Daudar Gora Book 1 page 44
_44_*
..........A hankali ta shiga ƙoƙarin buɗe idanunta da takejin sun mata matukar nauyi, sai kuma ta yunƙura ta tashi da ƙyar tana mai bin ɗakin da kallo. Dishi-dishi take ganin amintacciyar hadimar tata dake rukuɓe gefe ta zabga tagumi, _(An wayi gari da rashin
Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar.)_ kalaman hadimar na ɗazun suka shiga dawo mata tiryan-tiryan a zuciya. Da karfi ta rumtse idanun nata da sukai jajur, ga kanta dake matuƙar sara mata kamar zai rabe biyu. Amma haka ta yunƙura ta sauka a gadon cikin ƙarfin hali da jarumta, dan idan batai amfani da wannan lokacin ba tabbas damarta ta kuɓuce mata kenan, batajin kuma zata sake samun wata cikin sauƙi. Zumbur hadimar ta miƙe itama tana mata sannu, bata iya amsa ta ba, sai nuni da tai mata ta je. Jiki a sanyaye ta fice, ita kuma ta jawo mayafi ya naɗama jikinta.Hadimanta dake falon farko duk suka miƙe, hannu ta ɗaga musu alamar bata buƙatar rakkiyar ta fice ita kaɗai dan babu yanda zasuyi. Da gaske masarautar a hargitse take matuƙa, duk da ba wannan ne karo na farko da aka rasa Zawjata-almilk ba, sai dai haɗi da mutuwar Sayyid Khairul-Bashar ta sake girmama ta Zawjata-almilk ɗin itama a wannan karon, da kuma tsallakewar Iffah da aka fara kaiwa babu abinda ya sameta. Cikin dabara da amfani da harmutsewar gidan tai amfani wajen kutsa kai sashen Shahan-shan. Zuwa yanzu fuskarta ba ɓoyayyar fuska bace ga masu tsaron sashen, dan haka babu wanda ya dakatar da ita sai ma gaisuwar girmamawa da suke miƙa mata duk da ganin nata ya basu mamaki. Su kansu hadimai masu girka abincin Tajwar Eshaan ɗin data samu a falo na uku saɓanin na karshe da ta san suna zama ganinta ya girgizasu, musamman daya kasance har yanzu ba'a fita da gawar Zawjata-almilk ɗin ba. Hasalima babu wanda yaga Shahan-shan har yanzu balle jin motsinsa. Kamar yanda tun a ƙasa bata tanka gaisuwar kowa ba anan ɗin ma bata kulasu ba dan ganinsu ya tabbatar mata anan abun ya faru kenan, ita wannan Zawjata-almilk ɗin a ɗakunan barcin falo na uku aka ajiyeta. Duk da bata san ya suke ba babu ko ɗar tattare da ita ta shige abinta inda take kyautata zaton ɗakunan barcin nan ɗin suke.
Ido rufe take bin ɗakunan ɗaya bayan ɗaya, sai dai har kusan uku duk a rufe suke, bata gajiya ba ta cigaba sai a na biyar ta samu a buɗe. Cikin rawar jiki ta afka ɗakin, yayi kaca-kaca tamkar anyi dambe a cikinsa, dan wasu abubuwan ma duk gasu anan a fashe ƙasa, sai ɗigo-ɗigon jini ta wasu wajajen da dama. Idanunta suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar budurwar da a shekaru zata iya zama sa'ar Arfa shimfiɗe a ƙasa ta jikin gado. Yanda gashinta da jikinta ke a birkice zai tabbatar maka da ta jigata matuƙa kafin ta rasa ranta, dan hanunta na dama dake kaca-kaca da jini riƙe yake da wata kwalbar filawar doco... Alamar ta riƙe domin kare kanta, amma duk da haka sai da akaci galaba a kanta. Iffah da jikinta ke karkarwa ta durƙushe hawaye na rige-rigen sakko mata, dan ji take kamar Fariha da Arfa ne take kallo kwance. Ta jima tana kuka akan gawar kafin ta zabura sakamakon maganganu da takejin suna tunkaro ɗakin, zumbur ta muƙe ta fara daukar video recording ɗin ɗakin har gawar, sai kuma ta ɗauka hoton gawar ta kowacce kusurwa. Jin shigowar za'ai da gaske tai saurin fara neman wajen ɓuya....
Miran Jasim, tare da Miran Arshaan, shugaban jami'an tsaron masarauta, Daneen Ammarah sai Malikat Bushirat da a wannan karon ta kasa haƙuri itama suka shigo. Sai da suka gama bin ɗakin kaf da kallo kafin su ƙarasa kan gawar. Shiru babu wanda ya iya magana a cikinsu har tsahon wasu mintuna kafin shugaban jami'an ya nisa.
“Exactly kisan irin na baya ne dai babu wani banbanci gaskiya, da alama kuma tayi ƙoƙarin kare kanta itama shine dalilin kasancewar ɗakin a haka harma da wannan jinin”.
“Wannan lamari daban mamaki yake, taya za'ai kisa amma babu wani alamar yanda akayisan, a wannan karon kodai za'a canja likita ne? Dan dole dole akwai abinda yake a ɓoye. Yarinyar nan itace ta goma sha biyar da aka rasa, kisan kuma iri ɗaya babu wani bambanci sai kace abun tsafi”.
“Haba haba wane irin kuma tsafi? Jasim Akh. Dole dai akwai abinda bamu sani ba ɗin kam gaskiya”.
“Zancena nakan hanya Ukhti Ammarah. Idan ba aikin tsafi ba mi zamu kira wannan al'amarin ne? Bagashi ita waccan da yake ta gagara ko kuma wani abu daban ta tsira babu abinda ya sameta ko ciwon kai ba”.
“Inaga yanzu duk ba lokacin yin wannan maganar bane, ayi abinda ya dace, a wannan karon kuma ya kamata Abni yace wani abu bawai ya cigaba da yin shiru ba kamar yanda ya saba”.
“Maganarka nakan hanya Miran Arshaan”. Miran Jasim ya faɗa cikin son sake tabbatar wa. Shiru Daneen Ammarah da Malikat Bushirat basu tanka ba, hakama jami'in yanata cigaba da zagaye ɗakin alamar nazari.. duk wannan al'amari Iffah na maƙure a maɓoyarta tana sauraren komai hannunta danne kan bakinta kar kukan da take ya fito har su farga da ita. Koda suka gama abinda suke bayan shigowar doctor da fitar da gawar kasa fitowa tai, sai dai ta zame ƙasa da sake fashewa da wani irin kuka mai ban tausayin dan mutuwar yayunta biyu ta dawo mata ne a rai sabu a yau ganin ta hanyar da suma suka rasasu a zahiri gabanta......
“Kuka bashi zai kuɓutar dake ba kema...”
A razane Iffah ta buɗe idanunta dake kaca-kaca da hawaye gasu jajur. Miran Jasim da tun ɗazun ya lura da ƙafar Iffah amma ya basar har sai da suka fice yayo sau da baya ne a gabanta. Duk da so ɗaya ta taɓa ganinsa ranar liyafar cin abinci da aka kawota nan hakan baisa ta shaida fuskarba a ɗan fisge.
Kai ya jinjina mata cikin ɗage kafaɗu “Yanda ya kashe na baya kema babu tantama hakance zata kasance. Karki ga ya ƙyaleki zata iya yuwuwa shirinki na musamman ne. Amma in har kin shirya kuɓuta daga tarkon sa ni mai iya taimaka miki ne”.
Iffah dai kallonsa take kamar gunkiya, sai hawayen da suka kasa tsaya mata ne kawai ke tabbatar da ita a mai numfashi. Bai nuna ya damu da yanayin nata ba ya cigaba da faɗin.
“Ni sunana Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy. Ƙani ga mahaifin mijikin kenan. Nasan kina buƙatar sanin abubuwa masu yawa akansa amma kinƙi samun kowacce irin dama saboda iyayensa dake zagaye da ke. Duk yanda kike zaton abin ko tsammani ya wuce nan, Malikat Haseena da Malikat Bushirat da kike gani sun san komai game da mutuwar matansa, hasalima da taimakonsu komai ke gudana, zaki iya lura da hakan a yanzu ta yanda duk muka nuna damuwa amma su ko'a jikinsu. Abinda zai tabbatar miki da sun sani kuwa duba da abinda kika ganema idonki ne, taya za'a kashe mutum amma a kasa gane hakan, sannan kuma a sake kawo masa gobe ta mutu hakan baisa an dakata ba. Waɗan nan likitoci da jami'an da kike gani duk an siyesu ne, shiyyasa suke pretending cewar basu san komai ba ko basu gane komai ba. Koda yake su a zahiri bazasuga komai ɗin ba, dan ana kashesu ne ta hanyar tsafi domin ƙarama ƙarfin mulkinsa iko.....” yaja numfashi tare da fesarwa idonsa a kanta yana nazartar yanayin tasirin da maganarsa ke samu a wajenta. Da alama akwai nasara dan haka ya cigaba da faɗin, “Mu ajiye wannan, dan bashi da amfanin cigaba da faɗa miki. Ko kin san mahaifinki da ɗan uwanki ma anyi amfani da jininsu a maimakon naki shiyyasa ke kika tsira saɓanin wannan”.
Zabura Iffah tai jikinta na rawa. Sai dai ta kasa faɗin abinda ke son fita a bakinta. Ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Kinga kwantar da hankalinki, amshi wannan ki kalla. Idan kin kammala sai ki yankema zancena hukunci. Amma ki sani tabbas ta hanyar da aka halaka iyayen nan naki da ita ake bi wajen halaka waɗan nan matan nasa shiyyasa likitoci basa gane komai na barki lafiya..”
Harya ɓacema ganinta Iffah bata iya ta motsa ba, sai dai rawar jikinta da karkarwa a bayyane take. Jin kamar motsin mutane ya sata ɗaukar flash ɗin daya ajiye mata ta sake ɓoye wa. Jami'in ɗazunne ya dawo ɗakin, a wannan karon sun ɗauka hotunan komai a ɗakin da ɗan sake bibbincikawa dan tare yake da yara biyu jami'ai suma. Dole Iffah ta sake lafewa har suka fice sannan itama ta fito.
★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar komawa sashenta cikin matuƙar tashin hankalin abinda ya faru da zantukan wannan mutumi. Kulle kanta tai a ɗaku ido rufe ta saka flash ɗin a jikin laptop ɗinta da bawani amfani dake da shi ba. Abin tamkar wani film video ya fara da shigar Babiy riƙe da Abu Moosa cikin gidansu a waccan ranar, shimfiɗa tabarmar Ummu da bayanin Abu Moosa da bai kammala ba har mutuwarsa. Zuwan matar Abu Moosa da jami'an tsaro abinda Hanash yay mata da tafiya dasu. Daga nan ya yanke. Da sauri tai playing na gaba. A yanzu kam su Babiy ne a mawuyacin hali duk sun rame sunyi baƙi a cikin wani ɗaki. Kan Babiy a saman cinyar Hanash alamar babu lafiya tare da shi, Hanash nata faman shafa masa ruwa a fuska yana kuka. Sautin dariya ne ya fara tashi a ɗakin, kafin shigowar wani mutum da iya jikinsa kawai ake gani babu fuska. A take su Hanash suka zabura yayinda sautin dariya ke tashi da tafa hannayen mutumin. Bayan anyi dariyar mai tsawo aka tsagaita, ƙirjinta yay wata irin bugawa jin muryar Shahan-shan. “A tunaninku bayan samun tagomashi a jinin yaronku ƴan baiwa zan haƙura ne. Ina bazai yuwuba, dan a kaf yaran dana halaka jinin ƴaƴankune na farko daya bani fiye da nasarar da nake buƙata, shiyyasa na fara bibiyar ta uku daku kanku saboda bincikena ya nuna min daga jinin ubansu ne”. Hhhhhhh! Hhhhh!! Kune nasarata ahalin Zayyan. Kune nasarata dole ne kuma na samu hhhhhhh!!!”.
Kuka Hanash keyi da roƙonsa amma babu alamar zai sauraresa. Sai ma wani irin salon siddabaru da yakeyi da hanunsa a take ɗakin ya turniƙe da hayaƙi, sai kuma wata irin guguwa mai ƙarfi ta nannaɗe hayaƙin a tsakkiyar ɗakin. Su Babiy dai tuni sun maƙure a bango. Sai kuma suka shiga ihu ganin guguwar ta zama wani irin maciji daya kusa cinye kashi ɗaya bisa ukun ɗakin, sara ya fara kaima su Babiy da suka dunƙule waje ɗaya shi da Hanash, kafin macijin ya kafa kansa a wuyar Hanash dake ƙanƙama Babiy. Tuni duhu ya gama mamaye jikin Iffah dake karkarwa, ta rufe laptop dan zuwa yanzu ma kukan ya kafe ƙaf a idanunta. Sai wani irin mahaukacin ja da sukayi kai kace wuta aka haɗa a cikinsu. Tun tana iya jin surutan masarautar har ta daina jin komai. Daga haka sai farkawa tai ta ganta a gadon asibiti Daneen Ammarah tare da ita..
Gaba ɗaya ta tsani komai daya shafi Tajwar Eshaan. Dan haka tun buɗe idon farko da tai ta ga wadda ke tare da ita bata sake yarda ta buɗe ba. Hakan yasa Daneen Ammarah bata san ta farka ba. Dama itama kuma tayi matuƙar nisa ne a cikin tunani a kallo ɗaya ma zaka fahimci bata tare da nutsuwarta. Ga wata ƴar rama ta yini ɗaya sakamakon tashin hankalin da ake ciki tattare da ita. Dan tun kai gawar Zawjata-almilk da Sayeed Khairul-Bashar makwanci ba daular ruman kawai ba gaba ɗaya ƙasar ruman a harmutse take. Yau wasu a cikin talakawa sunyi ƙarfin halin fitowa zanga-zanga a wasu jahohin suna kiranyen Shahan-shan ya sauka ko su ɗauka doka a hanunsu.
Fitsari daya takura Iffah ne ya tilastata tashi har Daneen Ammarah ta farga. Da sauri takai hannu ta riƙota tana mata sannu, dauriya kawai Iffah tai na dannewa dan tunanin datai a ɗan farkawar nan Tata zuciyarta ta bata shawarar ɓoye sirrin ranta domin samun cikar burinta. Dan tayi alkawarin a wannan karon sai ta halaka Shahan-shan, ta riga ta ƙuna bata tsoron mutuwa. In har burinta ya cika danta mutu ba komai bane a gareta a yanzu ma tafi buƙatar mutuwar fiye da rayuwa tunda har ta rasa sauran ahalinta kuma miya rage mata.
“Ya akai na zo nan Mamy?”.
Ta faɗa cikin danne komai dake ɓoye a ranta. Daneen Ammarah da farin cikin farkawar Iffah ya sata sakin murmushi yaƙe da ita kuma Iffah ta fassara da wani abu daban ta amsa mata da faɗin, “Sakamakon abinda muke tunanin ya rikeki aka sameki a sume shine aka kawoki asibiti, amma Alhamdullah tunda gaki kin farka”.
Maimakon ta amsa mata wannan zancen sai ta jefa mata tambaya. “Mamy da gaske ta mutu ko?”.
Take idanun Daneen Ammarah suka cika da hawaye. Cikin ɗaci tace, “Sun kasheta Ibnati, sun sami damar da suke buƙata akansa. Gaba ɗaya ƙasa ta harmutse da bore akansa kamar yanda dama suke son cimma buri”.
Iffah ta ɗan lumshe ido ta buɗe zuciyarta na karajin tsanar Daneen Ammarah ɗin da mamakin salon yaudararsu, amma a zahiri sai itama ta marairaice fuska. “Mamy ban fahimta ba?”.
Hawaye Daneen Ammarah ta share, “Ibnati a yau ruman baki ɗaya a harmutse take, talakawa nata zanga-zanga a wasu jahohin akan sai Abni yayi murabus a kujerar Shahan-shan inba hakaba zasu ɗauki mataki. Gashi tunda abin nan ya faru babu wanda yaga idonsa ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi ya buɗe yaƙi”.
Iffah ta rumtse idanu da karfi tana taune lips ɗinta, yayinda take faɗi a zuciyarta da kakkausar murya. (Ni zan ƙarasa musu aikin da kawo musu ƙarshen matsalarsu. Dan ba murabus kawai ya cancanci yi ba mutuwa gaba ɗaya yabar duniyar ya cancanta da shi ba kujerar Shahan-shan da ƙasar ruman kawai ba)..........✍️
Leave a Comment