Daudar Gora Book 1 page 29


 *_29_*

.........Barrister na ƙoƙarin shiga layin gidan Abu Moosa wata baƙar mota na ficewa. Babu wanda ya damu da ganinta a cikinsu, suka ƙarasa kutsa kai har ƙofar gidansa. Ganin gidan rufe daga nesa baisa sun kawo wani abu a ransu ba duk suka fita. Abu Zainab ne ya ƙarasa har jikin ƙofar. Kansa tsaye ya kai hannu ya fara knoking, amma har tsahon mintuna biyu babu alamar motsin mutum.

     Juyowa yay ya ɗan kalli su Kaka dake kallonsa. Cikin sarewa ya girgiza musu kai. “Banajin fa akwai mutum a gidan nan, dan babu wani motsi”.

    “Kara dai bugawa”.

Cewar Barrister cikin bashi ƙwarin gwiwa. Kai Abu Zainab ya kaɗa ya cigaba da bugawa, maimakon a buɗe nan sai ƙofar makwaftansu ce ta buɗe. Wani matashin saurayi ya fito. Abu Zainab ya maida hankalinsa garesa suka gaisa. Kafinma ya tambaya saurayin ya bashi amsa.

       “Ai banajin akwai kowa gidan nan. Saboda yanzu babu jimawa matar gidan aka ɗauke a mota harda ƙaton akwati”.

    Da mamaki Abu Zainab ya ce,  “Kana nufin yanzun?”.

       “Eh, dan banajin sunma rufa minti goma. Ta kuma yima mahaifiyata sallama akan zata koma garinsu ne. Harma mukayi mamakin hakan ganin duka rasuwar mijinta bai wuce kwanaki goma sha biyar ba”.

    Godiya Abu Zainab yay masa jiki a saɓule ya koma gasu Kaka. “Waifa kunji babu jimawa tabar anguwar nan. A yanda tacema makwaftansu ma ta koma garinsu ne”.

        “Garinsu kuma?”.

   “Haka dai yace. Nifa na fara tsorata da lamarin nan, dan tabbas akwai abinda ke ɓoye da bamu sanshi ba”.

   Tsakanin Kaka da Barrister babu wanda ya iya cewa komai....


        *_MASARAUTA (JASRAH)_*


   “Wai ni naga sai faman moso kike, kinma kasa bani labarin yanda kukai da Akia akan zancenmu na jiya. Kuma naga wucewarku ke da ita ɗazun zuwa sashin Mamma (Malikat Haseena)”.

     Cike da zolaya ta ɗan hararesa. “Ko kuma dai ƴan leƙen asirinku sun sanar maka ba”.

   “Leƙen asiri kuma? Haba sai kace dai ku. Kudai matan masarautar nan ne dai da baƙwa iya rayuwa sai dai ƴan leƙen asiri. Amma mu maza miya haɗamu da wani leƙen asiri kamar marasa aikin yi”.

         Ta ɗan dara kaɗan da taɓe baki. “Muma ɗin ba kowa ne yake hakan ba kamar yanda kuke zargi. Niko waya dameni a daular nan dahar zan damu da saka wani bibiyarsa. Ko lamarin Zaki addu'a ce tamu a garesa kawai”.

     “To ALLAH yasa hakan. Yaya zaman naku ya kasance?”.

   “Zama an samu nasara. Dan inama Akia bayani a take ta amince, ta kumace muje sashen Mamma itama muji ta bakinta. Alhamdullah sai aka dace itama zancen ya ƙayatar da ita. Na taƙaice maka zance a yanzu haka ma mun zauna da ita yarinyar. Insha ALLAHU zuwa gobe ma zata koma sashenta. Sai dai abu ɗaya ne fa Mamma bata amince da shi ba”.

      “Minene shi?”.

  “Sake kai wata Zawjata-almilk turakarsa. Acewarta za'a ƙara jinkirtawa aga abinda yarinyar zata samo. Sannan za'a sakema duka Zawjata-almilk ɗin sabon horo akan kasancewar su Zawjata-almilk a wannan karon”.

         (Wata sabuwa kenan, wannan tsinanniyar tsohuwar ko) ya ambata a zuciyarsa. A fili kam fuskarsa ya kawata da sabon murmushi da faɗin, “Woow wannan tsarin yayi, shiyyasa Mamma ke daɗa birgeni. Hakan ma wani mataki ne da zai taimakemu matuƙa. ALLAH kuma yasa mu dace”.

    “Amin dai Abu Harith. Dan gaskiya a wannan gaɓar ina tsoron a ce abinda ya faru ya sake maimaita kansa. Saboda zuwa yanzu hankalin manyan ƙasashen duniya ya fara dawowa kan ƙasar ruman. Dan ma ana shakkarmu ne da tuni wani zancen ake ba wannan ɗin ba. ALLAH dai ka bayyana gaskiya ka kuma wanke wanda ake neman disashewa saboda son zuciya”.

          “Amin Meera. Amma ko yanzu ɗin ma akwai abinda baku sani ba. Shahan-shan na ɓoyewa ne kawai dan karya tashi hankalin kowa. A wata mai kamawa shugabannin manyan ƙasashe bakwai na africa zasu kawo ziyara ƙasar ruman. Bisa jagorancin shugaban ƙasar Nijeriya, bama raba ɗayan biyu akan wannan al'amarin ne kuma”.

    “Ya Arrahaman”.

Jasrah ta faɗa a tsorace.

  “Ki kwantar da hankalinki, dan ALLAH kuma kar kowa yasan wannan, dan na sanar miki ne kema saboda na yarda da ke”. 

            Badan hankalin nata ya kwanta ba ta jin jina masa kanta kawai. Cigaba da kwantar mata da hankali yay cikin kwantar da murya har barci ɓarawo ya kwashe ta. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya zare jikinsa cikin sanɗa ya fice zuwa ɗayan ɗakin dake jikin wanda suke kwance da waya a hannunsa......


         *_ZAWJATA-ALMILK_*


   Dukan matakin shawarar da Sir Fawzan ya bata shi tabi, dan tunda sukai bankwana da Daneen Ammarah tai shirin barci ta sakama ƙofarta key. Ta fara da buɗe Watsap, sannan ta lalubo number Ajmaal. Cikin sa'a kuwa yana online, wani farin ciki ne ya ratsata. Taja kakkauran numfashi da godema ALLAH.

      _Assalamu alaikum_

   Ta fara turawa da fatan samun amsa zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Tsahon mintuna kusan goma babu alamar zama a buɗe saƙon. Sake tura sallamar tayi a karo na biyu. Ta dasama wayar ido kamar mai irgan fitan numfashinta. Kamar a mafarki taga an buɗe, tai kasare tana jiran taga an amsa sai dai shiru har kusan wasu mintuna goman. A yanzu kam zuciyarta ta sosu, dan duk yanda take buƙatar abu ga mutum ta tsani a wulakantata. Ta cije lips da ƙarfi tana danne fushin dake son mata tasiri.

    _Wa'alaikissalam_.

Aka amsa mata a bazata. Nannauyar iska  ta furzar, itama ta buɗe saƙon ta share. Da ƙyar ta iya danne zuciyarta mintuna bakwai suka cika. 

    _Sunana Fareedah bint Zayyan_.

Tsahon mintuna kusan goma yanzu ma sannan aka buɗe.

      _Na sani_.

Tai shiru tana kallon amsar, sai kuma taja tsaki na takaici. A fili ta furta, “Aikin banza. Ka sani shine baka san aikinka ba mtsoww!!”.

           Sharewa tai, ta rubuta masa. 

   _Kwanaki na kira, amma akaimun tarbar da har yau ina mamakinta. Shin dama manyan ƴan jarida haka suke da wulaƙanta bukatar marasa ƙarfi?_

     Tsahon minti ashirin da buɗe saƙon babu alamar za'a amsata. Hakan yay mata ciwo matuƙa. Sir Fawzan ta kira, bugu biyu kuwa ya ɗaga. A ɗan rikice yace, “Iffah baki ganin akwai matsala yawan kiran nan? Masarauta fa ba irin ko'ina bane sunada hanyoyin tsaro ɓoyayyu ciki harda cctv”.

         “Hakane Sir, amma nima dole ce ta sakani kiran. Anya kuwa wannan abokin naka da gaske ɗan jaridar ne? Sam baya ɗaukar al'amarina da muhimmanci, duk ɗan jarida na kwarai zaka samesa da zumuɗi akan labari, musamman ma irin nawa daya kasance babba”.

      “Miya faru? Bai amsa saƙonki ba ne?”.

    “Ya amsa. Amma yanamun yanga. Harna fara jin gundira a huɗɗa da shi”.

         “Karki saurin karaya, amma nayi mamaki dan masan Ajmaal ba mutum bane mai irin wannan siffar wlhy. Inaga dai akwai aikin da yake yi a wannan gaɓar shiyyasa. Kin san su abubuwan nasu da yawa. Kin san kuwa yanda ya ƙagu akan son jinki, dan ɗazun na fara ƙyara masa abinda ke ranki kaɗan”.

     Ta ɗanji sassauci daga haushinsa. Taja ajiyar zuciya a fili da faɗin, “Shike nan bara na koma”.

   Sallama yay mata ya yanke wayar.

        _Am sorry na haɗa wani aikin ne da saurarenki. Yanzu ina jinki_.

    Da wannan saƙon taci karo bayan yanke wayar. Sanyi ta ƙaraji a ranta. Cikin ɗan karsashi ta maida amsa.

    _Ayya kayi jaƙuri na maka gurguwar fahimta._

   _Babu damuwa_

Aka amsa mata cikin ƴan sakanni. Cike da karfin gwiwa ta rubuta. 

        _Nasan abokinka ya fara maka bayani akan nemanka da nake ido rufe._

     _Hakane. A yanzu haka ma munyi dashi zai bani wani yankin rubutunki dake hanunsa._

   _Alhamdullahi. A yanzuma akwai cigaban wancan rubutun a hannuna nima. Sai dai ban san ta hanyar da zai zo garesa ba ko gareka_.

        _Wannan mai sauƙine ai. Zaki iya turamin shi tanan_

     _Wai! Amma typing ɗin zaimun wahala gaskiya_.

    _Karki damu ki ɗauki hoto_

Cike da zumuɗi ta miƙe. Gado ta ɗaga ta ɗakko notebook ɗinta, a take ta ɗauka hoton duka rubutun ta tura masa.

         _Gashi, insha ALLAHU duk bayan kwanaki uku zaka iya ganin saƙona_

     _Masha ALLAH hakan yayi, sai dai a maimakon kwana uku mizai hana muyi mako-mako. Dan wani abun da zai zo yana buƙatar bin diddigi da faɗaɗa bincike mu tanan a garemu._

        _Yanda kace haka za'ayi. Ni dai fatana ka kasance ɗan jarida mai gaskiya da riƙon amanar kimar ƙasarsa. ALLAH shine shaidata na baku dukkan yarda kai da Sir Fawzan. Idan akasin nasarata ya biyo bayan yunƙurina ku zan zarga. Duk kuma yarinyar data samu kanta a irin halin da ƴan uwana da ni muka kasance kuma zaku amsa sunan azzalumai ne kamar yanda Shahan-shan ɗin ke amsawa a yanzu. Ku kuma dinga tunawa da mala'iku tare da ku masu rubutawa daga ayyukanku na zahiri da baɗini. ALLAH ya cigaba da tsare ƙasar ruman. Idan kanada wata tambaya zaka iya tura min text message na Barka lafiya_.

      Bata jira amsa daga garesa ba ta fita gaba ɗaya. Watsap ɗin ta goge ta kashe wayar gaba ɗayama tana sakin ajiyar zuciya a  jajjere. Sai takejin wani kaso na damuwarta da nauyin zuciyarta ya ragu kaɗan. A wani gefe kuma kamannin mutumin can da wanda ta gani a jiya matsayin Shahan-shan ne ke ta faman mata kaikawo babu alamar zai barta ta huta......


          ★★.... “★★” .....★


    “Lafiyarki da tsahon zamani su da ɗa tabbatuwa uwa mai share kukan masu kuka”.

        Ta-kurya dake kai gwuyawunta ƙasa ta faɗa sakamakon zuwan Uwa gareta a bazata. Kamar ko yaushe, cikin shigarta ta jajayen kaya, ta gyara zaman ƙasaitar ta. Ƙoƙon dake hanunta ta miƙama ta ƙurya. Hannu biyu ta karɓa, ta kafa kai ta shanye abinda ke ciki. 

     “Tukuycin cika umarninmu na yanka babbar baƙar dabba da kikai  ne. Azamarki da himmarki zaisa bazaki taɓa nema daga garemu ba ki rasa Ta-kurya (Wa'iyazubillah 😭).

   “Nagode uwa mai share kukan masu kuka”.

   Murmushin daya sake munana fuskarta ta saki tana ƙara kalmashe ƙafafu a kujerarta. 

       “Karki damu ke mai nasara ce. Minene makomar ayyukan da muka barki da su?”.

    “Ina kan yunƙurin ƙarasawa. Na kuma samu ƙyaƙyƙyawan labari a majiya mai ƙarfi yarinyar zata koma sashenta. Sai dai akwai zaman sirri dasu Uwar masu gida sukai wanda babu wanda yasan misuka tattauna. Ina dai ƙyautata zaton duk akan komawar yarinyar ne”.

         “Kar tattaunawarsu ta dameki. Tabbatar da ƴan leƙen asirinki cikin hadimanta shine aikinki na gaba. Dan kunada yawa masu wannan burin kema kin sani basai na sanar miki ba. Ina kuma tunatar dake rigar can dake a sashen Uwar masu gida. Da zaran ta tare ki kasance ɗaya daga cikin masu janta a jiki. Yardarta gareki ne zai bamu damar amfani da ita wajen cikar burinmu”.

      “Na gode da kasancewar ki haske mai haskamin duk wani surƙuƙin da zai iya zamemin duhuwa uwa”.

    “Biyayyarki garemu ita ce tushen share kukanki Ta-kurya. Dan haka bazamu taɓa barin kiyi kuka ba maƙiyanki suyi dariya ba. Sai dai su suyi kuka ke ki kasance cikin dariya a kullum bisa nasararsu. Karki shagala ƴar shilar suda nada taurin kai, Karki zama cikin jerin mutane masu raina allura ta zame musu garma. Muna son tasha madarar nan a ƙalla sau uku daga gareki da zaran ta tare a sashenta”. Ta ƙare maganar da miƙama ta ƙurya ƙoƙon da bata san daga ina ya fito ba. Dan ganinsa kawai tai a hannunta tamkar ƙyaftawar idanu. Hannu biyu tasa a wajen amsa tana jera mata kirari da godiya. A hankali ta fara disashewa a idanunta tamkar baƙin hadarin da masha ruwa (Bakan gizo) ya shanye cikin sakanni.

     Ta-ƙurya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai kuma ta miƙe da ƙoƙon da Uwa ta bata. A guri na musamman da na'urar sanyi ke aiki ta ajiye madaran, murmushin jin cigaba da tabbatuwar nasararta na cigaba da ƙawata ƙyaƙykywar fuskarta. Ji take a ranta yanzu ne fa za'a fara wasan na gaskiya. Dan dama idan aski yazo gaban goshi masu iya magana kwance yafi raɗaɗi da zafi. Ta jima bata samu irin wannan damar ga uwa ba a ɗan tsakanin nan da mafi yawan lokuta sukafi ganawa cikin ɓacin rai da rabuwa da ɓacin ran. Amma a yau yanda uwa ta ziyarceta ya sakata jin karsashi da ƙarin kwarin gwiwar cigaba da ruguza duk wanda ya cigaba da yunƙurin shiga gaban nasararta.......✍️


     

     “Humm masu karatu, da gaske fa yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya. Ga dai Iffah zata koma ɗakinta. Komawar dake cike da burikan wasu dake zagaye da ita. Buri kuma irin wanda ke kamanceceniya da juna ta fuskar wanzuwa. Manufa kuma kowa da irin tasa. Ita kanta Iffah da nata ƙudirin karku manta. Shin wanene zaiyi nasara ne? Yaya batun su Babiy kuma? Dan maimakon haske komai ƙara cuɗewa yake. Kaka zaiyi wani yunkuri a alamarin kokuwa Barrister zai janye bisa gargaɗin da akai masa shima?. Kumuje zuwa dai dan ba'a fara komai ba sai yanzu😉🥱”.

        

No comments

Powered by Blogger.