Daudar Gora Book 1 page 38


*_38_*

........Duk da yanda zukatansu ke suya da tsagwaron salon wulaƙanci da raini da suke jifansa da shi game da wannan halin nasa da babu komai a cikinsa sai tsantsar miskilanci da kasancewar jinin mulki da ke yawo a jikinsa basu bari fuskokinsu sun nuna ba har ya gama shan ƙamahinsa da basarwarsa ya tanka.

     “Amfanin kasancewarsu cikinmu yafi rashin amfanin muhimmanci Aam. A lokuta da dama nafi son zama da maƙiyi fiye da masoyi saboda dalilai biyu”.

     Wani irin kallo suke masa har fuskokinsu na barazanar bayyana sirrin zukatansu. Miran Arshaan yay saurin katsesa da faɗin, “Abni wace irin magana ce wannan? Kakuwa san illar hakan da kakeyi?”.

    Miran Jasim dake masa kallon gefen ido cikin takaici yake masifa a zuciyarsa. (Shifa wannan wawa ne baima iya jin ƙarshen zance sam). A zahiri kam kallonsa ya sauke ga Tajwar Eshaan da yay biris tamkar bashi ya ɗakko zancen ba. “Ihm kaga Abni ƙarasa, zata iya yuwuwa naka hangen gaskiyar cikinsa rinjaye ne ga namu. Domin kowa da irin yanda UBANGIJI ke fahimtar da shi abu”.

     Tajwar Eshaan da bai ko motsa ba ga zancen Amin nasa sai da ya shaƙi iska iya buƙatarsa kafin ya ɗan ɗage kafaɗu a yanayin ko'in kula. “Ku manta kawai muje kan magana ta gaba. Wataran zamu ƙarasa wannan ɗin”.

     Sosai takaici ya maƙure musu maƙoshi su dukansu. Sai dai Miran Jasim har Miran Arshaan yake jin takaici kasancewar shine sanadin katse zancen. Suma shiru sukai kamar bazasuce komai ba a wannan gaɓar. Kafin Miran Jasim ya nisa. “Abu na gaba shine farin cikin tsallakewar matarka. Alhamdullah addu'oin mu sun karɓu, ALLAH yasa ta kasance uwa ga ƴaƴan da zaka haifa masu albarka”.

       A maimakon amsawa da Amin daga garesa ƙasaitaccen murmushinsa mai ƙara bayyana ƙyawun da ALLAH ya azurtashi da shine ya saki kaɗan yana mai kauda kansa gefe babu alamar zaice wani abu. Suma basu nuna alamar sun damu da sai yace ɗin ba Miran Jasim ya cigaba da faɗin, “Ya kamata a zauna da Tajwar na jihar Hubab da shugaban tsaro akan waccan matsalar itama. Kar muyi sakaci dayin biris da wannan maganar dan bamu san minene manufa ko dalilin faruwar komai ba. Abu mafi ruɗanin shine makamancin haka bai taɓa faruwa a ƙasar ruman ba sai dai muji a wasu ƙasashe har ma mu bada shawara da gudun mawar ganin sun samu zaman lafiya. Idan haka kuma ta fara faruwa a garemu lallai maƙiyanmu na barazana akan nasararmu kenan”.

      Nan ɗin ma dai kamar bazai tanka ba sai kuma ya dubi Miran Jasim ɗin da alama zancen ya shigesa. “Na baku damar yin duk yanda ya dace Aam”. 

    A take fuskokinsu suka nuna jin daɗin wannan girma daya basu. Sanin halinsa yasa daga haka sukai masa sallama. Har sun miƙe Miran Arshaan yace “Af niko kaga na shafa'a da wannan batun. Abni baka ganin yayi kusa kuwa ace fitar Zawjata-almilk har cikin books room? Yakamata ace tayi haƙurin cigaba da killace kanta kodan maƙiyan da bamu san ta inda suke shirya sabon shiri ba, dan yayi wuri ace mun shagala da tsallakewar ta ta a nawa ɗan hangen. Ai ƙoƙari a tsawata mata ALLAH ya cigaba da kare mana ku ku duka dai”.

       Miran Jasim ya amsa da Amin yana jinjina kai alamar tabbatar da maganar, sai dai ganin Tajwar Eshaan bashi da alamar cewa wani abu suka fice abinsu. Koda suka fitan ya jima bai motsa a yanda yake ba, da alama dai maganar tasu ta ƙarshe ce ke masa kaikawo. Hasashen kam sai ya zama gaskiya dan akan lips ɗinsa daya motsa kaɗan ya ambaci, “Yarinyar nan ko”. Daga haka ya shanye sauran a cikinsa....


          ★★.... ★....


    Kamar yanda ta faɗa bayan sallar isha'i ta fito cikin abaya fara tas. Duk da dare ne ƙamshinta da kwarjininta mai ɓoye ƙarancin shekarunta na tare da ita. Fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙora take amsa gaisuwar hadiman da tuni sun kammala taruwa bisa umarninta. Ɗaya bayan ɗaya ta basu damar gabatar mata da kansu da matsayin ayyukansu. Har suka gama batace komai ba tana dai nazarinsu ne. Haka kawai take jin bai kamata ta yarda da kowa ba a wannan gaɓar, dan duk da tausayinsu dake nuƙurƙusar zuciyarta tayi imanin akwai masu gurɓatacciyar zuciya a cikinsu kamar yanda Daneen Ammarah ta karanta mata komai.

     “Okay duk naji bayanan ku, sai dai kuma Ni zan canja tsarin aikin da bama kowa abinda nake ganin zai fi dacewa da kasancewar tare da ni. Bazan roƙi kowa ba a cikinku cewar ya kasance mai gaskiya da riƙe amana, sai dai zan tabbatar muku zan iya hukunci ga kowa idan na kamashi da waɗan nan abubuwan biyu. Dan na matuƙar tsanar mai wannan halayar koda a sama dani yake. Zan kuma iya aikata harma abinda mutum baiyi zatoba akan hakan.....” ɗaya bayan ɗaya ta rarrabasu ga ayyukan saɓanin yanda aka turosu suyi, salon nata ya matuƙar girgizasu a take kuma tasirin gizagonta ya shigesu, har suke ambaton tsarin da gaba kura baya sayaƙi kenan, dan kuwa dai kamar yanda Iffah tai hasashe mafiya yawan cikinsu zasu kasance da itane bisa umarnin iyayen gidansu na ɓoye bisa ɗabi'ar tura ƴan leƙen asiri da manyan masarautar suka tasirantu a kansa. Bayan ta sallamesu akan aikinsu zai fara daga gobe ne ta tattare littafanta da kanta tai ciki da su. Sai da ta tabbatar ta ƙarema ɗakin kallo yanda ya kamata fiye da ɗazu bisa zargin za'a iya saka mata camara kamar yanda Ajmaal ya tabbar mata. Babu alamar akwai abinda take zargin dan haka ta ɗauka wayarta. A maimakon WhatsApp yau a text message ta tura masa saƙo, daga ƙarshe ta ƙara roƙonsa bincika mata lafiyar iyayenta dan zuwa yanzu zuciyarta na tabbatar mata akwai abinda Sir Fawzan ya faɗa mata ba dai-dai ba ko yake ɓoye mata. Dan kullum takan gwada number Hanash da Babiy sama da sau babu adadi amma babu alamar zata samesu. Ga mafarkinta a kansu duk kusan bayan kwana biyu cikin maimaita kansa yake gareta. Bawai tayi imani da hakan bane, kawai dai zuciyarta takan rinjayu da tsoro akan mafarki musamman idan ta auna da abubuwan da suka tabbata akan wasu mafarkai da sukai wa riƙon wasarere ita da iyayenta a baya.......


         *_★MALIKAT HASEENAT★_*


     Kamar yanda labarin fitar Iffah yaje kunnen kowa a masarautar itama yaje nata kunnen, sai dai saɓanin malikat Bushirat ita murmushi tayi batare data furta komai ba akan zancen. Rashin cewar tata ya Bama Hadimar damar ƙarasa mata zancen akan Iffah kuma ta koma sashenta bayan barowarta books room. Anan kam idanu Malikat Haseenat ta tsurama hadimar Tata tamkar zataga fuskar Iffah a jikinta ne. Sai kuma ta janye da wani ɗan murmushi a fuskarta ta maida ga hadima Banou. 

       “A haɗa abincin karin kumallo da Zawjata-almilk ta uku”.

    Cikin tashin hankalin wannan umarni na Malikat Haseenat kamar Banou zata fasa kuka ta jinjina kai, har hakan ya bama malikat Haseenat mamaki, sai dai batayi magana ba kasancewar tasan shirmen Banou fiye da haka. Itama dai tana zaune da itane batare da tasan dalili ba, amma wasu lokuta takanji yanayi mai wahalar fassara koda a kallon hadimar tata ne amintacciya a bangaren girka mata abinci...


7

         *_BARRISTER_*


    

    “Su waye ku? Miyasa kuka kawoni nan? Mina muku?”. Barrister ya faɗa yana mai bin zaratan samarin da kallo harma da ɗakin da suka kawoshi mai ƙarancin haske gashi a ɗaɗɗaure a kujera. Fahimtar bazasu bashi amsa ko ɗaya ba daya bukata ya sashi cigaba da magana a hasale. Dan shi mutum ne mai saurin fushi musamman akan gaskiya da mai gaskiya. Baya son zalunci shiyyasa ko baka da ƙarfi zai tsaya maka akan haƙƙinka in har ka kasance mai gaskiya.

       “Idan ma akan case ɗin nan ne kuke ganin sakayeni ko ɓadda rayuwata zai baku damar yin yanda kuke so akan bayin ALLAH da basujiba basu gani ba ku sani ni bamai hukunci bane. ALLAH shine mai hukunta kowa, zai kuma iya kawo wanda ya fini ƙarfi ya cece su”.

    Yanzu ɗinma dai babu alamar wani a cikinsu zai tanka masa. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na masa ƙuna. Bashi da wani buri yanzu a duniya sama da yasan asalin tushen wannan case ɗin nasu Babiy, yayi alƙawarin tsayawa da ƙarfinsa dana aljihunsa insha ALLAHU.


     Har dare babu wani haske daya samu dan har lokacin yana a ɗaure, sai da aka kira sallar magriba ne suka bashi dama yay salla harda isha'i. Hakan ya ɗan sassauta masa zuciya, dan koba komai damar yin salla da suka bashi yaji a ransa masu sassauci ne. Abinci suka kawo masa basu sake ɗauresa ba, sai dai yaƙi yako kallesa hakan yasa suka sake zuwa kusan ƙarfe tara agogon ƙasar suka sake ɗauresa sukai ficewarsu da kullesa ta baya. Babu irin tunani da takaici da baijiba amma ya cigaba da ambaton sunan ALLAH dan yasan shine kaɗai zai kuɓutar da shi a wannan gaɓar.

     Kusan ƙarfe sha ɗaya gyangyaɗi naɗan kwasarsa yaji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar, idanunsa ya buɗe duk da baya iya ganin mai shigowa saboda ƙarancin hasken ɗakin. A ɗan hasken ya fahimci yanzu mutumin uku suka shigo, wanda ke gaba kuma da alama ogansu ne dan yanda ya shigo da takun izza cikin ɗakin. Da sauri suka ajiye masa kujera ya zauna yana mai facing ɗin Barrister yay wani irin zaman ƙasaita yana ƙarema Barrister ɗin kallo ta cikin glasses ɗin daya toshe idanunsa....

      “Miyasa kuka dauresa?”.

Ya faɗa a kausashe. Kame-kame yaran nasa suka fara kowa na ƙoƙarin kare kansa. Yaja tsakin daya sakasu nutsuwar dole yana mai faɗin, “Ku kwance sa”. Bayan an kwance Barrister ya sake bada umarnin a bashi abinci da ruwa. Barrister dai kallonsa kawai yake da mamakin wannan izza tasa. Baiyi niyyar cin wani abu ba dan haka yay saurin faɗin, “Bana buƙatar wani abinci. Kusanar min kawai dalilin da yasa kuka kawoni nan da kuma inda nake dan ALLAH”.

       Har Barrister ya fidda rai ga samun amsa yaji an karɓama zancensa a kausashe. “Barrister Abdallah Aas ba shiririta ta kawoni nan ba. Dan na baro abubuwan da suka fika muhimmanci nazo nan. Duk da rayuwarka ce ba sanin inda kake ko sanin mu su wanene ba matsalarka. Dalilin kawoka nan kawai zaka iya sani, damar hakan kuma na hanunka ta hanyar bin umarninmu”.

       Haka kawai kwarjinin wannan mutum da ko fuskarsa Barrister baya gani da ƙyau yay matuƙar mamayesa, duk da yanaji a ransa ba alkairi yasa suka kawosa nan ba sai yaji bazai iya jayayya da shi ba. Cikin sanyin jiki ya fara cin abincin, yaci kusan lauma bakwai yasha ruwa duk suna a ɗakin. “Na gama”. Ya faɗa cikin sanyin murya.

      “Good for you”.

Aka bashi amsa cikin halin ko'in kula. Sai kuma yay shiru kamar baida abin faɗa kafin yaja numfashi cike da isa ya fesar. 

         “Lokacina ƙurarrene dan haka bani da lokacin cigaba da ɓatashi a rikeka nan. Aiki zakamun baka da kuma zaɓin cewa e ko a'a. Nasan kasan Barrister Akeem Ibn Behnam”.

   “Hakane, dan abokina ne ma ranka ya daɗe”. Barrister ya amsa mishi da kalmar giramamawa a ƙarshe batare da yasan dalili ba. Kawai dai yana jin matuƙar girman wannan mutum da ko a murya yasan ya girme masa.

         Cikin yaransa ɗaya ya cigaba da faɗin, “Sanin hakan yasa aikin ya wajaba a kanka. Akwai aikin da Barrister Akeem ɗin keyima wasu mutane, Boss naso ka maye gurbinsa....”

     “Tayaya hakan zata faru, bayan su sun san wanda suke huɗɗa da shi”. Barrister yay saurin katse mai maganar.

   “Ai mun fika sanin hakan shiyyasa muka zaɓeka. A yanzu Barrister Akeem na hanunmu kamar yanda kake a hanunmu, munada hanyoyin bi wajen canjaka ka koma shi bisa dalilan da kaima kasani, yayinda su a wajensu kai ka mutu a yanzu, zuri'arka kuma basu san inda kake ba. Zakai aikinne na kwanakin da basu gaza goma ba, idan sun zarta hakan kuma kai kaso”.

         “Kun sani a duhu wlhy, Barrister Akeem fa wani babban jigone a rayuwata, muna taimakama juna matuƙa taya kuke tunanin zanci amanarsa ta hanyar yin amfani da kammanin da mukeyi ace na masa kutse akan aikinsa bayan haka cin amana ne?”.

     “Wannan damuwarka ne. Aikinmu zai fara daga gobe”.

   Ogan nasu ya faɗa cikin kausasa harshe yana miƙewa. “Ranka ya daɗe dan ALLAH ka saurare ni”. Barrister ya faɗa cikin rauni. Sai dai baiko nuna alamar yama jisa ba yay ficewarsa yaransa biye da shi..........✍️


    🤔????. Nama rasa abin faɗa.

     


*AYYIRIRIRI AHAYYE CHAS 💃🏼💃🏼💃🏼 sunan wata waƙa wai ita LUWAI*

_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg's skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziƙin mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci😱😱?_

   Ah haba madam yunƙuro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko'ina ake fatan gani  dan an daɗe ana jin su watau *team glow by Mg's*

   Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haɗuwarta da kyan fatarta

Mg's skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a ɗaga kai a kira da suna mace wacce ba'a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haɗe a wannan ƙasaitacciyar tafiyar ta Mg's skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh  kiyi smooth wow🥰🥰🥰kina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg's skin care* ba kya buƙatar ko wanne irin mai product ɗinmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari  nace  ba sister shin  meye matsalarki ta gaban goshin ƴallaɓai? 

Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.

to hutas bi'izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg's* matsalarki tazo ƙarshe  bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuɗi gida *MG's skin care gagarabadau*

Price ɗinmu daidaitacce ne  sannan kuma dai dai da aljihunku


No comments

Powered by Blogger.