Bakon Lamari 9

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *009*

Ko ina na jikin Amatullah rawa yake gaba ɗaya tsoron Ummanta ya gama mamaye mata Ilahirin jikinta bakin ta ya Rufe ruf ta kasa furta koda kalma Guda ɗaya, Maganar Ummah ke tashi cikin ƙaraji wadda ta cika ɗakin baki ɗaya.

"Wallahi tunda kika kaso auren ki kika dawon gida Ni ba zan cida ke ba kuma ba zan sha dake ba Kuma ba zan miki rainon ƴaba Kuma ba zaki zauna mini a ɗakina ba, Ga ɗakin itace can na kusa da ƙofar Shigowa ki tattara ki koma can bana Buƙatar ki a kusa dani Tunda zaman gidan kike so ai gaki gashi nan yunwar Cikin kima ta ishe ki"


Tunda Ummah ta fara maganar Amatullah ta kafe ta da ido yawun bakin ta ya ƙafe hawayen ma ya daina zuba tabbas Bada ban tana da wayo Ummah ke goyata ba ada Kafin haihuwar su Hassan da tabbas tace ko Ummah ba mahaifiyarta bace tana ƙoƙarin Buɗe baki tai magana Ummah ta daka mata tsawa akan ta tashi tabar mata guri batare data Ji yadda sukai da Imran ba.


Jikin Amatullah na rawa ta ɗauke Kayanta da Iman tabar ɗakin.


Ɗakin da Umman ta umarci ta kwana aciki shita buɗe wanda yake duk ƙura ga itace aciki na girki, Ga duhu haka ta sanya zaninta a ƙasa ta kwantar da Iman wadda ta daina Kukan sai ajiyar zuciya.

Zama tai a ƙasa tana kaɗewa yarinyar sauro sabida anyi ruwa an ɗauke sauro ya sami damar Ƙyanƙyasar ƴaƴan sa.

Har akai asubah tana zaune idanunta sun bushe babu alamun Bacci Kiran sallar assalatu yayi daidai da tashin Iman wadda duk zazzaɓi ya rufe Yarinyar sai kuka take.


Da ƙarfi Ummah ta turo ƙofar tana haska Amatullah da fitila tana cewa.

"Ki sami tsumma ki toshewa ƴarki baki duk ta cika mana gida da kukan ta na jaraba sannan ki fito ki gyara Babanki daga yau na daina yi masa komai dan bazan kashe kaina ba"

Daga haka ta juya tabar ɗakin.


Amatullah ta ɗaga Iman wadda ta lura hannunta ke mata ciwo da alama faɗuwar Jiya ta saka ta bugu haka ta tura mata Nono abaki wanda yarinyar taƙi amsa sai ma gantsare war da take tana Kuma canyara kukan azabar zafin da hannunta ke mata.

Rashin sabo ga yarinta ga haihuwar ta fari ce yasa Amatullah saɓa ta a baya ta goyata wanda hannun ƴar ya kuma matsuwa azaba ta saka Iman baccin dole.

Haka ta fita tai alwala Batare datai sallah ba sabida Jinin biƙin dake zubo mata wanda yau suke kwanaki ashirin da biyar bai ɗauke mata ba.


Daga nan ɗakin Baba ta nufa taje ta gaishe dashi sannan ta fara gyara masa ɗakin wajan shidda ta kammala gyaran baba sannan ta sami Koma wa ɗakin da Ummah ta ware mata nan ma gyara wajan da zasu zauna da ƴarta tayi sannan ta fita Wajan Murhu ta nufa zata ɗora ruwan zafi.


"Lah Anaty yaushe kika zo?"

Cewar Nana dake fitowa daga ɗaki.


"Jiya da daddare"

Ta faɗa batare da sakin fuskarta ba ruwa zata  ɗora mai ɗan Ɗumi dan tai wanka sai dai Fitowar Umma ta dakatar da ita wajan Ɗora ruwan wanda ta tura mata wani kurofeti tace ta dinga Duk abin da zatai na girki akai kada ta kuma taɓa mata nata takaici yasa Amatullah ta rushe da Kuka tana cewa.

"Nifa Ummah Imran ba sakina yayi ba dan kawai yace nazo gida sai ya neme ni shine duk zaki bi ki tsanan kamar bake kika haifan ba"

Wannan maganar ta fusata Ummah wadda ta ɗauki mujiya tabi Amatullah a guje wai zata duketa.


Da gudu tai ɗakin itace ta rufo ƙofa tana silalewa a ƙasa tana kuka!

"Dan ubanki ki kuma gayan  wata magana akan auren ki in banyi ƙasa ƙasa dake ba Yanzu haka bashi na lafto da Yawuna zan biya daman na saka rai Imran zai mana aiken ƙarshen wata kin tashi kin kaso aurenki da bazar wa nake rawa inba ta Imran ɗin ba"

Hassan ne ya fito yana wa Ummah magana wanda shima ta koma kanshi da faɗa kamar zata dake shi ya girgizakai kurum yay ficewar shi daga gidan.

Haka Ummah ta ƙaraci faɗace faɗacen ta tayi ɗakinta duk abun duniya ya isheta.


Minti Goma Hassan ya dawo da baƙar leda a hannunsa ya faki Idanu ya faɗa ɗakin Amatullah wadda ta buɗe shi yanzu ganin Hassan yasa ta saki ajiyar zuciya.

"Yaya kiyi haƙuri da halin mahaifiyar mu Ɗazun nan ta gama ce mana kada wanda ya taimakeki Wanda ni kuma naga hakan ba daidai bane yanzu kike buƙatar taimako Ga wannan kici zan fita aiki inna dawo zan tawo miki da Kuɗi"

Da yake yana jan adaidai ta sahu.


Amsa tayi tana masa godiya bayan ya miƙa mata ya fita.

Ta buɗe ledar Bread ne da indomie bata ci da yawa ba ta naɗe ta aje agefe ta rafka uban tagumi.


Ameerah ce ta faɗo gidan a gigice tana kiran Amatullah.

Nana ta dubi Ameerah da rashin kunya tace.

"Tana ɗakin icce Kuma sai na gayawa Umma kin shigo mana gida"

Ameerah bata kula Nana ba tayi ɗakin ta tura tana cewa.

"Yanzu naji baƙin labari Bakin Baffa wai jiya Alhaji ya buɗe miki Ƙofa Kin dawo gida ya Allah yasa ba auren kine ya mutu ba"

Ameerah ta faɗi cikin Kuka.

Tagumi Amatullah tayi tana share hawaye.

"Ameerah wallahi Imran yace na dawo gida Jiya haka na tawo nan cikin dare Ga Ummah taƙi fahimta ta"

Duka ta kwashe yadda sukai da Ummah ta gayawa Ameerah wadda take kuka kamar itace Amatullah Ɗin Rungume juna sukai suna Kuka.

Ameerah tace mata.

"Allah ya kawo Miki mafita Amatullah haƙiƙa Kin bani tausayi ina ma ina da dama dana taimaka Miki amman Ba komai taso Muje gidan su Nafisa akwai wata mata dake kai ƴan aiki koza ta samar Miki yafi miki wunin gidan Kya rage takaici dan koda kin zauna takaici ne zai kashe ki"

Haka suka tashi suka Fita gidansu Nafisa ƙawar suce Nafisan dan haka daga nan gidan su Nafisan suka ɗauketa suka tafi gidan matar wai ita sabuwa mai kai ƴan aiki.


Ameerah ce taima sabuwa bayani wadda sai da tayi ƙwallah dataji halin da Amatullah ke ciki tai kuma Ala wadai da halin Ummah.

"Bani da aiki mai tsoka a ƙasa amman akwai wani anan Jambulo Gidan Alhaji Idi mai kwano Idan zaki anjima sai na kaiki gidan Tun safe ne ake zuwa har Sai magari ba gida ne Gidan karamci"

Da sauri Amatullah ta ɗago tana cewa.

"Zanyi mama nagode"

Haka suka gama magana da sabuwa sannan suka tawo gida Ameera nacewa Amatullah zata na riƙe mata Iman har ta dawo amman sai ranar da ba makaranta.


Koda ta koma gida Ummah sai da tai mata tas akan ta fita yawon zubar mata da mutunci agari.

"Ummah Kince ba zaki bani ci da sha ba to zan zauna Yunwa ta kashe Ni shiyasa na ɗauki Ameerah muka fita yawon Neman aiki"

Jin furucin hakan yasa Ummah ɗaukar mayafi taje ɓangaren su Ameerah dan ta ciwa Ameerah Mutunci sai dai bata sami Ameerah ba sai ƙannenta wai Ita sunje airport dasu Surayya zasu ɗauko AHMAD sai anan Ummah taji ma maganar zuwan nasa.


Haka ta dawo Gida tana cigaba da mita Ita kam Amatullah batai mata magana ba tana fama da Iman wadda har hannun nata ya Kumbura sosai yayi kamar jan ruwa ( subuhanallahi )

Da Yamma ta koma gidan sabuwa suka ɗauki hanyar Jambulo dan kaita gidan aikin nata..........


AIRPORT.*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.