Daudar Gora Book 2 page 32
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (32)
.........Fitowarta kenan a wanka tana ƙoƙarin shirin barci dan sanyi-sanyin da garin ya ɗauka yasa tuni masarautar tai wani irin yin tsitt, duk da bawani dare ne yay ba. A bazata wayar landline ɗin ɗakin ta fara bada sautin dake nuna alamar kira ya shigo. Kamar wata mai son rarrabe gaskiyar hakan ko akasinta
ta tsaya tana kallon wayar harta yanke. Wani kiranne ya sake shigowa. Da ƙyar ta iya saita kanta ta kai hannu ta ɗauka tare da kaiwa kunne tai shiru. Daga can ma shiru akai babu alamar za'a tanka har na wasu sakkani da suka kusa haɗa minti ɗaya. Cikin ɗan yanayin ƙufula-kufula da ƙosawa tace, “ALLAH zan yanke dan inada abinyi”.Ba'a tanka ɗin ba, sai dai kuma taji kamar alamar an ɗan motsa da ga can. bata fahimci motsin na miye ba, sai taji ta ƙara hawa sama. “Na kashe ne?”. Ta sake faɗa a ƙufule.
(Fitinanniya komai masifa) ya faɗa a zuciyarsa yana ɗan sakin wani murmushin da shi da babu duk ɗaya, dan sai ma mai tsananin saka ido ne zai tabbatar da yayi. “Ki sameni a room 2. Idan kika ɓatamin lokaci kuma hummm...” Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi batare da ya ƙarasa ba dai-dai tana shirin katse kiran.
“Ya arrahaman Iffah kin kaɗe”. Ta faɗa a fili cikin waro ido tana sauke wayar da tunanin ya yanke. Sai dai sarai ya jita. Safa da marwa ta shiga yi kamar wata wadda ke'a cikin tashin hankalin rayuwa. Ita gaba ɗaya ma ta rasa mima take ji akan al'amurin ta na yanzu da bawan ALLAHn nan. Tsoro ne ko miye?. Itace fa Iffah ɗin nan maijin zata iya tunkarar kowa akan gaskiyarta. Mai ikirarin tabbatar da ɗaukar fansar ƴan uwanta kansa. Mai jin zata fuskancesa fuska da fuska batare da taji zata iya masa ragi a duk abinda ta shiryo masa ba. Sai gashi tun ba'aje ko'ina ba lissafinta ya rikice. Abubuwa suna neman canja kansu a canjin data kasa fahimta. Gargaɗinsa na ƙarshen umarni ya fara maimaita kansa cikin kunenta. Birki taja da ga kaikawon, fahimtar halinsa data farayi na in har ya faɗa sai ya cika ya sata saurin neman kaya ta saka a gurguje. Abaya ce mai matuƙar ƙyau red and black data haska farar fatarta sosai. Ita kanta bata san kiyasa sai da ta zaɓo ba kafin tasa duk da kayan barci tai niyyar sakawa da farkoa. Ga wani uban ƙamshin turarrukan sa data baza tare da wanda aka kawo mata cikin kayan online shopping ɗinta da tun ɗazun suka iso, kayan sunfa yi ƙyau babu na kushewa, amma kuma fa an ciri uban kuɗi da har sai da ta razana daga baya. Dan hakama yanzu duk takeji ta rikice da tunanin koma kuɗin data kashe masa ne zai mata faɗa a kai, ita wlhy bata san da gaske kuɗin kayan da suka rubuta a jikin kowanne zasu iya cirewan ba fa.
Taku take a hankali kamar mai sanɗa ko wata budurwar hawainiya, babu abinda zuciyarta keyi sai dukan tamanin-tamanin. Idan yace ta biyasa kudinsa itako batama san yaya zatayi ba. Da ƙyar ta gano room two ɗin duk da bedrooms ɗin biyar ne kawai take tunani a wajen. Sauran ƙofofin bazata iya tabbatar dana minene ba tunda ba kowacce karambaninta ya taɓa kaita taɓawa ba bayan ta Gym a ɗazun. Taja wasu mintuna uku masu ƙyau a ƙofar kafin tai ƙundun balar ɗaura hanunnta a handle ɗin ta murɗa. Da sallama ciki-ciki ta shigo ɗakin da babu wani haske sosai, sai wani uban ƙamshi mai ratsa kwanya da uban sanyin ac kamar ba sanyi ake a garin ba. Hannunta na dama ta ɗan kai kan kafaɗarta ta haggu tana shafawa alamar sanyin ya ratsata. Can ta hangosa cikin ƙyaƙyƙyawar kujerar da ke gefe guda biyu, yana sanye cikin kayan barci farare tas da sukai masa ƙyau sosai, yanda hannun rigar ya kamashi sai ya fiddo murɗaɗɗen damtsensa da a kallo ɗaya zaka san yana samun isasshen motsa jiki. Lap-top ce a gabansa yana sarrafawa cike da ƙwarewa, sai butar shayi mai ƙyau da ƙaramin kofin da ke tabbatar da sha yake yi. Duk da motsin buɗe ƙofar tata da uban ƙamshin turarensa data bulbula ya zo hancinsa bai ko motsa ba balle ya nuna alamar yasan da zuwanta, aikinsa yake hankali kwance.
Idanunta data zuba masa ta janye, a karo na farko ta fara jin tana son sanin wai mi yake yi a laptop da a koda yaushe zaka gansa yana sarrafawa. Ko waya takan daɗe bata ganta a hannunsa ba. Amma computer in har yana zaune to baka rabashi da ita. Ganin har tazo gaf da inda yake bai nuna alamar yaji shigowarta ba tai tunanin ko bai jitan bane. Sallamar ta sake maimaitawa ƙasa-ƙasa. Idanu ya ɗan lumshe kaɗan ya sake buɗewa saboda yanda sassanyar muryarta ta wani ratsashi. Da ƙyar ya iya danne abinda ke taso masa ya buɗe idanun akan lap-top ɗin ya cigaba da aikinsa batare da ya motsa ɗin ba dai. Haushi ne ya kama Iffah a karo na farko, ta san dai in har baiji sallamar farko ba babu yanda za'ai ace baiji ta yanzu ba. Idanunta ta juya kamar zata ɓalla masa harara dan takaici, amma bazata iya ba, sai kuma tai tunanin koma ta juya ta koma, nan ma tasan ko giyar kokino ta sha bazata iya hakan ba dai. Tsaiwar ta cigaba da yi batare data sake motsawa ba itama, sai bin ɗakin dai take da kallo. Duka bedroom ɗin data taɓa shiga a sashen nasa tasan sun haɗu matuƙa, sai dai fa wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Dan kamar ma duk yafi waɗancan girma. Ƙatone na gaske, bayan katafaren gadon da zai iya cinye mutane goma tsaf akwai wadrobe na glass kamar yanda gadon ma take ganin kamar glass ɗinne. Hakama mirror da duk sauran tarkacen furnitures ɗin sun haɗu. Sai wasu rukunin haɗaɗɗun kujeru suma pitch and gold ɗin kamar yanda gadon yake... Kai ita fa idan tace ma zata cigaba da lissafi sai ta gaji, kawai dai ɗakin ya haɗu, komai na cikinsa pitch and golden ne da suka dace da kansu.....
“Kin koma soja ne?”.
Nutsatstsiyar muryarsa mai cike da kamewa da ƙasaita ta ratsa kunnuwanta a bazata. Kallonsa tai tana tunzura baki na haushi, yana a yanda yake tunda ta shigo, ɗan latsin ashe yasan da shigowar tata. A zahiri kam cikin muryar shagwaɓa-shagwaɓa haushi-haushi ta ce, “To ai ba'a bani wajen zaman ba”.
Shiru kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ɗago kamar wani mai ciwon wuya ya sauke idanun nasa masu haske da kaifi a kanta. Ƙasa tai da nata fuskarta har yanzu a ɗan shagwaɓe, bata sake gigin ɗagowa ba sum-sum taje kujerar gabansa ta zauna tai gefe da fuska. Ɗauke idanunsa kawai yay da ga kanta ya cigaba da abinda yake yi, sai da ya sake kwashe wasu cikakkun mintuna huɗun sannan ya ɗago a hankali yana ɗan firzar da iska. Ɗahowar tasa sai tai dai-dai da fara ring na landline ɗin gefensa. Ganin yay kamar baiji wayar ba ta ɗago ta kallesa, bashi da niyyar ɗaga wayar har ta tsinke, sai da a kira na biyu ya kai hannu ya ɗauka. Bayansa ya kwantar a jikin kujerar da kai wayar kunnensa yana lumshe ido. Maimakon amintaccensa da yay tunanin ji sai yaji muryar Malikat Bushirat tana sanar masa gata a falonsa.. kansa ya jinjina tamkar yana a gabanta, sai kuma ya buɗe baki da ƙyar yace, “To”. Daga haka ya miƙe yana kallon Iffah da ke binsa da kallo. “Muje” ya faɗa a taƙaice nan ma. Bata da zaɓin da ya wuce bin umarninsa, bakuma tada hurumin tambayar ina zasuje ko miya faru. Ta ɗaga kafa kawai a bazata taji lallausan hannunsa cikin nata, da sauri ta ɗago ta dubesa, sai dai shi sam bama ita ɗin ya ke kallo ba.
Suna kusantar falon bugun zuciyarta na ƙara hauhawa. Da masifar sauri taja wani irin bahagon burki lokacin da suke ƙarasowa tsakkiyar falon tai ido biyu da Malikat Bushirat da ke zaune hakimce fuskar nan tata babu alamar ta taɓa sanin minene ma murmushi a duniya. Hannun nata ta zare a cikin nasa ta fara ja da baya-baya, cak ya tsaya a wajen tamkar wanda aka dasa, sai kuma ya basar batare da ya ko waiwaya ba ya cigaba da tafiyar nan tasa ta ƙasaita.
Da sauri Malikat Bushirat da sam bata lura da Iffah ba ta miƙe, kafin ya ƙarasa isowa inda take ita ta miƙe zuwa garesa ta wani rungumesa. Idanunsa ya lumshe a hankali da sakin sassanyar ajiyar zuciya, dan abune da ya jima yana buƙata amma bai samu ba. Kusan sakan ashirin tana rungume da shi kafin ta ɗagoshi tana share hawaye, kallonsa ta ke cike da son tabbatar da babu abinda ya taɓa mata shi, dan duk duniya babu abinda take so da ƙauna sama da shi. Tana masa wani irin makahon so da ya zarta hankalin duk wani mai tunani...
“Ammie”.
Ya faɗa a hankali yana riƙo hanunta cikin nashi. Ɗayan kuma ya kaisa kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta ya share mata hawaye hankalinsa duk a tashe, dan ganin hawaye a fuskar Ammien sa abune da bazai kasance ƙarami ba. Ya santa ya san mahaifiyarsa jaruma ce da ko'a cikin dubu zai faɗa babu wani ɗar.
Sake rungumesa tai tana magana cikin ɗacin murya. “Wlhy da yau wani abu ya sameka kamar wancan karon babu abinda zai hanani ɗaukar mataki akan koma wanene, dan bazan yafe musu ba, na baya ma ba yafe musu nai ba Eshaan” sai kuma ta sake ɗagosa da sauri, takarda da biron data ajiye a kujerar data zauna ta ɗauka, ta kamo hanunsa shi dai yana binta da kallo, a cikin tafin hannun ta saka masa, babu alamar wasa ko sassauci akan fuskarta ta furta, “A matsayina na UWA mahaifiya a gareka bin Haysam Abdul-majeed, ina baka umarnin ka saki yarinyar nan, ka kuma janye duk wata garkuwar da kai mata...”
Wani irin mummunan bugun zuciya mai kaɗawa da tashin hankali da bai taɓa cin karo da shi ba a rayuwarsa yaji yana taso masa, amma yay jarumtar shanye komai ya zubamata idanunsa a dake. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, kamata yay ya zaunar a kujerar data taso, kafin shima ya kai zaune gefenta a hankali dan ji yake hajijiya na neman zubdashi ƙasa. Amma kasancewarsa gwanin kamewa ko'a fuska bazaka taɓa tantance komai da ga garesa ba..........✍️
Leave a Comment