Daudar Gora Book 2 page 18

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (18)



.........A haka idanun nata suka kai garesa, zuba masa su tai a yanayin kallo na ƙasan ido, har ranta take jin bugun zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Ba yau ta fara ganinsa cikin ƙananan kaya ba idan yana sashensa a keɓe, amma sai taga yau ɗin kamar special ne. Baƙaƙen kayan sun masa ƙyau matuƙa da sake bayyana haskensa da ƙuruciyarsa kamar wani matashin saurayin da bai taɓa mallakar ko budurwa ba.

Tsantsar ƙasaita da izzar mulki dake yawo a jininsa na ƙara masa wani irin kwarjini mai cika ido da barazana. A hankali ta ƙara ƙasa da kanta jin kamar yana nufota. Gareta ɗin ko ya iso fuskar nan ɗam-ɗam babu alamar yasan minene murmushi ma balle a kai ga dariya. Mug ɗin hanunsa da keta faman tururi da tashin ƙamshin haɗaɗɗen shayi na musamman ya ajiye a side drawer ɗin batare da yayi magana ba. Shayin ta ɗan kalla da sake maida kallonta gareshi cike da mamaki, dan ya ajiye baice komai ba ya bar wajen, bathroom ya shige, ta ɗan lumshe idanu batare data iya cewa komai ba. Babu abinda take buƙata sama da shayin a yanzu, dan haka ta ɗauka ta fara sha lokaci-lokaci tana atshawa ɗin a wahalce da duban hanyar bathroom ɗin. Tsahon mintuna biyar sai gashi ya fito yana faman sake tsuke face. Da sauri ta ɗauke idonta kamar bata gansaba itama, ta ajiye mug ɗin hanunta data kammala shanye shayin da ya zuba matan tana yaye duvet ɗin da take a ciki jin zufa na karyo mata tako ina a jikinta. Yunkurin sakkowa take a gadon dai-dai yana isowa gab da ita, hakan yasa ta dakata da miƙewar ta ɗan dubesa ta kauda kai. Idanu ya tsura mata kamar mai tunanin ta yanda zaice wani abu, kusan minti ɗaya ya ɗan yamutsa fuska cikin motsa lips da ƙyar yace, “ki shiga ruwa a bath....” ya haɗiye sauran a maƙoshi batare da ya ƙarasa ba. Sake ɗago ido tai ta kallesa, ganin nasa idanun a kanta sai ta tura baki kawai ta kauda fuska gefe sai kace wata ƴar yarinya.

       (Taɓara) ya ayyana a zuciyarsa shima yana ɓata fuskar. Ƴan jin kanne yau a kusa, wanda dama ita su ta sani a zahiri. Bama ta taɓa kallonsa a jerin mutane masu sauƙi ba. Batare da sake cewa uffan ba kawai taji ya ɗan duƙo kanta, zabura tai baya, sai dai kafin tai wani yunƙuri ya ɗagata cak kamar wata ƴar baby. Yo akansa micece wata Iffah. Tsayayyen namiji ne fa ingarma da duban damtsen hannunsa kawai ya iya saka mai tsoro zawayi a wando. Baka gane hakan sai yana sanye da ƙananun kaya. Gaba ɗaya ta waro idanunta sai cikin nasa, da sauri taso kauda natan ya hana hakan ta hanyar sarƙesu. Sai kawai taji zafin zazzaɓinta na ƙaruwa ma...

      “Ni dai ka daina kallona”.

   Furucin ya fito cikin suɓutar baki tana laɓe fuska kamar zatai kuka, dan da gaske idanun nan nasa tsoro suke bata. Ta ɗan so bashi dariya, sai dai a zahirinsa babu ko alamar hakan sai ma sake tsuke face ɗin da yay bai kuma janye idanun nasa ba. Sai ma tafiya da ya farayi da ita a hankali. Rumtse nata ta samu nasarar yi da ƙarfi dan gaba ɗaya jikinta yamutsawa yake har zuciyarta na zallo a cikin ƙirji. Zabura tai da buɗe idanun nata a lokaci guda jinta cikin ruwa mai ɗumi sosai. Taja ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo Ummuna”.

       Bai kulata ba ya ida ajiyeta a ruwan dake ta faman tashin ƙamshi na masifa, ga wani ɗumi mai ratsa ƙashi da ɓargo. Fuska a ƙwaɓe take duban kanta da yanda ya sakata ita da kayan gaba ɗaya cikin ruwan. Sai taji kamarma ta saki kuka kawai ta huta. Wannan wane irin kalar walaƙanci ne. Idan yace mata taje tai wanka kawai ai ya wadatar, amma yanzu gashi ya jiƙa mata kaya duka al'halin bata da yaƙinin wasu dan ta fahimci a sashensa take. Bai dai san tanai ba, dan tuni ma shi ya fice abinsa. Haka ta cire kayan a jiƙe ta ajiye a gefe, nutsa kanta ta sakeyi a ruwan tana mai lushe idanu kamshin ruwan da ɗuminsa na ratsata, ga yanda kumfar tai a sama ful-ful na wani irin ƙayatar da ita.....


        ★Ta jima a bayin kafin ta fito, sam batai tunanin samunsa a ɗakin ba. Dan haka ta fito kanta tsaye a zatonta ai zai fita ya bata waje tunda ya san wanka ta shiga. Sai da tazo tsakkiyar ɗakin tana ƙoƙarin sharce ruwan dake sakkowa daga jiƙaƙƙen kanta data wanke zuwa kan fuska ta tsaya turus. Da sauri ta juya bayanta kamar zata fasa ihu. ALLAH ma ya sota bathrobe ta sanyo ba towel ba. Ai da yau taji ƙarshen kunya a duniya.

      Babu alamar zai motsa a zaman ƙasaitar da yay cikin haɗaɗɗiyar kujerar da yake duk da yaji fitowar tata. Sai da ya mula dan kansa ya ɗan ɗago idanunsa ya dubeta kaɗan ya kauda kai. (Bata tausayama kamata) ya ayyana a zuciyarsa yana jan sirrin tsaki a can ƙasan maƙoshi. System ɗin dake a cinyarsa ya ajiye saman ɗan coffee table ɗin gabansa ya miƙe fuska a daƙile, ta gabanta ya raɓa ya wuce kamar bai ganta ba. Jitai kamar tasa ihu dan takaicinsa, sai dai kuma ta kasa motsawa da ga tsaiwar har ya sake dawowa. A bazata yanzun ma taji tattausan hanunsa kan dogon gashinta data naɗe dan ya tsane da wuri kasancewar ta jiƙesa lungu da saƙo dan wanki ta masa mai ƙyau. Warwaresa yay sannan ya ɗaura karamin towel ɗin hanunsa baby pink a kanta ya fara tsane mata ruwan. A yanzu kam ba mamaki ne ya kashe Iffah kawai ba har da suman wucin gadi tai na ɗunbin mamakinsa. Ita Iffah, ɗiyar Babiy da Ummu ne tsaye Shahan-shan ke mata hidima, Shahan-shan fa ba wai hadimin daular ruman ba. Shahan-shan gaba ɗaya, wanda ke amsa shugaban na ƙasarta baki ɗaya, shugaban kuma al'ummar ƙasar ruman baki ɗaya. Sarkin da duniya ke shakka da tsoron nunama koda ƙasarsa yatsa. Ɗan gata da iyayensa suka haifa shi ɗaya ƙwallin ƙwal a duniya. Shi ɗin nan dai da duniya ke kallo matsayin wani babban tauraro mai girman gaske. “Kai ya ALLAH anya ba mafarki nake ba?”

     (Idonki biyu) zuciyarta ta bata amsa da tabbatar da abinda takewa kokwanto. Ai kanta bai nema kwancewa ba sai da ya kama igiyar bathrobe ɗin jikinta ya kwance. A ɗan zabure ta riƙe hannunsa caraf cikin nata tana waro idanu. “Mi zakayi...?” kalmar ta fito a suɓuce daga bakinta. Wata irin dariya ce ta nema kufce masa ya danneta da ƙyar. Cikin ƙara kame fuska ya tsareta da idanun nan nasa masu kaifin tsiya, hanun nata ya ture zai ƙarasa kwancewa abinsa. Sai kawai ta daka uban tsalle ta faɗa masa a jiki “Ni wlhy ba ƴar iska bace, babu fa komai a c....” ta kasa ƙarasawa tana ƙara cikuykuyesa da ƙyau.

        Jikinsa rawa ya neman farayi saboda yanda ta ƙanƙamesa, tunda yake a rayuwarsa bayajin ya taɓa rungumar mace kamar haka. Gaba ɗaya abinda ya ɗauka tsahon shekaru yana dakon dannewa ya nema yunƙurowa. Ƙoƙarin janyeta yake tana sake ƙadandanesa a tunaninta so yake ya cire matan koda tsiya. (Ya arrahaman zata halakani) ya faɗa a zuciya yana mai rumtse idanunsa da masifar ƙarfi a zahiri. Cikin zafin nama ya finciketa da sauri yana ƙoƙarin riƙe rawar da jikin nasa ya fara. Cikin wata ƴar sassarfar da bata hana takunsa na ƙasaita fita a yanda yake ba ya bar wajen, a kujerar da ya tashi ya koma ya zube. Faɗi yake (shike nan ta buɗe aiki, Fitinanniyar yarinya zata halakani).

      Oho Fareedatu batama san yanai ba, dan tana samu ya jayetan daga jikinsa ta kwasa da gudu sai saman katafaren gadon da aka gyara tsaf kamar ba yanzu ta sauka akansa ba. Bata da nutsuwar tunanin yanda akai aka gyara ɗin ko wanda ya gyara taja lafiyayyen duvet ɗin ta naɗe jikinta dake faman kakkarwa. Dan jinta take kamar wadda ta jonu da lantarki. Shiru ɗakin kowa yay ɗif a cikinsu. Babu ko motsin ac dan bai kunna ba saboda ita, duk da yana buƙatarsa, sai dai ya kashe na'urar ɗúmama ɗakin dake aiki tun ɗazun saboda itan. Sai da ya ɗan saita kansa kaɗan kafin ya miƙe, batare da ya dubeta ba ya nufi hanyar fita. Ƙasa-ƙasa ta bishi da kallo, ganin ya tsaya tai saurin kauda kanta. Bai juyo ba sai dai yaji a jikinsa ana kallonsa, murya a shaƙe can ƙasan maƙoshi ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ki canja wannan rigan”. 

     Jitai kamar ana narkama jikinta ƙanƙara, ta wani lumshe idanunta dake faman yin mar-mar, sai kuma ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya dai-dai da rufe ƙofar da yay bayan ya fice. Jitai gaba ɗaya kanta yama tushe, ta gagara tunanin komai kamar yanda take buƙata, kamar wadda aka zabura ta miƙe, idanunta ne suka sauka kan wata ƙyaƙyƙyawar abaya mai ɗaukar idanu. Karasawa tai ta daga rigar, sai kuma ta ɗan waro idanu ganin b&p a ƙasa, “Kam babbar buta, duk shi ya ajiye wannan ma? OMG! Wannan Shahan-shan ɗin daular ruman ɗin ko”. Ta ƙare faɗa kamar zata fashe da kuka. Dan ji take duk ta daburce tsabar wata kunya da take ji na ratsata tamkar tana a gabansa.........✍️




     _🥱🏇🏇🏇🏇Babu abun faɗa yau kam, nayi nan kar ace kuma..... To bara dai nai shiru kawai._


No comments

Powered by Blogger.