Daudar Gora Book 1 page 37



_37_

 .........Duk ta inda suka gitta kwarjininta dake ɓoye shekarunta kansa a bata girma irin wanda ya dace ga Zawjata-almilk da suka isa a masarautar. Hadimai kam sai zubewa suke bisa gwiwunsu sakamakon sanarwar da ɗan kazagin da Iffah bata farga da shi ba sai da suka fara tafiya taji shelanta tahowarta da yake yi. A yau kam ta ƙara jinjinama girman wannan katafariyar masarauta mai

abubuwan kallo matuƙa. Sai dai ga mai kallo bazai taɓa fahimtar hakanba a yanda take faman basarwa kai kace ita ɗin tun fil'azal jinin sarauta ce. Ba wani nisa bane zuwa books room ɗin, hakan ya sakasu isowa cikin ƙanƙanin lokaci dan ma tafiya ce ta ƙasaita....


        Cikin ƙankanin lokaci labarin fitowar Zawjata-almilk ya karaɗe masarautar. Hadimai ƴan leƙen asiri dake watse ta ko'ina sun gama kai labari ga iyayen gidansu. Da yawa mamaki ya kamasu tare da gane lallai yarinyar tazo da tsageranci. Inba tsageranci ba wace Zawjata-almilk ce ta taɓa fitowa bayan kaita turakar Shahan-shan da kwana ɗaya kacal. Wasu kuma kai tsaye fassara wannan fita suke da gatsali, acewarsu Iffah nason tabbatar musu tafi ƙarfin iyawarsu, ƙarfin ikon su kuma ba komai bane dan ta gagaresu.


       ★Malikat Bushirat kanta isowar wannan labari a kunenta sai da tai wani tsamm na nuna mamaki, sai dai bata ce uffan ba kasancewarta mace mai tsananin jin kai da izza. Tana son Iffah, kuma ƙarfin halin yarinyar na kawatar da ita. Sai dai hakan ba yana nufin zata dama damawarta ne a yanda taso ba ko ƙetare tsarin zama a masarautar musamman ga Zawjata-almilk irinta da ƙa'ida komai sai da umarnin Malikat zatayi sa. (Kamar dai ita dake mahaifiya ga Tajwar Eshaan. A ƙa'ida dole komi Iffah zatayi sai ta nema izinin mahaifiyarsa kafin ta aiwatar). Jin al'amarin ya cigaba da caccakar zuciyarta ta sallami duk hadimanta. Kamar ƙiftawar ido suka ɓace kuwa. Rai a ɓace ta ɗaga waya tai kiran Jasrah da ita bama tasan wainar da ake toyawa a masarautar ba kasancewar a ɗan tsakanin nan tana fama da laulayin ciki ne sama-sama.

       Duk da a halin rashin jin daɗi da take ciki bazata iya ƙin amsa kiran ƴar uwar tata da takema kallon uwa a yanzu ba. Haka ta kimtsa cikin dauriya ta nufi sashen Malikat Bushirat ɗin. A tsaye ta sameta cikin yanayin ɓacin rai da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta. Sai duk taji itama nata ran a jagule...

    “Akia kina lafiya kuwa? Miya ɓata miki rai haka har fuskarki ta kasa ɓoye wa?”.

          Malikat Bushirat ta zuƙa kakkaurar iska ta fesar tana mai kallon ƴar uwar tata. Cikin ɗacin murya tace, “Yarinyar nan ce”.

    “Yarinya kuma? Wace yarinya kenan?”.

    Kamar bazata tanka ba, tai taku ɗaya zuwa uku batare data dubi Jasrah ba tace, “Zawjata-almilk. Da alama tana buƙatar sai an saita mata zama da tuna mata nan daular ruman ce ba getto eria ɗin data rayu ba. Komai muna yinsa da ƙa'ida bisa umarnin na gaba”.

        “Kiyi haƙuri Akia. Amma na kasa fahimtar miya kawo wannan maganar, wace kuma Zawjata-almilk ce a cikin yaran? Dan nasan dai kinfi kowa so da ƙaunar wadda ke tare da shi a halin yanzu”.

     “Ina sonta bashi zai bata lasisin shimfiɗa abinda ta gadama na a saman nawa ƙarfin ikon ba. Yanzu labari ya iso gareni ta fito daga sashen Saiful-malik zuwa books room tare da hadimai”.

    “Tofa, ita kuma da wannan tazo? Mu muna murnar samunta matsayin wadda zata share kukanmu amma zata fara da haka?. To amma fa Akia wani hanzari ba gudu ba. Shin baki ganin salon yarinyar a wani mahangar nasara ce a garemu. Na farko dai babu wanda yasan ta fito ne batare da umarninki ba. Na biyu koba komai ta sake jaddada isar da saƙonmu akan maƙiya. Na uku salonta tamkar barazana ce ga duk wani shu'umi dake rayuwa a wannan masarautar. Inaga bai kamata ki damu ba, dan a wani ɓangaren ma kamar mune masu laifi, karki manta Mammah ta mikata sashen Abni batare da bin ƙa'idojin da ake kai Zawjata-almilk turakarsa ba. Sannan inada tabbacin ba'a sanar da ita komai game da tsarin komai ba fa, sai aikin da muka faɗa mata zatayi a garemu”.

      A hankali Malikat Bushirat ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya. Cikin kwantar da murya ta ce, “Hakane kumafa Jasrah, kin tunatar da ni abinda ya ɓacemin har idona ya rufe. Sai yanzu na fahimci lallai wannan fitar tata ma da alama tanada manufa akan umarnin aikinmu. Duk Mamma ce da wannan kwamacalar da muka kasa fahimtar manufarta a kai, nayi niyyar zuwa sashen nata ma naji dalili baƙin nan na ɗazun suka cinyemin lokaci. Amma munyi magana da Ammarah zuwa anjima zanje ko cikin ɓadda kama ne”.

        “Hakan yayi, dan koni ina son sanin yaya akai hakan ta kasance. Duk da dai Alhamdullah yarinyar ta kuɓuta. Amma mun kwana a fargaba ai dan ko barci jiya banajin waninmu yayi wlhy. Hatta da Abu Harith kwana yay tunani”.

     Murmushi Malikat Bushirat tayi, dan har cikin ranta tana ƙaunar ƙanin mijin nata kuma mijin ƙanwarta, tare da yaba ƙoƙarin sa akan kulawa da kaunar da yake nunawa ga gudan jinin nata tilo da har wasu ke jin zafinsa a gidan bisa hakan.....


       ★★....


   Katafaren ɗakin daya kasance mai cika ido ga Iffah tsarinsa ya matuƙar ƙawatar da ita. Ta samu jagorancin shiga lungu da saƙo na cikinsa bisa taimakon masu kula da ɗakin. Inda a zagayen nasu suke nuna mata abubuwan tarihi na tun farkon ƙarnin kafa Daular ruman ɗin da suka shuɗe cike da girmamawa a gareta. Tafiya kam mabuɗin ilimice haƙƙun dan Iffah ta ilmantu da abinda yafi wanda ta sani ƙalilan a baya dangane da tarihin daular ta ruman da akan tsakura musu a darasin makarantu. 

     Shugaban masu kula da sashen ya matuƙar nuna jin daɗinsa da bata shawarwari kan tsarin zama mai nazarin tarihi data ambata dan abune daba kasafai ake ganinsa ga matan cikin masarautar ba. Akwai wadda ma bata taɓa taka ƙafarta cikin ɗakin litattafan ba. Amma ita gata ƙaramar yarinya da rayuwarta ke kamar akan ɗar-ɗar abinda ta fara nuna sha'awa na farko akansa kenan. Shine ya fara zaɓa mata books daya ga ya dace ta fara dubawa, hakan yasa ta basar da waɗanda ta shigo nema kai tsaye, dan a ganinta bin shawarar tasa zaifi bata fiye da abinda take buƙata ɗin. Shugaban da shekaru sunyi matuƙar ja a garesa yaji daɗin amsar shawarar tasa da tayi, dan yasan duk da zai iya haifarta matsayinta ya bata ikon yin duk yanda taso a sama da shi...


          A cikin farin cikin daya goge duk wani damuwarta a wannan yini ta fito hadimanta na take mata baya ɗauke da ɗirka-ɗirkan littafan da ta ɗebo. A yanzu ɗin ma dai tako ina hadimai faman zubewa suke domin girmamawa a gareta harta isa sashenta data basu umarnin su kaita saɓanin sashen Shahan-shan daya kamata ace ta koma tunda a ƙa'ida sati guda zatayi kamar yanda Malikat Haseena ta sanar da Tajwar Eshaan. Iffah kam da ba zama akai aka faɗa mata komai na ƙa'idojin ba haka kawai taji bata bukatar komawa zaman takura da zuciyarta ta ayyana mata rashin amfaninsa. Shi dai wanda aka kaita dominsa ko kallo bata ishesa ba, hasalima baya kallonta da suffar da suka miƙata garesan kai tsaye. Yo dole ta faɗi haka, tunda wane mijin ƙwarai ne zai jefama matarsa kalmar tambaya ta ita (wacece?) Bayan da saninsa aka kai sadakinsa domin aurota. Bazata iya ɗaukar waɗan nan abubuwan ba, dan bama abinda ya kawota nan ɗin ba kenan tun fil'azal. A ganinta kuma ba sai dole an kaita garesa an ƙaskantar da ita ba, zatabi hanyoyin daya dace na haɗuwa da shi har lokacin da zata cika ɓoyayyen burinta....

      Da wannan tunanin suka ƙarasa sabon sashen nata. Tabbas ta jinjinama ƙoƙarin su, dan ko makaho ya laluba yasan wannan sashen yayma wanda aka kaita fintinkau a komai duk da shima wancan ɗin dai ba baya bane a tsaruwar. Ta ɗan sauke numfashi da kaiwa zaune bisa ɗaya daga cikin lumbutsa-lumbutsan kujerun da aka shirya falon da su bakinta ɗauke da bismillah. Suma dai hadiman nata bayan sun ajiye litattafan a saman Centre table a gabanta suka zube. Taja tsahon mintuna goma tana mai nazarinsu kafin ta ɗan sauke numfashi da miƙewa.

        “Ina buƙatar zama da duk wanda zai kasance da Ni a wannan sashen zuwa anjima”.

    Cike da girmamawa duk suka amsa mata kawunansu a ƙasa. Ta ƙara jan numfashi ta fesar batare data farga da salon izzar da yay kutse ga al'amarin ta na yanzu ba ta kai dubanta ga agogon falon. “Muna da sauran lokaci yanzu da zai ishemu zagaya sashen kafin na shige salla”.

         Anan ma sun amsa mata ɗinne da girmamawa. Batare da ta sake cewa komai ba tai gaba duk suka miƙe suna take mata baya. A yanzu ma dai wadda ta jagorancesu zuwa books room ce ke mata bayanin sashen da tsarinsa yanda ya kamata. Cike da gamsuwa batare data furta komai ba koda so ɗaya take gyaɗa mata kai. Sashen ya ƙunsa abubuwa masu yawa da zaman lissafinsa zai zama ɓata lokaci da cinye mana page, bayan sun kammala zaga ko'ina Iffah ta shiga bedroom ɗin da zuciyarta tafi aminta da shi matsayin master bedroom ɗin ta. 

      Mamaki ya kamata lokacin da taci karo da guntuwar takarda a saman duvet ɗin saman gadon. _Ibnati wannan ɗakin ki tabbar ya kasance ɗakin sirrinki, shiyyasa nasa a shirya miji duk wani abu na buƙatar ki._ takardar ta ɗan juya tana mai jan numfashi da fesarwa. Sai kuma ta saki murmushi dan ta fahimci saƙon na Daneen Ammarah ne. Wayarta ta ɗauka a ɗan gaggauce ta aika mata saƙo. Sannan ta nufi bayi gabatar da al'wala.......


   

           *_★★SHAHAN-SHAN★★_*


      Tun bayan faruwar komai daya shige ɗaya daga cikin ɗakunan barcinsa bai sake fitowa ba sai yanzu a cikin shirin zuwa Masallaci. Sau ɗaya ya ɗagama hadiman dake zube ƙasa a dalilin fitowarsa hannu ya fice. Da kallon ƙasan ido duk suka bisa, kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa game da shi...


       Bayan idar da sallar isha'i bai samu damar shigowa ba yay zaman ganawa da Aamin sa su biyu da suka buƙaci hakan. (Miran Jasim da Miran Arshaan). Miran Arshaan shi yafi jansa a jiki tun fil'azal, sannan kuma kamar yafi kusanci garesa ta bangarorin biyu kasancewarsa miji ga Khaalti (Aunt) ɗinsa da yake kallo tamkar yaya. Shima dai Miran Jasim ɗin bai taɓa nuna masa wani abu mara kyau ba a zahirin rayuwa, a komai ma da zai taso yakan bada ƙarfinsa wajen karesu ne ga kowa koda a fada ne. Waɗannan hallayya tasu ya sashi ɗaukar yarda ya basu har yakan iya tattauna wasu abubuwa da suka shafi mulkinsa, sai dai abinda duk ya shafesa a karan kansa duk yanda zasu so sani baya taɓa basu fuskar hakan dan ko'a zahiri kowa na masa kallon mutum mai wuyar sha'ani, bahagon mai bauɗaɗɗen hali da zurfin ciki ne. 

     Bayan ficewar hadimin daya gama hidimar zuba shayi a gaban kowannensu ya fice Miran Jasim ya fara katse shirun dan yasan in zasu kwashe awa ɗaya a wajen Tajwar Eshaan bazai sake tofa komai ba bayan gaisuwar da yay musu. “Abni nasan zakai mamakin wannan zaman namu, sai dai a dubi da abinda ya faru ɗazun ba abin mamaki bane. Abinda ya faru ɗazun ya matuƙar Kona mana zuciya, dan bazamu taɓa so a aibantaka ba muna ji muna gani kodan amanar da Haysam Akhi ya barmana taka. Akwai wasu abubuwan da yawa daya kamata dama mu tattauna da kai kafin wannan ɗin, amma a yanzu kamar wannan ɗin ne importent”.

       “Hakane Jasim Akhi”. Miran Arshaan ya karɓe fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Ya cigaba da faɗin, Abni lokaci yayi da nake ganin ya dace wasu a cikin iyayen nan namu dake zaman fadanci ya kamata su huta ƴaƴayensu su karɓesu. Duba da kai matashi ne, a koda yaushe ra'ayinka da hangenka zai cigaba da zama banbanci ne da nasun. Koda yake su a gare sun ma ba haka bane, dan haka mahaifinka yasha gwagwarmaya matuƙa da su a yayin nasa mulkin. Amma kai mi kake gani akan hakan?”.

     Shiru babu alamar Tajwar Eshaan zai tanka, sai ma cigaba da kurɓar shayinsa yake cike da ƙasaita idanunsa akan television dake aiki a falon..........✍️



*AYYIRIRIRI AHAYYE CHAS 💃🏼💃🏼💃🏼 sunan wata waƙa wai ita LUWAI*

_Ana tayi muna tayi manyan mata dai da gaske sun dage sai sun zama kalar gaban mota kalar camera tare da gudummawar Mg's skin care Hajia ta kina ina ake ta wannan harkar arziƙin mata nata glowing suna faranta zuciyar mazajensu da laushi da santsin fatar su ke kina nan kina fama jiki duk kirci😱😱?_

   Ah haba madam yunƙuro ayi tafiyar nan dake ki shiga ki wataya acikin shahararrun matan nan da ko'ina ake fatan gani  dan an daɗe ana jin su watau *team glow by Mg's*

   Macen da ta isa itace mace karki bari ki zama cikin irin muna matan nan da suka rako mata duniya kuna tafe da mijinki yana kallon wata har miyau na zuba tsabar haɗuwarta da kyan fatarta

Mg's skin care sune sirrin duk wata macen da ta isa a ɗaga kai a kira da suna mace wacce ba'a jin kunyar shiga taro da ita daga nan har villah kizo/kuzo mu haɗe a wannan ƙasaitacciyar tafiyar ta Mg's skin care domin sune na gaban gaba sune suka ciri tuta indai a harkar gyaran skin ce hajiata kiyi wani fresh  kiyi smooth wow🥰🥰🥰kina tafe kina walwali idan fa kina amfani da *Mg's skin care* ba kya buƙatar ko wanne irin mai product ɗinmu katt ne duk matsalar fatarki muna da maganinta uhmm inata miki labari  nace  ba sister shin  meye matsalarki ta gaban goshin ƴallaɓai? 

Acne?, pimples? spot?, strech marks?, sunburn?.

to hutas bi'izinilLah muna da maganin matsalarki kina ganin mata a tiktok fuska luwai lumus kice dama ni ko? to in dai kina tare da *Mg's* matsalarki tazo ƙarshe  bama cika baki gaskiya itace takenmu haka nan kuma siyen nagari mai da kuɗi gida *MG's skin care gagarabadau*

Price ɗinmu daidaitacce ne  sannan kuma dai dai da aljihunku


No comments

Powered by Blogger.