Daudar Gora Book 1 page 28


 *_28_*


........Na farko ji a ranta UBANGIJI ya amsa mata addu'ar ta akan burin data shigo da shi Daular ruman. Na biyu minene dalilin waɗan nan mutane na buɗe mata cikinsu?. Na ƙarshe da yafi kowanne razani da ban

mamaki a ƙwaƙwalwarta dama suma sun san shike aikata kisan kenan? Amma suka zaɓi yin shiru saboda ba ƴaƴansu ake halakawa ba kokuwa suma tsoronsa sukeji? A ɗan ƙaramin tunaninta tanaga zasu iya yin amfani da ƙwanji wajen sanin mi Shahan-shan ɗin ke aikatawa musamman Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Amma miyasa suka zaɓi yin amfani da ita? Kodai sun gama gane manufarta ne a kansa.....?

      “Ibnati!”.

   Daneen Ammarah ta katseta daga nisan da tai a tunani ta hanyar kiran sunanta da taɓata. Firgigit kuwa ta kawo ajiyar zuciya. “Karki kasance a dogon nazari, manufarmu ta sakaki a wannan sabgar tana da nasaba ne da dalilai biyu. Na farko juriyarki ta bamu ƙwarin gwiwar kallonki a jaruma. Na biyu jinki wata abu mai muhimmanci da muke fatan nasara ta dalilinta kodan tsallake tarkon masu aikata wannan ɓarna da kika tsallake a harin farko da muke jin shine lagon da aka dinga ɗanawa a farko wajen salwantar da rayukan da suka gabata....”

     “Mamy nima zata yuwu bana tsallake bane dan nafi ƙarfinsu, maybe na tsallake ne saboda tsayawarku da fatanku akan ganin na tsallake ɗin. Amma tabbas zan iya sadaukarwa, zan kuma iya bin umarninku badan inajin ƙarfina ya kai ba sai dan kun isa ku bani umarni”.

          Su dukansu kalamanta sunyi wani tasiri na musamman a zukatansu tare da ƙawatata a cikin idanunsu. A wani gefen sunyi amanna irinta ɗansu ya dace ya samu tun farko, dan ƙarfin gwiwarta sunyi dai-dai da Zawjata-almilk da akafi buƙata ga kowane Shahan-shan. Sannan Malikat da sukema kansu fata.

    “ALLAH yay miki albarka”.

Suka faɗa kusan a tare su duka huɗun. A kan laɓɓanta ta amsa da amin.

      Sun cigaba da tattaunawar da gaba ɗaya ta saka Iffah cikin ƙagara, ƙagara mai nasaba da shiga ruɗanin wani furici daga Daneen Ammarah. Wai jiya Shahan-shan ne wanda ya ziyarcesu a wannan falon, tana buƙatar samun filin tunani dan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta fa gaba ɗaya sun kulle, ruɗani ya gama mamaye duk wani hangenta da dama bai wuce iya tsayin ƙafafunta da shekarunta ba....


       ★★....


    A hankali ta maida ƙofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta lumshe ido da sauke numfashi tamkar mai kokawar jawosa. Shin murna zatayi a wannan gaɓar ko kuwa shiga ruɗani?. Idan ance Shahan-shan ne a jiya ta yarda, shi kuma wanda tai gamo da shi a mabanbanta wajeje kafin shigowarta masarauta wanene shi?. Wannan tambaya tafi kowace tambaya girma da girgiza zuciyarta a duk abubuwan dake cin ranta. “Kai nifa nama ruɗe wlhy”.

      Ta faɗa a zahiri tana zamewa cikin sarewa ta zube ƙasa. Ta jima a wajen cikin halin shiru da ambaton hasbinallahu wa ni'imal wakil ko zata samu dai-daiton komawa cikin hankali dan da gaske komai na halittarta mai motsi ya raunana da rauni mafi ban tsoro da shiga ruɗani. Tsahon lokaci ta kwashe a wajen tana kokawa da raunin zuciyarta da rashin ƙarfin gudanar jini. Fahimtar wancan tunanin na buƙatar lokaci ya sata turesa ta maida hankali akan tattaunawarsu da su Malikat. Tabbas wannan shine babban ƙudirinta dayin ƙundunbalar juriya na tunkarar rayuwar da bata da tabbacin tsallakewa. Duk da tasan anfi ƙarfinta, dama duk wani mai ƙarfi da take kallon ƙarfinta ta zaɓi fuskantar mutum mafi girman iko da tsaro domin ɗaukar fansa. A kwanakin da suka gabata na kasancewarta cikin wannan daula ta fara fidda ran samun cikar burinta saboda dalilai masu yawa. Ciki harda rashin samun koda ƙanƙanuwar ƙofar sanin minene ma daular ruman ɗin ta ƙunsa balle Shahan-shan da kansa. Sai gashi a yau cikin sauƙi an buƙaci kaita inda zuciyarta ta fara raya mata zuwansa ba ƙaramin tsalle bane da ba'a da tabbacin fita idan an shiga, aka kuma sanar mata wani yanki na sirrin daular ruman mai girman gaske da ko na ciki basu san da shi ba ƙila. “Anya babu wani abu a ran mutanen nan saɓanin abinda suka faɗa?” bakinta ya furta a zahiri cikin sake dulmiya a ruɗani. (Koda akwaisa yardar ki dasu ce zata baki ilimin sanin hakan) zuciyarta ta faɗa cikin ƙarfafata da ture raunin dake neman rinjayarta....

     Knoking ƙofar daya wanzu a dai-dai lokacin ya sata jan numfashi a sauƙaƙe. Da ƙyar ta iya miƙewa daga zaman daɓaron da tayi ta buɗe. Daneen Ammarah ta sakar mata murmushi. Cikin yaƙe ta mayar mata da murtani da matsawa ta bata hanya. Rissinawa hadimar da suke tare tai ta gaisheta, hannu kawai ta ɗaga mata alamar amsawa tana bin ledar hanunta da kallo......


      ★★.... ★.... ★★.....


     Kamar yanda aka sanar da Barrister kai tsaye station ɗin da akace su Babiy suke suka nufa. Kasancewarsa babba kuma sananne basusha wahalar ganin ogan station ɗin ba kai tsaye. Sunyi gaisuwa irin tasu ta manyan ma'aikata, su kai kuma gaisuwar girmama juna da su Kaka.

   Barrister ya gabatar da kansa, ya kuma gabatar da abinda suke tafe da shi harda hoton su Babiy domin sauƙaƙawa. Jami'in yay shiru yana kallon hotunan kamar mai hasashe, sai kuma ya ɗago ya kalla Barrister “Gaskiya banajin akwai waɗan nan mutanen a wannan station ɗin Barrister”.

      Barrister daya fahimci matsala ce ke neman shigowa yay ɗan murmushi da muskuta zamansa. “Yallaɓai adai sake dubawa, zata iya yuwuwa ko akwaisu ɗin baka da labarin hakan. Amma tabbas suna a wannan station ɗin. A matsayina na Barrister ba nazo nan dan a bani belinsu bane ba, duk da nasan basu da hannu a abinda ake zarginsu. Nazo ne dan na gana da su, sannan a miƙasu kotu saboda nasan dai ita matar data saka aka kawosu nan burinta a kwatar mata hakkin mijinta”.

      “Iya gaskiyata nake faɗa maka Barrister babu waɗan nan mutanen a wannan station ɗin. Amma mizai hana ku sami ita matar na tabbata tunda tare da ita akaje tasan wane station ne”.

    Barrister yay shiru yana kallonsa cike da nazari. Hakama Kaka da Abu Zainab. Kusan minti biyu shiru babu wanda ya motsa, kafin Barrister ya miƙe yana ɗan murmushi ya bashi hannu. Suma su Abu Zainab miƙewar sukai...


      Da kallo ya bisu har suka gama ficewa, ya kai hannu kan wayarsa dake saman desk ɗin sa yana wani murmushi. A bugu biyu aka ɗauka wayar daya kira. Sallama kawai yay da faɗin, “Kamar yanda kai hasashe ranka ya daɗe yanzu suka bar office ɗina”.

       Shiru yana sauraren mi'ake faɗa daga can, sai kuma yay murmushi da amsawa da “Angama ranka ya daɗe”. Daga haka ya ajiye wayar yana wata ƴar iskar dariya...


      Abu Zainab daya kasa fahimtar komai saɓanin Kaka da Barrister dake hangen wani abu dalilin kashedi da akai musu kafin zuwansu nan dama ya katse shirun da motar ta ɗauka ta hanyar nisawa. “Anya kuwa wannan jami'in akwai gaskiya a maganarsa Barrister. Kagafa yanda yake ƙyaf-ƙyaf da idanu kamar tsohon ɗan jari hujja. Nifa wannan al'amari ya fara bani tsoro wlhy”.

          Barrister da zuciyarsa ke kai kawo ya fesar da huci, “Kana tunanin yaƙi faɗa mana gaskiya ne Zakariyya?”.

      “Fuskarsa ta nuna hakan ai Barrister, ko kuwa Kaka?”.

    Kaka da shima dai yake aune-aunensa a rai ya girgiza kansa. “Zata iya yuwuwa gaskiyar ya faɗa, sai dai kumin wani taimako ɗaya dazai warware mana gaskiyar tasa ko saɓaninta, bayan nan zan sanar muku abinda ya faru kafin zuwanmu nan”.

        Barrister da shima abinda ke'a ransa kenan ya ɗan juyo ya kalla kaka ta madubi, “Muna jinka Baba”.

    “Muyi gaggawar isa gidan Dawood”.

“Shawara mai ƙyau Baba”. 

Barrister ya faɗa yana juya motar hanyar da zata kaisa gidan Abu Moosa.


       ★★... ★★... ★★...


     “Mamy kuma duka wayar da lap-top ɗinne nawa?”.

  Iffah ta faɗa da mamaki. Murmushi Daneen Ammarah tayi, “Ibnati wannan ai ba komai bane ba, sannan ko baki faɗa ba kina buƙatar su tare da ke kodan ki dinga jin motsin gida. Na biyu kuma wannan aikin da zaki fara kowa yasan mai haɗari ne, dolene ki kasance da waya a duk inda kike a masarautar nan. Da zarar Kinga abinda zuciyarki bata kwanta da shi ba a cikin mu huɗun zaki iya kiran kowa ki sanar masa. Lap-top kuwa ni naga ya dace na kawo miki ita domin ɗebe kewa. Amma kiyi taka tsantsan ki kuma kula sosai, dan samun waɗan nan na nufin zaki iya mu'amula da kowa musamman a yanar gizo batare da kin samu tabbacin wanene ɗin ba”.

      “Haka ne Mamy, insha ALLAH zan kiyaye. Nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi”.

    “Karki damu kin cancanta ne ai”.


  ★Iffah ta daka tsallen murna bayan ficewar Daneen Ammarah, harda ƴar rawarta. Duk wani tunani da kaikawon da zuciyarta ke mata akan Shahan-shan zuwan wannan waya da lap-top ya kauda mata shi. Domin a ganinta dama biyu ce tazo mata a lokaci guda kuma zata damata ta yanda dole sai Shahan-shan ya shata. Yanzu dai abu na farko da zata fara shine malam Fawzan. Ta tura masa saƙo bayan nemansa da tai shi da abokinsa wayar Arfa dake hanunta ta mutu ba caji, tana buƙatar tasan ko yaga saƙon? Ya kuma iyayenta suke?.

     Samun wayar da caji yasa tun a daren ta haɗata, duk da taga akwai sim card batai amfani da shi ba ta cire na Arfa ta sanya. Tamkar jira saƙon Malam Fawzan ne ya fara shigowa, jikinta har tsuma yake wajen buɗewa.  Batako kai ƙarshen karantawa ba kira ya shigo. Gabanta ne ya faɗi ganin baƙuwar lamba, amma tsabar ƙarfin hali sai ta ɗaga.

        “Sir!”.

    Ta faɗa cikin gwalalo idanu da nufar ƙofa da sauri ta saka key. Daga can aka amsa mata da “Na'am Fareedah. Ina kika shiga haka? Tun bayan ganin saƙonki na kasa samunki, har zuciyata ta karaya da ko wani ya gano ki ne?”.

     “Babu wanda ya gano ni Sir, akasi aka samu wayar ta mutu, na kuma rasa ta yanda zanyi cajinta dan na manta da cajan a gida”.

    “Ayya. Kin ganni akoda yaushe cikin gwada wayarki nake koza'a dace. Saboda ke na samar da wannan layin na sirri. Yanzu ma gwadawa kawai nake amma banyi tunanin samunki ba sam”.

       Iffah ta share hawayen da suka silalo mata tana ɗan murmushi. “Nagode Sir, koda banyi nasara ba bazan taɓa mantawa da kai ba. Ina fatan ka bincika min su Ummu. Dan sam na kasa samun kwanciyar hankali na rashin jin su”.

    Ɗan jimm yay kamar mai tattaro abin faɗa, sai kuma yay ɗan murmushin basarwa. “Suna lafiya dan har gida naje, sai dai ban samu shiga ba kasancewar suna tare da tsaron dakarun masarautar har yanzu. Amma nayi ƙoƙari mun haɗu da Hanash....”

   “Amma miyasa wayoyinsu basayi?”.

Ta katsesa a ƙagauce. Da ƙyar ya iya tattaro abin faɗa a wannan gaɓar ma. “Shi Babiy wayarsa ta samu matsala ne. Hanash kuwa network ne dan yace min shima yasha nemanki amma baya samunki”.

        “Bani da lafiya ne, ba koyaushe kuma wayar ke kunne ba. Amma yanzu zan sake nemansa insha ALLAHU dan ina matuƙar bukatar son naji muryoyinsu kozan samu nutsuwa”.

    “Hakan yana da ƙyau. ALLAH kuma ya ƙara lafiya. Kinyi waya da abokina kuwa?”.. 

   “Eh nayi, amma kamar yanda na sanar maka a text message an ɗaga amma ana mun wani shirmen banza. Daga ƙarshe ma akace wai na saɓa lamba”.

        Karan farko malam Fawzan yay ƴar dariya. “Taku ne kawai irin na masu iyawa. Amma a yanzu na tabbatar zai saurareki”.

    Iffah ta ɗan taɓe baki kamar tana gabansa. “Ni ALLAH harna ɗauka ko ka yaudareni ne ka bani number daba itaba ma”.

         “Iffah koda abin wasa kikazo da shi bazan masa riƙon banza ba balle wannan mai matuƙar muhimmanci da ma'ana. Yanzu dai ina fatan wayar taki akwai caji?”.

     “Ai bama waccan bace, sabuwa fil aka bani a kwali yau harda lap-top”.

    Jimm yay na wasu ƴan sakkani. Sai kuma ya cire wayar a kunnensa ya duba. Tuna ashema shine ya kirata ya sashi sake maidawa. “Amma baƙya zargin akwai wani dalili a baki wayar? Mutanen nan fa sunada haɗari sosai Iffah. Bazan ɓoye miki ba inajin tsoron ƙarfin ikonsu”.

         “Nice zan baka wannan labarin Sir kasancewata a cikinsu yanzu. Sai dai kuma wanda suka bani wayar yanki ne na mutanen kirkin cikinsu. Kasan a ko ina akwai ƙyakykyawa akwai kuma mummuna”. Tsaf ta kwashe yanda sukai ta sanar masa saboda ta matuƙar yarda da shi. Shine kuma takema kallon wanda zai taimaka mata a wannan yaƙin kamar yanda tai fata. Ya jimanta al'amarin matuƙa, ta wata fuskar kuma yayi murnar ganin hanyar samun nasararsu ce tazo.

      “Lallai mun samu hanya ta jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya Iffah. Sai dai dole kiyi taka tsantsan da waɗan nan wayoyin. Ki buɗe account da duk kike ɓuƙata da layin da suka sanya miki, shi kuma wannan nakin watsap kawai zaki buɗe da shi, sai dai karki barsa akan wayar, da kuma kinyi magana da Ajmaal da shi ki goge watsap ɗin ki cire layin sai zaku ƙara ki maida. Akoda yaushe wayarki ta kasance da security na idanunki bana wayar ba. Dan inada tabbacin suma zasu saka ido a kanki. A daren nan ki buɗe watsap ɗin ki sake ma Ajmaal magana”.

     “Nahode Sir, insha ALLAHU zan yi duk yanda kace”.........✍️

     

No comments

Powered by Blogger.