Daudar Gora Book 1 page 6


 *_6_*


......Baki ta murguɗa da juya idanunta farare tas tamkar madara cikin nasa da ya kafeta da su. “Inma kai mayene to wlhy bazan ciyu ba, Babiy kullum addu'a yake min shi da Ummu”. Tana gama faɗa tabar wajen.

     Yaransa na waccan ranar ne dai yau ma a tare da shi. Kuma suma sarai kalaman Iffah da bazasu manta muryarta da wuri ba ta shiga cikin kunnuwansu. Dama sune suke dubama yaran dake tare da su books ɗin, shi ko yana biye da su ne kawai da binsu da idanu. Ɗaya daga cikin yaranne ya nuna littafin da Iffah ta ɗauka, su kuma kasancewar suna ɗakkoma sauranne sai shi da kansa yay yunƙurin ɗakkowa kafin su suyi hakan. Yunƙurin zagayowa wajen Iffah ɗaya daga cikin yaransa yayi, dan yay alƙawarin yau sai ya daddala mata mari, amma sai ya dakatar da shi ta hanyar yima ɗayan alamar ya tsayar da shi da ido. Da sauri wancan da shima yake jin kamar suje su haɗu su faffasa mata baki ya kira sunan wancan. 

      “Azaan!”.

   Cak ya tsaya tare da rumtse ido da cije baki dan yasan dai ogane zaisa Fakhir ɗin ya dakatar da shi. Gashi harya hango Iffah dake gaban mai biyan kuɗi. Dole ya haƙura badan yaso ba, amma yaci alwashin duk randa suka sake haɗuwa da yarinyar can babu oga sai ya mata karyawar gasashshiyar masara danta tabbatar itace zata gujema haɗuwarsu ba su ba kamar yanda ta faɗa.

      Iffah dai tuni ta biya kuɗin littafi daya cinye mata duka kuɗinta babu ko na bawa mai Mototaxi (napep). Sai mita take a ranta Littafin yayi tsada, koda ta fito ta iske mai Mototaxi ya cika yayi taf. Tana isowa inda yake hannu kawai ya miƙa mata alamar ta bashi kuɗinsa ya wuce. Fuska ta ƙyaɓe ta cikin niƙab ɗinta tana wani kif-kif da idanunta da kawai yake gani. “Oh oh kaiko duk daɗin asara ai ta jira samu ko? Idan mukaje inda zani nace maka bazan biyaka bane?”.

      A fusace yana mai dalla mata harara yace, “Na fasa kaiki, dalla malama bani kuɗina kije ki hau wata. Kuma har na zaman danai anan sai kin haɗamun”.

    “Lallai sannu shugaban ɓarayin Ruman. Saboda Babiy yamun baki ko? Idan kaga zaka ɗaukeni muje na baka kuɗinka ka daukeni, in kuma zaka zauna wage baki kana ihu ne na tare wata na hau ka biyoni a baya dan bani da shi anan sai naje gida”.

         “Baki da hankali”. Mai Mototaxi ya faɗa a matuƙar fusace yana fitowa. Harga ALLAH Iffah ta tsorata, dan tasan wannan mai zubin samudawan ƙarnin farkon fyaɗa daya zai bazar da itane a titin nan sai dai a kaima su Ummu gawarta. Amma tsabar ƙarfin hali sai faman fiki-fiki take da idanu da faɗin, “To sai kayi duk abinda ma zakayi mana”.

      “Hakama kika ce?”.  Ya faɗa yana matsota. Jikinta taja baya tana wani zazzaro masa manyan idanunta masu matuƙar sheƙi tamkar ta tara ruwan hawaye a ciki, “Idan hanunka ya taɓa koda abayar jikina sai na ɓallashi! Idan kuma ka isa ka gwada”.

    “Kan uban can kayyasa, ke yarinyar nan kin san wanene ni kuwa? To dan ALLAH gwada ɓallamin hanun nagani”. Ya faɗa yana yo kanta da gaske. Securitys ɗin dake a bakin bookshop ɗinne sukai saurin taresa, dama dai ganinsu yasa Iffah wannan hura hancin, ganin ta samu yanda takeso baki ya ƙara buɗewa ta buɗe baki zata cigaba da tsiwa idanunta suka sauka a kan mutumin nan. Yanayin takunsa na isa da ƙasaita kawai saka rawa a zuciyar Iffah yake, sai dai kasancewarta yarinya mai ƙarfin halin tsiya da rashin son a ga gazawarta yasa baka isa ganin wannan tsoron ba a kan fuskarta. Janye idanunta tayi tamkar bata gansa ba, shima sai ya cigaba da takowa tamkar bai ganta ɗin ba yaransa da tawagar yara kusan goma sha biyar biye da su. Kamar waccan ranar yau ma sanye yake cikin suit da sukai matuƙar fidda ƙyawun halittarsa ta tsayayyen mutum, saɓanin ranar na yau baƙaƙe ne, sai dai sunyi matuƙar dacewa da lallausar farar fatarsa mai matuƙar sheƙi da ɗaukar idon mai kallo. Ga mayataccen ƙamshinsa irin na ranar mai saka zuciyar mai shaƙa raunana da nutsuwa. Harya gotasu zai wuce a binsa sai kuma ya tsaya cak, hannayensa duk biyu ya zuba a aljihun wandonsa tare da juyowa. Ita ya fara kallo, sai kuma ya janye lulu idanunsa masu tabbatar da kwarjininsa da kamewarsa ga duk wanda ya kallesu ya maida kan securitys ɗin nan dake riƙe da mai Mototaxi ɗin har yanzu. Azaan daya fahimci mi ogan nasu ke nufi yay saurin faɗin “ku sakesa” duk da har cikin rai baiso hakan ba. Babu musu suka sakesa, shiko sai huci yake idonsa akan Iffah data juyar da kai gefe irin bata sanma mi'ake ɗin nan ba. Hanunsa ɗaya ya zare daga cikin aljihunsa ya ɗan ɗaga rigar suit ɗin tasa. Kuɗine masu yawa ya zaro ya miƙama mai Mototaxi ɗin. Cikin rawar jiki ya kai rissine kamar gwiwarsa zata taɓa ƙasa ya amsa yana godiya kamar zai haɗiye harshensa. Kansa kawai ya ɗauke zai juya suka sake haɗa ido da Iffah. Baki ta tura gaba tana fiki-fiki da idanu da sake ɗauke kanta...

      Takaici kamar ya kashe su Azaan. Babu wanda a cikinsu bai harari Iffah ba kafin subi bayan ogansu da tuni yabar wajen. Mai Mototaxi da bakinsa ke washe uwa gonar audiga ya kalla Iffah. “A to hajjaju taho na kaiki koda karshen Daular Ruman ne ma”. Wata banzar harara ta balla masa da jan tsaki tabar wajen. Cike da takunta na nutsuwa ta gitta motarsu dake ƙoƙarin barin wajen. Azzan yay ƙaramar ƙwafa, a ransa yana raya shine zai zama sanadin nakasa yarinyar nan kuwa wataran. Mai gayya mai aiki kam da gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tabbatar masa yarinyar nan aljanar ce idanunsa ya lumshe a hankali yana mai ƙara gyara zamansa na ƙasaita tamkar ba'a mota yake ba....


          Tunda ta samu wata Mototaxi ɗin ta shiga zuciyarta ta tafi tunani. A karan farko take tambayar kanta waye wai wannan mutumin a garin nan?, da ganinsa dai kasan ɗan masu farcen susu ne ko shi a karan kansa ne mai farcen susar. A ƙasan zuciyarta taji tana buƙatar sanin shi ɗin wanene badan wani abu nasa ya birgeta ba. Hasalima haka kawai haushinsa takeji tun akan bige yaron nan da suka kusa yi a waccan ranar da ƙoƙarin guduwa da sukai. Ko kuma ma dai aljanin ne?, dan inba aljani ba taya zata dinga ganinsa duk inda taje gashi har karo biyu.. Tasha ji a bakin mutane ana faɗin ita ɗin ƙyaƙyaƙyawa ce, tafi kowa ƙyau a gidansu, amma ƙyawun wannan bawa da dirarriyar halittar jiki data fuska mai cike da kwantaccen gashi tamkar shiya zaɓama kansa komai sai dai aljanin kam..... Isowarsu anguwarsu ya sata ture tunanin ta nunama mai Mototaxi inda zasu ƙarasa ta amso masa kuɗinsa. Cikin sa'a suna isa ƙofar gidansu sai ga Babiy da Hanash suma an saukesu da alama yanzun ne suke dawowa. Su suka biya mai Mototaxi ɗin kafin su shige cikin gidan bakinta washe tana jera musu sannu da zuwa...


        Labarin alkairin da aka samu na kayan da suka kai kasuwa su Babiy ke basu ita da Ummu, amma ita rabin hankalinta naga abinda take yunƙurin yine kawai. Ta matuƙar ƙagara ai kiran sallar magrib su Babiy su fice masallaci Ummu ta shiga ɗaki. Ana kwaɗa kiran salla kuwa itace farkon miƙewa yin haramar alwala. Hakan da tai baisa wani yaji daban ba dan kowa yasan Iffah da himmar yin salla. Komi take aka kira salla, ko'a ina take inhar wajen zaiyi ibada zata ajiye abinda takeyi kuwa tayi sallar. Wannan halin nata na ƙara sakama iyayenta da ƴan uwanta sonta, dan tunsu Arfa na raye ma sukansu Ummu takan zaburar dasu akan halin Iffah ɗin na kiyaye ibada da ƙoƙarin yinta akan lokaci. Koda ta shiga ɗakin bayan tayi alwala bakin gadonsu takai zaune dan tana fashin salla ne, sai da taji tsakar gidan yayi tsitt sannan ta ɗan leƙo, babu kowa kuwa Ummu ta shige su Hanash sun fita massallaci. Da sanɗa ta fito ledar maganinta na ɗazu da taketa ɓoyo riƙe a hanunta. Wuff ta afka ɗakin Babiy, cikin sa'a bata wani sha wahalar ganin tulunan da aka cika da zuma ba sabbi ƙal. Ta saki murmushi dajin kamar tai ihu dan farin cikin da takeji a zuciyarta. Amma sai ta kanne cikin rawar jiki da ɗan yin leƙe-leƙe irin na mai tsoron a kamasa yana laifi tana ƙoƙarin buɗe kwalbar. A tulun farko ta zuba kusan rabi, sai kuma ta dakata bisa shawarar zuciyarta akan ta zuba duka tunda bata da tabbacin dukansu Tajwar ɗinne zaiyi amfani da su. Ƙaramin sandan data shigo da shi tasa ta motsa da ƙyau har saida ta tabbatar ya gauraye sannan ta sakama ɗaya, tana tsaka da juyawa ta tsinkayo muryar Ummu na kiranta. Ido ta rumtse da sauri tana ambatar sunan ALLAH, da hanzari ta shiga rufe roban sauran maganin saboda jin kamar Ummu na nufi ɗakin, cikin riga ta saƙa maganin da sandar sannan taɗan leƙo. Can ta hango Ummu ta nufi kitchen ɗinsu, aiko tai wuff ta fito ta faɗa ɗakinsu. Ummu data juyo saboda jin kamar motsi ta sake ƙwala mata kira. Yanzu kam amsawa tai da fitowa tana gyara mayafin abayarta. 

      “Yi haƙuri Ummu ina karatune”.

   “Shine kuma bazaki mun ko gyaran murya ba zaki barni ina wage baki”.

   “Kiyi haƙuri to Ummuna”.

Ummu ta fito daga kitchen ɗin tana gyara mayafin jikinta itama. “Jeki ki cigaba da karatunki dama motsi naji kamar, amma fara duba kosu Hanash sun bar mana ƙofa buɗe ne”.

         Da to Iffah ta amsa tana nufar hanyar soro da sauke ajiyar zuciya...


  Tana shiga ɗaki wani uban tsalle tai ta dirga saman gadonsu dan farin ciki. Mulmula take tana dariya irin wadda ta jima batayi ba, wauta da ƙuruciyarta tafi hango mata nasararta na ɗaukar fansar ƴan uwanta fiye da tunanin idan wani abu ya faru Babiy ne na farkon wanda za'a tuhuma kasancewar zumar daga hanunsa ta fito. Haka Iffah ta ƙarasa wannan dare cike da zumiɗin ganin wayewar gari Babiy ya kai zuma masarauta. 

      Bayan ta idar da salla yau ko fama da ita Ummu batai ba akan shirin tafiya makaranta, a da kuwa saita tasota daƙyar kasancewarta mai son barcin safen tsiya da tayi salla take komawa barci. Babiy kansa saida yay mamakin wannan sammakon tashi nata yau, Hanash kam kasa haƙuri yay saida yay magana. Sai cewa tai ai sunada program ne a makaranta yau... Koda taje makaramtar ma dai bawai ta nutsu bane, rabin hankalinta ne kawai ga duk malamin daya kasance da su har aka tashi.


      ★A ɓangaren Babiy kam duk da tabon da masarauta daular ruman ta bar masa a zuciya bai taɓaji koda wani zai bari ya cutar da su ta hanyarsa ba ko shi ya aikata hakan ta damar dake hanunsa na kai musu zuma. Tsaf yay shirinsa kasancewar yau juma'a ce ya ɗiba tulunan zumar nan guda uku ya nufi daular ruman. Idan yaje ba kaitsaye yake ɗaukar zumar nan ya kai ga Tajwar ba, dan ganin Tajwar kam babban abune da sai wanda ya cika ya tumbatsa keda wannan damar. Akwai wanda keda alhakin amsarta shi ya isar da ita inda ya dace har ta isa ga sashen Tajwar ɗin. Bayan ƴan bincike a kansa na kullum da basa ƙarewa ya shiga daular ruman iya ƙofa ta biyu. Dattijo da kamanni da suturar jikinsa kawai ta isa tabbatar maka da shima wanine ya iso ga Babiy bayan zaman jiran kusan mintuna goma da yayi. Cikin girmamawa Babiy ya gaidashi duk da zasu iya zama kusan sa'anni da shi. Shiko ya amsa yana hura hanci irin na masu dama ta mulki a hannu. Umarni ya bama Babiy akan ya ɗanɗana zumar, Babiy da yasan babu wani abu na razani ko shiga dogon tunani kafin ɗanɗanawar kansa tsaye ya kai hannu ya ɗauka cokali dake bisa tire a hanun hadimin dake biye da dattijon nan. Tunda dama haka ba sabon abu bane garesa duk sanda ya kawo sai ya ɗanɗana ɗin. Tulun farko ya kwancema baki kasancewar a ɗaure bakin yake da ganyen ayaba, yasa cokalin nan ya ɗibo zumar da bismillah ya nufi bakinsa.........✍


     *_😬😬😬Iffahhhhhh!!!!🙆🏻._*

No comments

Powered by Blogger.