Daudar Gora Book 1 page 32


 *_32_*



........Ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a katafaren ɗakin ta zuƙa ta fesar da cigaba da bin komai daki-daki. Ɗaki kam ya cika a kirasa ɗaki ga masu arziƙin dake ɗaukar duniya gidan zama. Sai dai ta gama ayyanawa a ranta babu wani ƙyale-ƙyale da zatai sakacin da zai ruɗeta har ya dakatar mata da ƙudirinta data fara taka tsanin nasararsa a yau insha ALLAH. Ta saki

kasaitaccen murmushi da ware hannayenta iskar na'urar ac ta busota tare da ƙamshi, idanunta ta lumshe ta buɗe tare da tsuke fuska. Cikin wani kakkausan sauti daya bambanta da nata na baya ta furta.

       “Yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Dodon matsafa MATAN ƘWARAI bisa kanka!!”...


    (🥱 Iffahn mu irin wannan alwashi haka🤔 kinfa fara bani tsoro😱🏇).


       ★★...


   Tun wucewar Malikat Haseenat ya bar falon shima. Tsaye yake jikin windown ƙaramin falonsa na hutawa da babu mai shigarsa sai shi ɗaya tak da amintacen hadiminsa mai gyarasa. Dan a doka ma hatta matarsa bata da hurumin shiga wannan falon a tsari da ƙa'idar masarautar. Hasken daya ƙawata cikin masarautar ya bashi damar iya ganin abubuwan dake kusa daga inda yake, sai dai kuma a zahiri idanun nasa ne kawai ke kallon zuciyarsa sam ba'a nan take ba. Ya kwashe tsahon lokaci a wajen kafin ya warware hannayensa dake goye a bayansa ya furzar da numfashi. Ƙofar ɗakin barci ƙwaya ɗaya dake a falon ya nufa. Shima tsaf yake tamkar anan yake zaman din-din-din. A maimakon kwanciya anan ɗin ma zaune yakai cikin kujerar dake ajiye a gefe domin hutawa kawai. Tun agogon ɗakin na juya sakanni da mintuna har ya koma awanni yana zaune idanunsa lumshe, ya kwantar da bayansa a makarin kujerar dake ɗan juyawa a hankali. A kallon fuska baka isa gane yanayinsa ba balle ka samu damar masa fassara. Bugawar agogon ɗakin mai nuni da cikar ƙarfe biyu dai-dai ta sakashi buɗe idanunsa da ƙarancin hasken ɗakin ya hana damar iya tantance launinsu a yanzu. Agogon ya tsurama ido tamkar mai lissafa daƙiƙun da suka cigaba da motsawa.....


      A ɓangaren Iffah wannan lokaci na dai-dai da kai goshinta ƙasa domin yima UBANGIJI suduja a karo na babu adadi. Tun bayan kammala lissafe-lissafenta da ƙidaye-ƙidaye ta zanzare rigar jikinta, ƙaramin akwatinta ta buɗe babu alamar damuwa tattare da ita ta sauya kayanta zuwa abaya. Daga haka ta nufi bayi bakinta ƙunshe da tarin addu'oin da taketa yi tun shigowarta ɗakin. A karan farko data buɗe fanfo da nufin yin alwala saɓanin zubar ruwa sai taci karo da jan abu tamkar jini. Tabbas taji firgici, amma sai tai yaƙi da rauninta wajen cigaba da addu'a da son daidaita harbawar da zuciyarta keyi da sauri-sauri. Tamkar almara kalar jan ya ɓace a idanunta ainahin ruwa ya maye gurbinsa. Numfashi taja ta fesar zuciyarta na tabbatar mata ta ƙara dakewa. Tsaf ta ɗaura alwalarta kuwa ta miƙe, tana ƙoƙarin gyara ɗan kwalinta taji tamkar an gitta ta bayanta. Anan ɗinma dai zuciyarta ta tsinke, amma sai ta cigaba da ambaton sunan ALLAH ta basar. Bata damu da nan wanin abin salla ba, dan tsaftar dardumar da aka ƙawata ɗakin da ita ya gamsar da ita. Mayafinta ta naɗa tai nagartacciyar tsayuwar salla domin fuskantar UBANGIJIN talikai mai jin kukan wanda ma basu fara kukan ba, mai bada kariya ga wanda ya yarda babu abin dogaro sama da shi...

       Taja tsahon lokaci a sujidar tana mai zubda hawaye da ƙaskantar da kai ga mai gani a duk inda ka ɓuya. Bayan ta sallame tai zaman karatun Alkur'ani a cikin wayarta dan batajin zata samu Alkur'ani a wannan ɗakin da ƙyaleƙyalen cikinsa ya tabbatar mata zamowa fadar aljanu ba komai bane. Sai da ta gama karance baƙara har zuwa inda suka tsaya a makaranta sannan tai addu'a mai tsawo itama. Sosai taji wata iriyar nutsuwa na ratsa dukkan jikinta, ta sauke ajiyar zuciya da miƙewa. Hankalinta kwance ta haye katafaren lafiyayyen gadon da Shahan-shan ne kawai ya taɓa hawansa a tarihi. Nanma zama tai tai addu'ar barci ya shafe jikinta ta gyara lausasan filos ɗin da aka ƙawata adon gadon da su ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Barci mai daɗi ya fara fisgar idanunta a sannu-sannu sai gata tana sauke numfashi.......


       ★★...... ★★..... ★★.......


      Bayan wucewar saurayin da Kaka ya shimfiɗama sha tara na arziƙi gidan yay shiru. Kamar yanda bai cema Iyyani komai ba itama batace ba, tsahon wasu mintuna sannan ya miƙe ya shiga ɗakinsa. Tashi Iyyani tai ta bisa, dan ta fahimci maganarce baya buƙatar ayi sam..

          A ɗakin ma baice mata komai ba har tsahon wani lokaci, ganin haka ta katse shirun da faɗin, “A haɗa maka ruwan wanka?”.

    Batare da ya bar abinda yake ba ya jinjina mata kai. Fita tai jiki a sanyaye, babu jimawa ta koma ta sanar masa an haɗa. “ALLAH yay miki albarka”. Ya faɗa kamar yanda ya saba. Ta ɗan ji sanyi a ranta, dan haka ta amsa da “Amin tare da kai” cikin sauke ajiyar zuciya....


       “Ai bakaci wani abincin kirki ba”.

Iyyani ta faɗa idonta akan kwanikan gaban Kaka da ya gama cin abincin data kawo masa bayan fitowarsa wanka. Kai ya jinjina mata da sakin murmushi a karan farko tun bayan shigowarsa gidan. “Alhamdulillahi wanda naci ya wadatar dani”. Kai kawai ta jinjina masa jikinta na ƙara sanyaya. Duk wanda zai sam mijinta a bayanta yake, ta san murmushin sa ba yana nufin farin ciki bane na tsantsar damuwa ce.....

     “Yaya jikinta?”.

Ya katse tunaninta da abinda taketa zumuɗin san ji a bakinsa. “Alhamdulillahi da sauƙi”.

     “ALLAH ya ƙara afuwa. Bara na ganta”.


   Ummu na zaune shiru ta tsurama waje ɗaya idanu suka shiga. Har suka kai zaune gefenta babu alamar tana san da zuwan nasu. Kaka ya kafa mata idanu na wasu sakanni sai kuma ya kauda kai. Taɓata Iyyani tayi, ta kawo nannauyan numfashi da ɗan zabura na ganinsu a ɗakin dan da gaske bata san da shigowar tasu ba. Kaka ta kalla idanunta na cikowa da ƙwalla, sai kuma ta duƙar da kai ta fara gaishesa. A hankali ya nisa kafin ya amsa a taƙaice kamar yanda tai gaisuwar.

        “Jumaimah!”.

      Ya kira ainahin sunanta. 

   “Na'am Baba”.

Ta amsa akan laɓɓanta.

        “Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa. Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka”.

    “Hakane Baba”.

  Ta faɗa cikin rawar murya.

Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta. “ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a garemu baki ɗaya.”

      “Baba mun rasa su suma ko?”.

  Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa. Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma mu fidda rai da samunsu ba”.

      A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa.......


       

       ★★.... ★★.... ★★.....


       Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta ya ambato addu'ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya ɗoramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon data lulluɓa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take ƙyautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken ɗakin ta kai hannu ta ƙara, ta bi ko'ina na cikinsa da kallo tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ƙarin gwiwar sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin Tajwar Eshaan a ɗakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta ambata nan ɗin matsayin ɗakin barcinsa na daren jiya. Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata ɗauki tsallakewar komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take da damar yi shine buɗe kunne da idanuwa taga mizai biyo baya ga kowa da kowa. A yanzu ɗin ma tayi zaton ganin jinin kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin dauriya tai zaman yin azkar, da ƙyar ta iya kammalawa barci yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi alamar barcin nata mai nauyi ne....


         ★★....   ★★.....


       A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar.

    Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faɗa akan abinda suka wayi gari da shi mai matuƙar rikitarwa da zai maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk ɗunbin yawan abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko'a tsakaninsu bai faɗuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce zagaye da su.....


       *_★MALIKAT BUSHIRAT★_*


    Ba'a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga da nutsuwa. Gaba ɗaya a daren ko sau ɗaya bata iya ta rintsa ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunƙurin kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake ɗaga mata hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a karo na farko. A ganinta ganganci ne miƙa nagartacciyar yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce zata fito takanji ƙwalla sun cika idonta. Amma takan danne ta hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa...

     Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ƙirjinta ne ke matuƙar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.....


No comments

Powered by Blogger.