Daudar Gora Book 1 page 47

 




*_47_*

........Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen Sayeed Khairul-Bashar ta'aziyya har ya isa kunnen surukarta dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat

Haseenat da su Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah ya shigo wayarta. Bata ɗaga ba, aka kuma sake kira nan ma dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah ɗin back. A bugu biyu ta ɗaga, Iffah ta taɓe baki cikin rashin damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaƙa ma da fitar.

        “Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin hankali matuƙa, gashi yana ƙara harzuƙa mutane ƙasa, kinga dai yanda ƙasar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma yana cikin masarautar nan?”.

     Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku manya bakuce komai ba.”

         “Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarƙaƙiyar dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai matsala, akwai kuma gagarumin al'amarin dake ɓoye amma yana son bayyana kansa a wannan gaɓar.....”

    Cikin zumuɗi Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”.

   “Humm Fareedah kinyi ƙarama da yawa ba yanzu ba. Ke dai kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min idan Abni yana a gidan nan...”

          “To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa. Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”.

     Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke dai gwada sa'arki mu gani”.

    Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba sukai sallama.....


      ★★.... ★.....


   Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake faruwa ne?”.

      “Zai dai faru”.

Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi kake son cewa ba Jasim Akh?”. 

     Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki. “Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da gaske.”

        “Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.

     “Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu ba?”.

   “To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh. Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma jami'an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai......”

       “Amma shine kai shiru?!”.

Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.

    Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna.

          “Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.

     Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.

    “Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”.

     “Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan uwana”.

    Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da ɗan boto ina daga kwance). 

    Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah da Daneen Ammarah daga can......


       ★★.....


     Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar. 

     “Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.

   Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani bane ba dai?”.

        Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.

     (Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.

          Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo...


      ★★....


    Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba ƙaramin hatsabibiya za'ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko tsallaken kalma ga shegen wayo”.

       “Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga fiye da hakan tattare da ita. Irin waɗan nan yaran masu taurin zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su mata ga mai mulki ba karamin ƙara samun power bane. Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen ƙyau da ƙira tamkar ita ta zana kanta...”

      Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba, na ɗauka tuni ka jingine batun son matan nan naka kodan kujerar da ke gab da zama taka”.

         “Bazaka gane bane Arshaan Akh”. Miran Jasim ya faɗa yana tasa ƴar dariyar shima da komawa jikin kujera ya lafe ƙyaƙyƙyawar surar Iffah da bata wuce sa'ar autarsa ba na masa kaikawo. Shima dai Miran Arshaan ɗin hakance a ransa, dan tun randa suka haɗu da Iffah a wajen wasan takobi da Tajwar Eshaan yarinyar ta kasa barin ransa. Duk da dai shi yanzu kam ya ɗan rage bin mata tun aurensa da Jasrah. 

     Humm masu karatu Bara na ɗan tsakura muku wata gulma dai karna wuce. (A baya ƙiyayyar ƴan ɗakin su Miran Jasim da Miran Arshaan a bayyane take fiye data ƴan ɗakinsu Tajwar Haysam (mahaifin Tajwar Eshaan kenan) amma a wasu shekaru bayan hawa mulkin Tajwar Haysam sai aka wayi gari sun ɗinke, ƙiyayyar da sukema juna ta koma ta ƙarƙashin ƙasa. Wannan haɗin kai nasu kuwa ya samo asaline a dalilin kasancewar halinsu da yazo ɗaya. Awani lokacin bikin al'ada kamar yanda duk suka saba sun baza yaransu samo musu yara matasan ƴammata masu jini a jika da basu gaza sha bakwai zuwa ashirin ba. Karku ɗauka da yardar yaran wai ake kai musu su, ko ɗaya, ta karfin tsiya za'a ɗaukeki bayan an shaƙa miki abu ko an yaudareki, bazaki tashi tsintar kanki ba sai a ɓoyayyen gurin da in zaki kwana dubu ihu babu mai jinki. Idan sun gama lalata rayuwar yaran kuma a jefar da su. Alokacin da labarin yaje ga Tajwar Haysam hankalinsa ya tashi, dan a shekarar an samu gawar yara ƴammata kusan biyar da waɗan da aka jikata, iya bincike kuma na jami'an tsaro ba'a sami komai ba. Da shekara ta dawo kuwa yasa tsatstsauran tsaro akan kaikawon mata fiye da maza, aka kuma sake sabon tsarin yanda bikin al'ada zai kasance. Ransu Miran Jasim ya ɓaci matuƙa, dan ƙarshe sai a yaran masarauta suka huce haushinsu ƴaƴan talakawa sun gagara ɗauka. Duk da ba tare suke aikatawa ba sai shirunsu yazo ɗaya a lokacin, har ya kasance yaransu dake sato musu ƴammatan sunyi haɗaka akan yarinya rigima ta kaure, kowanne ya sanarma ogansa, a zafafe Miran Jasim da Miran Jasim suka buƙaci sanin juna kowanne da tunanin shike da ƙarfin iko, sunko haɗun a yanayin da hantar kowanne ta kaɗu dan mamaki, amma ƙwallafa rai da kowannensu yayi akan yarinyar ya sasu amincewa juna yin tarayya da ita a tare Wa'iyazubillah 😭🤦. Haka suka haɗu suka lalata rayuwar yarinyar daga ƙarshe ta rasa ranta, a cikin masarautar suka bizneta har a yau kuma babu wanda ya san hakan sai ɗauka da ake yarinyar ta ɓata ne a taron bikin al'ada. Wannan shine sanadin zamowarsu inuwa ɗaya dan wannan ya basu ƙofar dinga kawoma juna mata, sai dai Miran Jasim yafi Miran Arshaan ƙwarewa a harkar, dan shi har order mata yomasa ake daga wasu ƙasashen ma🤦). Wanda ya gane na tayasa murna, wanda bai ganeba ya tsallake kawai😂🥱.


      

       ★★ BARRISTER ★★

  

    Kamar yanda su Barrister ke zaman tsammani a yau sai ga kira daga Sayeed Harun Al-rashid, sun tattauna sosai ciki harda yarjewar fita da su Babiy zuwa wata ƙasa da kuma tsananta bincike wajen gani maɓoyar Barrister Abdallah Aas kamar yanda Barrister suka tsara musu. Abu mafi saka Barrister a ƙololuwar farin ciki shine damƙa fita da su Babiy ɗin a hannunsa, amma a zahiri sai ya nuna hakan ba aikinsa bane, shifa ya bada shawara ne kawai.

          A ɓangaren su sun nuna masa sufa sun yarda da shine, bayan shi kuma bazasu iya bama wani aikin ba gudun abinda zai je ya dawo. Bayan dai ɗan cigaba da tirjewa da ga ƙarshe Barrister ya amsa. Hakan ya musu daɗi suma, dan a nasu ɓangaren sun bashi aikinne domin ƙullama rayuwarsa, acewarsu koda ta tashi salin alin zasu zare hanunsu su barsa a ciki.

        Barrister da ya gama fahimtar su da ƙudirinsu duk da basu fito sun faɗa ba yay murmushi yana mai girgiza kansa da mamakin mutanen wannan duniya mai cike da rikici.  “Son kai shine tushen rugujewar kawunan mu a wannan duniyar. Mai mulki kansa kawai ya sani. Mai arziƙi kansa kawai ya sani. Talaka kansa kawai ya sani. Mai ilimi kansa kawai ya sani. Jahili kansa kawai ya sani. Iyaye kansu kawai suka sani. Matasa kansu kawai suka sani. Yaro kansa kawai ya sani. Kowa akan buƙatarsa kansa kawai yake iya kallo. Duk shaƙuwa irin ta ma'aurata akan son kansu kowanne zai iya aikata komai. Duk shaƙuwa irin ta ɗa da iyaye akan son kansu zasu iya komai. A wannan duniyar yanzu samun cikakken amini sai an tona, ka gama yarda da mutum amma akan son kansa zai iya komai. Son kai dai! Son kai dai ya rabbi. Ƴan uwa son kai fa na kawo abubuwa da yawan gaske. Yana gina hassada a zuciya, ƙyashi, zalunci, raunana imani, ƙarya, munafunci, kai komai ma wlhy, hatta shirka tana iya shiga a cikin son kai batare da mun sani ba. Ya rabbi ka ganar damu gaskiya tun kan ta nisanta a kunnuwanmu da idanunmu.......✍️  


      (Wannan zance haka yake Barrister, ALLAH dai ka shiryar damu🤦).


No comments

Powered by Blogger.