Daudar Gora Book 2 page 29

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (29)


.........Bayan kamar mintuna ashirin da tafiyar Iffah sannan shima ya mike, zuwa lokacin ruwan ya tsagaita sai ɗan yaf-yaf da akeyi ga garin ya ɗauki wani irin sanyi mai ratsa ɓargon jiki. A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe a kan sararin samaniya da tai wani irin fayau, ga garin yay luf-luf ƙamshin ƙasa na ratsa hancinan mutane. A kan lips ya shiga furta addu'ar nan ta bayan saukar ruwan sama.

         *مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ.*

_Mutirna bifadlil-lahi warahmatih._

    (An yi mana ruwa saboda falalar ALLAH da Rahamarsa).

     Kafin ya cigaba da tafiya cikin takun nan nasa na ƙasaita da izza tamkar mai irga steps....

         ★★..... 


   Tunda ta dawo ɗakin kaikawo kawai take faman yi hankali a tashe. Duk nacin son sanin wanene Ajmaal ɗin da takeyi bata kawo a ranta zai zama shi ɗin ne ba. Tunaninta kawai ya kama Ajmaal ɗin ne kodai wani abu da ba shi take zato ba yana mata yawo da hankali ne. Ji take komai ya kwance mata, komai ya ƙare mata. Ta sadaƙar dan tata ta riga ta ƙare kawai. Yaya akai hakan ta kasance, yanzu komai daya wakana tsakaninta da Ajmaal da Shahan-shan ɗin ne kenan? Kai ina impossible, taya hakan zai kasance ma? Miyasa sir Fawzan zai mata hakane? Miyasa? Miyasa ya rabbi shike nan ita kam.

        Yanda take yi dolene ya baka tausayi da dariya. Ƙululu taji cikinta ya murɗa kamar mai jin gudawa. Ta kai hannu ta matse cikin ƙirjinta kamar zai tarwatse dan tashin hankali da tsabar ruɗanin da take ciki.....

          “Nace na gama da ke ne?”.

     A wani irin haukace ta ɗago ta kalla ƙofar jin sassanyar muryarsa bazata a cikin kunneta, shi ɗinne dai tsaye hannayensa duka cikin aljihun wandon jikinsa. Sam bataji shigowarsa ba, koda yake a buɗe tabar ƙofar tsabar ruɗani. Tafiya ta farayi da baya-baya, jin zata ma iya sakin gudawar a wajen sai kawai ta sake kwasa da gudu tai hanyar toilet.


       Ta ɗauki tsawon mintunan da zuciyarta ke faɗa mata ƙilama ya gaji ya fita, sai dai wani sashe na gargaɗinta. Jin an fara kiran sallar azhar ta sauke ajiyar zuciya, ta san dai tabbas dolene ya fita ai yanzu. Alwala tayi, kai tsaye ta fito tana ayyanama ranta ta saka ma ƙofar key kawai. Da sauri taja birki ganinsa zaune a harɗe cikin zaman ƙasaitar nan tasa a saman kujerar ɗakin, sai kuma ta juya da sauri zata koma dan yayi wani ɗam-ɗam da fuska.

     “Zaki sha mamaki idan kika koma”.

     Kamar zata fasa ihu ta dubesa, sai kuma ta ɗauke kanta ƙwalla na cika idonta. (Shikenan Iffah kekam sai abinda ALLAH yayi, gaki dama ba uwa ba uba miya rage kuma? Kawai yasa a tsireki) a zuciyarta take sambatun tana cigaba da takowa sum-suma batare data yarda ta sake kallonsa ba. Miƙewa yay shima fuskar nan babu alamar fara'a, idonsa a kanta. A gabanta ya tsaya mayen ƙamshin turarensa na cigaba da addabarta, ga mamakin yanda yake abubuwa kamar ba Shahan-shan ɗin nan nasu da suke hange da ga nesa ba mai shegen isa da izza na ƙara bata mamaki da ɗaukar komai tamkar wani mafarki. Jinsa a kusa da ita sai kawai ta rumtse idanunta da ƙarfi tana jiran abinda zai biyo baya.

       “Na tafi?”.

    Ya faɗa a hankali yana wani shanye idanunsa ƙasa-ƙasa a kanta. Da wani irin sauri ta buɗe idanunta da ɗagowa ta kallesa tana sakin nannauyar ajiyar zuciya saboda shock da furicin nasa ya sakata. Sai kuma ta kaudar da kan gefe dan salon kallon nan nasa birkita ta yake. Muryarta can ƙasa-ƙasa ta jinjina masa kai.

      “Magana nake so”.

   Ya faɗa a fisge kamar wanda akaima tilas. Tsabar yanda take jin kusancin nasu kamar zata shiɗe a hankali ta ce, “Uhhm”. 

       Ɗan sake matsawa yay gareta dab har tana iya jin saukar numfashinsa a kan fuskarta. Jin saukar yatsunsa kan haɓarta ruf ta rufe idanunta da ƙoƙarin riƙe rawar da jikinta ke neman farayi. Ya ɗan lumshe idanunsa dake yawo akan fuskar tata yana ƙoƙarin shanye murmushin dake taso masa. A bazata kawai taji saukar lallausan lips ɗinsa saman goshinta ya manna mata sumba mai lafiya da har sai da ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi. Batare da ya sake cewa komai ba ya ja da baya ya juya ya bar ɗakin fuskarsa shimfiɗe da murmushin da duk sonshi da basar da shi hakan ya gagara. A ransa rayawa yake (Damisar takarda ga tsoro ga ban tsoro)

        Da kallo ta bishi har ya fice, ta sauke ajiyar zuciya da kaiwa zaune jagwab kamar wadda tasha gudu ta gaji, sai faman matse jikinta take waje guda amma yaƙi daina tsumar dole ta kai kwance na wani ɗan lokaci, badan taji ƙarfi ba dai ta miƙe tai sallar ganin lokaci zai shige....


            Duk yanda yaso dai-daita kansa hakan ya gagara. Tabbas ya yarda SO wani abune mai matuƙar kaifi. Duk yanda kaso ɓoyeshi da ƙin son bayyanashi hakan gagara yake. Duk matsayinka, duk girman shekarunka, sai ya kaika ƙasa. Shi shaida ne akan hakan, tunda gashi yana gani akan kansa. Gaba ɗaya idan yana a gaban mitsitsiyar yarinyar nan manta shi ɗin wanene ya ke da matsayinsa. Ya rasa wannan abu haka mai kama da kamar wata almara. A gurguje ya canja shiga da ɗaura alwala ya fita masallaci. Ya wani tsume kamar bashi ba, dan a Shahan-shan ɗin sa ya fita mai tsananin ƙasaita da izzar nan ga miskilancin tsiya.

         Bayan idar da salla bai shigo ba ya zarce fada, umarnin isar da saƙon tattaro masa wasu a cikin manyan masarautar ya bada. Cikin ƙanƙanin lokaci duk wanda sunansa ya fito a zaman saƙo ya riskesa. Kafin cikar wasu mintuna duk sun hallara. Duk da kasancewar yana a cikin fadar a wani matsakaicin falonsa yake zaune ba cikin ainahin fada inda karagar mulki take ba. Da ga shi sai amintaccen hadiminsa na amana da ako ina ka gansa shima zaka ganshi, idan ka cire ɗakin barcinsa kawai. Suma ɗin yana shiga kai abinda ake buƙata da kuma gyarawa.

        A zahiri zaka ɗauka hankalinsa kan television ɗin da ke aiki a falon suke, dan manyan kaifafan idanunsa na kanta ne. A gabansa ƙyaƙyƙyawar butar shayi ce irin ta hamshaƙan sarakai kalar golden mai tsananin ɗaukar idon mai kallo. Dan har wasu irin fararen stones aka jera jikinta da ya sake ƙayatar da ita. Sai dai hankalin nasa sam ba'a nan ɗin yake ba. Gaba ɗaya a tunanin zantukan Iffah ne na ɗazu. Dan shauƙin da yake ciki bawai ya mantar da shi bane ba. Ya dai tattarasu ne ya ajiye gefe domin basu nasu lokaci.

       Sallama Sayeed Fayzul-haq ta saka amintaccen Ghazi ɗinsa da ke gefensa tsaye ko gajiya bayayi amsawa. Sai kuma ya nufi ƙofar domin duba wanene. Shi dai bai motsa a yanda yake ba, kai kace ma bai san abinda ake ba. Minti ɗaya da wasu sakanni amintaccen nasa ya dawo, a gabansa ya zube murya cike da tsantsar girmamawa yace, “Kariyar UBANGIJI ta cigaba da kasancewa zagaye da adalin shugabanmu. Sayeed Fayzul-haq ne ke isar da saƙon kammalawar kasancewar kowa”.

        Shiru babu alamar zai tanka har kusan mintuna biyu, sai ka rantse baima jisa ba. Sai da ya mula dan kansa ya motsa lips da ƙyar. “Zasu iya shigowa”.

    “Umarninka shine abin jiran kowa”.

Hadimin ya faɗa yana rissinar da kai sannan ya miƙe da sauri. Cikin abinda bai fi minti uku ba dattijai masu cikakkiyar kamala da nutsuwa suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya a nutse. Duk wanda ya shigo sai ya miƙa gaisuwa kafin ya wuce ya zauna. Sayeed Fayzul-haq ne ƙarshe hannunsa ɗauke da ledar da aka zuba kayan surkullen nan. A gaban Tajwar Eshaan ɗin ya kai ya ajiye yana ɗan matsar da ƙyaƙyƙywar butar shayin nan kaɗan. Leda ɗin ya buɗe sannan ya ja da baya shima ya zauna.

      Yanzun ma sharewa yay tsahon wasu mintuna kamar bashine yasa a tarasu ba, kowa kuwa a cikinsu ya zubama ledar ido musamman Miran Arshaan da jikinsa har tsuma yake, sai dai yana ta faman taushe kansa. Tajwar Eshaan da ke nazartar kowa ta ƙasan ido ya motsa lips ɗinsa da ƙyar yana mai buɗe idanunsa masu saka mara gaskiya tsuma tar-tar a kansu da ƙyau. 

        “Bana bukatar sanin wanda ya ajiye su balle dalilin ajiye sun. Sai dai zan gargaɗi mai ajiyewar da abu uku. Eshaan a koda yaushe yana zagaye ne a cikin kariyar UBANGIJINSA insha ALLAHU. A komai na ina amfani da zuciya ne fiye da ƙwanji na da ƙwaƙwalwa. A kuma duk sanda maƙiyi ya sokeni ta baya sunansa matsoraci a wajena, jarumi gaba-da-gaba yake zuwa filin daga in har ya cika sunansa jarumi. Saboda haka, idan har ya shirya na bashi tabbaci ɗan Haysam bin Abdul-majeed Aliy Qutb a shirye yake shima”.

       A take falon gaba ɗaya ya ɗauka kalmar neman afuwa da fatan hucewar zuciya ga Shahan-shan. A baɗini kam baka jin komai sai bugun zuciyoyi, yayinda ake ma juna ƴar kallon kallo, dan ba ƙaramin ratsasu kausasan kalaman Tajwar Eshaan ɗin suke ba, duk da a zahiri shi ya yisu ne cikin sanyin nan nasa mai amon nutsuwa da cikakkiyar ƙasaitar tabbatar da shi ɗin wanene. 

       Ƙananun maganganu ne suka nema fara tashi kowa na ƙoƙarin son ganin ya kare kansa. Yi yay kamar bama jinsu ya ke ba, sai da Sayeed Fayzul-haq ya fargar da su sannan falon yay tsitt. Wani ɗan ƙyamusashen tsoho da suke kira Sayeed Tasadduq-Husain da fuskarsa ke nuna alamun ɓacin rai ya dubesu cikin ɗacin murya, a karo na farko da tun shigowarsa falon yay magana. Shima ɗin kamar Uncle ya ke a wajen Tajwar Eshaan, mutum ne mai tsananin tsage gaskiya a duk yanda tazo shiyyasa bai cika farin jini a wajen su ba, alokuta da dama idan yaga an dabaibaye rayuwar Tajwar Eshaan da yawa yakan nuna ɓacin ransa har ya faffaɗi maganganu masu ɗaci, to a yau ɗin ma tin ganin waɗan nan kayan sirkullen ɗazun ya nuna takaicinsa, hasalima shine ya ingiza Sayeed Fayzul-haq kan Tajwar Eshaan ya tarasu ayi maganar kar a wani rufe, gara wanda ya ajiye abubuwan ya san an san ya ajiye ɗin.........✍️


No comments

Powered by Blogger.