Daudar Gora Book 1 page 48
*_48_*
...........Babu kwanciyar hankali gasu Kaka, dan har yanzu basu sami bakin zaren jin komai ba game da wadda aka rasa a cikin matan Shahan-shan. Ga tashin hankalin ɓatan Barrister dan sun je har gidansa amma a rufe alamar iyalansa ma dai basa nan. Acewar makwafta kuma dai anzo an
kwashesune a cikin dare, yau kusan kwanaki takwas kenan. A lissafinsu kuma ya kama randa Barrister ya ɓata kenan. Zuciyar kaka ingizashi take kan abubuwa masu yawan gaske amma yana gocewa, dan duk tsanani yayi alƙawarin dogaro ga ALLAH majiɓincin al'amuran bayi a kowane tsanani da sauƙi. Kwanansa ɗaya ya juya ƙauyen Jumna, dan yasan ya baro su Iyyani a tashin hankali.Ilai kuwa koda ya koma sai ya samesu a birkice, dan suma dai zuwa yanzu labarin halin da ƙasar ke ciki ya isa har kunnuwansu. Ummu tayi kuka har hawaye sun daina zuba. Ta gama sadakarwa ta rasa autarta itama. Dama ta jima da fidda rai ga su Babiy tuni. Kaka rasa ma mizai ce da su yayi, dan shima dai nasa kan a zafafe yake. Sai kawai ya shige ɗakinsa ya rufe kansa yana mai safa da marwa.......
★★..... BARRISTER ★★......
Da taimakon masu tsaronsa bisa umarnin ogansu da tun a ganin farko da yay masa bai sake ganinsa ba sai ta waya tun a yammacin ranar suka fara tattara abubuwan da zai basu kariya wajen fita da su Babiy duk da basu zo hanunsu ba har yanzu. Sai dai a daren ranar su Sayeed Harun Al-rashid sukai alkawarin danƙasu hannun Barrister, duk da ya nuna musu shifa yana jin tsoro su bari komai ya kammala sannan suka nuna masa suna tare da shi da kuma tsaro na musamman duk da kuwa ƙarya ne a baɗini.
Zancen kam nasu ya tabbata, dan a daren ranar ƙarfe kusan tara na dare aka damƙa Babiy da Hanash a hannun Barrister Abdallah Aas matsayin Barrister Akeem da zukatansu su suka ɗauka. Daga gani kasan sun jigata matuƙa, sun rame sosai sunyi duhu. Ga rashin ƙarfin jiki da zaman waje ɗaya harma da ƙarancin abinci dana iska mai ƙyau. Hankalin Barrister ya tashi matuƙa, ya dinga share hawayen tausayinsu. Ya sake tabbatar da mutanen nan da suka kamashi mutanen kirki ne a yau, dan ana iso da su Babiy hanunsu sai ga likitoci, dan-da-nan suka duƙufa kansu da kulawa kai kace dama a shirye suke da hakan.......
★★..... MASARAUTA ★★.....
Duk da ƙarancin shekarunta ALLAH ya bata basira irinta masu hangen nesa. Tun bayan gama wayarta da Miran Jasim zuciyarta bata aminta da yarda su gana fuska da fuska ba. Dan haka ana idar da sallar magrib ta tura masa saƙo kamar haka duk da ita ba sallar zatai ba tana fashi.
_Na amince mu tattauna, sai dai bata haɗuwa ba, muyi magana ta video call._
Miran Jasim ya karanta saƙon yafi sau ashirin, takaici kam ba'a magana ga ɗunbin mamakin basirar ƴar ficikar yarinyar. A take ransa duk ya jagule, ga boka Barbushi ya tabbatar masa haɗuwa da yarinyar fuska da fuska yafi fa'ida. Dan kwarjininsa da suddabaran da ya basu zai sakamata tsoronsa mai tsanani ya dinga yanda yaso da ita har zuwa sanda itama zasu ɓaddata bayan ta cika musu aikinsu. Gashi yanzu guri ya ƙure, bazai yiwu masa ba zuwa ga Barbushi ɗin dan zai iya rasa wannan damar da bokan nasu ya tabbatar musu itace ranarsu mafi Sa'a akan yarinyar kasancewar tana fashin salla, tana kuma cikin ruɗanin da ba komai yake iya banbancewa yanda ya kamata ba zasu iya sarrafata a duk yanda sukaso musamman akan Shahan-shan. Duk da sallar isha'i data gama gabatowa haka ya miƙe ya fice a masallacin bayan yayma Miran Arshaan alama da ido. Bai jima da fita ba kuwa yabi bayansa....
“ALLAH yasa dai lafiya na ganka duk a wani birkice?”.
Miran Jasim ya sauke idonsa akan Miran Arshaan mai maganar yana mai jan tsaki. “Wane kwanciyar hankaline da ni inba gani nai komai ya daidaita ba Arshaan. Yanzu ma ƴar iskar yarinyar nan ce wai fa ta turamin text message bata yarda mu haɗu fuska da fuska ba sai dai video call”.
“What! Waini wace irin hatsabibiyar yarinya ce wannan? Nama fahimci kallon sa'aninta take mana”.
“Ka barta karka damu, zata yabama aya zaƙinta ta dai gama mana aikinmu. Anan zata gane ko wanda ya ajiyeta a gidan bai isa ba balle ita karamar halitta. Ni yanzu damuwata ma shine Barbushi ya tabbar mana da wannan ranar ta sa'a, haɗuwarmu kuma fuska da fuska wani babban cigabane garemu.”
“Komai ya kwaɓe kam, sai dai ni a wannan gaɓar ina masa kallon mai sauƙi. Kaga dai a yanzu bamu da isashen lokacin komawa wajen Barbushi, na biyu barin wannan damar ta wuce a garemu kuskure ne. Dan haka kawai mubita a yanda take so ɗin, da sassafe mu nufi Barbushi”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Miran Jasim ya sauke domin gamsuwa da zancen Miran Arshaan ɗin, daga haka basu koma masallacin ba sukai zaman kulla yanda zasu tunkari Iffah bayan sun tura mata saƙon amincewa ayi video call ɗin.
*_10:30pm_*
Ƙarfe goma da rabi na dare agogon ƙasar Iffah zaune gaban laptop ɗin ta, sanye take cikin suturar ta mai sirrinta jiki, iya zagayen ƙyaƙykywar fuskarta kawai ake iya gani. Tayi fayau ga mai kallo baka iya ganin komai sai damuwa da tsantsar ƙuruciyarta. Cikin girmamawa ta gaida dattijan guda biyu dake a fuskar lap-top ɗin tata. Miran Jasim da Miran Arshaan suka amsa mata da kulawa da nuna tausayawa tsantsa a fuskokinsu. Ita dai idanunta a rissine, dan tun kallo ɗaya datai musu bata sake yarda ta ƙara ba.
Miran Jasim yay ƴar gyaran murya da fara magana bayan gaisuwar tasu. “Ibnati mu mun sauke nauyin dake kammu naki, abinda kika yanke kawai muke buƙatar ji domin tsallakar da rayuwarki data ƴan baya. Dan a yanzu mun shirya tsaf ba tsafi ba ko bataliyar ifiritai Eshaan zai sauke a kammu domin danne cewarmu bazamu taɓa yin shiru ba”.
Iffah ta jinjina kai a hankali da faɗin, “Uncles naji daɗin hakan, kuma tun farko dama haka ya kamata ku kasance, duk da dai nasan bai zama lallai kuji irin zafin da iyayenmu sukaji ba. Amma a yanzu daya fara taɓaku gashi kun zaburo. Duk da haka bazamu ƙi karɓar taimakonku ba, dan a yanzu bani da wani abu dana tsana sama da shi, a shirye nake kuma na zama ajalinsa koda nima zan rasa nawa ranne. Sai dai ina son dan ALLAH uncle ka faɗamin gaskiya taya ka samu wannan videon? Ta ya kuma kasan na cikin videon nada alaƙa da ni ne? Miyasa kuke son taimaka mini? Miyasa duk da kun san yana kan rashin dai-dai baku taɓa wani yunƙuri ba a baya sai yanzu?”.
Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai kowanne ransa na susa da mamakin tsaurin idon wannan yarinya da sukema kallon hatsabibiya. Amma a zahiri sai Miran Jasim yaja ajiyar zuciya ya fesar cikin ƙoƙarin danne razanin da tambayoyinta suke neman jefasa. “Ibnati duk wannan ai na abin mamaki bane da har zai saka miki shakku, amma tunda kina son sani yanzu zakiji komai. Wannan video ɗin da kike gani na samosa ne a system ɗin Eshaan, bakuna shi kaɗai bane ba. Akwai ire-irensa da yawa harma dana yanda aka hallaka matansa na baya. Ina haɗasu ne domin miƙasa kotu a kwatarma masu hakki hakkinsu duk da ina fargabar ƙarfin iko irin na Shahan-shan bazai bari a hukunta shin ba kasancewar komai sai da say ɗinsa ke gudana a ƙasar ruman baki ɗaya. Sanin alaƙarki da wannan video kuwa ta samune duk a dalilin bibiyar tasa, sai dai bamu tabbatar ke bace ba sai a ranar da kika samesa tare da Arshaan Akh suna wasan takkubba. Sannan kasa tunkararsa a baya Ibnati bazaki gane ba, ƙarfin ikon Shahan-shan fa bana wasa bane ga kowa....”
“Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faɗin, “Idan baki manta ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari data dace da shi a yanzu. Buɗar bakinsa sai ya sake tsaki da faɗin, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba'asin hakan amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa ya duƙufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a ƙauyen Jumna”.
Sosai Iffah ta zabura da jin sun gana da kaka harta ɗago ido ta na kallonsu. Tabbas sihiri gaskiya ne, kuma yakanci kowama tunda har yaci ma'aikin ALLAH. A take wani abu mai sanyi ya dinga shiga jikin Iffah tamkar ana kwararashi cikin jininta. Hawaye ne suka silalo a idonta ta buɗe baki a hankali ta furta “Tabbas zan kashesa da hannuna, zan kashesa da dafin maciji na gaskiya kamar yanda yake halaka mutane dana tsafi. Nayi alkawarin yanda ya wargaza min ahali nima sai na wargaza rayuwarsa..”
Miran Arshaan da Miran Jasim suka kalli juna sukai murmushi. “Zako mu baki dukkan gudunmawar da kike buƙata Ibnati. Tare da kariya ta musamman ga duk wanda zai iya kawo miki hari, balle ma a yanzu abinda zakiyi sai dai ya ƙara kawo miki ɗaukaka dan irinki ƙasar ruman ke nema. Mi kike buƙata a yanzu?”.
Kai tsaye ta amsa da cewar, “Dafin maciji mai matuƙar haɗari”.
“Zako ki sami na macizai ma ba maciji kawai ba. Ki saurari saƙo zuwa safiyar gobe. Mun barki lafiya”.
Wani irin kuka mai taɓa zuciya Iffah ta saki, a hankali ta zame takai kwance kanta da yay mata nauyi na sara mata. Gaba ɗaya duniyar tai mata dummm bata gane komai, burinta kawai shine ta ɓatar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Gawarsa kawai tafi bukatar gani kwance a ƙasa fiye da komai. So take taga ahalinsa na kuka fiye da wanda sukai a dalilin rasa ƴan uwansu saboda son kansa. Haka ta kwana a wani irin bahagon yanayin da bazata iya koda tunawa ba. Ita bamai barci ba ita ba ido biyu ba, ita ba matacciya ba ita ba mai rai ba gadai tanan. Duk da tana fashin salla ana kiran salla ta miƙe, bayi ta shiga ta tsaftace jikinta duk da babu wani ƙazanta tattare da ita, tana ƙoƙarin naɗe gashinta daya ɗan warware takeji kamar magana a ƙofar ɗakin nata. Cikin shakku ta gyara rigar wankar jikinta ta nufi ƙofa ta buɗe. Da mamaki take kallon amintacciyar hadimarta mai suna Abal dake a durƙushe hanunta ɗauke da ƙyakywan bowl.
Da sauri Abal takai ƙasa tana gaidata. Batare da Iffah ta amsa ba ta ɗaga bakinta da yay mata nauyi da ƙyar tace, “Lafiya.....?”
“Lafiya Lau ya Zawjata-almilk. Saƙone daga sashen mai Babban ɗaki”.
Hakan ya ɗan saka Iffah a shakku da mamaki, amma sai bakinta yay mata nauyi bata iya ta sake cewa komai ba ta amshi tambulan ɗin mai ɗauke da sabuwar madara fara ƙal. Idanu Iffah ta tsurama madarar wani shawa'ar shanta na fusgarta. Amma sai ta dake ta ajiye ta da nufin sai ta gama kimtsawa tasha ko kaɗanne kaffin ta sake komawa barci. Harta nufi kayan data fiddo zata saka kira ya shigo wayarta. Ruɗewa tai dan abune da bai taɓa faruwa da ita ba, kofa sallar asubahi ba ayi ba. Kamar wadda ake ingizawa da remote ta ɗauka wayar, ganin Miran Jasim ta amsa da tsumar jiki tana gaisheshi kai kace yana a gabanta ne. Bai amsata ba, sai ma umarni daya bata cikin kakkausar murya saɓanin wadda yake mata magana da ita a baya.
“Wannan madara ce mai ɗauke da dafin macizai masu haɗarin gaske har guda biyar, daga yanzu zuwa ƙarfe takwas na safiya ina buƙatar jin kukan mutuwa. Kukan mutuwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed nake buƙatar ji har gadon barci na ta dalilinki”.
“An gama ranka ya daɗe”.
Iffah ta amsa da rawar murya hawaye na ciko mata ido ga girmamawa har tana rissinawa kamar tana a gabamsa.........✍️
*_🤦ALLAH sarki Iffah baki shike yanka wuya. Kin ɗauka niyya badan zuciyarki zata iya ba a zahiri, gashi masu babban burin sharri zasuyi jifa da hannayenki batare da kin san illar hakan ba a gareki._*
Leave a Comment