Daudar Gora Book 2 page 14
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (14)
........Zabura tai saboda yanda yaja (faaa) ɗin ƙarshe da wani salon busa mata numfashinsa mai ɗumi. Tare da waro idanunta waje tai baya gaba ɗayanta ta zube ruguf a gadon idanunta na kif-kif na shiga ruɗani. Sai kuma ta tura bakin gaba da ɓata fuska tamkar mai shirin fashewa da kuka. Idanunsa da ke a kanta ya sake shanyewa, a yanayin son basar da salon nata ya ɗan ƙara kusanta fuskokin su tamkar zai rungumeta har lips ɗinsu na gogar juna. A yanzun kam bata da zaɓin da ya wuce rumtse idanun da masifar ƙarfi, ƙoƙarin danne tsumar da jikinta keyi tayi ta hanyar son damƙo bedsheet ɗin gadon sai ta damƙo tattausan hanunsa. Da sauri ta janye nata zata yarfar ya sarƙe yatsunta cikin nasa ya matse da ƙarfin da har sai da tai zaburar da jikinsu ya manne da juna, cikin rawar baki da rashin sanin abin faɗa ta fara magana a sarƙe.
“D... Dan ALLAH k.. kafin ka kashe ni ka faɗa min game da Ajmaal. Ka faɗamin game da Iyayena da aka ce ka kashe?”. Ta faɗa maimakon amsa masa tashi maganar tana mai sauke ajiyar zuciya da sauri-sauri saboda kusancin nasu ya yayi yawa. Ga ƙamshin mayen turarensa wani irin harmutsa mata lissafi yake har gashin jikinta na mimmiƙewa alamar tashin tsigar jiki.
Lips ɗinsa ya motsa kaɗan tamkar zaiyi magana sai kawai jin saukar duminsu tai a kan nata, da masifar ƙarfi ta matse idonta da ƙanƙame illahirin jikinta da ya ɗauka karkarwa. Miya rage mata ita kam, kawai ta saki ihun da sai ya girgiza masarautar ko wani zai tai maketa daga ɗaurin goron da Shahan-shan ya mata, wannan salon nasa ya girmi kanta bazata iya ɗauka ba. Hannun tai ƙoƙarin janyewa a karo na biyu da lips ɗinta da ya ɗan ciza mai makon sumbatar da tai zato tamkar wadda ta ɗosana kan wuta tana mai fisgar numfashinta shima a sarƙe.
Sosai abun ya so bashi dariya amma ya haɗiye kayansa yana ɗan janye jikinsa baya, dan ya fahimci zata ma iya sume masa. Aiko wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta miƙe zaune zumbur, cikin son kame rawar da jikinta keyi ta dunƙule kanta waje ɗaya. Ƙoƙarin haɗiye murmushin da ke neman suɓuce masa a zuciya yayi, a fuskarsa kam babu alamar hakan sai ma sake tsuke ta da yay fiye da farko. Jikinsa ya ɗan ja baya ya koma a kujerar da ya tashi ya sake zama yana mai harɗe hannayensa a ƙirjinsa da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya zuba mata idanu kawai. Tsahon kusan mintuna uku suna a haka kafin shi ya katse shirun ta hanyar gyaran murya.
“Su waye su?”.
Kaɗan ta ɗago tare da buɗe idanunta. A yanda taci karo da fuskarsa sai taji wani irin shakkarsa da kwarjinin sa ya sake baibaye numfashinta. Yana zaune a kame tamkar daɗa duniya tun shigowarsa bai motsa a yanda yake ba. Wani kallo data kasa bama fassara ya jefa mata ya kauda idanun. Itama sai ta ja iska ta karasa risinar da nata tana ɗan kallonsa ƙasa-ƙasa.
“Saninsu kai tsaye da ga gareni ba shine ya dace ba *_Sultan_*, taka tsantsan da rayuwarka da sanya ido kan wanda duk suke zagaye da kai shine mai muhimmanci. Idan ni banci nasara a yau ba, su zasu iya ci watarana, duk da nima ba haƙura nai ba zan sake gwada sa'a ta a karo na biyu”. Ta ƙare maganar a salon juya manyan idanunta da yamutse fuskarta dake tsuke tana laɓe baki idanunta dake cike da hawaye a kansa. Sai kuma ta janye su ganin yanda ya tsareta da nasa.
Bai iya ya motsa ba, kallonta kawai yake da ƙoƙarin danne abinda ke taso masa a kanta tun daga yatsan ƙafarsa har zuwa cikin tsakkiyar kansa. (Yarinyar nan ko) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam tsaf ya shanye komai daga kan fuskarsa ya haɗiyema ransa yana mai furzar da iska kaɗan tare da sake yin gyaran muryar da ta sakata sake ɗagowa dole, sai dai bata jure kallon nasa ba ta maida kanta ta rissinar. Shima ɗauke nasa yay daga kanta tare da miƙewa, ta ƙasan ido tabi takun sawayensa mai cike da izza da nutsuwa da kallo, sai da ya kai ƙofar fita gab ya dakata sai dai bai juyo ba, “Na baki dama ta biyu, in har kikaci nasarar kaudani a karo na biyu daga nan zuwa shekara ɗaya tukuycinki zama sarauniyar daular ruman bisa karagar mulkin Shahan-shan. Idan kika gaza hukuncinki zama uwar yarana biyar a ƙarƙashin ƙarfin iko ba soyayya ba....”
“Bana yarda aci riba kaina bisa ƙarfin mulkin mallaka koda anfi ƙarfi na. Taya zakaci riba biyu a shekara ɗaya duk a kaina, Iffah ba tsuntsuwar da ake ajiyewa a gida domin ado bace”.
Wani ɗan murmushin gefen baki yaso suɓuce masa amma sai bai bar hakan ba. A ransa ya furta (Ƴar barazana ce yarinyar nan) a zahiri kam sai yay ƙoƙarin ficewarsa maimakon bata amsa. Dan kansa har ya fara ciwo. In ba da iyayensa da Malikat Haseenat ba bayaji ya taɓa magana mai tsaho da wani a rayuwarsa kamar ta yau, shi kansa mamakin ma hakan yake, a rayuwarsa babu abu mafi bashi wahala kamar yin magana mai tsawo, shiyyasa yafi yarda da yaren kurma koda a fada ne...
“Banfa yarda ba.... Soyayya kuwa ni bama ta taɓa zama abinda nake kallo da muhimmanci ba da har zanyi kwaɗayin yima wani bayan ta ahalina”
Ya tsinkayi furucin nata yana ƙoƙarin ficewa. Yanzu kam sai da yay murmushin a zuciyarsa da sake jinjina ƙarfin halinta. Bai kuma juya ɗin ba yay tafiyarsa. Ta ɓarauniyar hanyar da ya fito ya koma sashensa, dan dama fita ce ta ɓadda kama. Turus ya ɗanyi da ganin Malikat Haseenat da bai zaton gani a irin wannan lokacin ba, kuma a falonsa da bazai iya tuna sanda ta shigo shi na ƙarshe ba. Basar da yanda take binsa da kallon tuhumar da ya gani a idanunta yay ya ƙarasa takowa gareta. Sai da ya kai zaune ya riƙo hanunta ya sumbata. Sannan ya furta “Idan amintacciya na buƙatar ganin gudan jininta shin ba umarni kawai zata bada ba ya isa gareta”.
Murmushi ta saki a karo na farko, itama cikin nata salon girmamawar garesa duk da matsayinta kanta ta ɗan rausayar. “Idan uwa ta girmama ɗanta da ke amsa sunan shugabanta laifi ne Hafidi?”.
Kansa ya girgiza yana ɗan murmushi a karo na farko. Ta san iya amsar kenan daga garesa. Dan haka cikin rashin nuna damuwa ta cigaba da faɗin, “Fita ce ta sirri, dan idanuna sun kasa rintsawa a wannan daren a dalilin furucin Zawjata-almilk”.
Idanunsa ya ɗan motsa, kamar bazaice komai ba sai kuma ya nisa, “Jadda-ti miye abin hana barci a ciki? Faɗin akwai wanda ta ambata bayan mun san da su? ko kuwa furtawarta kasancewar bamu taɓa ji da ga bakin wani ba?. Shirmenta da son kare kanta da ga laifinta ne kawai ya sata furtawa itama, nasan tana da hujja kan wani ba.....”
“Ina bazai yiwu ba Eshaan. Na jima da fahimtar wannan yarinyar nada wasu ɓoyayyun al'amura tattare da ita, sannan tana da ɗabi'ar zama kaifi.....”
(Mai hatsarin gaske ma kuwa, dan tafi duk yanda kike tunaninta Jaddah) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai ya ɗan yamutsa fuska kaɗan, dan kansa ke ciwo. Can ƙasan maƙoshi ya ce, “Yanzu mi kike son ayi?”.
“Karmu matsa mata da son sanin da wa sukai wannan aikin. Kamar yanda tace mu bincika da kammu muyi ƙoƙarin hakan, dan akwai wata hikima a zancen ta na bamu damar mu bincika ɗin”.
“Yanda kikace haka za'ayi Jadda-ti. Sai dai kuma idan bamuyi bincike ba taya za'a yanke mata hukunci? Ni fa ƙara aka kawo min, dolene na hukunta mai laifi ko na wankesa akan gaskiyarsa”.
Murmushi tayi mai ma'anoni da yawa da ita tasan dalilin kayanta. Taja numfashi ta fesar da ƙara damƙe hannunsa cikin nata. “Wannan sune siffofin adalin shugaba. Sai dai inaji a jikina a kwanaki ukun nan daka bada wani abu zai iya faruwa, dan duk masu hannu a ciki a yanzu hankalinsu ba'a kwance yake ba sam. Suna can neman hanyar ɗaukar mataki a kanta kafin cikar kwanaki uku harma da mu kammu”.
Idanu ya tsira mata da mamakin jin kalamanta. Amma sai bai iya cewa komai ba. Itama bata sake cewar ba ta sumbaci hannunsa tana mai lumshe idanun da buɗewa alamar sallamar kenan. Shima nasan ya lumshe tare da rissinar da kansa ya buɗe a hankali fuskarsa da ɗan yanayin murmushi sai dai bayin yake ba. Sai dai ta kurema ganinsa sannan ya janye idanunsa da ke binta da kallo. Ya maida bayansa jikin kujera ya maida idanun ya lumshe...
Duk yanda yake son hana tasirin kaikawonta a zuciya hakan ya gagara. Ƙarfin halinta, tsaurin ido da kauɗin zance na matuƙar zaburar da shi. Koda a tsoracan take sak take a zahirinta. Ba mata ba mazan ƙasar ruman gaba ɗaya shakkar masa magana suke kansu tsaye, amma ita tar idonta da muryarta ke fita garesa. Itace ta farko dake iya kallon cikin idonsa ta faɗi magana bayan mahaifinsa, amma ko Malikat Bushirat da Malikat Haseenat bejin tunda ya mallaki hankalin kansa sun taɓa hakan musamman a yanzu da yake matsayin Shahan-shan, suna masa magana da taushin harshe da kuma kimantawa, duk da kasancewar sa ɗa garesu. Amma ita duk da akwai girmamawar tattare da fitar sautinta garesa kai tsaye take babu alamar shakku, bata kuma iya ɓoye abinda ke ranta koda a inda tasan anfi ƙarfi ta ne.
“Fitinanniya”.
Ya furta a hankali kan tausasan lips ɗinsa yana mai miƙewa da wani irin makirin murmushi a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa..........✍️
_🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️wanga Shahan-shan ya fara bani olo_
Leave a Comment