yana ji kamar ya sake shaƙesa shima. “Shaƙar da Husam ya maka ba komai bace akan wacce ke tunkaro rayuwarka”. Ya ɗan ƙara waw-wai-gawa alamar gudun kar wani ya jisu. Cikin sake ƙasa da murya ya cigaba da faɗin, “Idan ka bari ka sake awa biyu anan nadamace ta har abada zata zama abokiyar rayuwarka in har ma matsiyacin yaron nan ya Barka da ran naka kenan”. Yana ƙare faɗa ya ficewarsa da ƴar sassarfa dan dama yay amfani da lokacin shiga sallar magrib da akayi ne......


         ★.... ★....


     Bayan idar da sallar isha'i koda ya nufi sashensa maimakon ƙarasawa ciki sashen Malikat Haseenat ya nufa ta ɓoyayyar hanya. Tayi sallamar wutiri kawai sai ganinsa tayi. Ba yau ya saba mata irin wannan zuwan ba na sirri, sai dai yafi yinsa a bayan sallar asuba. A nutse take dubansa bayan shafa addu'ar data taƙaita cike da kulawa. Shima sai ya taso a hankali da ga zaman ƙasaitar da yay a bakin gadonta ya dawo inda take kan lallausan carpet ɗin dake fes babu datti sai ma tashin ƙamshi da yake da ɗaukar ido na sabunta. Ga taushi matuƙa da ko'a ido zaka iya fahimtar hakan. “Barka da dare Jadda-ti”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi ya na kaiwa kwance bisa carpet ɗin ya ɗaura kansa kan cinyarta ya wani lumshe idanunsa da a kallo ɗaya ta fahimci damuwar dake tattare da shi a cikinsu tama ƙaru fiye da ɗazun. Murmushi ta saki mai sanyi a ranta tana faɗin, (Yau kuma ƴan shagwaɓan ne a kusa haka), a zahiri kam hanunnta kawai ta ɗaura kan ƙyaƙyƙyawar baƙar sumar sa siɗik ta fara ɗan tausa masa kan kaɗan-kaɗan. Idanun ya sake lumshewa da ƙyau har yanajin barci-barci na ɗibarsa. Tsahon mintuna kusan uku sannan ta magantu cike da kulawa.

         “Waya taɓamin kai Niger?”.

     Shiru bai motsa ba har wasu sakanni. Kafin ya buɗe idanunsa da suka ɗan fara shanyewar barci a hankali. Sai kuma ya ɗan ɓata fuska yana ƙoƙarin kaudawa gefe. Riƙo fuskar tai cikin tafukan hanunnta tana murmushi da faɗin, “Oh oh  beautiful Hafidi na faɗamin kaji”.

         Idanunsa ya ɗan lumshe da jujjuya mata kansa kaɗan ya motsa lips ɗin da ƙyar da maganar nan nasa kamar ta dole, “Kawai ina son jin ɗuminki ne”.

     “Uhyim, ita kuma Hafida-ti na aka barta ita kaɗai”.

  Shiru yay kamar bazai tanka ba. Sai kuma ya yamutse fuskar daɗa duniya har cikin zuciyarsa ne ya wani kauda kai gefe, “Tanada hayaniya, gata da surutu”.

           Mi Malikat Haseenat zatai banda dariya. Cike da nutsuwarta da ƙasaita ta shiga yin abinta. Ta ce, “Wayyo ni kai kuma gashi baka son hayaniya da surutu. Nikam ai ta burgeni, gara ta koya maka hayaniyar tata da surutun ko zamu samu ka dinga amsa mana magana biyar cikin goma. Naji daɗin hakan, dan itace dai-dai da kai”. A yanda take maganar zaka san lallai tana matuƙar jin daɗin. Shima dai acan ƙasan ransa murmushi kawai yake, dan ya sake tabbatar da kakar tasa mafi soyuwa a ransa na matuƙar ƙaunar ƴar hayaniyarsa da gasken gaske. Dama shi baya shakku a kanta, dan duk abinda Malikat Haseenat ta so to da gaske tana sonshi ne har cikin rai, idan kuma ta nuna ƙi to da gaske take ƙin nasa. Kamar tasan abinda yake tattaunawa da zuciyarsa ta cigaba da shafa kansa har yanzu da sauran murmushin dariyar da tai akan fuskarta. “Eshaan da gaske ina son yarinyar nan har cikin raina batare dana san dalili ba nima. Halayyarta kuwa na tuna min wasu abubuwa masu yawa. Yarinyar nada shiga rai, sannan tana da ɓoyayyun abubuwan ban mamaki tattare da ita. Karo na uku kenan ina aikawa nemomin iyayenta batare da kowa ya sani ba amma ana tabbatar min wai basa gidansu, a binciken ƙarshe ne na samu cikakken bayanin dalilin barinsu gidan, nasaka an bibiyar min kakaninta a ƙauyensu da aka tabbatar min su suna nan amma sai suma aka taki rashin sa'a. Na fara jin tsoron kar wani a cikin masarautar nan ne ya shirya cutar da su, dan tabbas abinda ya faru tsakaninka da yarinyar nan aike ne.. Bazaka tabbatar da hakan ba sai ka kusanta kanka da ita, kusanci mafi girma da a yanzu shine babban mafarki na, ina fata kafin na bar duniya naga jininka, a koda yaushe kuma na ayyana hakan zuciyata hoton yarinyar nan take kawo min matsayin uwar ƴaƴanka”

      Yanda muryarta ke fita da sautin tabbatar da abinda ke zuciyarta ne ya saka shi ɗan buɗe idanu kaɗan yana kallonta, sai kuma ya tashi zaune shima a serious ɗin sa, shiru babu alamar zaice wani abu, ita har ta fidda rai ma da cewar tasa. Sai kuma a hankali taji sassanyar muryarsa ya ce, “Jaddah”.

      “Yes Niger”

   Ta amsa masa da kulawa. Kaifafan idanunsa masu nutsuwa da haske mai cika idanu da a yau launinsu ya ɗan surka ya zuba mata. Murya a can ƙasa maƙoshi da kamar an masa tilas ya jefa mata tambayar da ba ita tai tsammanin ji da ga garesa ba. 

         “Tambarin baƙi mai kamar tawadar ALLAH duk wani zuri'ar gidan nan ke da shi ko wasu ne a ciki?”.

    Yanzu kam kallonsa take da mamaki matuƙa da ya gaza ɓoyuwa har a kan fuskarta. “Ban san miye dalilinka na wannan tambayar ba, ko kake son sani. Faɗamin miya faru?”.

        Kansa ya girgiza mata alamar babu komai, sai kuma a hankali ya ce, “Ina son sani ne”.

      Sam zuciyarta bata aminta da haka kawai bane, sai dai bazata matsa da son ji ba dan yana da hujjar ƙin faɗar, idan yaso wataran da kansa zai sanar mata. “In dai daga zuri'ar Aliy Qutb (mahaifin kakanka Abdull-Majeed) ka fito wannan tambarin shike tabbatar da kai. Sai dai bawai haka kawai ake gane kai ɗan zuri'ar bane da'an gansa. Akwai ajiyayyun hujjoji da ke tabbatarwar domin ana haihuwar jariri bayan yanke masa cibiya shine abu na biyu da ake duba masa. Yin wannan tambari a jikin duk wani jinin ahalinku ya samo asaline a dalilin kakanku na huɗu da yake da shi, mahaifin Aliy Qutb kenan, shi kuma Aliy sai yazam bashi da shi lokacin da aka haifesa amma sauran yan uwansa na baya duk sukazo da shi, maƙiya sai suka riƙe wannan hujjar a lokacin da za'a naɗashi sarki suka shigo da wata magana mai ban tashin hankali data girgiza masarautar nan baki ɗaya, har sai da ta kai anbi diddigin jinin Aliy da mahaifinsa. Wannan al'amari shi kuma sai ya riƙesa, bayan hawansa mulki duk wanda aka bincika bashi da tambarin sai an masa da wata alama da ke tabbatar da a cikin masarauta aka masa da hujjojin masu ƙarfi a rubuce. Idan aka haifi jariri kuma bayan yankan cibi shine abu na biyu da ake masa idan har babu shi...”

        Idanunsa da ya zuba mata tun fara maganar ya ɗan motsa kaɗan zuciyarsa na wani irin bugu da sauri-sauri. Amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar a wane yanayi ya ke ba. Murya acan ƙasan maƙoshi ya sake furta, “An cigaba da samun masu tambarin da yawa ne? Ko wanda akai mawa ne suka fi rinjaye bayan farawar?”.

            Shiru na wasu sakkani Malikat Haseenat batace komai ba, sai kuma taja ajiyar zuciya. “I to ni dai a yanda na samu labari a ɗan binciken tarihi wani lokaci akan samu yawaytar masu shi, wani lokacin kuma sai kaga anata haihuwar marasa shi, al'amarin kamar yana tafiya a ƙarni-ƙarni ne, amma kaga tashi kaga”.

     Babu musu ya miƙe kamar yanda ta buƙata, da taimakonsa ta hau wheelchair ɗinta, kai tsaye inda ƙaton hoton kakansa Tajwar Abdul-majeed ke manne kamar ka masa magana ya amsa ta nufa. Yatsanta manuniya ta kai a saitin fuskar hoton ta shafa, zuuu ƙaton frame ɗin hoton ya shiga wani naɗe kansa kamar ana naɗe tabarma da ga sama yayo ƙasa. Ƙofa ce ta bayyana, bai wani nuna mamaki ba dan ya riga yasan da kofar nan tun ba yanzu ba, dan shi wannan sashe da Malikat Haseenat ke rayuwa yanzu a ciki asalinsa sashen kakansa ne Tajwar Abdul-majeed, shiyyasa akwai sorrika masu yawa a cikinsa da ita kaɗai tasan da su sai wanda kuma taso ya sani. Da taimakonshi ta shiga yana biye da ita a baya. Ɗakine madaidaici mai ɗauke da tarin littattafai kala-kala. Gurin yayi ƴar ƙura alamar bawani shigarsa ake akai-akai ba. Kekenta ta wulwula zuwa bangaren arewa tana bin jerin manya-manyan littattafan wajen da kallo, shi dai yana tsaye da ga tsakkiyar ɗakin yana binta da kallo a ƙasaitance. Juyowa tai ta yafitoshi da hannu, cikin takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufeta. Littatafai biyu masu girma da tudu sosai-sosai ta nuna masa. “Ciro min su”. Hannu ya kai a hankali yana ɗan yamutse fuska ya cirosu, duk sunyi ƙura, amsa sai ta shiga karkaɗesu, yanda ƙurar ke tashi sama ya sashi ja da baya har sai da ta kammala. Ƙara yafitosa tai da hannu ya sake dawowa gabanta, ta kamo tattausan hanunsa cikin nata ta ɗaura masa littattafan. “Wannan zasu taimaka maka samun duk amsar da kake nema, duk wanda ke cikin zuri'ar nan da aka haifa da tambarin ko akai masa akwai bayaninsa anan. Ka kula da ƙyau suna da muhimmancin da ba kowa yasan inda suke ba a cikin wannan masarautar”.

       Kai ya jinjina mata yana lumshe idanunsa da buɗewa a kanta......


    ★★......


     Taso share umarninsa na ta samesa bayan sallar isha'in amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Sai ma ta samu kanta da yin sabon wanka da canja kayan jikinta zuwa wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai laushi da santsi kalar fari da akaima adon manyan fulawa da golden mai ɗaukar idanu, ga stones taji farare da duk inda ta motsa sai sunyi ƙyalli kamar wani diamond. Samun kanta tai da nutsuwar naɗa veil ɗin ya zauna ɗam a kanta har wani ɗan gashi siriri data zubo ta gaban goshin na reto a fuskarta. Tayi ƙyau matuƙa, dan ko maƙiyinta sai yaji ta burgesa kasancewar Iffah yarinya ce mai shiga rai, ga ta ƙyaƙyƙyawa komai nata dai-dai da ita. Yau dai har an ɗauki turarurrukansa za'a bulbula sai kuma aka fasa. A cikin wanda tai shopping akai amfani da su, sai kuma aka koma dai aka saka nasan ƙaɗan. Yanda tayi haɗin sai ya bada wani irin ƙamshi mai sirrin da ko shi mai gayya mai aikin da wahala ya iya gane ainahin nasa ƙamshin. Taku take a nutsenta kamar wata ƴar wahainiya. Bedroom ɗin jiya ta nufa dan tafi tunanin samunsa a can duk da bata da tabbas.........✍️

No comments

Powered by Blogger.