Daudar Gora Book 2 page 17

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (17)


........Samun gawar ɗaya daga cikin jami'an dake tsare da Iffah, da ɗaya daga cikin na sashen Tajwar Eshaan ya sake tabbatar da akwai ƙullalliya. Dan alamomi na bayyane sun nuna an fara kashe jam'in sashen Tajwar Eshaan ɗin ne akai amfani da kayansa zuwa kurkuku, sai kuma gawar jami'in dake cikin masu tsaron Iffah da bayanin sauran jami'an ya tabbatar da koma miye a lokacin da yace zaije ya binciko gaskiyar zuwan jami'in da yace yazo kawoma Zawjata-almilk kaya ne. Sarƙa-sarƙar ta ɗaure kan mutane matuƙa da yanda tama faru, sai dai jami'an sun tabbatar da sai sun gano koma wanene anan kusa cike kuma da alwashi.....


         ★★.... ★....


    Tunda akace ta farfaɗo hankalin duk masu hannu akan al'amarin ke'a tashe musamman ta-ƙurya da hadimin da yay aikin. Tashin hankalin ta-ƙurya rashin mutuwar Iffah ne, dan tanada hanyoyin da zatabi na ɓatar da hadimin cikin sauƙi, kai koda ta barsa da rayuwarsa ma bai san ita wacece ba. Amma kasancewar cigaba da rayuwar Iffah na nufin MATSALARTA na nan har yau da gobe dama ranar da bata san iyaka ba. Idan har tace kuma zata sake wani yinƙuri a yanzu akwai matsala, mafitarta ɗaya ce sake komawa ga UWA ɗin da take hangen ta gaza a baya. Wasu irin zafafan hawaye ne masu raɗaɗi suka shiga bin kumatunta, ɗuminsu kawai taji batare da tasan ta farasu ba. Hakan ya ƙara ƙona ranta dan akan ƴar yarinyar data raina hawayenta na zuba a karo na babu adadi, abinda bai taɓa faruwa da ita ba kasancewarta mai nasara ga duk abinda ta sanya gaba. Shawarar da zuciyarta ta bata akan sake kiranyen uwa ya sata miƙewa. Surkullen jiya ta shiga fara maimaitawa. Tsahon lokaci har ta fidda rai a yanzu ma sautin mummunar dariyar uwa ta fara karaɗe ɗakin. Dariya ta tsaho lokaci babu alamar za'a daina kafin uwa ta bayyana a gabanta. “Ashe k! ƙaramar mara kunyace ta-ƙurya. Ashe baki shirya yaƙin ba kika yanki filin yinsa ba! Ashe b......”

         “Tuba nake Uwa mai share kukan masu kuka. Nayi kuskure a gafarceni bazan sake ba. Ni mai biyayyace ga umarninki a koda yaushe. Wannan ma saɓanin fahimta aka samu”.

    Shiru kamar uwa bazata tanka ba, sai kuma ta hura mummunan hancinta dayin ƙwafa. “Dalilai biyu zasu sa na miki afuwa ta-ƙurya. Baki taɓa saɓama umarninmu ba sai a wannan karon. Na biyu darajar wannan masarautar da kike ci. Kije ki kalmashe bakin zaren aikinmu na ƙarshe, dan aikinki na gab da buɗewa. Ki kuma kiyayi kaima yarinyar nan hari kai tsaye, dan duk yanda kike tunanin zaki iya a kanta ta waɗan nan hanyoyin al'amarinta ya fi ƙarfin nan. A yanzu haka Ajlaan ya fara shinshinar ta. Kuma komai zai iya faruwa, dan muna a gaɓar da zai iya kashe ƙishinsa kanta a yanzun, babu makawa magajin kujerar daular ruman na kusanto duniya kenan.....”

        Zabura ta-ƙurya tai jikinta na matuƙar rawa, sai wani irin rawa da lips ɗin ta keyi suma tama gagara furta abinda ke bakinta tsabar shiga tashin hankali. Uwa ta miƙa mata hoto cikin bada umarni. “Itace muke buƙata ta zama uwar Miran mai jiran gado, ki gaggauta, ki gaggauta tabbatar da ita cikin masarautar nan matsayin Zawjata-almilk daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci. Inba haka ba kiyi kuka da kanki ta-ƙurya! Kuyi kuka da kanki!! hahaha!! hahahah!! hhhhhh!!!!!”.

       Ta ɓace ɓat sautin mummunar dariyarta na amsa kuwwa cikin ɗakin kai kace duk masarautar za'a iya jinta...


   ★★....  


        “Wannan na sake tabbatar mana da ƙamshin gaskiya akan yarinyar nan Mammah”.

     Daneen Ammarah ta faɗa cikin sanyin murya da jimamin abinda ya faru ya haddasa mata. Numfashi mai nauyi Malikat Haseenat ta sauke, kamar bazatace komai ba sai kuma ta dubi ɗiyar tata. “Akwai al'amarin dake tare da yarinyar mai girma da ko iyayenta bana jin sun san da shi tattare da ita ba. Inaji a jikina a dalilinta komai na gab da buɗewa a wannan masarautar”.

         Cikin nuna mamaki Daneen Ammarah ta ce, “Babban al'amari kuma Mammah? Kamar wane iri kenan?”.

     A karo na farko Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ƙayatarwa, batare da tace komai ba ta danna kekenta yay gaba. Da kallo Daneen Ammarah ta bita baki sake, ita kam wani lokacin Mammah na hargitsa mata tunani da sakata a wasiwasi gaskiya.....


     ★★....


     “Idan har ya kasance bakai bane kamar yanda ka faɗa to wanene kenan? Dama da gaske kamar yanda muke zargi bayan mu akwai masu harar rayuwar yarinyar nan kenan akwai ɗin?”.

       “Ga alamun hakan ka gani. Sai ma nakega su ɗin sun fimu shiri. Sai dai abinda ke ɗauren kai su kuma miye nasu dalilin? Dan na hanga na hango a duk cikin wanda zasu iya aikata hakan burinsu zai kasance irin namu ne amma basu da hujjar yin hakan. Idan a matan mahaifinsa ne miye ribarsu tunda ba wasu ƴaƴane da su ba balle ace suna yaƙi irin namu ne? Anya kuwa ba iyalan Sayeed Khairul-Bashar bane ke son ɗaukar fansa?”.

       “Idan kuma zasu ɗauki fansa sai su ɗauka akan wadda ba'ita ta musu laifin ba?. Idan har sune rayuwarsa zasu hara bata matarsa ba. Kuma ai tun farkon shigowarta masarautar nan aka fara wannan wasan. Akwai dai wata a ƙasa daya kama mu sani mu kuma san mai wannan shirin dan dalilinsa mai ƙarfi ne.”

      Cikin gamsuwa Miran Jasim ke gyaɗama Miran Arshaan kai fuskarsa ɗauke da murmushi, dan koda basu suka aikata ba abinda ya farun ya musu daɗi har cikin rai yake jin farin ciki da nishaɗi..


        ★.....


   Tunda Doctor ta gama dubata ta fice ya cigaba da tsaiwa akan ƙafafunsa lumsassun idanunsa da suka canja kala kaɗan na ɓacin rai ƙyam a kanta. Kallonta yake tamkar wata sabuwar halitta a rayuwarsa. Kallonta yake zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Kallo yake mata irin na miyasa kika zaɓi shigowa rayuwata a haka?, bayan ba haka na so ki kasance ba. Ƙanƙance idanun ya sakeyi a kanta yana mai datse lips ɗinsa da haƙori har yanajin raɗaɗin hakan a karan kansa. Sannu a hankali ya fara kai kawo a ɗakin hannayensa duk biyu goye da bayansa. Sosai a wannan gaɓar fuskarsa ta nuna matsanancin fushi. Zuciyarsa ta fara kaiwa maƙura akan abubuwan dake faruwa a masarautar, ya fara jin bazai iya cigaba da jurewa akai gaɓar da yake buƙata ba tun farko. Kalaman wasiyyar mahaifinsa ne suka shiga dawo masa ɗaya bayan ɗaya. A yanzu kam idanun ya rumtse tare da kaiwa zaune cikin kujera. Zuciyarsa na gudu da sauri-sauri. Sosai yake jin ɗaci mai sosa zuciya. Hawayene suka cika masa ido domin shima mutum ne kamar kowa, zuciyarsa irin ta kowa ce, yanajin zafi, yanajin farin ciki. Sosai yake buƙatar son jinsa a jikin wani. Mahaifiya ko mata. Sai dai yasan hakan shine abu mafi wahala a gareshi bayan abubuwa masu yawa da ALLAH ya azurtashi da su. Yanada tarin dukiya daya nema da guminsa, mahaifinsa ya bar masa tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. ALLAH ya bashi mulki, mulki mafi daraja sama da kowane shugaba da ke a ƙasar ruman. Ya azurtashi da ƙyawu irin wanda ko'a cikin ƙyawawa yasan zai zama abin kallo. Ya azurtashi da ilimi na boko dana addini da babu abinda zaice sai Alhamdullah. Sai dai ya tawaya ta ɓangaren mace, shi mutum ne mabuƙaci, ya daɗe da fahimtar hakan, amma ƙaddarorimsa sun nisanta shi da samun cikamakin waɗan nan ni'imomin da UBANGIJI ya mallaka masa. A hankali ya sauke lumsassun idanunsa kan Iffah zuciyarsa na kaikawo. (Abbie miyasa kace na kasance haka?) Ya ambata a zuciya cike da ƙunar da take masa mai raɗaɗi..


      ★★......


      Jigum-jigum aka yini a masarautar cike da jimamin abinda ya faru. Al'amarin ya fara ɗaure zuciyar kowa a yanayin da yake da wahalar fassara. Sai dai a zahiri babu mai iya cewa komai sai ƴar ƙus-ƙus kai da abokin maganarka. Har yamma Tajwar Eshaan na tare da Iffah, duk da damunsa da na'urar ɗumama ɗakin da aka kunna saboda ita keyi haka ya cigaba da zama a ɗakin. Hatta da fada da akai zaman fadanci da tunanin zai fito yace wani abu akan abinda ya faru bai fitan ba. Sallama a ɗakin yayi ta yau. Hakan ya fara ankarar da mutanen masarautar kenan duk lokacin daya killace kansa yaƙi fita yana fushi ne ko cikin damuwa. Dan yau dai kusan kowa a haka ya fassara rashin fitowar tasa.

       Su dai ke kiɗansu suna rawarsu, dan shi dai bai ce ba babu kuma alamar zai ce ɗin har yammaci. A hankali ta fara motsi dai-dai lokacin da yake zaune yana raira karatun Alkur'ani mai girma da wata irin sassanyar murya mai tsaushi da ratsa zuciyar mai saurare. A duk lokacin da ya samu kansa a irin wannan yanayi  na damuwa mai ƙuna yafi buƙatar zama yayta karatun Alkur'ani sai ya samu nutsuwa. Da atshawa ta fara a jere har guda huɗu, hakan ya ankarar da shi farkawar tata. Amma tsabar ƙasaita da miskilanci baiko motsa ba ya cigaba da karatunsa har inda yaji zai tsaya dan kansa. Koda ya ajiye Alkur'anin ma bai juyo ɗin ba kai tsaye duk da atishawar da ta cigaba da jerawa a wahalce kuma a jajjere. A nutse ya miƙe babu alamar gaggawa ko garaje tattare da shi, sannu-sannu ya sauke manyan ƙyawawan fararen idanunsa kanta dai-dai ta sake yago tissue dake gefenta a bed side drawer ta toshe bakinta domin tare atshawan da ya sake taho mata. Kusan uku ta sake jerawa kafin ta ajiye tissue ɗin inda ta tara sauran cikin ƙanƙanin lokaci. Numfashi take saukewa a ɗan wahale kumburarrun idanunta na lumshewa da buɗewa.........✍️


No comments

Powered by Blogger.