Daudar Gora Book 1 page 36



*_36_

........Isowar labarin tashin nakiya a jihar Hubab ya matuƙar tada hankalin duk wani mai faɗa a ji a daular ruman. Dan abune da bai taɓa faruwa ba a kasar ta ruman. Amma abin mamaki ga Tajwar Eshaan ba hakan bane, dan babu wani alamar damuwa ko

nuna kaɗuwa da lamarin. Kallo ɗaya yayma akwatin talabijin ma ya ɗauke kai kamar ba'a ƙasar da yake mulka matsayin shugan kowa da kowa al'amarin ya faru ba. A karan farko wani abu da tun shigowar Iffah masarauta bataji akansa ba ya tsikari zuciyarta sakamakon ganin halin da ya nuna akan wannan al'amari da duk wanda ya kwana ya tashi a ƙasar ta ruman bazai ce bai shiga ruɗani ba. Duk da ance ba'ai asarar rai ko ɗaya ba taji kamar ta tashi ta shaƙure wuyan Shahan-shan ɗin ta huta da ganin wannan azzalumin shugaba da kansa kawai ya sani sai ahalinsa. 

     “Mi hakan ke nufi?”. 

Ta faɗa tana faman kai kawo a ruɗe itama duk da a labarin an sanar da ba'a samu asarar rai ko ɗaya ba sai dai dukiya. Abu mafi caja ƙwaƙwalwa ga kowa ma ba ita kaɗai ba shine jin wai wanda ya dasa bomb ɗin ya tsere Bayan wasu sun tabbatar da sunga fuskarsa da shigarsa motar, musamman ma wasu samari huɗu da suka tanbatar da tare suke da wannan mota tun daga ƙauyen Lufana da alama mutumin daga can ya fito. Tabbas sai tayi ajalin wannan mutumin a zuciyarta zataji salama. Dan a ganinta idan yau ya tashi kowa bai rasa ransa ba na gobe kuma fa? A wannan gaɓar ta fara zargin anya wannan sarkin bada wata manufa dama ya dawo ya karɓa mulkin mahaifinsa ba? Dan alamu sun fara nuna uban nasa ma shine ya kasheshi. 

    “Lokaci yayi da zan fara aikina gadan-gadan”. 

    Ta faɗa a zahiri cikin tabbatarma kanta da yanayin ɗaukar alwashi....


(Muma kam muna bayanki Iffah, dan muna son sanin mike zuciyar wannan bahagon sarki haka mai wahalar fahimta😉🥱🏇).


        ★★★


     A babban zauren majalisan manyan masu faɗa aji na daular ruman kuwa na can yana neman hargitsewa dangane da faruwar wannan al'amari. Kowa faɗar albarkacin bakinsa yake a duk yanda zuciyarsa ta ayyana masa musamman masu sukar mulkin Tajwar Eshaan a fakaice. Duk wannan kace nace da akeyi Tajwar Eshaan ɗin na zaune cikinsu amma uffan bai tofa ba har suka ci suka tsire. Sai da suka lafa dan kansu da kuma maganar Miran Arshaan cikin ɓacin rai a garesu sannan Tajwar Eshaan ɗin ya buɗe idanunsa dake a lumshe ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya..

        Akan Miran Arshaan dake cigaba da faɗa rai ɓace kan kausasan maganganu nasu ga ɗan ɗan uwansa kuma sarkinsu a yau basu dace ba ya sauke idanunsa. Cikin muryarsa mai zurfi da ƙasaita ya fara magana a gadarance kuma a fisge...

       “Barsu Aami. Waninsu bazai canja komai ba, kamar yanda bazai tirsasa Eshaan yin komai ba. Abinda kawai nake son ku sani, Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed guguwace data gama turniƙeku, kuma babu ruwan kogin da zai iya shayar da ita ruwan da zata lafa. Ku daina bama kanku wahala ƙasar ruman da jama'ar cikinta a rubuce suke tsakkiyar tafin hannuna. Idan na murza kwafsanku kawai duniya zata gani a cikin guguwata, idan na matsa, jininku ne zai dinga ɗiga a ƙarƙashin sawun ƙafata na ringa bi ina takawa matsayin kwalta, ya rage naku ku zauna a inda na baku zaɓi ko ku zaɓo mummunan ƙaddararku da kanku tun lokacin ɓacewarku a doron ƙasa baiyi ba”.

     Yana gama faɗa ya miƙe cike da takun Izza da kasaita ya bar falon. Da kallo duk suka bishi ran wasunsu na ƙuna, zukatansu kam tamkar zasu kifo ƙasa dan firgici. Cikin dauriya da nuna jarumta wani ƙyamusashen dattijo da tsufansa ya fara bayyana a cikinsu yay ƙwafa rai ɓace da kausasa murya. 

        “Lallai wannan yaron ya cika ya tumbatsa kuwa. Wai kenan haka zamu cigaba da zama yaro ƙarami na tafka kuskure da mulkin zalunci yana kuma takamu a yanda ya gadama. Akaf tarihin mulkin daular ruman ba'a taɓa tsageran yaro kamar wannan ba, amma ubansa ya ɗaura shi matsayin Shahan-shan bayan babu mai makamancin shekarunsa daya taɓa zama a wannan matsayin. lokaci yayi da zamuyi bore wajen tsigesa kafin ya gama halaka ƙasar baki ɗaya tunda naga shi ran ɗan adam ba'a bakin komai yake garesa ba. wama ya sani ko shine yasa a dasa nakiyar kamar yanda ya kashe ubansa da ƴaƴan mutane da aka aura masa. Koda yake minene ma na tantama tunda ga amsa ya bamu da bakinsa cewar ƙasar da ƴan ƙasar duk a tafin hannunsa muke”.

      A zahiri dai kowa yay tsitt yana sauraren dattijon, amma a zukatan wasunsu farin cikine fal da zantukan wannan tsoho ga Tajwar Eshaan ɗin da mafi yawansu shakkarsa ta gama zagaye tunaninsu duk da kuwa kusan duk sun haifesa dan babu wani sa'ansa, dan har yanzu tun ƴan majalissar mulkin mahaifinsa ne bai canja ba. Dattijon na rufe baki Miran Jasim ya miƙe rai a ɓace shima. Dattijon ya watsama wani mummunan kallo da faɗin, “A lallai ka cika dattijon banza dan bazan kalleka matsayin Aami ɗinmu ba yau kam. Mun godema ALLAH daya fara nuna mana ku a zahiri, ai bamu san ɗan ɗan uwanmu ya kai muku har haka a zuciya ba sai yanzu. To ku sani duk ma mai irin wannan tunanin ya makaro, Eshaan kuma a gareku sai gani sai hange sai hararar nesa, dan badai mutum ba ku rubuta ku aje”. Ya kare maganar yana ɗan ƙyaftama Miran Arshaan daya saki baki tsabar al'ajabin ɗan uwan nasa da kasa fahimtar inda ya dosa. Cikin sauri ya kaɗan kansa da amshe zancen a fusace shima yana miƙewa. “Aam ai ban san haka kakeba wlhy sai a yau, ashe zaka zama na farko a jerin wanda zasu soki jinin Haysam Akhi kuma ɗan uwanka mahaifinmu dan ƙasa ta rufe idanunsu? To bazamu ce da ku komaiba a yanzu, amma kusani duk wanda yake da wannan ƙudirin a ransa jininmu fansa ne ga kare Eshaan tako wace fuska. Mun barku lafiya”.

      Waɗan nan zantuka na Miran Jasim da Miran Arshaan sun matuƙar saka ruɗani a zukatan duk wanda ke a wannan zauren taron. A take wasu suka shiga barranta kansu ga wannan magana ta dattijon Aamin sun ganin waɗanda ma ya dace suyi hanƙoro da kwarema Tajwar Eshaan ɗin baya saboda kwaɗayin kujerar da yake kai tunda suma sunada hakki a kanta na tare da shi su kuma a wa. Anan fa rikici ya kaure aka tashi baram-baram....


      ★★


     “Nikam na kasa fahimtar dalilin ka nayin hakan”.

   Miran Arshaan ya faɗa bayan fitowarsu daga zauren tattaunawar. Wani shegen murmushi Miran Jasim ya saki cike da basarwa. Sai da sukai nisa da sashen Tajwar Eshaan gaba ɗaya sannan yay wata ƴar dariya batare daya kalla Miran Arshaan ɗin ba. Shimfiɗa kenan daga cikin plan b, harinmu na gaba shine ƙulla alaƙa da yarinyar nan, dan na san yanzu abinda zatai yinƙurin farawa shine bincike akan wanene shi”.

       “Wai ya akai duk kake sanin hakan?”. Miran Arshaan ya tambaya cikin mamaki. Dariya Miran Jasim yayi sosai da faɗin, “Arshaan Akhi har yanzu kai ɗin yaro ne. Waya gaya maka mai nema yana zaman jiran tsammani. Tashi yake da ƙwanji da zuciya wajen samowa ai. Karka damu da inda na sani, kai dai kawai ka tabbatar littatafan nan da mukai magana kwanaki an kaisu books room an ajiye a daren yau, dan bana raba ɗayan biyu zuwa gobe zata iya bukatarsu”.

     Cikin halin ko'in kula Miran Arshaan ya ɗage kafaɗu da tabe baki, sai dai acan ƙasan ransa dariya yake dan shima akwai nasa shirin akan hakan tun randa sukai maganar......


      ★★


    Duk da fuskarsa mai tsananin ɓoye sirrin zuciyace a yau ɓacin ransa sai da ya bayyana. Huci kawai yake faman furzarwa a kai-akai. Dan daga ɗakin meeting ɗin nasu da ba'a samu damar tattauna abinda ya dace ba kai tsaye sama yay can ƙarshen rufin ginin sashen nasa da aka gyara domin hutawa kawai. Ko gaisuwar hadiman dake tsare da ƙofar shiga wajen baiyi ba. Ya jima yana faman kai kawo hannayensa zube cikin aljihun farin wandonsa. Bakajin komai tattare da shi sai shaƙa da furzar da numfashi. Sai da ya ɗan samu nutsuwar da yake bukata ya zaro waya dake cikin aljihunsa. Kira yay, bugu ɗaya kuwa aka ɗaga, batare daya amsa gaisuwar da ake masa ba a kausashe ya furta. “A sakaya min shi, inda babu wani mahaluki da zai taɓa hasashe a kansa”. Yana gama faɗa ya yanke kiran cikin sake tsuke fuska da zuƙa ya fesar.....


     (Anya kuwa....?? 🤭bakina kanen kafa ta dai🏇).


     ★★


      A ɓangaren Iffah tana tsaka da kai kawonta da ƙullawa da warwarewa itama wani tunani ya sata tsayawa cak. Miƙewa tai cikin gamsuwa, sai kuma ta koma ta zauna bisa wani tunanin da yazo a bayan wanda ya sata mikewar. A kallo ɗaya zaka fahimci tana cikin yanayin da duk wani ɗan ƙasar zaka iya ganin ya shiga sakamakon wannan baƙon al'amari daya shigo musu. Da farko bai lura da ita ba saboda idonsa rufe yake da ɓacin rai har lokacin, sai da ya kai zaune yay ƙoƙarin lumshe ido sai kuma ya buɗesu a kanta dai-dai itama ta kallesan mamakin yanayinsa na yanzun kuma fes a fuskarta. Ita ta fara janye nata shima sai ya furzar da huci mai zafi yana maida nasa ya lumshe kamar yanda yayi a farko.

     Falon ya ɗauka shiru babu alamar wani zai tanka sai karar na'urorin ac dana tv da har yanzu ake cigaba da nuna al'amarin da yanda hankulan jama'a ke tashe. Kiran sallar la'asar ne ya katse zaman shirun nasu. Iffah ta fara yunƙurawa ta tashi batare da ta ko sake kallonsa ba dan da gaske har cikin rai haushinsa takeji yau. Da kallon ƙasan ido ya bita harta ɓacema ganinsa. Ya ɗan sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya da maida idanunsa ya rufe. Sai da Iffah tai kusan mintuna huɗu da barin wajen sannan ya mike shima har yanzu da alamar ɓacin rai tattare da shi....


           ★★★....


     Bayan Iffah ta idar da salla kamar yanda ta tsara tai shirinta tsaf cikin wata doguwar riga mai tsananin ɗaukar idon duk wanda zai iya kallonta. Kamshin data gaje batare da umarnin mai shi ba ta baza tamkar tayi ɓarinsa a jikinta. A cikin dukkanin shirinta babu bijirema umarnin waɗan da tazo wannan matakin a dalilinsu, dan haka kai tsaye tai kiran number Daneen Ammarah. Ana ɗagawa tai sallama cikin sauƙaƙa murya mai nuna ladabi. Daga can Daneen Ammarah ta amsa cike da zumuɗi da nuna jin daɗinta da wannan kira.

      “Shahrbano ce da kanta haka?”.

Murmushi Iffah tai mai bayyana haƙora jin sunan da Daneen Ammarah ta kirata da shi. Ta girgiza kai tamkar tana a gabanta. “Mamy zakisa a tsire ni a tsakkiyar daular ruman fa”.

     Dariya sosai maganar ta bama Daneen Ammarah. Dan haka ta dara sosai kafin ta tsagaita. “Waya isa ya tsire Ibnati kuma Shahrbano duk faɗin ƙasar ruman. Babu mai wannan power ɗin Ibnati, ko maƙiya sun san kin gagara sai kallo daga nesa, dan kowa ya tabbatar a yanzu ke ɗin ce _Lady of the city_”. 

          Komai Iffah bata iya tace ba, sai dai Daneen Ammarah na iya jiyo sautin murmushinta harta gama kwarzantata. 

    “Mamy dama na kiraki ne na shaida miki ina ɗan son na fito zama waje ɗayan ya isheni, daga nan sai na ɗan leƙama ɗakin karatu kozan samo abin ɗebe kewa”.

    “Hakan kam yana da ƙyau Ibnati. Dan haka ki shirya kawai, hadimanki na sashenki za'a sanar da su su tsumayi fitowarki”.

   “Nagode Mamy, ALLAH ya ƙara miki lafiya da tsohon rai mai amfani da albarka”.

         Cikin jin daɗi Daneen Ammarah ta amsa da Amin tana mai saka mata albarka itama.


      A yau kam Iffah ta ƙara tabbatar da tsantsar ƙarfin ikon mulkin wannan daula. Dan tunda ta baro hawa na ƙarshe hadiman sashin na Shahan-shan ke faman zubewa gabanta batare da dubi da ƙanƙantar shekarunta ba, matsayinta kawai suke kalla. Duk sai taji zuciyarta babu daɗi ganin kusan duk shekarunsu zai iya kaiwa dai-dai dana Hanash, wasu ma sun girme masa. (Nace Iffah danma Tajwar Eshaan yayi sauyi ne da matasa kikaga hakan, da har sa'an kaka da Babiy sai kin gani kuwa). Kamar yanda Daneen Ammarah ta faɗa tako samu hadiman na zaman jiranta. Ta gane hakanne ta hanyar zuwa da sukai suka zube a gabanta da sanar mata matsayinsu. Batare da damuwa ba duk ta bisu da kallo, su biyar ne cif kuma duk yara ƴammata matasa, za'a iya samun sa'aninta dama wanda suka girme mata kamar su Fariha.

      “Ina buƙatar zuwa books room ne akwai wani tsari akan hakan?”.

    Da sauri ƴar babbar dake ta gabanta sosai ta girgiza kai. “Ga Zawjata-almilk babu wani dokar yin hakan ALLAH ya ƙara miki lafiya”.

        “Okay zamu iya tafiya”.

   Iffah ta amsa mata kai tsaye. Hadima ɗaya ce tai gaba sosai Iffah na biye da ita cikin takunta na nutsuwa da wasu kan iya gani su fassara da abinda zuciyarsu ta basu. Bayanta Hadimai huɗu na biye da ita cikin taka tsantsan da nuna girma da ƙarfin ikonta a bayyane...........✍️

    

No comments

Powered by Blogger.