Daudar Gora Book 2 page 35

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (35)

.........Karan sigarin hannunsa ya ajiye a ƙyakykyawan ƙaramin bowl ɗin gabansa na glass “Ya akai banyi wannan tunanin ba, ya ALLAH”. Yay maganar yana miƙewa hannunsa duka kan sumarsa ya shiga cakuɗata. Shi dama akwai ruɗewa idan

abubuwa suka masa yawa. Harara Ameera Haifah ta balla masa tana faɗin, (Kai dama ai jaki ba komai kake fahimta ba, shegu biyu burina na cika na kawar da shegen yaron nan kuma bazaku sha ba ai, kubar ganin da taimakonku na shigo masarautar nan, bazaku sha da ga maidani abinda na za na yanzun). A zahiri kam sai ta saki murmushin yaudara. “Kaga zauna Shahan-shan ɗin gobe, kai daɗina da kai ruɗiyar masifa”.

      “Bazaki gane ba Haifah, duk yanda kike zato da tsammanin hatsabibanci shegen yaron nan ya wuce nan. Wlhy yace ubansa bai iya komai ba akan taurin kai da shegen kaifi”.

    “Duk kaifinsa da taurinsa mune ajalinsa shi da wannan ƴar iskar yarinyar mai bakin reza. Na rasa gidan ubanda suka samota sai kace ƴar ifiritan aljanu”. (Iffah 😂).

        “To dama micece inba ƴar ifiritan aljanun ba. Kina gani har yanzu iya bincikenmu mun gagara gano inda tsinannun mutanen nan suke. Wai mu Barrister Akeem zaici ma amana bayan mun yarda da shi”.

     “Nifa gaskiya bana tunanin haka, nasan waye Barrister Akeem batun yanzu ba, zaka tabbatar da yana da hujjar ɓoye kansa shima a duk randa ya bayyana kansa garemu. Ai tunda har ya bamu haɗin kan salwantar da iyalan Barrister Abdallah Aas da yake abokinsa dolene ya bada ƙafa. Kai dai mu cigaba da jiransa ɗin, Ni yanzu duk bama wannan ke gabana ba, wannan haukan yayan naka ne, sai kuma ita waccan kuna bibiyar lamarinta da gaske har yanzu shegen bakin nata na kulle dai ko?”.

        Nannauyan numfashi Miran Arshaan ya saki, “Boka Barbushi baya aiki ya warware sai in da kansa ya warwaresa, amma duk da haka Inaga zan jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya. Zan ziyarce a safiyar gobe da safe”.

    “Hakan ma yayi, ni bara na wuce dan naga asuba ma na gabatowa.” ɗan riƙota ya sakeyi yana wani ɗan murmushin da kai hancinsa jikinta, murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ki ɗan ƙaramin lokaci mana, kwana nawa bamma sakaki a idona ba”.

        Baki ta ɗan taɓe da janye jikinta tana cigaba da maida kayanta. Cike da muryar yaudara tace, “Nima ina kewar taka ai, sai dai lokacin barina nan ɗin yayi. Kaje ga wawuyar matarka can nasan ta kasa barci saboda kai ƴar wahalar”.

     Haka kawai sai yaji zuciyarsa ta ɗan sosu da zagin da akaima Jasrahn yau, duk da ba yau ne karo na farko da Ameera Haifah ke zaginta ba. Baice komai ba ya koma ya kwanta yana ƙoƙarin sake kunna karan sigari. Itama tsaf ta gama kimtsawa cikin kayan ɓadda kamarta, gabansa tazo ta ɗan kamo hanunsa mai riƙe da sigarin ta zuƙa, a fuskarsa ta bulbula hayaƙin, hannu ya kai zai cafkota ta zille tana ƴar dariya ta fice....


     (Humm, na san dai masu karatu basu mance wacece Ameera Haifah ba. Itace amaryar Tajwar Haysam mahaifin Tajwar Eshaan kenan. Bari na baku a buɗe. Ameera Haifah dai itace su Miran Arshaan ke yawan ambata da matar nan. Sun santa ko nace Miran Jasim ya santa tun kafin ta shigo masarautar. Dan karuwarsa ce, ko nace shine ya maidata karuwar🤦 . Dan da farko tazo neman taimakonsa ne ya shige mata gaba ta auri mahaifin Tajwar Eshaan marigayi Tajwar Haysam kenan saboda sonsa da take na masifa. Ita kuma ɗiyar wani shahararren mai kuɗi ne Anwarus-sadat, ƴar gata ce ta gaske a gidansu, ta fara son Tajwar Haysam ne lokacin data rako mahaifinta sukai masa gaisuwar salla. Tunda ta gansa ta rikice itafa sai shi, shiko bai taɓa bi takanta ba, a wajen mahaifinta ta amshi number sa, ta dinga takura masa da sakwanni shiko ya share. Iya haukacewa tayi kansa har mahaifinta ya tunkari Tajwar Haysam a lokacin amma ya bashi haƙuri kasancewar Ameera Haifah bata wuce sa'ar Tajwar Eshaan ba ma, acewarsa tayi ƙarama a duk cikin matansa, dan ko Ameera Danish-Ara ta girmeta sosai. Kamar ta haƙura sai kuma ta kasa a wata haɗuwa da sukai da Miran Jasim cikin jirgi, shi da ya ganta sonta yake a lokacin, sai dai kuma ita kafin ya furta sai tazo masa da batun yayansa, wannan abu yay masa zafi, amma da yake shegen kansa ne sai yay mata alƙawarin mallakar Tajwar Haysam amma ta yarda da shi. Masifaffen son ganin ta zama matar Shahan-shan Haysam ya sata amincewa. Kasancewarta ƴar gata babu ƙwaɓa a cikin gidansu ya fara lalata mata rayuwa. Tun kamar za'ai ɗaya a haƙura har ya maidata kamar wata matarsa😭, sai dai da ga ƙarshe yaci nasarar cika mata burinta na zama matar Shahan-shan Haysam da taimakon Miran Arshaan daya shige gaba wajen Malikat Haseenat kasancewar shi ɗan ɗakinta ne. Tunda Ameera Haifah ta auri Tajwar Haysam bata sake yarda da Miran Jasim ba duk da yana mata nacin hakan, ga shi kuma taƙi samun soyayyar Tajwar Haysam shi kuma, baya wulaƙantata amma kuma babu ruwansa da ita, dan takai kusan wata bakwai kafin ya yarda ya kusanceta dan gudun kar UBANGIJI ya kamashi da laifin tauye mata hakki. Duk matansa babu wadda bata kawo masa mutuncinta ba, hakan ya bada gudunmawar jin ya ƙara tsanar Ameera Haifah saboda yanda ya sameta. Da ga nan fa ya tattarata ya watsar ko kallo bata ishesa ba. Itako tarayya da ita da yay sau ɗayan nan taji ta sake haukacewa a kansa. Zamansu sam babu daɗi a tsahon shekara bakwai da suka kasance tare, dan sai tayi da gaske yake haɗa shimfiɗa da ita. Farin ciki kam babu tsakaninsu, dan ko murmushi sai dai taga yanayi amma ba ita ba har ALLAH ya ɗauke abinsa. Bayan barinsa duniya ta koma cikinsu Miran Arshaan a dalilin jin sirrinsu da tayi, a nan ne itama take sanar da su burinta na rama duk abinda Tajwar Haysam yay mata akan Tajwar Eshaan. Daga nanne kuma Miran Jasim ya koma nemanta, a ɓoye kuma tana tarayya da Miran Arshaan shima. Wannan kenan ALLAH yasa dai kun gane dan nidai na zayyano babu ruwana🥱).


      ★... MALIKAT BUSHIRAT ★....


   Tunda ta shigo sashen nata ta zube tama kasa motsawa. Babu abinda ke mata zuwa da dawowa sai fuskar yarinyar da abinda ta gano a cikin idanunta. Tabbas anzo wajen, kuma lallai anzo gaɓar. Gaɓar da a farko ba ita tai hasashen zuwa ba. Wai ita, ita Malikat Bushirat, mahaifiyar Shahan-shan mai mulkin karagar ikon ƙasar ruman baki ɗaya, yarinya ƙarama, ƴar talakawa ta kalla tsabar idanunta, ta sanar mata _inma ta kasheta ta kashe maciji ne bata sare kansa ba, ko bata numfashi, ruhinta zai dawo bibiyar fansar ruhin ƴan uwanta_. Kai kai kai, wannan wace irin rana ce, wace rana ce haka tazo gareta? Itace fa, ita ɗin nan dai, tauraruwar taurari, farin wata fitilar samaniya, rana mai rabama kowa aiki, taiku mai ruwan ban mamaki, zakanyar da ba'ai mata wargi, buhun ƙayar da ba'ai masa danni, mace mai kamar maza kwarine babu. Bahun barkono ba'ai masa shiƙa. Kokino ba giyar yaro ba sai dai manya karami yasha ya kwana a jeji. Giwa taku da ga nesa isharar yara, ƙarfe baka karyuwa sai da wuta, MALIKAT matar Shahan-shan uwar Shahan-shan ƴar asali jinin asali. Takai zaune daɓas jin hajijiya na neman zubar da ita. A hankali ɗakin ya shiga juya mata, sai kawai ta lumshe idanun ko hakan zai bata salamar da take buƙata.....



         ★★.. SHAHAN-SHAN ★★...


   Bayan ta gama zayyane masa birkitattun zantukanta guduwa tai tabar ɗakin, har yayi yinƙurin bin bayanta ya fasa. Amma ko sau ɗaya bai rintsa ba, saboda yanda kalaman nata masu tsananin saka ruɗani ke masa kai kawo. Zai iya rantsuwar wani mahaluki bai taɓa bashi tsoro na gaskiya ba kamarta, tabbas yana buƙatar sake sanin ainahin wacece yarinyar nan bayan sanin da ta sanar masa a baya. A hankali tambarin nan ya sake masa flash a cikin idanunsa, tare da kalamanta akan bashi madara da cewar ita ke amfani da su ba sukeyi da ita ba, ita ta kawo kanta nan bashi ya kawota ba, sai kawai yaji zuciyarsa na wani irin rawa, ga kansa da ke masa sarawar ciwo tun a dare da ta barsa.

      Da ƙyar ya iya ajiye komai a gefe ya tashi zuwa bathroom, sai da ya fara wanka sannan ya fito yay nafila ya ƙarasa da shirin fita massalaci.


    ★....

   

  Saɓanin shi kaɗan ita Iffah tana baro ɗakin zubewa tai a inda ta shigo sai barci, takai tsahon awa uku tana barcin kafin ta farka a firgice. Ta jiƙe sharkaf da zufa bata wasa ba, ga mummunan mafarkin da tai na mata matuƙar kai kawo, dole ta dangantashi da mummuna, dan yau ne karo na farko data farayinsa. Addu'a ta shigayi kamar yanda kaka ya gargaɗeta a duk sanda tai irin mafarkin, sai da ta samu ƴar nutsuwa sannan ta miƙe. Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta, tsaye tai a gaban mirror tana kallon kanta, sai ta dinga hango kamar duhu-duhu ta bayanta, babu alamar zata tsorata, sai ma sake ƙurama mirror ɗin ido tayi, amma a ranta addu'oi take karantawa. Dishi-dishin ta cigaba da kallon abun, sai kuma ya shiga bajewa kamar wani hayaƙi ya fara ɓacewa. Juyowa tai a hankali, abin mamaki sai ko gashi a zahiri hayaƙin yana bajewa cikin ƴan sakkani ya ƙarasa ɓacewa ɓat. Ajiyar zuciya mai nauyi ta ja ta fesar, cikin halin ko'in kila kuma sai ta ɗage kafaɗa da sake juyawa ga mirror ɗin tana kai hanunta ta baya ta ɗan shafo gefen kafaɗarta ta dama, zuciyarta na raya mata ta ɗaga rigar ta gani, wata kuma na ture mata tunanin da cewar mafarki fa ba gaskiya bane. Rashin matsaya ya sata ajiye komai gefe ta ɗaura alwala ta fito. Nafila tayi kusan awa ɗaya harda karatun Alkur'ani duk da batai mai yawa ba ta koma gado ta kwanta. Maimakon barci sai abinda ya faru tsakaninta da Malikat Bushirat ɗazun ya shiga dawo mata a rai, tasan ta shaƙeta, bata tashi tsintar kanta ba sai a jikin Shahan-shan tana haɓo. Ya taimaketa ya tsaya har tai wanka ya bata kayansa ta saka ya bata shayi, da ga shan shayin ne bata tashi tsintar kantaba sai yanzu a ɗakin nan da ta farka da ga mummunan mafarkin nan. Ya akai ta shanye shayin daya bata da yanda tazo nan ɗakin bata sani ba..........✍️



     _🚴Tofa wata jiƙaƙƙiya, Shahan-shan kayi takanka Iffah dai da alama ba.... (🥱Bara dai na gimtse bakina)_


No comments

Powered by Blogger.