Bakon Lamari 7

 *BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*


*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *007*


Juyi kawai yake a saman kujera hannun shi riƙe da wayar shi yana duba posting Ɗin da aka turo mishi yanzu na zuwa Kano wanda zai ɗauki watanni kusan uku acan, Shine zai jagoranci  rindunar sojoji ta farko da zasu shiga wasu daga cikin ƙauyukan Kano

waɗanda ake tunanin wasu mutane da ba'a san ko su waye ba suna haurawa cikin dare suna kwashe musu dabbobin su tare da ƙona musu Gidajen su wannan tasa Aka buƙaci sojoji kusan Rinduna Biyar don ta shiga ƙauyukan ta bawa mutanan dake ciki kariya.


Duba Map ɗin ƙauyukan ya shiga yi wanda suke Cikin Ɓangareron Kano maso kabashin Gudu Batare da wata shakka ba ya tura shaidar Gani tare da aje wayar tashi yana Cike wata takarda dake gaban shi.



Tura Ƙofar Office ɗin nashi akai tare dayin sallama Abokin Aikin shi Captain Khalil ne ya shigo sanye Cikin kakin su na soja Miƙa masa hannu yayi suka gaisa sannan ya nuna masa Kujerar dake kallon Shi.


"Khalil yanzu nake ganin Wani posting letter ko kai ma ka gani?"


Captain Khalil yaja tsaki tare da cewa.


"Kai dai Bari Makama nagama Shirin tafiya zamfara kasan  Gida ce amman Mutanan nan suka sauya mana rinduna"


Murmushi Ahmad yayi tare da cewa.

"Au kaifa gida aka tura ka ko? to ka sani Ko kanon ce alheri gare mu?"


Khalil bai yi magana ba ya janyo wayar shi yana nunawa Ahmad cikin ta.

"Kaga nan zamu sauka a Bakabo barrack fa na can janguza wannan posting sam bai min daɗi ba wallahi"


Ahmad yace.

"Na gani mana Allah ya zartar mana da alheri haka kwanakin Baya Nai shirin katsina naga an mayar dani Barno haka na tafi kasan a rundunar mu ni kaɗai nayi rai"


Haka suka ɗan tattauna akan tafiyar tasu wadda Shida Abokin aikin sa Khalil sune zasu jagoranci Rindunar sojojin ɓangaren su, sauran tawagar ukun daga wata tawagar ta daban take.



Bayan gama maganar tasu Khalil ya tashi ya koma office ɗinsa.


Bayan sallar azahar suka soma training da tawagarsu sai wajan yamma ya koma gidan shi duk ya gaji haka ya watsa ruwa ajikin shi ya kwanta agado yana mai jin wayar shi tana ringing!


Idanun shi a rufe ya ɗaga wayar yana sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.

"Tunda mukai magana rannan Shikenan ka share ni ka manta dani wato dani da Babu duka a ɗaya a rayuwar ka Ko Baby?"


Muryar Zee wadda take maganar cikin shagwaɓar da take masa a koda yaushe idan suna waya.


Ya janyo pillow ya matse a kirjinsa ya gaji Hutu yake buƙata amman yasan idan yace mata haka wata rigimar ce zata kuma tashi.


"Kiyi haƙuri zainab wallahi ayyuka ne suka sha kaina yanzu ma haka".....


"Ni babu wani ayyuka kawai kace dai ka sami wadda ta fini"

Ta tare mashi maganar daya ke Niyyar gaya mata.


"To shikenan ƙarya zan miki tunda ni maƙaryaci ne ko?"

Ya faɗa a zuciye yana ƙoƙarin datse wayar.


"Kayi haƙuri nima bai laifi na bane laifin zuciyata ne data ke maitar son ka"

Ta faɗa muryarta na rawa kamar zata yi masa kuka!

Zuciyarshi ta karye sam baya son jin kukan ƴa mace yana mugun sanya mishi rauni.

"Shiii! ya isa Bana son jin kukan ki Nama kusa zuwa kano In sha Allah ki tare ni nan da kwana ki Uku"



Wata ƙara ta saki tana Ihun murna duk azaton ta, ta ɗauka sabida ita zaizo jin ƙarar tai yawa yasa ya datse kiran yana mai kashe wayar Baki ɗaya ya mirgina ba jimawa bacci yay awan gaba dashi.


Bai tashi ba sai magariba yayi sallah ya kuma fita Filin training wanda anan suka ɓata Lokaci har zuwa isha'i sallah kawai yayi ya soma haɗe tarkacen sa yana addu'ar In sha Allah daga wannan tafiyar yabar lagos gaba ɗaya In sha Allah arewa zai koma koda ba Kano state ba.



Zainab.

Ta rungume ƙawarta Rahma tana cewa.

"Alhamdulillah naji daɗin zuwan ka my love"

Rahma ta tureta tana cewa.

"Dallah ajikina kike ba ajikin sa ba mayyar Ahmad ni wallahi har kin soma bani haushi nifa a rayuwa bana son naga mace ta zaƙe a soyayyar namiji sabida ƙarshe sai yayi breaking heart Ɗinta"


Zee ta harari rahma tana cewa


"Ramcy zamu yi faɗa akan Baby wallahi ban haɗa soyayyar Baby data kowa ba rannan da Hajiya tai min baki akan Ahmad sai da nai kwana Uku ban ci abinci ba sabida haka kema zamu ɓata akan shi nina san Baby baze ci Amana taba yadda yake sona har yayi yawa"


Ramcy tabi zee da kallo tana mamakin rawar kanta akan wannan Ahmad mai wa mutane kallon banza.

Dan ita tunda tagan shi sau ɗaya taji baya burgeta sabida kama gidan shi yayta wani haɗe rai yana wani shan ƙamshi kamar wani basarake!



A gurguje Zainab taiwa Rahma Sallama ta wuce Gida ta ɗauki sabon kaya takai Ɗinki tun a ranar ta umarci masu Hidimar Gidansu akan su soma ƙara gyara gidan na musamman don akwai babban baƙon da zai zo.


Ranar haka zainab ta Ishi Hajiya da Dadyn ta da maganar Ahmad wanda suka Biye mata suna taya ta Murnar zuwan Masoyin nata don Dadyn ta har kuɗi ya kuma ƙara mata yace ta gyara Jikinta da kyau.

Washe garin ranar kuwa Zee ta wuce gidan gyaran Jiki wanda aka gyare mata Jikinta daga nan ta wuce wajan Mai make up tai Booking wanda zata je ranar da Ahmad zai sauka in an mata ta wuce airport ta ɗauko shi dan tuni tai masa waya akan cewa ita zata ɗauko shi idan ya sauka daga nan ta wuce dashi Gidan su inya Ci Abinci ya Huta sai ya wuce nasu Gidan ( kuji fa )


Shiko Ahmad koda zee tai masa wannan maganar kawai yaji tane batare daya bata amsa ba don shi tuni Yayi wa Kamal ƙanin shi waya wanda shine zai ɗauko shi don shi baze bi tawagar suba daban zai tawo sa haɗu a filin daga.


Burin shi ya ganshi a gaban Maman shi dan yayi masifar Missing ɗinta Ji yake kamar yay tsuntsu ya janyo Jibi ya ganshi a kano.


Itama kuma Maman tun da yay mata waya zaizo take hidimar tarban shi dan takanas zata shiga Kicin ta shirya masa abinci na musamman wanda rabon ta da kicin tun da Ahmad yabar gida don baya cin abincin kowa sai nata wannan yasa tunda yabar kano ƴammatan ta ke mata girki sai yanzu da yace zaizo Jibi take Hidimar haɗa masa abincin da zai ci idan Allah yasa yazo ɗin wanda zatai mai abincinmu na gargajiya don yafi son shi fiye da kowani abinci.


*ƊAN BARE*


Yau tunda Imran yabar Gidan bai dawo ba sai Cikin dare gaba ɗaya ran shi a ɓace yake sabida haka komai ya gani a gidan ball yake dashi sakamakon Maganganun da Uban gidan shi ya gaya masa.


"Ina son ka Imran wannan auren da kayi ma dan babu yadda zanyi ne amman duk ranar dana tabbata ka kusanci matarka daga ranar zaka gane kuranka kasan ba'a yaudarar Tani Ɗan Manu"

Wannan maganar da Tani ɗan manu ya gayawa Imran shine ya sanya Imran bacin rai ba kaɗan ba Tsoro fargaba ɗimuwa shine ya ke ɗawainiya da IMRAN DARE ƊAYA sunan da jama'a ke kiran shi dashi kenan.

Tsoron shi ɗaya shine kada Tani Ɗan Manu ya gano fa ya kusanci matar shi har ta haihu wanda Auren ma sai da Imran yakai ruwa rana sannan tani ya bar shi yayi sabida a tsarin su tani babu auren wani jinsi wannan alƙawari ne sukai da ƙungiyar su koda yabar Imran ma yay auren dan babu yadda zai da son Imran ne wanda shi kuma Imran Mahaifiyar shice ta matsa masa akan sai yayi auren wannan tasa yayi aure akan sharaɗin babu kusantar matar.


Zama yayi akan Kujera yana saƙa wa da kwancewa na matakin daya dace ya ɗauka akan Amatullah da ƴarta ji yake kamar ya kasheta ya Gudu yabar Gidan.


A fusace ya Nufi ɗakin daya kulleta ya sanya Key ya buɗe ya shiga cikin sa............*Wannan karon ba zan sai da Baƙon lamari complt ga kowa ba domin na riga da na sayar da labarin ga wata kafa jira kawai suke na gama posting na basu kayan su daga na gama shi ya tashi daga mallakina ya koma mallakin  su don na sayar musu dashi, dan haka duk mai son karantawa ya saya tun yanzu da nake posting inna gama ya zama complt ba zan sayar da shi ba sannan innai nisa a paid page nan ma bazan amshi kuɗin kowa ba sabida abubuwa suna Mini yawa bazan iya turawa Mutum shafukan dana wuce ba dan haka duk mai buƙatar ayi wannan tafiya dashi sai ya hanzarta Biya kafin na gama free page dan wannan karon babu sanya Dana gama free pages zamu soma posting paid page babu tsayawa har sai mun gama da Izinin Allah*

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*






*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.