Daudar Gora Book 2 page 16


 ?𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (16)

........Kamar yanda al'adar take duk wani hadimi da karfe huɗu tayi zai fara gudanar da aikinsa in har yana cikin hadimai masu kula da tsaftar masarautar. Musamman ma masu shara da tsaftace irinsu garden barga da sauransu. Yauma hakance ta kasance, hadiman duk sun tashi domin kama ayyukansu, kowa ƙoƙarinsa ya kammala kafin sallar asubahi. Swimming pool ɗin garden ɗin gabashi dake kamar ta bayan

sashen Shahan-shan gab, babban swimming ne da masu aikin tsaftace ruwan cikinsa suka kasance har su huɗu, kowace kusurwa da mai gyarawa. Sukan saka raga domin tace duk wani datti daya shiga ciki, tare da sake ingantashi ya fita fes yana bada kalar blue mai ɗaukar ido ko daga nesa. Aikinsu suka fara a nutse, tare da yima juna magana jefi-jefi, can wanda ke a bangon yamma ya zabura tare da ƙwala ƙarar da tai amsa kuwwa zuwa kunnen duk hadiman dake aikinsu suma gab da wajen. A take ƴan uwansa sukayi kansa suna tambayar lafiya. Jikinsa na rawar karkarwa yay musu nuni da cikin swimming pool, kallonsu suka maida wajen zukatansu na dukan tara-tara, dan basu mance tsautsayin da ya taɓa faruwa ba da har yay sanadin rasa ran Miran Nayyar (ƙani ga Marigayi Tajwar Haysam). A tare suma suka zabura jikkunansu na sake shiga mazarin rawa. 

      “Tabbas mutum ne mun shiga uku!!”.

   Wani ya faɗa a cikin sauran hadiman da ihun wancan ya jawo hankalinsu. Sake daburcewa duk sukayi, an rasa wanda zai yi hoɓɓosan kai agaji ko neman agajin, gashi motsin da suke gani anayi a cikin ruwan ya fara lafawa alamar wanda ke cikin yana sake ƙasa. Wani da yazo kusan a ƙarshe-ƙarshe ne ya zabura zai afka, da sauri wani ya rikoshi yana girgiza kansa. “Wannan bashine mafita ba, ayi azamar sanar da jami'ai gudun kar mu aikata kuskure tunda bamu san wanene ba. Duk wanda ya kai shekara arba'in da biyar baya anan yasan miya faru a dalilin irin wannan kuskuran”. Sun gamsu da jawabinsa, duk da wasu labari kawai sukaji dan sannan girmansu bai kai ba, wasu ma ba'a haifesu ba.


      Cikin ƙanƙanin lokaci jami'ai suka iso wajen, hakama mazan masarautar dake ƙoƙarin tafiya masallaci sallar asubahi. Rashin sanin wanene a ciki yasa shugaban jami'an ya hana a shiga kai tsaye, sai dai tuni an gama dasa na'urorin da zasu iya fiddo koma wanene. (Dan tun rasa Miran Nayyar da masarautar tayi Tajwar Abdul-majeed ya tanadar da na'urorin domin tsaro). Tayi ƙasa sosai ga swimming pool ɗin da girma sosai, cikinsa kuma anyi style kamar wani sashe-sashe da suffar ado. Hakan yasa akaja lokaci mai tsawo kafin a samu nasarar samota, zuwa lokacin har an idar da sallar asuba. 

         Kasancewar tsirarun mutane da Tajwar Eshaan ne kawai suka sami damar yin sallar asubahin ya bada mamaki har Tajwar Eshaan ɗin yasa akai tambayar ko wani abu na faruwa ne haka?. Waɗanda suke a masallacin duk basu sani ba, dan haka suka tabbatar da babu komai, sai dai ko makarace ta kawo hakan. Baiji ya gamsu ba, amma sai bai musa ba ya miƙe ya fito Sayeed Fayzul-haq da ya zama kamar amintaccensa yanzu biye da shi. A falo Sayeed ya dakata, shi kuma ya nufi bedroom domin shiryawa ya shiga grm. Dai-dai nan kiran waya ya shigo ta landline. Tsayawa yay cak, dan duk kiran da zai iya shiga a wannan wayar direct dole mai muhimmanci ne da shi ya shafa, kuma kai tsaye ake bukatar magana da shi. Tana gab da tsinkewa ya juyo, idanunsa ya sauke akan sayeed, cike da ƙasaita yay masa nuni da wayar alamar ya ɗaga. Cikin bin umarni sayeed ya ɗaga wayar, shiru kusan na minti ɗaya ya janye a ɗan zabure yana kife wayar. “ALLAH ya ƙarama shugaban sarakuna da al'ummar ƙasar ruman baki ɗaya lafiya da tsohon rai mai albarka. Kirane da ga shugaban jami'an tsaro. An samu accident ne a cikin swimming pool ɗin babban garden, mace ce kuma, ana kyautata zaton bata cikin hadimai, gashi tana buƙatar taimakon gaggawa da basu da hurumin taɓata su”.

       Ƙirjinsa ne yay wata irin mummunar bugawa, mafarkinsa na gabanin asubahi da har yasa shi ƴar makara ya shiga maimaita kansa a kwanyarsa. Ƙoƙarin basarwa yay kamar yanda ya saba, sai dai zuciyarsa taƙi bashi goyon bayan bada umarnin waninsa yaje. Har ya daga ƙafarsa da niyyar cigaba da tafiya hakan ya gagara, idonsa ya rumtse da ɗan ƙarfi ya buɗe, batare da yace uffan ba ya nufi ɓoyayyar hanyar da zata sadashi da babban garden ɗin. Sosai mamaki ya kama Sayeed Fayzul-haq, sai dai bashi da hurumin tambaya dan haka ya take masa baya da sassarfa...


        ★Cikin rawar jiki hadiman wajen suka shiga zubewa bisa gwiwunsu ganin mai ruman ɗin ne fa da kansa. Yayinda jami'an suma duk suka risinar da kawuna. Taku yake a nutse cike da ƙasaitar da ke tabbatar da kasancewarsa bajimin namiji da ko a cikin jaruman gwarazo ne. A ƙirjinsa bugu yake kamar zai hantsilo waje, a zahirinsa kuwa babu mai iya fahimtar komai koda daga fuskarsa ne. A hankali matan da ke zagaye da ita suka dare, dan sune suka sanar cewar Zawjata-almilk ce, shugaban jami'ai ya faɗa a rufe ne saboda shakkar isar da saƙon kai tsaye ga Shahan-shan ɗin. Suma kawunansu duk a rissine suke, cikin rawar murya ɗaya daga cikin matan data kasance amintacciyar hadima mai ƴanci dake da alhakin kaiwa da komowar duk wani abinda ya shafi Shahan-shan da matansa ko makusancinsa (kamar jakadiya a ƙasar hausa) ta ƙarasa zubewa cikin gurfana, 

      “ALLAH ya huci zuciyar shugaban sarakunan ƙasar ruman da al'ummar cikinta. Umarninka muke jira domin taɓa Zawjata-almilk, dan rayuwarta zata iya salwanta.....”

           Idanunsa da ke ma Iffah kallon ƙasa-ƙasa ya ɗan lumshe, cikin jarumtar son danne zillon da zuciyar ke masa ya ɗaga ƙafarsa da ƙyar yay taku ɗaya biyu da ya sake saka matan darewa cikin rawar jiki mamaki na neman halakasu ganin gadan-gadan Iffah ya nufa. Dai-dai yana ƙarasawa ɗaya da ga cikin jami'an wajen da yay wata irin zabura ya sunkuto ɗaya daga kujerun dake a wajen ya dire masa, da sauri aka ɗaura hiramin sayeed Fayzul-haq daya fincike a kansa. A hankali ya kai zaune shanyayyun idanunsa na sake tar-tar a kanta cikin ɗan hasken da garin ya fara. An lulluɓe jikinta da mayafi kasanwar kayanta dake jiƙe zai iya bayyana ainahinta, kallon kusan sakanni biyar yaja numfashi ya fesar yana mai kai yatsunsa biyu saman hancinta, babu alamar numfashi, ɗaukewa yay ya maida a jijiyar wuyanta, nan ma bata harbawa, cikin jarumta da zaburo da sanyin da ke sauka a jijiyoyin jikinsa ya ɗan ɗaga mayafin ya ciro hanunta. A kan tattausan nasa ya ɗaura yana mai ɗaura yatsansa akan jijiyar tsintsiyar hannun ya lumshe ido. Da sauri ya buɗe sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimta ba. Dan a nitse yake sarrafa hannunsa dake motsi kawai a jikin nasa. Shugaban jami'ai da Sayeed Fayzul-haq dake ɗan satar kallonsa kasancewar duk wani hadimi da sauran jami'an tun zamansa a kujerar duk sun juya bayansu suka ɗan waro ido ganin ya kusanta ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da ta Iffah har hancinansu na gogar juna. Ya lumshe idanu tare da sauke tausasan lips ɗinsa kan nata, ai dole suma suka sake rissinar da kawunansu duk da sun san bawani abu zai yi ba illa bata taimakon gaggawa. 

     Shiko da bai ma san sunayi ba da harshensa yay nasarar raba lips ɗinta da haƙoranta dage datse cikin na juna ya turashi cikin bakin nata, sai kuma ya kai yatsunsa biyu kan hancinta ya matse. Iskar bakinsa mai ƙarfi ya hura mata cike da salon ƙwarewarsa akan iya ruwa da ceton duk wanda ya samu accident a dalilinsa. Da wani irin ƙarfi ta zaburo ƙirjinta na ballaƙowa sai ruwan bakinta bulla a kan fuskarsa. Idanu ya lumshe a hankali yana mai sauke wata irin nannauyar ajiyar zuciya daga cikin maƙoshinsa da ɗan jan fuskarsa data wanke da ruwan bakinta. 

        Cikin sauri Ama. Ta miƙama Sayeed ƙaramin towel cikin wanda ke hanunta, amsa yay ya matsa kusa da Tajwar Eshaan kansa a rissine ya miƙa masa. Bai motsa ba idonsa a kanta tana cigaba da amayo ruwan saboda ɗan danna ƙirjinta da ya cigaba dayi har tsawon kusan mintuna biyu, kafin ya miƙama sayeed hannu batare da ya juyi ba ya amsa. Kan fuskarsa ya kai ya tsane ruwan da tuni yama gangagare har wuyansa har ya ɗan jiƙa jallabiyar jikinsa mai tsananin ƙyau da ɗaukar idanun kai kallo. 

         “Duvet”.

    Ya faɗa a hankali ganin jikinta ya fara karkarwa har ɗan gadon agajin gaggawar da aka daurata na ɗan jijigawa. A cikin ƙanƙanin lokaci aka kawo, yanzu ma da kansa ya rufa mata. Sannan ya miƙe gaba ɗayansa yana ɗan duban Sayeed. “A maidata gareni”. Ya faɗa can ƙasan maƙoshi tamkar bashine yay maganar ba yana ƙoƙarin barin wajen. Sai yanzu ya lura da cikar garden ɗin da duk masu faɗa ajin masarautar a wajen. Idonsa ne ya sauka kan Malikat Bushirat da Malikat Haseenat da ke kusan tare da juna. Dan Daneen Ammarah da Malikat Ashwaq ne suka ɗan shiga tsakaninsu. Ɗauke idanun nasa yay ya cigaba da takunsa na bajimta. Dan kowa a wajen kansa a rissine yake har su Malikat Bushirat ɗin kansu domin tabbatar da girman da ALLAH ya bashi na shugabanci....

       A gaban idon kowa aka wuce da Iffah sashen Tajwar Eshaan ɗin tare da Doctor da zata sake bata taimakon gaggawa, a hankali ƙus-ƙus ya fara tashi a wajen kowa na jimanta al'amarin da jinjina faruwarsa kasancewar duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan Iffah na kurkuku ne, kuma a yau za'ai zaman shari'a ta biyu, hakama abinda ta faɗa a zaman waccan shari'ar kowa ya jisa. Sai dalilin faruwar al'amarin yau ya saka zukata fara rarrabuwa a kan al'amarin ta, masu ganin a wancan zaman shari'ar ta faɗi waɗan can kalamanne danta kuɓutar da kanta ko sharri, sai a yanzu suke ganinfa akwai ƙamshin gaskiya tunda a karo na biyu kenan ana yunƙurin kasheta. Idan babu rami to miya kawo rami? Wannan shine tambayarsu...........✍️

    


No comments

Powered by Blogger.