Daudar Gora Book 1 page 19
*_19_*
..........Shigar Malikat Bushirat sashen Tajwar da yanayin data fito ya sake zama wasu ƙananun maganganu a masarautar, musamman ga masu ikon faɗa aji. Dan ta ko'ina suna da masu leƙen asiri a cikin hadimai da masu tsaron gidan kamar yanda itama Malikat ɗin ke dasu a kowanne sashe. Ga hadimai dai babu damar yin faɗa da kuwwa sai ƴar ƙus-ƙus, ƙus-ƙus ɗin ma sai ka samu wanda kafi yarda da shi kuɗan zanta gudun karka faɗa tarko.
★★......
Tun barowarta sashen Tajwar ta kasa zaune ta kasa tsaye. Abubuwane birjik ke faman mata kaikawo a zuciya. A karo na farko kenan da zuciyarta ta fara rawa akan al'amarin dake faruwa tun daga randa aka ɗora tilon ɗanta karagar mulkin kujerar Shahan-shan. Anya kuwa ba'akwai lauje cikin naɗi ba a wannan al'amarin?. Sannan ba zaton wuta a maƙera sukema komai ba alhalin yana a masaƙa?. Ta rumtse idanunta da sukai matuƙar ja da ƙarfi, saboda zuciyarta ke hasaso abun, amma ƙirjinta ne keci da wutar ƙunar dangantashi da abinda tafi so fiye da komai a duniya. Sai dai ya zatai, hakan kamar dole ne a gareta kodan rashin samun wani bakin zare har yanzu....
Kalmar bakin zare data faɗo a tunaninta ce ta sata buɗe idanu da sauri, sai kuma ta jawo ɗaya daga cikin wayoyinta da dan tsumar jiki tana gyara zama. Danne-danne tai tare da kaiwa kunnemta. Daga can akai sallama tun kafin ita tayi. A taƙaice ta amsa da faɗin, “Jasrah ina buƙatar hadiman nan yanzun nan”.
“An gama Akia”.
Jasrah ta amsa mata da girmamawa. Mikewa tai itama ta hau shirin fita fadarta. Sai dai komai tana yinsa ne a tsanake amma yanayinta tattare da matsananciyar damuwa. Fitowarta dai-dai da shigowar Ghazi, ya zube ƙasa yana mai miƙa gaisuwa a gareta. Hannu kawai ta daga masa bayan ta kai zaune. Jasrah ma dake zaman jiran fitowar tata tai mata sannu da fitowa. Kai ta jinjina mata da maida hankalinta ga Ghazi dake gurfane kansa a risine. Itama Jasrah hankalinta ta maida kansa.
“Ghazi ya naganka kai ɗaya?”.
“Ranki ya daɗe an samu matsala ne”.
“Matsala kuma? Kamar ya kenan?”.
Ɗan jimm yay na jimamin faɗar abinda ke bakinsa. Sanin Malikat Bushirat bata buƙatar kawane-kwane a magana ya sashi girgiza kansa idanunsa na canja kala zuwa ja sosai. “Ranki ya daɗe gawar uku daga cikinsu kawai muka samu, tare da hadiman dake tsaron inda aka killace sun su duka biyun. Diwa da ta rage ma bana zaton zata kai labari, kuma da alama yanzu-yanzu aka aikata ta hanyar madarar da aka basu matsayin abincin rana.
Ba ƙaramar zabura Jasrah tai ba, yayinda Malikat ta rumtse idanu da sauri ƙirjinta yay wata irin harbawa da ƙarfi tamkar zai buɗe dan firgici. Amma a zahiri miskilancinta da ƙasaitar mulki bazai taɓa haska maka komai ba daga yanayin nata.....
★Kamar yanda labarin mutuwar hadiman nan ya isa kunnen Malikat Bushirat haka ya karaɗe kunen kowa a masarautar. Yayinda likitoci suka rufu akan Diwa da itama gab take da rasa tata rayuwar. Wasu kuma sun duƙufa ne akan binciken madarar da suka sha ta ƙarshe duk da kowa ya san daga cikinta ne akama zuba musu ko minene.......
*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Yayinda ake tsaka da jimamin rasa hadiman da sukai sanadin shigar Iffah a mawuyacin halin da take ciki, ita kuma waraka ALLAH ya saukar a gareta bayan duƙufar Baba yaro akanta da maganin da aka amso a wajen Kaka. Tun a mata hayaƙin farko jinin dake fita a jikinta ya tsaya. Hakan ya basu hope ɗin cigaba da bin dokokin da kaka ya kafa na maganin daki-daki har ALLAH yasa aka dace ta kawo wani nannauyan numfashi da ambaton sunan ALLAH.
“Ruwa!”.
Shine abinda ta ambata na biyu. Cikin sauri Daneen Ammarah ƙanwa ta biyu ga marigayi Tajwar Haysam da ayanzu ke tare da ita ta zabura da kanta ta ɗauka ɗaya daga cikin bottle water dake a ɗakin ta ɓalle murfin ta kafa mata a baki. Cikin mawuyacin hali Iffah take zuƙar ruwar, sai dai kasancewar shine abinda tafi buƙata a ƙanƙanin lokaci ta shanye sa tas. Yumma da itama dai uwa ce gasu Daneen Ammarah ɗin, sannan matsayin Kaka ga Tajwar Eshaan dan ƙanwace ga Malikat Haseena ta sake ɓalle wani ta zuba a hanunta ta shafa a goshin Iffah dake jiƙe sharkaf da gumi. Ajiyar zuciya ta sake ja a hankali tare da buɗe idanunta da sukai mata matuƙar nauyi. Kaɗan ta buɗe ta maida ta rufe. Alhmdllh suka shiga ambata da mata sannu, yayinda Daneen Ammarah cike da zumuɗi tai kiran Malikat Bushirat. Ita ta fara sanar mawa kafin mahaifiyarsu Malikat Haseena duk da tana cikin halin ciwon ƙafa da bata iya ko miƙewa sai da taimakon wheelchair dama ga tsufa.....
Cikin abinda baifi mintuna goma ba ɗakin da Iffah ke kwance ya cika da wasu a manyan masarauta. A fuska dai suna nuna farin cikin farkawar tata ne, amma a ƙasan zuciya mafi yawansu kowa da irin tasa manufar. Malikat Bushirat kuwa harda hawayen farin cikinta, farkawar yarinyar da a kallon farko ta gama shiga ranta ya goge mata sauran damuwar abinda ya faru game da kashe Hadiman da aka aika suka aikata sherin daya jawo komai. A take Malikat Bushirat ta bada ƙyauta mai tsoka ga Baba yaro. Hakama wasu a cikin manyan sun masa ƙyautar. Daneen Ammara ce ta biyu, itama kuma ta bada mai tsoka daya bama kowa mamaki.
Ana ƙoƙari daukar Iffah zuwa sashen Malikat Bushirat kamar yanda ta buƙata sai ga saƙo da ga Malikat Haseena cewar akai Zawjata-almilki sashenta. Take fuskokin mutane da yawa ya canja a wajen, saɓanin ta Malikat Bushirat data nuna tsantsar farin ciki da jin ƙaunar surukar tata. Dan dama zuciyarta cike take da fargabar sake kasancewar Iffah babu tsaro. Duk da sashenta ma bazai iya zama kanwar lasa ba ga wani mahaluki a zahiri, sai dai yaƙin sunƙuru. To amma idan ta danganta da abinda zuciyarta ke rawa a kai komawar Iffah sashenta kamar an gudu ba'a tsira bane. Sashen Malikat Haseena kuwa sunyi imanin ko ifiritu da kansa zaiji tsoron gittawa kai tsaye balle wani shiryayye dake a masarautar....
Rashin ƙarfin jiki da rashin dai-daiton tunani yasa Iffah ba fahimtar komai take ba, hasalima tun yunƙurin farko bata sake gwada buɗe idanunta ba suna a lumshe. Sai dai tana jin komai dake gudana har ɗaukarta da akai akan keken asibitin zuwa waje. A mota a ka sakata Daneen Ammarah tare da ita. Sai Malikat Bushirat da tabi bayansu a tata motar da ake tuƙata. Ganin haka sauran ƴan son ganin ƙwaf suma duk suka bisu can dan babu mai fatar yin laifi ga Malikat Haseena.......
*_GIDAN BABIY_*
Tun bayan barin Iffah gidan ɗan sauran kakkaɓin farin ciki da ƙwarin gwiwar da su Fareeha suka barsu da shi ya ida kakkaɓewa. Ummu bata da aiki sai kuka. A kwana uku kawai duk ta rame saboda ko abinci bata ci yanda ya kamata. Hanash kam ba'a magana dan makamancin irin ciwon Iffah na damuwa ne ke neman bugarsa (Depression). Shi kansa Babiy dake dauriya duk ya zuƙe a tsaye wani lokaci har yi yake kamar zai faɗi. Komai ya tsaya musu cak, kunnuwansu ne kawai a buɗe na jiran kiran jana'izar tilon ƴarsu mace data rage. Dan gushewar kwana uku bai sa sun saka ran ta tsallake ba. Suna tsaka da wannan zaman jigum-jigum akai sallama da Babiy ƙofar gida. Kamar bazai fita ba sai kuma ya miƙe cikin ƙarfin hali ya zura takalma ya fita. Ɗan turus yayi idanunsa kafe akan wanda yay sallamar da shi... Abu Moosa da shima ke kallonsa ya iso gabansa da ƙyar yana tangaɗi. Riƙesa Babiy yay da sauri da faɗin, “Subahanallahi Abu Moosa!”.
Bai iya ya amsa masa ba saboda halin da yake ciki. Riƙesa da ƙyau Babiy yay suka shiga ciki yana jera masa sannu. Zai zaunar da shi a soro ya girgiza masa kai cike da ƙarfin hali. “Kamin alfarma mu shiga ciki”. Ya faɗa da ƙyar tamkar numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa. Cikin sauri Babiy ya cigaba da riƙesa suka shiga cikin gidan, shigowarsu yasa Ummu miƙewa da sauri ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa a ƙasan bishiyar dake tsakar gidan...
“Ku bani ruwa dan ALLAH”.
Abu Moosa Ya sake faɗa da ƙyar yana fisgar numfashi. Ruwan Ummu ta kawo masa, dai-dai da fitowar Hanash daga ɗaki saboda jin maganganu na tashi a gidan nasu. Da ƙyar ya iya maƙwarwa uku saboda numfashinsa fisga yake. Babiy ya ajiye ruwan da sake tallafosa jikinsa. “Abu Moosa mike faruwa ne haka? Daga ina kake?”.
Da ƙyar ya iya ɗaga idanunsa dake zubar da hawaye ya kalla Babiy. Sai kuma ya girgiza kan yana jan numfashi da shashsheka. “Abu Hanash ka gafarceni dan ALLAH, nasan wannan yana cikin numfashin bankwana da nakeyi”.
“Babu abinda kamun nikam, dan ALLAH kuma ka daina faɗar wannan magana bara mu kaika asibiti”. Riƙo hanun Babiy dake yunƙurin tashi yay yana girgiza masa kai da ƙyar. “Babu buƙatar hakan, domin ban cancanci kwatankwacin wannan adalcin daga gareka ba, kayi haƙuri ka zauna ka saurari abinda zan faɗa maka da yafi kaini asibiti muhimmanci, nasan kuma insha ALLAHU zai maka amfani da kuɓutar da yarinyarka dama sauran yaran da zasu iya biyo baya a makamancin halin data tsinci kanta”. Numfashin dake neman kufce masa yaja da ƙyar kafin ya cigaba da faɗin, “Abu Hanash ka gafarce ni nine nai sanadin shigar ƴaƴanka wannan halin, dan nine nai shunensu ga masarauta”. Da ga Babiy har Ummu da Hanash wani irin zabura sukai mai bugawa da bugun ƙirji. Ya cigaba da faɗin, “Nayi hakane dan son zuciya da shegen son abin duniya. Sai hassadarka data daɗe a zuciyata saboda sana'armu ta kasance iri ɗaya, ada tare ake amsar zumar mu a masarauta amma daga baya aka koma amsar taka kawai saboda gaskiyarka da rashin algus. Maimakon na gyara nima na zama mutumin kirki kamarka sai na kasa hakan, shaiɗan ya dinga tunzurani akan kayi sammu ne shiyyasa. Tun daga wancan lokaci naketa ƙulla hanyoyin ganin bayanka a matsayin ɗaukar fansa, sai dai duk wadda na ƙulla sai ALLAH ya kuɓutar da kai, hakan ya cigaba da ƙaramin tsanarka, dan haka na cigaba da kutsa kaina cikin masarauta dan kawai naga na ɓataka an wulaƙantaka, nan ma banci nasara ba dai. Kwatsam sai aka samu canji gwamnati, ni kuma nai amfani da wannan dama wajen sake cusa kaina cikin tsakkiyar masarauta harna samu nasarar amsuwa, nasan komai game da mutuwar Zawjata-almilki, dan ina gaba-gaba a hadiman da ke aiki ga masu aikatawar”. Yaja numfashinsa da ke fisga da ƙyar. “Lokacin da aka sakamu aikin binciken yara mata guda biyu masu hankali dan a aurama Tajwar naji a raina lokacin nasarata a kanka ya yi, dan haka na bada sunanka da adireshin gidanka. An ɗauka tsahon kwanaki ana bibiyar yaranka da kai kanka kafin azo gareka. Ko bayan mutuwar ta farko ni na ƙara ƙulla aka sake dawowa ta biyu dan burina kawai naga na durƙusar da kai ƙasa. Ka gafarceni Abu Hanash dan nayi nasara, sai dai ramin muguntar dana gina daga ƙarshe ni na afka ciki......”
Babiy da hawaye suka gama wanke masa fuska ya share yana duban Abu Moosa “Kenan kai ne ka ƙulla na uku ma?”.
“Wlhy a'a bani da alaƙa da wannan, hasalima ban san ƴar wajenka bace sai ranar da aka kawo kuɗin aure”.
“Waye ya kashe min ƴaƴa? Kai kuma miya faru da kai?”.......✍
🤔Ikon ALLAH, wannan duniya ina zaki kaimu, baka damu da kowa ba amma kana barcine da rashin barcin wasu, kana ci ne da rashin cin abincin wasu. Kana numfashi ne da burin ƙaruwar na wasu. Kana farin ciki da gushewar farin cikin wasu. Kana shiga tarkon wahala da dariyar bakunan wasu. Ya ALLAHU ka ɗoramu akan maƙiyammu, ka hanemu yin hassada da zaluntar wani koda ace shi ɗin ya zaluncemu. ALLAH sarki Babiy namu🤦🏻
Leave a Comment