Daudar Gora Book 2 page 11


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (11)

.........Doctor dai da Sayeed Fayzul-haq kawunansu a ƙasa mamaki na ratsa su, dan ba abinda sukai zaton gani ba kenan musamman idan akai la'akari da laifin Zawjata-almilk ɗin. Daneen Ammarah kam idanunta ta lumshe tana mai sakin murmushi da addu'a mai girma a ƙasan zuciyarta. Duk da tasan gane ainahin abinda ke cikin zuciyar wannan gwarzon nasu abune mai wahala, mutum ne miskili da ya gajesa wajen uwa da uba. Ga zurfin cikin tsiya uwa uba jinin mulki dake yawo a jikinsa. Sai dai hakan baya nufin taƙi son tabbatuwar abinda take fata ɗin....

      “Wannan ya huce a canjashi da wani Mamy”. Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi yana miƙewa tamkar bashi ne yay maganar ba. Da alama Daneen Ammarah ta fahimci abinda yake nufin, dan kallo ta bisa da shi mai tattare da ɗan murmushi har ya fice Sayeed Fayzul-haq da Doctor suka take masa baya.

        “Muna godiya da wannan karamci”. Ta faɗa dai-dai zai fice a ɗakin. 

      A yanzun ma Sayeed ne ya amsa mata da tausasawa, yayinda shi ya fice abinsa. Daneen Ammarah ta sake sakin murmushi da zaunawa a gefen Iffah, kofin shayin ta amshe tana ƴar dariya. “Haba Ibnati, irin wannan rawar jiki haka! Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai faru sai alkairi. Abni adalin shugaba ne mai son kwatanta adalci wa kowa koda kuma maƙiyinsa ne”.

   Kalmar ƙarshe da ƙarfi ta zabiri Iffah. Sai kawai ta sake fashewa da kuka tana mai jujjuya kanta lips ɗin ta na rawa. “Mamy nayi kuskure, kuskure irin wanda bazan iya yafema kaina b.....”

      “Ya isa haka”.

Daneen Ammarah ta faɗa tana mai ɗora mata yatsa akan baki alamar tai shiru. Shirun kuwa tai sai dai hawayen basu bar zuba ba, ga jikinta na ɗan tsuma har sai da ta rungume ta cike da lallashi..


        

       *_★.. TA-ƘURYA ..★_*

    

       Da ƙyar take shaƙar numfashi da fesarwa sakamakon warin da ƙarin harma da tsamin dake tashi a cikin kogon dutsen mai tsananin saka hautsinawar ciki. Cikin son danne aman da ke ta yunƙuro mata ta sake gyara mayafin dake jikinta ta ƙarashe zancenta da, “Ruƙuƙi mai cika aiki na yarda da dukkan al'amarin ka tunda ƙawata ta bani labarinka. Na yarda zaka iya ƙarashemin abinda uwa ta fara, na yarda zan ƙarasa samun cikar burina a gareka, ina son a kawar min da duk wanda yace zai min karan tsaye ko wanene shi a duniyar nan.....” (Wa'iyazubillah. Ya rabbi ka hanamu ɓata akan son zukatanmu😭👏)

       Wata irin basamudiyar dariya Boka Ruƙuƙi ya kece da ita, hakan ya bama hamami da ɗoyin bakinsa damar sake busowa a cikin hancin ta ƙurya da takejin cikinta na hautsinawa, tun a shigowarta kogon dutsen sihirtaccen ƙamshin turarenta mai narka zuciyar mai shaƙa tuni warin kogon dutsen ɗakin boka Ruƙuƙi ya disashe sa. Amma ta jure ta danne domin samun cikar burinta ya shafe kowanne ƙalubale da zai iya shafarta. 

       Boka Ruƙuƙi ya gimtse fuska bayan ya gama kwasar dariyar tamkar bashi ba. Ya ƙara juya jajayen idanunsa da ke sake fidda munin fuskarsa yana mai girgiza ƙaton kansa. “Duk ƙasar ruman babu wani boka mai ƙarasa miki aikin da uwa ta fara. Ki ɓace, ki ɓace gareni butulu inba hakaba zan ruguza duk wanda tai jajircewar gina miki. Uwa uwar kowa ce mai share kukan masu kuka, butulu ki ɓace gareni, maza ki ɓace!!!!”.

       Ba ƙaramar gigitata tsawar tayi ba, tuni ta manta da matsayinta ta fito a matuƙar kiɗime har tana gware da dutsi ALLAH dai ya taimaketa kan bai fashe ba. Tana gama fitowa ta fara kwara amai, amai matuƙa tamkar zata amaryar da ƴan hanjinta. Kasancewar daji ne ga kuma dare ya tsala daga inda amintacen hadiminta ke jiranta ya dinga jiyo kakarin amanta. So yake yazo ya taimaka mata sai dai yana matuƙar jin tsoro, jin dai ta cigaba dayi yay ƙundunbalar nufarta cikin matuƙar sassarfa hannunsa ɗauke da gorar ruwa. Ƙasa ya zube duk da duhuwar da wajen ke da shi, cikin rawar jiki yake jera mata sannu da miƙa mata gorar ruwan. Amsa tai dan tana matuƙar buƙata, ta ɓalle murfin ta shiga sheƙama fuskarta batare da ta damu da yanda yake jiƙa har jikinta da tsadaddun kayanta ba. Sai da ta kusa juyesa tas kafin ta kuskure baki da sauran ta tsillar da robar tana sakin numfashi da ɗaɗɗaya. Batare da tace da hadimin ko ci kanka ba ta nufi motar da suka zo bayan ta maida norse mask ɗin fuskarta batare data bar hadimin ya ga ainahinta ba. Da gudu ya miƙe ya rigata isa, shi ya buɗe mata murfin har sai da ta shiga sannan ya nufi mazaunin driver...

         Daga nesa da masarautar ya tsaya a inda suka ɗauka motar, Ta-ƙurya dake a bayan motar ta jawo dukkan kayan ɓadda kamarta ta maida a jikinta, haka shima hadimin nata sannan suka fita a motar. Kamar yanda suka fita ta ɓarauniyar hanya da taimakon hadimintan haka suka koma cikin masarautar. Ta sauke bahaguwar ajiyar zuciya lokacin da take zubewa a saman ƙawataccen gadonta. Har yanzu kanta juya mata yake, har yanzu warin da ta shaƙo ya gagara barin hancinta. Ga matsanancin tashin hankali, taya ita kam zata lallashi uwa, bayan ɓacin rai ya rufe idanunta ta faffaɗa mata maganganu marasa da ɗi. Ta ina zata fara? Matsaloli sake yawa suke a rayuwarta....


       

        ★★.... ★....


       Samun lafiyar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ta saka razanin a zukatan wasu a cikin masarautar matuƙa. Dan da gasken gaske ba haka suka so ba. Ga soyayyar mutanen ƙasa tako ina bisa ɓoyayyun alkairansa da suka gano sanadin ganin fuskar a zahirin Shahan-shan ɗin su yanzu. A yanzu kam babu inda zakaje kaji ana zaginsa sai abinda ba'a rasa ba kasancewar duniya duk masoyanka sai ka samu maƙiya, hakama duk maƙiyanka sai ka samu masoya. 

      Shari'ar farko da yay shirin fara gabatarwa itace kawo dai-daito tsakanin iyayensa. Sai dai kuma sam hakan yaƙi yiwuwa saboda Malikat Bushirat ta matuƙar ɗaukar zafi. Dan gaba ɗaya tana kallon Malikat Haseenat ne a mai son kanta da fifita bare sama da gudan jininta. Harzuƙar tata na hauhawa ne bisa jagorancin rura wutar da su Miran Jasim keyi ta bayan fage. Yayinda ita kuma Malikat Haseenat tai biris kamar ma bata san mike faruwa ba. Ta kuma tsaya tsayin daka wajen bama Iffah kariya da ƙara tsaurara tsaro na hana bama kowa hanyar iya cutar da ita. Al'amarin na ƙara rikitar da kowa dan an kasa gane bakin zaren takun saƙar tasu akan Iffah balle manufar kowanne.

        A randa doctor ya sallami Iffah dole aka maidata kurkuku, dan rikici neman tashi yayi a zaman fada tunanin wasu haka shine take-taken Tajwar Eshaan ɗin. Shi dai komai baice musu ba har suka gama cece kucensu. Sai a washe gari ya bada umarnin tsaida ranar da za'ai zaman shari'a. Dan a zahiri ba su Miran Arshaan bane kawai ke tada jijiyar wuya kan ganin anyi shari'ar, har Malikat Bushirat zungurarsa take yi matuƙa akan al'amarin. Acewarta in har bai gurfanar da Iffah ba ita zata ɗauka duk matakin da ya dace a kanta... 


      ★....


   *21/4/2022* Rana ce data kasance na zaman shari'a tsakanin Iffah da ahalin Tajwar Eshaan akan yunƙurin halaka ɗan su. Ƴan jarida sun so halartar wannan shari'a ƙwarai da gaske, hakama jama'ar gari. Sai dai hakan bata faru ba sakamakon cewar Shahan-shan wannan shari'a ce ta cikin gida. Ba haka su Miran Jasim suka so ba, sai dai basu ce komai ba dan kar nuna zaƙewarsu yay yawa ya harbosu dan sun san hatsabibi ne. A yanzun ma suna cikin taka tsantsan ne a duk wani motsinsu.

      Kasancewar shari'ar cikin gida ce kamar yanda Shahan-shan ya faɗa da kansa anyi zaman gudanar da ita ne a falonsa na biyu. Zaman ya kasance a iyakar waɗanda ya shafa, sai manyan masu faɗa aji a ɓangaren shari'a. Falon yay tsit kowa ya nutsu kawunansu a rissine duk da kasancewar duk iyayensa ne a wajen da kuma yayunsa, sai dai girman da ALLAH ya ɗaura masa na shugabancin da har suma suka kasance a ƙarƙashin sa ya tilasta musu biyayyar da girmama wannan girman koda basa so. A sannu ya ke binsu da ido ɗaya bayan ɗaya har idanunsa ya sauka a kanta ƙyam. (Miyasa kika fi yarda da zaɓa mana haka a lokacin da zaɓin ya fi rinjayen kasancewa a zaɓin wasu?) Ya ayyana a zuciyarsa cikin ɗan jansu idanunsa luuu, lumshesu yay tare da ɗan matsesu, sai kuma ya buɗe yana mai kauda kansa. Kusan tsahon mintuna biyu yaja isaka ya fesar yana mai ɗanyin gyaran murya da sake saita kansa.  

       A nutse Sayeed Hanifud-Din ya fara da,  “Alhmdullih kamar yanda na sani kuka sani yau ranar 21/4/2022 zamu fara sauraren wannan ƙara. Muna roƙon UBANGIJI ya bada ikon kamanta zartar da hukuncin adalci wajen bama mai hakki hakkinsa batare da san zuciya ba”.

    A tare aka amsa da amin har lokacin kawunansu dai a ƙasa. Ƙoƙarin hana idanunsa da ke fusga gareta yay. Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da faɗin, Muna buƙatar sake ji da ga bakin masu ƙara. Muna fatan abinda ke a zukatansu ne zai fita a harsunansu, kuskuren hakan na nufin ɗaukar mataki takowace fuska da shari'a a ta koyar damu”.

       Kawuna suka shiga gyaɗawa da ambaton (Insha ALLAHU) alamar tabbatar da abinda ya bukata ne zai tabbatan. Miran Arshaan ya sake rissinar da kansa da gyara zama na tsantsar nutsuwa da duba ladabi. “Ni sunana Miran Arshaan ibn Abdul-majeed Aliy. Zan kasance mai wakiltar ahalina dangane da guba da Zawjata-almilk ta zuba ga ɗanmu a yunƙurinta na kasheshi ranar 21/2/2022. Muna roƙon adalin shugabanmu mai albarka daya yanke mata hukunci dai-dai da laifinta dan ya zama izina ga ƴan baya. Ngd.”

       Babu wanda ya motsa a falon, tsahon mintuna biyu Shahan-shan ya nisa yana mai ɗauke dubansa ga Miran Arshaan ya maida ga sauran ahalinsa. A karon farko ya motsa lips ɗinsa a hankali, “Ko masu ƙara nada sauran wani ƙarin bayanin bayan wannan?”.

    Kawunansu suka shiga girgiza wa alamar a'a. Komai baice ba ya ɗauke kansa ya maida ga Iffah da tun da aka shigo da su a falon bata ɗago ta kalla kowa ba. “Ko wadda ake tuhuma tana da ja akan abinda ake tuhumarta da shi? Ko abin cewa?”.........✍️



       Miran Jasim Miran Arshaan kuyi takanku aradu ba ruwana😂🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


No comments

Powered by Blogger.