Daudar Gora Book 2 page 28


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (28)........Cak numfashinsa ya tsaya da ga kaikawon da yake a ƙirjinsa. Kalmar *_a matsayin MATARKA_* ɗin nan tafi kowacce matuƙar ratsasa har tsakkiyar kai fiye da komai data faɗa, duk da suma sauran kalaman nasa nada wani muhimmanci da nasu tasirin. Amma a zahiri bai ko motsa ba,

yana dai kallonta ne a ƙasan ido kamar ya samu wani television. Shiru na tsawon wasu sakanni kamar masu sauraren saukar ruwan saman, sai kuma ya ɗago kaifafan idanunsa dai-dai da ɗago nata itama, cikin kallon ido cikin ido da wata sarƙaƙaƙƙiyar muryar da fitarta bai canja taushin ainahin muryarsa mai sanyi da nutsuwa ba ya furta, “Mi kika sani game da ni? A bayan burin da kika shigo da shi masarauta ta?”. 

       Kamar bazata motsa ba sai kuma ta motsa lips ɗin ta a hankali. Daurewa tai bata nuna ko gezau ba, itama ta zuba nata idanun da yanayinsu ke wani irin canja kala-kala maisa tsigar jikinsa tashi cikin nasa da ƙyau. Tai ɗan murmushi mai sanyi da ya nema ɗauke fitar numfashinsa a baɗininsa, janyewa tai gefe kaɗan fuskarta har lokacin da murmushin, “Sanin wani abu game da kai abu ne mai wahalar gaske ga baƙon zaman wannan gidan. Sai dai kai da kanka ya kamata ka duƙufa sanin komai a kanka, idan kuma ka sani ka ke shanyewa ka tuna kai shugaba ne. Haƙƙoƙin biliyoyin mutane ne a ƙarƙashinka, idan ka tauye ɗaya da gangan sai ALLAH ya tambayeka koda da ƙwayar zarra ne, inaji a raina kai ba mutum bane irin mutanen da tunaninsu ke a takure waje guda, in har bakai kake aikata laifin da mafiya al'ummar ƙasar nan ke kallonka da shi ba na tabbata kasan masu aikata wasu a ciki koda kaɗan ne, dan inba haka ba banga dalilin da zaisa su dinga farautar rayuwarka ba irin haka a matsayinsu na makusantanka”. 

      (Ya arrahaman) ya faɗa a zuciyarsa. Karo na farko ana faɗa masa gaskiyar da kowa ke shakkar tunkararsa a kanta hatta da wanda suke sama da shi a shekaru. Amma gashi yarinya ƙaramar da a haihuwar kaji ya haifeta yau tana jaddada masa shi ɗin wanene. Tsarge masa komai take a yanda ya jima yana buƙatar ji daga bakin wani koda mahaifiyarsa ne. Magana mafi dukan zuciyarsa itace ta ƙarshe. Ana farautar rayuwarsa kuma makusantansa. Yes ya jima da sanin wasu a makusantan sa na bibiyar rayuwarsa, kuma mahaifinsa ya fargar da shi hakan tun yana raye, amma a yau sai yaji kalmar daga bakinta ta sake girma matuƙa garesa. Kallonta yake cikin ido a wani irin yanayin da ke neman sarƙe fitar numfashinsa. Muryarsa a wani irin sanyaye ya furta, “Sune suka baki guba ki bani?”.

        Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. (To Miya rage kuma? Ai bataga amfanin cigaba da ɓoye masa ba) dan haka kai tsaye kawai ta jinjina masa kanta. “Ni nasan baka buƙatar sai na maimaita komai, domin ban ɓoye komai a zamana gidan nan ga Ajmaal ba, hatta randa nake neman dafin macizai ido rufe na sanar masa, shiyyasa har yanzu zuciyata taƙi daina mamakin miyasa kasha madarar tunda har kaga saƙon kuma...”

        Wani murmushi ne ya nema suɓuce masa a hankali, sai dai bai yarda ya bayyana akan fuskarsa ba ya hadiye kayansa yana mai lumshe idanunsa da launinsu ya canja baki ɗaya. Kamar bazai tanka ba sai kuma ya sake buɗe idanunsa ya sauke a kanta cikin wani irin kasalallen kallo da ya tilastata rissinar da nata. 

     “A ranar banga saƙonki ba dan bana cikin ƙasar nan”.

           Ɗagowa tai da sauri ta dubesa. Idanunta a ware cikin rawar harshe ta ce, “Kamar ya baka cikin ƙasar nan? Bayan matarka an mata kisan gilla a tsakanin, hakama tsohon da kowa ke tabbatar da jayayyar da yay da kai ce tasa ka ɓaddashi. Kana nufin kuma da gaske kai ne Ajmaal ɗin dai?”. 

     Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sai kuma ya miƙe a nutse zuwa gabanta, binsa take ita dai da idanunta da ke a waje gaba ɗaya kamar zasu faɗo har ya kai zaune a kujerar kusa da ita. Zamansa ya maida kafa ɗaya kan ɗaya idanun nan nasa masu kaifi shanye a kanta. Itama ta kasa daina kallonsa, dan gaba ɗaya kamar a rikice ma take. “Duk matar da aka kawo Masarautar nan da sunan tawa ni ke kaɗai na taɓa gani da idanuna, babu wacce ta taɓa rasa ranta ina a cikin masarautar nan kuma. Zaki san Ajmaal kamar yanda kike buƙata domin ina son muyi aiki tare”. Ya ɗan yi murmushin da ya nema ɗauke duka numfashinta batare da ya jira amasawarta ba ya cigaba, “Ki ɗauka anan tare kike da Ajmaal ba Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba. Mi kike son sani?”.

      Da ƙyar ta iya haɗiye yawu da rawar jikinta, dan itakam kallon komai take kamar a mafarki. Hasalima ya ƙara birkitar mata da kai ne. Cikin rawar murya kamar mai in ina ta ce, “Cafa kai baka taɓa ganin fuskar su ba, suna mutuwa kuma baka cikin masarauta? Taya hankali zai ɗauki wannan maganar?”.

         “Ta yanda ya ɗauki zaman Tajwar Eshaan tare da ke anan babu wani shamaki mai shari'a”. Ya faɗa a hankali kamar ba daga shi kalaman suka fito ba. Yawu ta haɗiye da ƙyar tana ɗan tura baki jin ya kirata mai shari'a, sam zuciyarta tama ƙi yarda da wancan zancen nasa, “Ya akai ka zama abokin Sir Fawzan?”. Ta faɗa a hankali tamkar mai tsoron wani ya jita. Shiru babu alamar zai amsa mata idonsa na kallon ƙasa, dan dauriya kawai yake da surutun nan, da alama ita kuma kamar ma yanzu ya fara mata daɗi. Ya ɗan ja numfashi ya fesar a hankali, “A baɗini Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed abokin kowa ne a ƙasar ruman da sunan Ajmaal, dan haka shima Fawzan ya shigo ne kamar yanda kowa ke shigowa, a taƙaice dai na haɗu da shi ne a ƙasar Cuba, lokaci ina wani couse, abinda ya fara haɗamu so bawai sai an maimaita faɗarsa bane, kawai dai sanda nasan shi ɗan ƙasata ne naji farin ciki, na kuma nuna masa cewa nima asalina ɗan canne...”

      Yanda yake maganar da ɗaɗɗaya kuma kamar da ƙyar sai taji ya bata tausayi da dariya, ta daɗe da fahimtar magana abune mai wahalar gaske a gareshi. Kamar ko yasan mi take tunanin, sai gani tai ya miƙa mata waya yana ɗan murza goshinsa da ke sarawa. “Mu cigaba a rubuce kaina yana ciwo”.

       Dariya abun ya bata, tai murmushi idonta a kan wayar da yake miƙo matan. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa a zuciyarta tana faɗin (Miskilanci ma ai cuta ce gaskiya), a zahiri kam sai ta ɗan taɓe baki tana rubuta, “Miyasa randa na haɗu da kai a Eira garden ban ganku tare ba?, bayan kuma shi ya kirani ne dan na haɗu da Ajmaal?” ta mika masa wayar. Rubutun kawai ya tsirama ido harta fara ƙosawa, dan bashi da alamar zai bata amsa. Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya amsa a rubucen shima. “Dama banyi niyyar mu haɗun ba, dan ina son na fara sanin waye ke”.

    Sosai ta waro idanu tana kallonsa lokacin da ta gama karantawa. Bama ta san bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Saboda mi to?”. Shiru yay kawai ya tsira mata idanu, sai kuma ya ɗago a hankali ya zare wayar daga cikin hanunta. 

      “Saboda yamun bayanin manufarki da kai tsaye ni ta shafa batare da shima ya san hakan ba” ta karanta. Sake kallonsa tai mamaki na bayyana a fuskarta. Nan ɗin ma bakinta ne ya suɓuce wajen faɗin, “Anya mutumin nan bada saka hanunka aka kawoni gidan nan ba?”.

    Wani irin lumshe idanu yay cike da salo ya sake buɗewa a kanta, sai kuma ya saki wani makirin murmushi yana kauda kansa.

        “Ka amsa min Please”. 

    Ta faɗa tana matsowa karshen kujeran da ya maida zaman nasu gab har ƙafanta na gogan nashi. Nan ma babu alamar zai tanka matan tsahon wasu sakkani, kafin ya fiskanceta da kyau kaifafan idanunsa a kanta. “Idan na matso da makashina kusa da ni sai ya zama laifi?”.

       Zumbur ta miƙa tafukan hannayenta duk biyu akan fuskarta ta furta, “Ya arrahaman ka kasheni, wlhy ka gama dani. Na shiga uku ni Fhareedah wace irin MAKAUNIYAR ƘADDARA ce kuma wannan ɗin?”. Yanda take kaikawo da sambatun jikinta na rawa kaɗan ya rage ya kwashe da dariya. Amma ya danne da ƙyar, sai dai duk da haka sai da ya kauda kansa gefe yana murmushi. A mamakinsa sai yaji kawai ta fita a wajen da ɗan gudu-gudu. Sosai ya zaro idanunsa, sai kuma kawai ya saki murmushi mai faɗin da har haƙoransa na bayyana a bazata. Murmushin yake shi kaɗai yana faman kare baki idanunsa akan hanyar da tabi.....           ★★.....  ★....     A yanda hadiman leƙen asirin nata suka shigo yasa ta bama duk sauran hadiman dake zagaye da ita umarnin barinta. Jikkunansu har rawa suke suka fice, a yanda ta zuba musu ido yasa bama su tsaya wani jan jeni ba suka shiga sanar mata komai dan sun san bata buƙatar jan zance da tsaho.

      “ALLAH ya ƙara miki lafiya mai amfani uwargida shugabar matan wannan daula. A yau Malikat Bushirat ta baƙunci Uwar masu gida. A yanzu haka ma suna a garden ɗin ta tare har da Daneen...”

         Wani irin kallo take watsa musu da kai tsaye suka fahimci manufarta. Sake gurfana sukai a gabanta cike da girmamawa. “Kamar yanda ki ka fi buƙata mun kasance da su a wajen muma, duk da kaɗan ya rage Daneen ta ganemu”.

    Fuska ta yatsine alamar ba wannan take son ji ba. Fahimtar hakan ya sakasu cigaba da faɗin, “Sun tattauna abubuwa da yawa, sai dai gaba ɗaya a dunƙule sun ta'allaƙa ne a neman afuwar Uwar masu gida da Malikat tayi. Ta faɗi maganganu masu yawa itama na nuna fushi, sai dai da ga karshe ta sakko harta yafe mata abubuwan da suka farun da dorawa da bata shawara game da al'amarin Zawjata-almilk. Da ga ƙarshen zancen sun kuma dai ya ƙare akan son ƙarin auren Shugaban wannan daula....”

      A karan farko Malikat Ashwaq ta miƙe zaune sosai tana kallonsu. “Sai me ya faru?”. Ta faɗa kamar idanun nata zasu faɗo a kansu.

         “Babu alamar dai Uwar masu gida ta bada goyon baya, daga hakanne kuma Daneen ta fahimci motsin mu a wajen iyakar abinda muka ji kenan”.

       Hannu kawai ta ɗaga musu alamar suje. Suna ficewa itama ta miƙe, da ƴar sassarfa ta bar falon hutawar tata zuwa ɗakin barcinta mafi zama sirri gareta har kafafunta na neman harɗewa........✍️     _Tofa, Malikat Ashwaq yaya dai🥱🏃_


No comments

Powered by Blogger.