Daudar Gora Book 1 page 30
*_30_*
........Kamar yanda su Malikat Haseena suka faɗa a yau aka tashi da gyaran sashen Iffah, sai dai abinda ya Bama kowa mamaki ba inda aka fara kaita bane. Ɗaya daga cikin sabbin sashen da babu wanda ya taɓa rayuwa a cikinsu ne a masarautar.
Hasalima an jima ana gutsiri tsomar dalilin gininsu da Tajwar Eshaan yasa ayi batare da ansan dalilinsa ba. Ba kayan ƙawata gida kawai aka zubama sashen ba, harda tarin sitturu da kayan ado na sakawar Iffah.A karan kanta kuma masu gyaran jiki na musamman ne suka duƙufa kanta a yinin wannan rana. Da dare ta samu hutawa. Washe gari aka cigaba da mata gyaran da ita kanta sai da zuciyarta ta fara shiga wasi-wasi. Koda yake dama a ciki take. Dan gaba ɗaya kwanakin nan aikinta kawai shine nazari da fasalta abubuwa masu yawa a rai da takasa gane bakin zarensu sam. Sai dai shawarar malam Fawzan ta waccan ranar ta ƙara mata ƙwarin gwiwa da maidota a hayyacinta da matsayin shigowarta daular ruman.....
Tsahon kwanaki uku ta gyaru ta ƙara ƙyau tamkar ba'ita tayi fama da jiyya na a kwanakin baya. Ƙamshin dake fita a jikinta ma kawai ya isa ai kiransa na musamman. Ita a karan kanta har gizago canjawar tata ke mata. Jikinta ya murje ta ƙara girma da cika ido tamkar ba autar Ummu da Babiy ba. Ga wani jin kai da takejin ta ƙara masu neman kere shekarunta. Babu shakka kuma hakan nada nasaba da girman da ake bata.
Masarauta da jama'ar cikinta zance ya yaɗu yau za'a maida Zawjata-almilk sabon sashenta tunda ta samu sauƙi. Shaidar haka kuma nada nasaba da walimar da Malikat Haseena suka shirya, acewarsu ta aure ce da ba'aiba sanadin abinda ya faru za'ayi yanzu. Shirya wannan walima ya kawo ƙananun magana matuƙa, dan kuɗi aka kashe tamkar za'a sake wani sabon auren. Abin mamaki sauran mata biyu kafin Iffah ga Tajwar Eshaan sai al'amarin ya sosa musu zuciya duk da har yanzu zaune suke batare da ko Tajwar ɗin sun san kalarsa ba.
Sam Iffah bata san da wani taron walima ba, sai da aka kammala mata shiri cikin wasu ƙawatattun kaya masu tsananin ɗaukar ido da tabbatar da ita amarya ta gaskiya mai amsa sunan Zawjata-almilk kanta ya fara ɗaurewa. A ganinta in har shigace ta iya rakata sashenta baici ace ta ƙawatu har haka ba kodan kasancewar dare ne ma. Kai mutanen nan fa sun fara caja mata ƙwaƙwalwa, ta faraji a ƙasan ranta akwai manufa. Amma dai koma minene zata jure har zuwa lokacin samun ƴancin kanta na komawa sashen nata dan ta shiryawa kowa talalarsa. A kwanakin baya ta kwantar da kai ne ga kowa domin fahimtar manufar wasu koda kalilanne a cikinsu. Alhamdullah kuma ta dace, dan koba komai ta gama samun yardar Daneen Ammarah da masu gayya da aiki Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Duk da dai tasan kada mage ba yankata bane. Amma koba komai raina allura yakan sa ta zama garma ga wanda yay sakaci ai.
Taji ba daɗi da barin ɗakin data rayu tsahon kwanaki cike da kewa. Koba komai bazata manta da rayuwar kusan sati uku da tayi a cikinsa ba. Ta koyi ilimi da yawa, harma da darasi data ɓoye matsayin sirrinta. Da wannan tunanin a ranta har aka iso babban ɗakin taro na cikin masarautar, wanda ya ƙunshi duk wani babba mai faɗa aji. Al'ajab ya kama Iffah, amma ta dake zuciyarta na sake tauri na nan dalilin ɓoye mata wannan zaman da akai. Amma a zahiri rashin ƙarfin cewa yasata yin luff kamar yanda ta kasance a kwanakin da suka gabata na samun lafiyarta. Daneen Ammarah data kasance mata ƴar jagora kasancewar fuskarta a sakaye take ta kaita har mazaunin da aka tanada dan ita a cikin ƙaton falon bisa tattausar dardumar da aka shirya walimar. Kamar yanda al'adar take, abinci aka fara ci yayinda Iffah ta gagara kai ko ruwan madara bakinta. Yanda tayi ɗin ya sake burge su Malikat Bushirat, suna ji a ransu sun dace da irin surukar da suke fata. Bayan anci ansha kowa ya nutsu. An fara buɗe taron da addu'a, tare da saƙon maraba ga sabuwar Zawjata-almilk, harma da fatan kasancewar ta abinda kowa ke fata. Kowa dai ya amsa da amin a zahiri, a baɗini kam sanin sirrin wasu sai ALLAH.
A mataki na biyu shine zagayawa da Zawjata-almilk takai gaisuwa ga duk wanda ke wajen, kasancewar kakanni ne makusanta da iyaye, da yayye. A yanzu dai kam da taimakon Jasrah ta motsa, bayan ta janye hular rigar alkyabbar jikinta data hana kowa kallon ainahinta a tun farko. Duk da Iffah taji ta takura, hakan wata damace a gareta na sanin dukkan masu faɗa ajin, zai kuma zama jagoran abinda zai taimakawa nata ƙudirin. Idanunta suka cika da hawaye, a lokacin da take durƙushe gaban Malikat Haseena matsayin bankwana. Tanajin tsohuwar a ranta, ta kuma samu wani kebantaccen ilimin zamantakewa da ita. Ta saka mata albarka tare da yaba ƙyawawan halayenta da jinjinama iyayenta tarbiyyar da sukai mata. Ta ƙare da fatan alkairi da samun zuri'a mai albarka tsakaninta da Shahan-shan. Waɗan nan zantika sun zama abin kaiwa da komawa a zukatan manyan masarauta. Dan kowa na ganin kamar wata isharace Malikat Haseena ta isar cewar ta karɓi Iffah ɗari bisa ɗari matsayin Zawjata-almilk fiye dana baya da suka gabata. Iffah a karan kanta taji tausayin tsohuwar bisa ƙudirinta na shigowa daular ruman data tabbatar yasha banban da fatan da Malikat Haseena tayi gareta a yau gaban duk wanda ya isa a ƙasar ruman ma ba daular ruman ɗin kawai ba. Har yanzu har gobe da jibi tana akan bakanta na ɗaukar fansar rasa ƴan uwanta. Abin harinta kuma ɗaya ne tal shine Tajwar Eshaan, inma da wanda zasu biyo bayansa sai ta gama da babban dodon nasu. Ta samu ƙwarin gwiwar hakanne da tabbacin jin sai an kai matan turakarsa ake fiddosu babu rai. Sai kuma bincike da shaƙiƙansa guda huɗu sukai yunƙurin ɗaurata a yanzu haka. Kenan babu buƙatar wasi-wasi koma minene shike ƙullasa...
Malikat Bushirat ma tayi irin makamancin addu'ar Malikat Haseena ne ga surukar tata. Ta ƙara da faɗin ita ɗiya takejin ta samu ba Suruka kawai ba, tana kuma fatan ta kasance kibiyar ajali ga masu ƙudirin sharri a ciki da wajen daular ruman. Tabbas maganar Malikat Bushirat tafi ta Malikat Haseena ɗumama zukatan wasu, yayinda mugun ƙudirinsu akan Iffah ya ƙara hauhawar farashi a zukatansu, amma duk sai suka ɓoye suma sukai mata irin tarbar data ɓoye dukkan ainahinsu. Dan Miran Jasim ma da akazo kansa har ƙyauta ta musamman ya gabatar ga Zawjata-almilk.
Iffah data kasance cikin ladabi da ƙawata harshenta gaban kowa yayin miƙa gaisuwarta duk da ƙarancin shekarunta kaifin basirarta da wayonta ya bata damar nazari da adana cewar kowa a wajen da fuskar daya tarbeta ta hanyar kallonsu a ƙyalkyalin jikin rigarta datai matuƙar taimaka mata harta ambata godiya ga Malikat Haseena data zaɓa mata rigar domin sakawa a yanzun. Ba kalaman kawai ta riƙe ba da fuskokinsu da suka fita tartar bisa taimakon hasken kwayayen wutar lantarki. Harda sunayensu sun kasance kamar wani zane akan dutse cikin ƙwaƙwalwarta da zuciyarta.
Ƙarfe goma da kusan mintuna talatin taron ya tashi na dare, aka fara fita da Zawjata-almilk da kowa ke tunanin sashenta za'a kaita kai tsaye. Sai kuma hakan ya bambanta da tunaninsu a lokacin da Malikat Haseena tabi bayansu akan wheelchair ɗinta matsayin maiyin wannan rakkiya. Abu ne da ba'a taɓa gani ba a masarautar. Dan hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sun sake jinjina wannan soyayya mai ƙarfi data shiga tsakanin Malikat Haseena da Iffah. Sai dai hakan ya musu daɗi, musamman Malikat Bushirat da take ganin hakan matsayin ƙarin sanin wanene Shahan-shan a zuciyar Malikat Haseena ga maƙiyanta.
A lokacin da kowa ke fitowa daga falon da walimar ta gudana bayan gama sallamar sai da safe gagarumin labari da ɗumi-ɗuminsa shine cin karo da motar data ɗauka Malikat Haseena da Iffah a ciki ƙofar sashen Shahan-shan. A wannan karo hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah sai da sukai turus dan shirine da sam basu san da shi ba. A take suka koma ƴar kallo a tsakaninsu, cikin tambayar juna yaya akai haka kuma? Da idanu. Rashin amsa da mai basu amsar ya sasu shanye komai......
★★.... ★... ★★.....
Komai ya tsaya cak a ɓangaren su Kaka a kwanakin nan da suka gabata dangane da neman inda su Babiy suke. Barrister ya sake bin duk hanyar da yake da yaƙinin samu koda na ƙarfin iko ne amma sai ya risketa a toshe. Zuwa yanzu kam su duka ukun sun fahimci komai shiri ne bisa la'akari da labarin da suka bama juna na gargaɗin da akai musu. Sai dai abu mafi ɗaure kai da ban mamaki, wanene mai shirin? A wane dalili yay shirin kuma? Miyasa zaiyi shirin akansu Babiy ɗin?.
Waɗan nan tambayoyi sune suka zama abun tattaunawa tsakanin Kaka da Barrister dama Abu Zainab daya saudaukar da dukkan lokacinsa domin ganin komai ya daidaita. Bisa shawarar Barrister Kaka yay shirin komawa Jimna, dan a cewarsa suna buƙatar bada ƙafa kodan harar rayukansu da aka farayi suma. Saboda a kwanaki biyun da suka gabata da ƙyar Barrister yasha a hanun wasu tankunan mai da suka sakashi tsakkiya bisa titi lokacin da yake tashi aiki. Haka yaron Abu Zainab a jiya anyi wuff da shi daga hanyarsu ta zuwa makaranta a cikin ƴan uwansa. Ba kuma a sakesa ba sai a daren jiya bayan sallar isha'i lokacin kowa ya gama jigata da nema da hasashen inda ya shiga. Rubutacciyar wasiƙar da aka haɗosa da shi yayin maidosa ya basu tabbacin daga inda tsiyar take.
Kaka ya kammala kulle ko'ina na gidan sannan yay sammala da su Abu Zainab tare da godiya ya ɗauki hanyar inda zai samu motar ƙauyen Jumna. Harya sauka a mototaxi aka dakatar da shi, da mamaki yake duban mai mototaxi ɗin dake miƙa masa ƙaramar jakkar hannunsa. “Baba kayi mantuwa, ALLAH yasa na farga da wuri”.
Kafin Kaka ya samu damar cewa wani abu saurayin ya ajiye jakkar gabansa ya koma cikin mototaxi ɗin da baiko waiwayo ya dubi Kaka dake yunƙurin dakatar da shi ba.
“Kar kai jayayya tsoho, ka ɗauka dan naka ne”.
Aka faɗa ta bayansa dai-dai yana kaiwa duƙe zai ajiye jakar. Ɗagowa kaka yayi, sai dai bayan mutumin kawai ya gani sai ƙurar motarsa. Ran Kaka ya sosu, har fuskarsa ta nuna haka. Alamar ƙosawa da wasan kwaikwayon waɗan nan mutane ya fara tunzura kawaicinsa da son bin doka a yanda tazo. Amma ya fuskanci burinsu kawai su kaisa maƙurar da sai ya gwada ƙwanjinsa akansu. Yay ƙwafa tare da ɗaukar jakar.......
★
“Boss ya ɗauka fa”.
Wani matashin saurayi siriri dake zaune cikin taxi nesa kaɗan da Kaka ya faɗa yana ɗan kai hannu a kunensa ya dafe bluetooth ɗin dake manne a ciki.
“Tabbas akwai alamar ɓacin rai tattare da shi a yau, dan fuskarsa harta kasa ɓoyewa”.
Saurayin ya sake faɗa da alamar amsawa wanda ya kira da Boss ɗin a farko idonsa ƙyam akan Kaka da har yanzu ke tsaye jikin wata mota. Kai ya gyaɗa alamar an sake masa magana daga wayar, sai kuma ya gyara baƙar facing cap ɗin kansa da faɗin, “Eh da alama bai samu motar garin nasu bane. Amma gani ina tunkararsa, komi kenan zan cigaba da riƙe wayar dan kaji komai”.
Kaka na shirin ɗaukar jakar da mai mototaxi ya barsa da ita zai bar wajen saurayin ya katsesa ta hanyar masa sallama. A ɗan daƙile ya amsa dan ransa babu daɗi har yanzun. A yanda ya kafe saurayin da idanunsa masu kaifi duk sai yaji ya tsargu. Ya haɗiye yawu da ƙyar cikin ɗan harɗewar harshe yace, “Baba tafiya ne?”.
Kaka dake nazartarsa ya ƙyabe baki cikin masa kallon sama da ƙasa yace, “Kaima nasun ne?”.
Sai da gaban saurayin ya faɗi, amma yay jarumtar ƙwaɓe fuska da faɗin, “Nasuwa kuma Baba? Ni fa mai taxi ne, na hangokane kawai na iso”.
Kaka ya cigaba da masa kallon nazari, sai kuma ya furzar da isaka da kauda kansa yana kallon mutanen daketa faman kai kawo a titin cikin son watsar da lamarin saurayin...
“Bar wajen kamar kayi fushi”.
Aka faɗa daga cikin bluetooth ɗin dake manne a kunensa........✍️
Leave a Comment