Bakon Lamari 6


 *BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *006*


Sannu a hankali allurar da aka yi mata ta soma sakinta Cikin nutsuwa take buɗe idanunta waɗanda sukai mata nauyi daga sama kuma suka kumbura sosai.


Da farko razana tayi da taga jaririya a gabanta idanunta Buɗe tana tsotsar Hannunta sai da ta yunƙura don ta tashi taji ba zata iya ba.


Bin jaririyar take yi da kallo sannan ta ɗauke idanunta ta mayar saman rufin ɗakin tana tuna tsayin lokacin data ɗauka bata Numfashi wato rabon ta da sanin inda kanta yake tun agidanta a ɗazu da Imran yaso yi mata aika aika tun daga nan kuma bata sake Sanin Inda kanta yake ba sai a yanzu data farka taga jaririya ɗanyar haihuwa a gabanta.


Ina ta sami jaririya? dan ita a iya saninta ba Ciki ne da ita ba bare ace ta haihu.


Sautin Kukan yarinyar shine ya saka ta Juyo da sauri tana bin yarinyar da kallo yadda take Buɗe maƙogwaro tana kuka kamar wadda tai watanni.


Da sauri Nurse ta turo ɗakin ta shigo Ganin Amatullah ta Buɗe idanunta yasa Nurse ɗin tace.

"Ma sha Allah, Amman allurar nan tayi saurin sakin ki sannu Ga babyn ki nan In mai gidan yana kusa sai ya siyo muku madara kafin ruwan maman naki ya kawo"


Gaban Amatullah ya faɗi ta kuma Bin jaririyar da kallo wadda har tari take sabida Kuka! Bakin ta ya gaza furta komai sai dai kawai ido da ta saka tana kallon yarinyar.


Bata san lokacin da hawaye ya jiƙa mata Ƙuncin taba har yana sakkowa saman kirjinta.


Bata shirya haihuwa da Imran ba, Bata so haɗa tsatso dashi ba domin tabbas tasan gaba ita abar turkewa ce wajan ƴaƴanta akan irin uban data Zaɓa musu Saka kanta tayi a saman Cinyarta tana Kuka wiwi sai ɗakin ya kaure da kuka biyu ita nayi ƴar tata tana yi.


Ko kallon yarinyar batai ba wani irin tsanar yarinyar taji har cikin ranta saboda Duk abin da ya danganci Imran bata ƙaunar shi.


Kuma adaidai nan Ummah da Imran suka turo ƙofar suka shigo.


"Yawwa daman ina mata magana akan a sai wa jaririyar madara kafin ruwan mama ya sakko sai ta saka Min kuka koda yake haihuwar fari ce"


Cewar Nurse ɗin wadda take gayawa Imran da Ummah.


Amatullah cikin ranta tana kuma jin al'ajabin cikin da babu laulayi bare alamun shi, hana rantsuwa dai Tunda taje gidan bata ga al'adarta ba wannan Kuma ta ɗauka ko fargabar Imran ce ta saka Jinin ma ya ƙafe ya daina zuwa kwata kwata ( Amatullah kenan ai fargaba tsinkar da jini take ba ɗauke shiba kedai Kice bakya cikin kwanciyar hankalin da zaki fahimci kwanakin Jinin ki )


Maganar Ummah ce ta saka Amatullah ɗago wa da sauri.


"Rabu da ita likita akwai abin da ke ranta na baƙin hali shiyasa take wannan Kuka kya kashe kanki a banza"


Amatullah ta ƙure Ummah da idanu wannan wace irin Uwa Allah ya bata marar tausayi.


Da sauri wata zuciyar tace mata shine kema zaki gwadawa ƴarda bata ji ba bata gani ba zuwan ta Duniya kenan


Cikin azama ta ɗauke ƴarta ta ɗorata saman Kirjinta tare da saka baki tana hura mata kunnenta wanda nan da nan Babyn tayi shuru tana Mayar da ajiyar zuciya.


"Ummah ki mata ahankali Please yau ta haihu kinsan akwai rashin sabo a tare da ita"

Cewar Imran Cikin kirsa.


Kafin yace bara yaje ya siyo madarar.


Ummah ta nemi gu ta zauna.


Dan a ɗazu da take zaune a waje ita take tambaye Nurse ɗin kota san ɗakin da aka kwantar da Amatullah shine Nurse Ɗin ta nuna mata tare da bata tabbacin Amatullah ɗin ta haihu wanda shine Umman taje ta shaidawa Imran da murnarta wadda take farin cikin sun haɗa iri da Imran zasu ƙara Cin dukiya dan ita asan samun tama Namiji Amatullah ta haifa ba mace ba.


Koda taje sai Imran ya nuna mata bai ma san Amatullan ta haihu ba bayan Kuma ya sani ɗin.


Haka sukai zama kamar na kurame a ɗakin har sanda Imran ya dawo da kaya niƙi Niƙi kayan jaririyar kusan kala Goma sai auduga da su pampers tare da madara haka ya dire Ummah sai faman yi masa sannu take wanda bata ma Amatullah kamar hakan ba, Dan ita ko arziƙin sannun ma bata samu ba sabida takaicin Maganar da Imran ya gayawa Ummah a waya har yau bata saki zuciyarta ba.Haka Amatullah ta miƙe tare da taimakon Nurse Ɗin ta shiga Toilet ta gyara jikinta ta fito Nurse ɗin ce ta gyara Babyn wajan azahar ya kawo musu abinci mai rai da lafiya ummah sai saka masa albarka ake Kuma babu wanda ta shaidawa Amatullah ta haihu daga Cikin Gidan har zuwa Danginta haka suka kwana a asibitin washe gari aka basu sallama.


Imran yaso Su wuce da ita gidansu amman Ummah taƙi tace tai zamanta a ɗakinta.


"Ummah to waze zauna da ita ke ga marar lafiya?"

Cewar Imran wanda wannan furucin sai da ya bawa Amatullah kunya amman ummah mursisi tai da idanu tace zata dinga asubanci tana zuwa.


Koda suka koma ba laifi ta gyara Amatullah tsaf ta wanke jaririya ita Kuma amatullah daman babu batun wanka amman ta samu gyara mai kyau wajan Ummah koda ta koma gida ma da zata dawo ta zo mata da Maganin wanka wanda zata ke sha.


Sai dai me a kwanaki Biyu Amatullah ta sami sauƙi wajan Imran wanda zai zo su gaisa amman bai taɓa ɗaukar yarinyar ba, Sai dai ya rage mata cin zarafin da yake mata Kuma abun mamaki babu wanda yazo mata barka da sunan ɗan uwan shi.

A kwana na uku ne ya soma tsiro da sabon cin mutunci wanda zai zauna a falo yana zuba mata habaici akan kwaɗayin mahaifiyarta tai kuka ta godewa Allah amman da Ummah tazo sai yayta nan nan da ita yana shirga ƙarya kamar ragowar yaƙi.Yau kwana Biyar da haihuwa Ameerah tazo gidan sosai takewa Amatullah faɗan cewar ta haihu bata gaya mata ba sai Jiya suka ji wajan Hassan ƙaninta Mamaki Amatullah tayi don laifin Ummah ne ba nata ba wannan zuwan na Ameerah tai mata kitso da ƙunshi sannan suka gyara gidan washe gari Maman su Ya Ahmad dasu Anty suka zo don Mama ce ma taiwa Babyn wanka, Dan ita mama barta da rashin son magana wadda ta zame mata kamar Izzah  amman babu ruwanta da Munafurci kamar na sauran matan gidan.


Don tana kallon Anty babar su Ameerah na nuna mama da ido wa Matar kawu, Amman maman bata ɗaga idanu ta dube suba.


A iya zamanta da mama waɗan can Halaiyar nata ta sani amman yanzu taji Ameerah tace tana ɗaga musu kai dan Ahmad zai auri ƴar masu Kuɗi sannan tana danne duk Kuɗin da Ahmad yake turowa.

Ita dai bata san Maman da haka ba amman bata sani ba ko hakan ne tunda Aminiyar Antyn su Ameerah ce, ita daman basa shiri da Ummah saboda Antyn su Ameerah aminiyar mama ce kuma anty tana nuna wa Ummah hassada da baƙin ciki da munafurci a cewar ummah wannan tasa tunda Ummah taga Anty na shigewa jikin mama yasa Ummah ta dena shiga hulɗar su dan ko cikakkiyar magana Ummah bata yi musu.  

 

Sauran matan gida kuma gulma ita kuma Ummah bata gulma barta da son abin duniyarta wannan yasa bata shiri da kowa a gidan take sabgarta ita ɗaya Ita ko Anty maman su ameerah kusan Kullum ma tana sashen mama wadda maman ta ɗauki Anty a matsayin aminiyarta akaf gidan babu wadda mama ta yarda dashi kamar Anty sabida yadda Anty take wa mama Biyayyah tare da nuna mata zahirin ƙauna.


"Kawo kayan a saka mata"

Cewar mama bayan ta shafe Jaririyar da mai Da sauri Anty ta miƙe tana bari ta je ta ɗauko kayan a ɗaki wanda Amatullah tasan ba domin Allah ta faɗi hakan ba kawai dan ta shiga taga ƙwaƙwaf ne.


Minti kaɗan ta dawo da akwatin ƴan kayan gaba ɗaya wanda mamaki ya cika Amatullah haka ta zazzage kayan waɗanda ba yawa gare su ba Matan gidan ko wacce tabi kayan da kallo banda Mama data ɗauki Riga mai kyau ta sanyi ta Sinke ƴar.


"Amatu bakya bata Nono hala?"

Da sauri Amatullah ta ɗago tana Bin mama da kallo kamar su da Ahmad har tai yawa sannan taji ta gaya mata sunan da ɗanta yake gaya mata.


Batai magana ba tai ƙasa da kanta.


"Amsheta ina zuwa"

Mamar ta faɗi.

Da kanta ta miƙe ta haɗowa Amatullah tea mai kauri nan da nan ta rufeta da faɗa tana ce mata.

"Gidan ki babu abin da zaki nema ki rasa cikin sa baza ki ci abinci ba Laifin Hadiza ne ( ummah ) tunda ita ba zata tsaya ta lura dake ba haihuwar fari ce in bata tsaya akanki ba zaki lalace shiyasa nacewa Mijin Hafsa ya kawon abata in watan haihuwarta ya kama"


Amatullah ta amshi tea ɗin ta kafa kai tana sha wanda Anty ta amshe maganar.

"Ai mama yaya hadiza sam ta gyara halinta ace mu ta mayar damu ababan gaba fisabilillahi rayuwar haka zata tafi Ace kaf matan gidanmu sai tazo da kanta taiwa Amatullah wanka"


Mama tai murmushi tace.


"Rabu da maganar Lami bata da amfani Allah dai ya ganar da Hadiza kawai"

Daga haka taja bakinta tai shuru bata bawa Anty ƙofar taba da haka zata ja gulmar Ummah ai tayi da matan gida.


Har la'asar suna gidan anan suka ci abinci ban da mama da take azumin alhamis.


Haka har ranar suna tazo ƴan uwan Amatullah basu yanke ba umma tai mitar zuwan nasu amman Amatullah tace mata arziƙine kuma tun daga wannan Dubarar shan tea da mama ta nuna mata shikenan ruwan Nono ya kawo yarinya ta sami abinci.


Anyi suna lafiya Yarinya taci Sunan Ummah Khadijatul Iman amman Iman ɗin za'a ke ce mata.


Kuma har lokacin Babu wani daga cikin ahalin imran daya zo gidan Amatullah bata sami fuskar tuhumar shiba a daddafe umma tai zuwan sati bayan suna.


Daga nan kuma Amatullah ta koma cigaba da kula da yarinyarta.


Lokacin datai kwanaki ashirin agidan Imran ya soma Tsiro mata da wasu halaiya na daban Son kusantarta acikin Jinin Biƙi ji wani jahilci ƙin amincewar da tayi shine ya tsiri hanata abinci tare da Kulleta a ɗaki tun safe har sai ya dawo zai Buɗeta..........


_EKEJA BARRACK LAGOS STATE_...........

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.