Daudar Gora Book 1 page 46
*_46_*
..........Lokacin da kaka yayi ma Abu Zainab rakkiya sukejin halin da ƙasar ke ciki, dan shima Abu Zainab kasancewar fitowar sassafe yayi sannan komai bai fasu ba. Hankalinsu yayi matuƙar tashi dan basu san wacece a cikin matan sarkin ta rasu ba.
“Zakariyya zama bai ganni ba, dole ne mu wuce tare kenan, kayi haƙuri kaɗan jirani anan ina zuwa”.
Kaka bai jira cewar Abu Zainab ba ya koma gida da sauri, koda su Iyyani sukaga a yanayin da ya shigo suma hankalinsu ya tashi, amma tambayar duniya yaƙi ce musu komai kan abinda ya farun, sai cemusu da yay shima zaije Daular ruman ne.”. jin wannan furucin nasa yasa jikin Ummu fara rawa, a hankali ta zube ƙasa dan zuciyarta ta gama bata kodai ta rasa Iffah ko su Babiy. Dama yau kusan gabbanin asuba tayi mafarkin Iffah na kuka da kiranta tazo ta ceceta, sai kawai ma zuciyarta tafi karkata akan Uffan..
Su Kaka sun iso daular ruman a harmutse, dan ƴan zanga-zanga nata da ɗa karuwa harma abin na bama mutane mamaki. Yayinda jami'an tsaro tuni sun fito ta kowane titi na masarauta sun tare. Da ƙyar suka samu ƙarasawa gida, kasancewar ana aikowa gidan domin halartar jana'iza yasa Kaka yay tunanin wannan ma indai Iffahr ce zasu aiko. Dan haka suka shiga tambayar ƴan anguwa amma kowa na tabbatar musu babu wanda yazo. Hankalin Kaka ya tashi fiye da farko, dan kuwa dai bayan wannan hanyar babu wata mai sauƙi da zai iya ji sai abokinsa dogon yaro da ke cikin masarauta. A yanda kuma garin yake hakan abune mai wahala a garesa kenan......
★ BARRISTER ★
Yanayin da aka wayi gari a ƙasar bai hana su Barrister fitowa ba, sai ma lokacin shi yasan abinda ke faruwar, al'amarin ya taɓa masa zuciya, dan ta wani fannin case ɗinsa tamkar kacokal yanada alaƙa mai ƙarfi ne da abinda ke faruwar. Har yaji yana tsoron ace yarinyar ce ma ta rasa ran nata. Dan dole dai ya daure ya isa inda ya nufa. A yau dai bai samu Sayyid Faizul-Anwar a falon ba, sai dai kasancewar an san da zuwansa ya samu tarbar data dace. Bayan zaman kusan mintuna arba'in Sayeed ya fito cikin shigar jallabiya, cikin girmamawa Barrister ya gaidashi, ya amsa masa da kulawa shima yana masa barka da zuwa. Suna tsaka da gaisuwar cikin yaran Sayeed ya shigo ya isar da saƙon zuwan wasu baƙin. Damar shigo da su ya bada dan yasan da zuwansu, daga haka ya maida hankalinsa kan Barrister.
Barrister yayi matuƙar mamakin ganin baƙin, sai dai ya danne hakan dalilin kallon da suke masa matsayin Barrister Akeem. Gaisuwa sukai ta mutunta juna, har suna tsokanarsa da cewa shine idonsu na gari. Murmushi yayi yana rissinar da kai alamar girmamawa. “Kar kuji komai ranka ya daɗe, a komai muna tare da ku kuma zamu kare mutuncin ku”.
Sosai suka nuna jin daɗi da zancensa. Nan suka shiga kwarzantashi. Shi dai nasa murmushi ne a zahiri, a kasan rai kuma yana matuƙar mamakin abokinsa da ɓoyayyun ayyukansa. Dan bai taɓa tunanin Barrister Akeem zai iya irin waɗan nan ayyuka ba.....
“Barriter ina alkawarin mu?”.
Sayeed Faizul-Anwar ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya yaja a ɓoye, sai kuma ya muskuta yana murmushi da taɓa bag ɗin daya shigo da ita. “Ranka ya daɗe komai yazo hannu fiye ma da yanda kuke buƙata. Sai dai kafin mukai ga nan ina son nace wani abu saboda wasu dalilai”.
“Faɗi kanka tsaye Barrister baka da damuwa akan hakan”.
“Nagode ranka ya daɗe. Bawani abu bane mai girma akan dai shi wannan case ɗinne. Komai dai gashi na gani anan kuma na tattaro, sai dai yanda aka bani aikin a dunƙule ina ganin ya kamata nace wani abu duk da dai naga komai a kansa, amma saboda nasan inda duk ya kamata na toshe a ramukan da zasu iya yunƙurin buɗewa koma su buɗe ɗin yasa nake son bada shawara bisa wani hangena”.
Shiru kamar bazasu ce komaiba. Sai dai sun maida dubansu ga Sayeed Faizul-Anwar, kai ya gyaɗa musu alamar tabbatar da babu matsala, dan haka kusan a tare suka sauke numfashi, kafin ɗaya a ciki ya shiga faɗin. “Barrister mun yarda da kai, sai dai ka sani koda baka san komai akan case ɗin nan ba bazamu taɓa bari wani rami a buɗe mana ba koya buɗe maka, zamu kasance a bayanka a kowanne lungu da saƙo na ƙasar nan.”
“Nagode da wannan karamci”. Barrister ya faɗa da girmamawa.
“Baka da damuwa Barrister ka cancanta ne.”
Murmushi ya sake saki tare da mikewa ya kai jakar gabansu, cike da farin ciki suka buɗe suna mai fiddo duk takardun ciki. Bayan sun ɗan dudduba su suka ɗago fuskoki cike da murmushi suna yabama Barrister namijin ƙoƙarin sa. Shi dai nashi murmushi ne kawai. Ɗaya daga cikin baƙin da ake kira da Sayeed Harun Al-rashid, babban mutum ne a ƙasar ta ruman, dan riƙƙaƙen ɗan kasuwa ne na gwal da kowa ya sani kasancewar sunansa yayi matuƙar shura a wannan harkar data zama babban tattalin arzikin su na ƙasar, dan Ruman kam bata san iya arziƙin gwal da ALLAH yay mata ba, shiyyasa duk wani riƙƙaƙen ɗan kasuwa zaka samu gwal ɗin ne mafi rinjayen makaminsa kamar dai Sayeed Harun Al-rashid. Ta wani gefen kuma yana riƙe da sarauta sai dai yafi bama kasuwancin muhimmanci matuƙa. Zamansa ya gyara sosai yana fuskantar Barrister. “Barrister yanzu mi kake son ka sani?”.
“Ranka ya daɗe ba komai bane dama sai akan waɗan da naga case ɗin ya karkata. Na duba dukkan bayanan Barrister Abdallah Aas, sai dai a yanda na fahimta kamar ya gano inda su mutanen dake hannun naku suke, dan kafin ma ya rasa ransa kamar ya fito da ga ƙauyen Lufana ne wajen matar marigayin, abinda nake son cewa anan ina tsoron yazam bayan Barrister ɗin akwai wanda yasan wannan sirrin. In kuwa hakan ta kasance zaman mutanen a station ɗin dana fahimci kun ɓoyesu zai zama barazana ke nan koda anan gaba”.
Kusan a tare sukai murmushi, Sayeed Harun Al-rashid ya muskuta zamansa cikin nuna damuwa da zancen Barrister. “Maganar ka nakan hanya Barrister shiyyasa tun kafin yau muka gama maganin duk abinda kake gudun. Tun daga farkon wannan case ɗin idanunmu akan komai suke, dan haka ka kwantar da hankalinka. Su kuma tuni basa a police station ɗin, dama mun kai ajiyar su ne domin ɓadda kama bayan kwanaki kuma muka ɗauke su, amma kai a yanzu mi kake son cewa?”.
Anzo dai-dai gaɓar da Barrister keson azo, dan haka ya ɗan murmusa yana mai ƙara bama kansa nutsuwa. “Alhmdullh kun fahimci inda nake buƙatar akai ranka ya daɗe. Abinda nake son cewa kai tsaye shine ayi duk yanda za'ai cikin kwanaki biyun nan abar ƙasar ruman da mutanen gaba ɗaya”.
“Eh maganarka abin dubawa ce kam, amma kuma mizai hana kawai a ɓaddasu a wuce wajen, dan abinda ya zama dalilin zuwansu hanunmun ma an sameshi cikin sauƙi yanzu haka”.
Barrister yay ɗan jimm dan bai fahimta ba, amma sai ya dake bai sake musu wata tambaya ba gudun karsu zargi wani abu. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Ɓaddasu bashine mafitaba ranka ya daɗe, dan a ɗan bincike da nayifa akwai babbar matsala game da mutuwar Barrister Aas”.
Babu wanda zancen bai daka ba a acikinsu, Sayeed Faizul-Anwar daya kafe Barrister da ido yay saurin faɗin, “Barrister bamu fahimce ka ba, mi kake son cewa?”
“Ranka ya daɗe yanzu zan fahimtar da ku. Idan har kun saurari dukkan labaran dake yawo har yanzu babu wani tabbaci na samun alamar sassan mutum a cikin motar Abdallah, wannan shine yaja hankalina tun a ranar farko bayan nabar nan na fara nazari da bincike. Tabbas Abdallah na raye, sai dai ya ɓoye kansa domin bada ƙafa. Na sanshi nasan mizai iya fiye da tunaninku. Shiyyasa nake ganin kashe mutanen a yanzu bashine mafita ba, muyi nesa da su da ƙasar nan ta yanda babu inda zasuji ɗuriyarmu, sai kuma mu samo wasu a madadinsu a buɗe shari'ar ta yanda zamu ƙona Barrister Abdallah Aas da ransa batare daya farga ba”.
Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci. Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji komai ta waya”.
“Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu yawa har mota.......
★★... BAYAN KWANA BIYU ★★....
A kwanaki biyun nan abubuwa da yawa sun faru tako wane ɓangare, sai dai marasa daɗi sunfi masu daɗin rinjaye. Zuwa yanzu dai da gaske ƙasar ruman da jama'arta suke basa buƙatar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed matsayin Shahan-shan. Dan tun tsirarun mutane na zanga-zanga a wasu jahohi takai yanzu ƙasar ma gaba ɗaya ta ɗauka. Abu mafi ban mamaki harda wasu a manyan ƙasar na nuna goyon baya ga talakawa, ciki kuwa harda wasu Tajwar na jihohi. Yayinda ta wani gefen kuma hankalin wasu manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan zanga-zangar dama dalilin yinta.
Babban abinda ke tunzura jama'a shine biris daga Shahan-shan, yayinda kuma a cikin gida hankalin ƴan majalissar sa ya rabu kaso biyu, wasu na goyen bayan ya saukan wasu na buƙatar karya sauka dan shine kawai ya cancanta da kujerar a ganinsu. A talakawan ma bai rasa tsirarun masoya ba, sai dai basu da ƙarfin ja da masu boren shiyyasa suka koma gefe sukai shiru matsayin masu kallo da ido.
*_IFFAH!_*
A kwanaki biyun nan yanda Daular ruman ke a hargitse haka Iffah ke a hargitse. Kuka kam idanunta har sun daina fidda ruwan hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wata irin rama mai ban tausayi. Haukan da iyalan Sayeed Khairul-Bashar keyi a masarautar da wanda jama'a keyi a waje sai ta ɗaukesa wasan yara. Idan su da suka rasa uba kawai zasu harmutsa masarautar haka ina ga ita data rasa ahalinta duka, a ganinta ita ya cancanci ta hargitse ƙasar ruman baki ɗaya ma ai. Sai dai yanda ƴan zanga-zanga ke daɗa ƙaruwa na saka mata farin ciki, dan abin ban mamaki har wasu a cikin Tajwar na jihohi suma sun ƙara tunzura wuta da bada goyon baya akan saukar Shahan-shan ɗin, hankalin ƙasashe kuma ya fara dawowa ƙasar ruman, da alama dai dama a jirace kowa yake da wannan damar. Hakan na sake tunzura ƙwarin gwiwar ƙudirinta.
Wutar wannan al'amari na ƙara ruruwane dalilin shirun Tajwar Eshaan. Babu shi babu cewarsa, harma wasu sun fara tunanin anya kuwa yana cikin masarautar ma ko?.... Duk wannan bai damu Iffah ba a yanzu, hankalinta gaba ɗaya ya tattara ne akan ta ina zata samo dafin maciji. Bata da wani amintacce a cikin masarautar, a waje kam sir Fawzan ne kawai, shima kuma zuwa yanzu ta fara shakku akansa saboda tana ganin ya ɓoye mata abinda ya faru da su Babiy ne bisa wata manufa. Idan tace zata fita a sulale daga masarautar taya kuma zata dawo cikinta? Wannan ƙalubalen keta faman mata kaikawo harya gagara samun mafita a kwanaki biyun nan. Tana a bangarenta bata ganin kowa kowa baya ganinta, waɗan da zasu iya ganinta hankalinsu a tashe yake dan kai tsaye su abin ya shafa, shirunsu kuma sai ya bama Iffah damar fassarashi da abinda zuciyarta ta gama tabbatar mata, dan haka itama a yanzu ta haƙƙaƙe bata da lokacinsu.
Kamar yanda ta tsara bayan sallar la'asar ta shirya tsaf cikin abaya data amshi jikinta, dan ma ta rame ga idanunta da suka ɗan kuklumburo amalar taci kuka bana wasa ba. Duk da masarautar a harmutse take haka ta keta cikinta hadimanta na take mata baya har sashen marigayi Sayeed Khairul-Bashar. Tayi matuƙar mamakin tarbar data samu dan batai zaton irinta ba, sai dai abinda bata sani ba shine su kallon tausayi suke mata da tabbatar da itama bawai ta tsira bane a hannun azzalumin. Dan malamin duba da matar Sayeed Khairul-Bashar ɗin ta ziyarta tun lokacin daya ɓata kafin aga gawarsa ya tabbatar mata akwai ƙulli mai girma da Shahan-shan keyi game da rayuwar Iffah shiyyasa itama bata mutu ba a sanda aka kaita sashenshi. A ranar bata ɓoyema ƴaƴanta komai akan zancen nan data jiyo ba, sun kuma yi niyyar samun Iffah har sashenta da batun washe gari aka tashi da wannan tashin hankali. Wannan shine dalilinsu na mata tarbar data bata mamaki. Ita kuma kasancewar zuciyarta a kusa take tana musu ta'aziyya tana share hawaye da handkherciff. Sai hakan ya ƙara mata kima a idon iyalansa. Yayinda ƴan uwansu kuma da basu san komai na ke jin zafin ganin Iffahr da fassarashi matsayin leƙen wani asiri dan a yanzu wasu a cikin ahalin masarautar su kuma suna ma Iffah kallon wata ƴar kaɗafin Tajwar Eshaan ce tunda har ta tsira daga kisan gillarsa..........✍️
Leave a Comment