Daudar Gora Book 1 page 40


_40_*

..........Tsam Iffah ta ƙara damƙe trayn hanunta jin rawar jikinta na neman fitowa, “Barka da safiya ranka ya daɗe”. Ta faɗa cikin ƙarfin hali da jarumtar saka idanunta cikin tsakkiyar nasa da ke tsaye a kanta har yanzu ƙyam. Sai dai duk ƙwaƙwƙwafin

mutum bazai iya gane abinda ke a cikinsu ba balle akan fuskarsa mai cike da gizago akoda yaushe. Ganin bai amsa ba, bai kuma daina kallon tsakkiyar idanunta da ayanzu take ƙoƙarin janyewa a nasa ba, bai kuma janye takobin da kallonta kawai zai iya tada tsigar jikin mutum daga wuyanta ba ya sata ɗan shammatarsa ta goce makoshinta da ga tsinin takobin daya ɗaura matan, sai dai a yanda ya wani lumshe idanu da sauke takobin yasata tabbatar da ya bartane kawai. Gaba tai yunƙurin yi, da yima hadiman da suka iso wajen yanzu nan kallon gefen ido a kaikaice ta saki wani lallausan murmushi mai ma'anoni da yawa a zahiri. A kuma ƙasan ranta ko ɗar babu.

     Duk wannan abun Miran Arshaan fa na tsaye a wajen ne yana ƙarema Iffah kallo a kaikaice cike da mamakin ƙarfin halin yarinyar, dan tunda yake a wannan masarauta bayan shi babu wani mahaluki daya taɓa zuwa wannan wajen sai Shahan-shan da hadiman dake kula da wajen. Amma a yau sai ga yarinya ƙarama da babu alamar tsoro a cikin idanunta a wajen. Sai kuma yanda tayi kamar bata gansa ba yay matuƙar ƙona masa rai amma ya dake dan yana buƙatar ganin ƙarshen wasan.... 


        Wajen duk da filine na karshen ginin (rufinsa kenan) ya ƙawatu da abubuwa kashi-kashi na more rayuwa. Ga wani ƙamashin furanni da aka ƙawata waje dana fresh air masu narkar da jinin mutum da sanya kasala. Da sauri ɗaya daga cikin hadiman da suka shigo wajen da abubuwa a hanunsu ya ƙarasa ga Tajwar Eshaan dake murza goshinsa kansa a ɗan rissine ƙasa. A gabansa ya dirƙushe yana mai miƙa masa kufan takobin hanunsa da babu tantama anyi adon jikinsa da gold ne. Takobin ya ɗaura masa kan dogon trayn da kufan yake. Hadimin ya miƙe da sauri yana ja da baya. Na biyu ya iso da sauri shima, sai dai saɓanin na farko shi bayansa ya koma yana warware farar rigar hanunsa mai maɗauri. Hannayensa ya ware da ɗan kai idanunsa inda Iffah ke tsaye tana tsiyaya shayi a karamin kofi, ya wani irin ɗage kafaɗu da juya rigar cike da salo ta rufe jikinsa tare da zarge igiyoyin biyu akan damammen cikinsa. Hadimi na uku ya iso shima ya durƙushe hanunsa dauke da ƙaramin farin towel. Nan ma dai ɗauka yay ya rataya a kafaɗa bayan ya ɗan tsane zufan daya taru masa a gefen wuya da goshi alamar dai jininsa a tsinke yake a lokacin. 

       A yanda hadiman suka sani daga haka hanyar da zata maidashi bedroom ɗin daya kwana yake bi, acan zai samu shayinsa na ƙa'ida mai dafawa ta kai, bayan yasha zai shiga wanka kafin ya fito inda aka shirya masa karin kummalo. Sai dai saɓanin yau yana ɗaga ƙafa domin barin wajen bayan ya dubi Aamin nasa ya rissinar da kai kaɗan na alamar sallama da girmamawa a garesa Iffah dake faman baza ƙamshin da ga Shahan-shan ɗin kawai suka sansa ta isowa wajen ɗauke da ƙaramin kofin shayi dake tururi fari tar na glass.

      Da sauri duk hadiman suka juya bayansu, dan kallon abinda zai iya biyo bayan wanda suka gani ɗin haramunne a garesu. Iffah dake taku a nutse kamar wata hawainiya takalmanta da ba wani tsinin kirkine da su ba na bada sautin isar da saƙon tahowar tata ta iso gabansa.. Ƙin yarda tai koda wasa su haɗa idanu. Idanunsa da kallonsu ke canjawa ya sauke akan kofin shayin da take miƙo masan. Shiru babu alamar zai amsa, har hanunta na ƙoƙarin fara yin dayi. Sai da ta fara ambatar sunan ALLAH kafin ta ɗago fuskarta a dake, 

      “Ƙin sha na nufin rauni da muhimmancin Zawjata-almilk a gareka. Ko kuwa cigaba da tabbatarma duniya abinda suka sani shine gaskiya ranka ya daɗe”.

   Yanda lips ɗinta da suka sha pink lipstick ke motsawa ya zubama ido, sai dai maimakon mata sharhi akan zancenta kamar yanda taso yau gefe ya ɗan maida kansa da amsar shayin kamar wanda ya shiga halin tarkon kasala. Karan farko ta sakar masa wani lallausan murmushi da faɗin, “Thanks”.

      Basarwa yay ta hanyar ɗan duban gefensa a takaice ya furta,

   “Aami”.

Da sauri Iffah ta duba wajen tamkar sai yanzu ne taga Miran Arshaan ɗin, “Ya salam”. Ta faɗa a zahiri da nufarsa ta zube ƙasa domin miƙa gaisuwa a garesa. Ya ɗan murmusa zuciyarsa taf da al'ajabin wannan figigiyar yarinya da da auren wuri yayi ya haifa wanda suka fita nesa ba kusa ba. Cike da salonsa na fuska biyu ya amsa yana mai ƙare mata kallo ta ƙasan ido. Iffah daba kula da hakan tai ba cike da girmamawa ta miƙe da faɗin, “Uncle bara a baka shayin kaima”.

      “Zan so kasanwa na farko da zai ci abu daga hanunki Ibnati”.

   Jin daɗin kalamansa yasa Iffah sakin murmushi da ɗan rissinawa ta furta, “Na gode Aam”. Shima dai shayin ta kawo masa, nan ma yay mata godiya da sanya albarka yana ɗan duban sashen da Tajwar yake tsaye dafe da ƙarfen da aka zagaye wajen ta bakin ginin yake ya tsurama cikin masarautar idanu yana ɗan kai shayin bakinsa tamkar bai san abinda ke gudana a wajen ba. A hankali ya taka inda yake shima yana shan nasa. 

     “Yanzu ne daular ruman ta tabbatar da samuwar Zawjata-almilk”.

     Sarai Tajwar Eshaan ya jisa. Amma halinsa na ƙasaita da mafi yawan iyayen nasa suke ambato da girman kai yasa yay tamkar baiji ɗin ba. Sai ma juyawa da yay bayan wasu sakkani ya dubi Aamin nasa cikin tausasashiyar muryarsa mara hayaniya da kamewa ya furta. “A huta gajiya”. Ya bar wajen.

       Ga mamakin duk wanda ke'a wajen gaban Iffah dake ɗan nisa da su ya isa. A bazata taji tattausan tafin hanunsa da yay sanyi ƙalau sakamakon iskar wajen a cikin nata. Da sauri ta rumtse idanu tana mai ambaton sunan ALLAH a zuciyarta da ɗan dubamsa. Ba ita yake kallo ba, sai ma fara takawar da yay wanda ya tilastata binsa tamkar raƙumi da akala. Batare da sun luraba takun sawayensu na sauka da ɗagawa a tare sakamakon shima tafiyar izza da ƙasaita irin na masu mulki yasa baida garaje a tafiya tamkar wani mace. Anan ɗin ma dai tana sanya ƙafarta na'ura ta sanar da ita wacece, haka shima. Da sauri hadimin dake a ƙofar ya zube yana kwasar gaisuwa. Hannu kawai ya ɗaga masa yay gaba abinsa har lokacin hannunsa na cikin nata ya riƙe gam kamar wanda aka bama amanar riƙon nata dan karta suɓuce......


         ★★.....  ★★......


   A ɓangaren Barrister kamar yanda mutanen can suka sanar masa hakance ta faru. Sunyi amfani da kamannin da mutane suka daɗe da sanin sunayi, wanda shine ma tushen zamowarsu abokai, aikinsu kuma ya maidasu aminai. Sai dai muryarsu ta banbanta da wasu abubuwa na ɗi'ar yau da kullum. Akan wannan ne mutanen suka bashi training na dole dalilin barazana da sukai masa akan iyalinsa dama kashe Barrister Akeem ɗin da yake gudun cin amana. Bayan kimtsawarsa da shiga irin ta Barrister Akeem da bashi wasu bayanai akan aikin da zai musun suka bashi key ɗin motar Barrister Akeem. Sun sanar masa dukkan motsinsa akan idonsu ne, kuskure ɗaya akan ganganci fansar rayuwar ɗaya daga cikin ahalinsa ne kona Barrister Akeem. Dole Barrister ya kwantar da hankalinsa dan ya fahimci mutanen sunfi ƙarfinsa, gashi koba komai yana buƙatar kuɓuta kodan tarin ayyukan dake gabansa musamman akan aikin da ayanzu ya tasa a gaba da alƙawarin cika alƙawari.

     Su da kansu suka bashi address ɗin inda zaije, yayinda ya hau titi kuma sai ya fahimci suna biye da shi a mashina wasu a mota. Ya ɗan rumtse idanu da jan kakkauran numfashi ya fesar lokacin da ya gama dai-daita parking a inda suka umarcesa zuwa. Sai da ya karanto addu'ar neman ɗauki ga ALLAH sannan ya fito riƙe da brefcase ɗin Barrister Akeem a hannu. Ƙaton gidan ya ɗan ƙarema kallo kafin ya nufi inda suke sanar masa yabi ta hanyar bluetooth ɗin kunnensa. Kansa kawai yaɗan gyaɗa tamkar yana gabansu ya nufi ƙofar......


         ★★★....... ★★.....


   A cikin masarauta kam kusan ƙarfe tara da wasu mintuna labari mai razanarwa na rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar (Aami gasu Miran Arshaan. Kaka kuma ga Tajwar Eshaan. Shine wanda yay maganar jiya a ɗakin tattaunawa bayan tashin Tajwar Eshaan). Zancen rashin ganin nasa ya fito ne daga iyalansa, da farko an ɗauka yana cikin masarautar ne dan sun tabbatar daga sallar asuba bai dawo ba. Amma ganin har lokacin shigarsa gida ya wuce ƴaƴansa kuma sun bincika a inda suke tunanin ganinsa amma babu shi sai suka fitar da maganar. A take sojojin gidan masu bada tsaro dama hadimai suka bazu lungu da saƙo amma babu alamar hakan. Anbi diddigin wasu daga cikin cctv footage amma fitowarsa kawai aka gani daga sashen nasa babu komawarsa. Hakan ya matuƙar bama kowa mamaki da ɗaure kai. Dan ta ko'ina masu tsaron ƙofofi sun tabbatar basuga fitarsaba sukam. Gashi kuma an duba lungu da saƙo na gidan amma babu wata alamarsa..... 


       ★★......


     Lokacin da labarin rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar ya iso kunnen Miran Jasim da Miran Arshaan dake tare kallon juna sukai, sai kuma duk suka kauda kawuna suna murmushi. Cikin son basar da zancen Miran Jasim ya cigaba da magana kan zancen da Miran Arshaan ya kawo masa dangane da Iffah 

      “Lallai wannan yarinyar hatsabibiya ce, aini tun isowar labarin kasancewarta raye a safiyar jiya al'amarin ta kemun kai kawo. Zancen ka na yanzu kuma ya sake tabbatar min da shirinta ta shigo masarautar nan.”

    “To ai ta tara ta samu, dan dama mu irinta muke nema”. Cewar Miran Arshaan yana ɗan murmushi.

       Miran Jasim ya jinjina kai shima yana murmushin nasa na izza da ƙasaita. “Hakane kam ta kawo kanta inda ake jirace da zuwanta. Dan kam zamu sauke ƙuruciyar dake izata a tunanin yin rawa da bazarta dake ɗawainiya da ita. Zata ƙarasa mana aikinmu cikin sauƙi batare da ita kanta tasan a cikin tarko take ba”.

    Nan ma murmushi Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan nasa. “Zuwa yaushe aikinmu zai fara?”.

      Miran Jasim ya ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki. “Bazai ɗauka lokaci ba. Sai dai muna bukatar wani point ne dole”.

   “Wanda yake hannunmu fa?”. 

Cewar Miran Arshaan da mamaki.

       “Kai wannan bashi da wani ƙarfin da zaiyi tasiri ita a gareta, duk da dai zai iya zama kamar share mana fage ne. Zaren da nake ganin zamu ja ya kaimu gareta ɗaya ne, duk da dai har yanzu babu wani shaida dangane da tsallakewarta itama. Amma zamu yi amfani da damar, a wannan karonma matarka ce zata mana aikin”.

     “A wannan gaɓar fa ya kamata mu canja salo, Jasrah nada matuƙar wayo, kar yawan bugar cikinta fa yasa ta fara fahimtar wani abu”.

  “Sai idan kaine ka bada ƙofar hakan Arshaan. Shekara nawa muna amfani da itan bata fahimtaba sai yanzu. Ka dai kawai ka kasance mai lura”.

      Kai kawai Miran Arshaan ya jinjina batare daya ce komai ba......


     ★★★......


    Suna yin ɗan nesa kaɗan da masu tsaron ƙofar Iffah ta zare hannunta da sauri tana ɓata fuska. Bai ko juyo ya kalleta ba balle ya nuna alamar yasan mitayi yay gaba abinsa cikin takunsa na nutsuwa da tsantsar ƙasaita tamkar baya son taka kafafun nasa. Da ƴar hararar ƙasan ido ta bisa tana ƙunƙuni a zuciyarta. (A haka dai kamar na wani limamin masallacin Saudiyya, sai dai zuciyar ko kafiran farkon ƙarni haka suka gansa suka barsa. Wanda duk zai iya salwantar da rai yay barci lafiya babu ko ɗar ai ya dace ka kirasa da duk sunan daya zo maka a rai dan ya cancanci haka). “Ni zanyi maganinka da izinin ALLAH”. Ta faɗa a zahiri fuskarta na nuna gaskiyar ɗacin da zuciyarta ke mata.......✍️


   🥱Bazamu hanaki ba Iffahn mu🏇😉.

No comments

Powered by Blogger.