Bakon Lamari 3

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *003*


Zaune yake akan doguwar kujera wadda ya miƙe dogayen ƙafafun shi waɗanda har sun sauko ƙasan carpet sabida yanayin tsayin shi, Ya sanya yayiwa Kujerar Girma.


Jikinsa sanye da singlet army green ta sojoji sai threeqauter jeans, wanda shigar tashi ta bawa kirar jikinshi ta cikakkun maza damar bayyana.


Hannun shi riƙe da Tabar sigari Yana zuƙa ya haɗa ƙaramin Hadari acikin Falon Kunnen shi maƙale da waya wadda yake sauraran Muryar Zainab Budurwar shi wadda aka sanya musu ranar aure nan da wata Biyu masu zuwa.


Dawowar shi kenan daga wajan training ɗin koyar da dabarun yaƙin da suke wa ƙananun sojoji, waɗanda za'a tura Rinduna Shida kwantar da tarzoma a wani ƙauye dake zamfara Wanda har dashi acikin posting ɗin wanda shine ya kasance mai jagorancin rindunar farko kasance warshi ƙwararran captain ɗin soja wanda yasan ta kan dabarun yaƙi sosai.


"Baby yau she zaka shigo Kano ya kamata ka shigo wannan satin Momy nata tambayar ka sabida shirye shiryen auren mu"

Muryar Zee cikin iyayi take masa maganar.


Ya lumshe idanun shi cikin tsananin son da yake mata shima ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a kano don ya ganta yau kimanin watanni Biyar kenan baije Kano ba sai dai suyi waya da ƴan gida dakuma Zee ɗin shi.


"Nima ina ishir war son ganin ki My zee matsalar kawai yanayin aikin namu ne, amman idan kika yi haƙuri Very soon zamu kasance tare"

Ya faɗi maganar cikin dakakkiyar Muryar shi ta jaruman maza.


Kuka ta soma yi masa tana buga ƙafarta a ƙasa cikin yanayin shagwaɓarta dake ƙara narkar dashi cikin tafkin Kogin sonta.


"Ni yanzu kenan bazan ƙara ganin kaba sai kazo Biki fisabilillahi ka min adalci kenan? zuciyata da gangar Jikina son ganin ka suke amman kai ka zaɓi Ka nesanta kanka dani?"


Ta faɗa tana turo baki gaba tana zubar da hawayen Missing Ɗinshi.


Ya Shafa kanshi tare da aje Tabar Hannun shi bayan ya kashe ta, ya ɗauko cingam Guda ya jefa cikin bakin shi yana taunawa a hankali sautin muryar shi ke Fita wanda yake bata haƙuri.


"Kimin uziri My zainab idan kika yi haƙuri ma kwana nawa ne suka rage mu kasance tare"

Ya faɗi maganar Cikin rashin sabo da yawan magana.


Ya jima yana kwantar mata da hankali Cikin kulawa ta musamman wanda ita kuma sai faman Botsare wa take tana zuba masa Complain kala kala Daga ƙarshe ma cewa tayi Zato zo ita ta ganshi In baze zoba shi.

"What! Zainab baki da hankali ne zaki ce zaki zo wajena To mu a tarbiyar mu hakan ba daidai bane ga Yarinya Budurwa, Look zainab Kada ki ga ina lallaɓa ki kice zaki min sokon ci ranki zai ɓaci yanzu"


Ya faɗa yana kashe wayar Cikin takaici Yasan Zainab tana Masifar Son shi amman bai son son nashi ya zama hauka ba da har take Tutiyar biyoshi lagos Jiyay zuciyar shi na rawa akanta da sauri Ya kori shaiɗan tare da tashi ya Nufi ƙaramin Kicin ɗin shi ya tsiyayi Coffee a cup ya nufi Bedroom Yana kurɓa duk yadda wayarta Ke Shigowa cikin tashi wayar Bai Ɗaga ba Yama barta a falo tana ta faman Ringing laptop ya janyo tare da zama saman Sopa ya jona cajin laptop Ɗin sannan ya kuma Fita ya Koma falo lokacin wayarta Tagama Ringing Ya ɗauka baibi takanta ba ya shiga Neman Layin mahaifin shi domin su gaisa.

*************


*KANO*

Unguwar Jambulo.

Cikin ƙaton gidan mahaifin Zainab Alhaji Idiris Mai kwano Dattijon arziƙi Mutumin ƙwarai mai taimako Domin Allah Ba domin duniya ta yaba mashi ba.


Ƙaton Falo ne wanda ya sami damar lashe manyan saitunan Kujerun Royal har Guda Biyar Babbar Mace Zaune  A saman One seater tana danna wayar dake Hannunta Hajiya Zahra Kenan Uwar Gida kuma amaryar Alhaji Idiris mai kwano Haifaffiyar Jahar sokoto Mahaifiya Ga Zainab Wadda Zainab Ɗin kaɗai Allah ya basu a kaf Duniya Duk yawan arziƙin su da tarin Dukiyar su Basu da wani ɗa inba zainab ba wadda suka ɗauki Son duniya suka ɗora mata.


Daga Alhaji Idi har hajja zahra mutanan sokoto ne kasuwanci ya kawo Alhaji idi kano wanda yake zaman sa anan Jambulo ya gina ƙaton gidan shi, Wanda kullum gidan baya rabo da jama'a da yake taimakawa Haka zalika matar shi Hajiya zahra bata da matsala ko kaɗan matsalarta ɗaya shine taga ƴarta Zainab Cikin damuwa.


Zainab Itama bata da wulaƙanta Mutane tana da kirki matiƙa haka in kaga tana wasa da masu aikin su sai ka rantse Ba ƴar gidan bace gaba ɗaya karatunta Na likitanci tayi shine a ƙasar Indiya yanzu haka tana a matsayin Cikakkiyar likitar mata a asibitin Malam Aminu Kano Zainab tana da Mugun kuɗi in ka cire na mahaifanta itama kanta mai kuɗin kanta ce.


Zainab bata da wata damuwa Ko Matsala a rayuwarta sama da Aikin ta Na asibiti da take dan tana masifar son aikinta ,  Sai kuma Ahmad wanda ta ɗauki son duniya ta ɗora mishi tana mai wani irin maitar So wanda ji take kamar ta lashe shi ta mayar dashi Cikinta,In kaga zainab tai kuka akan Ahmad ne in kaga Zainab tai dariya akan Ahmad Ne tana Masifar son shi tana mugun jin tsoron shi bata da dama akan Ahmad, Zainab tana da ƙawaye sosai ƴaƴan manya kasancewarta Mace mai son jama'a da kwashe kwashen ƙawaye Shiyasa bata rabo da su ko gida ko Office matsalar Zainab ɗaya ce tana da mugun Zargi Daidai da ruwa ka bata in bata yarda dakai ba bata sha mace ce mai zargin gaske sai dai Duk zargin nata akwai ta da saurin ɗaukar shawarar ƙawaye kasancewarta Ita kaɗai a gidan su bata da abokin shawara sai Hajiya Babarta wadda take masifar son ƴar tata tamkar tsoka ɗaya a miya, Da wuya kaga Zainab taiwa Hajiya laifi sabida bama cika zaman gidan tayi ba sai week end.

Ita ma Hajiyar da wuya kaga taiwa Zainab faɗa sai dai in tai abun da baya cikin tsari wannan tana ƙoƙarin kai son nesa tai mata faɗa amman ba sosai ba.


Cikin sauri Zainab ta fito daga Cikin ƙayataccen ɗakinta harta tana Tuntuɓe Ta nufi wajan Hajiya mahaifiyarta Jikin zainab sanye ike da riga iya gwiwa da dogon wando kanta babu ɗankwali Doguwa ce fara siririya mai far'a da Sakin Fuska.


A jikin Hajiya ta zauna tana Tura bakinta gaba kamar wata ƙaramar yarinya Duk da Zainab ba yarinyar Bace don zata kai shekaru talatin da Biyu aduniya ( 32 ) amman tsabar Hutu da gogewa ya hana a gane yawan shekarunta.


"Yaya akai Abuwata?"

Da yake sunan da Hajiya ke kiranta dashi kenan.


"Hajiya Ahmad Ne ina ta kiran shi bai ɗauka ba Kodai yana tare da wata Ne?"

Da sauri Hajiya ta ƙwaɓe mata baki tare da cewa.

"Kull kada na kuma ji kina zargin Mijin da zaki aura, Dan Allah Abu ki dinga rage kishin nan da zargi kina son ɓata imanin ki babu fa mai yi sai Allah babu kuma mai hanawa sai Allah"


Kuka Zainab tasa.

"Amman Hajiya danna ce masa zanje nai week end wajan sa zai hauni da masifa dan yaga ina son shi"


Salati Hajiya ta soma tana tafa Hannu 

"Ah dole ya hau masifa yace miki Kin haukace ai a garinku na Shasha shai aka ce ana zuwa wajan wanda ba'a aura ba a kwana ko? tashi ki bani waje wadda bata da girma sai na jikinta"


Zainab ta Rumgume Hajiya tana cewa.

"Hajiyata ban da fushi mana Allah ya Huci Zuciyarki"


Hajiya tace.


"Na kasa gane kanki akan yaron na dan Allah ki dinga kama kanki Ina gudar Miki wulaƙancin Ɗa Namiji idan ya gane mace ce tafi damuwa dashi akan shi"


Kuka Zainab tasa tana Birgima a ƙasa wai Hajiya tai mata Baki Ahmad ya wulaƙantata.......


*Unguwar Ɗan bare gidan*

Amatullahi...........


Auta 09022260850.*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.