Bakon Lamari 20


 *BƘNLMR020*

Cikin Hukuncin Allah Ginin da Ali keyi yayi tsayi domin ana gab da kammala shi A lokacin ya ɗauki Malam Makama da Mahaifiyar shi domin suje su gani Alhamdulillahi sun gani sun yaba har suka saka Mai albarka ginine yayi shi mai kyawun gaske dan In ka dubi Ginin ba zaka ce a

wannan Lokacin ya yi shi ba.


Shekara kamar kwana ce gamai yawan rai!

Haka zalika Kuma dukkan abin da aka sama rana zai zo har ya wuce ya zama Tarihi Irin hakan ce ta kasance a tsakanin Auren Binta da Ali wanda Ko wani Ɓangare Ke shiri kamar babu Gobe kasancewar daga kowani Ɓari aure ne na fari.

Biki na sauran wata Ali ya kammala Gininshi mai azababban Kyau Yayi fainti irin na zamani Lefe Kuwa Malam makama yace Ya barshi Shi zai haɗa wanda aka haɗa kayan Lefe na kuzo Mu gani masu Uban yawa da tsada aka kai gidansu Binta wanda aka tsaida Maganar aure sati mai zagayowa Biki akai gagarumin Biki a wannan Lokaci Ranar juma'a Binta ta tare agidan Mijinta A farkon Zamanta tsoro take Ji sabida Gidan yana da Girma dan sai da aka sadata da Ƙanwarta saudatu wadda take taya hira kafin a hankali ta saba da zaman kaɗai cin.

Babu Abin da Surukan Binta zasu ce mata sai Godiya don ta kama Ƙannen Ali dasu mahaifan nashi ta riƙe Gam wanda hakan yasa Soyayyarta mai ƙarfi a zuƙatan Surukan nata wanda Kusan Koda yaushe Binta tana Galadanci Gidansu Ali anan take wuni Idan ya taso daga kasuwa su wuce Gida kuma a wannan Wunin nata da take bata barin Mahaifiyar Ali tai komai ita keyi mata.

Sai da Binta tai shekaru Biyu a gidan Ali sannan Allah ya bata Ciki Mai azabar laulayi wanda sai da takai da Ta koma Gidansu Don sai da ta share watanni Biyu a wajan Innarta sannan ta dawo Gida bayan an sadota da Saudatu dan take kama mata wasu Ayyukan na gidan.

Cikin Binta nata Girma Ƙoshin lafiyarta na samuwa Cikin Binta yana wata takwas Hafsatu Babar Ali tace ga garin kunan rai yayi halin shi Mutuwar Babarsu Ali ta ɗagama Dukkan wanda Ke cikin zuri'arsu hankali Kuka kam ƴaƴanta sunyi Shi har ba Gobe shiko Malam Makama atake anan ya faɗi wanda daga wannan faɗuwar Kuma Ɓarin Jikinsa ya taɓu Tashin hankalin da wannan ahali suka shiga ba'a cewa Komai a haka aka ƙare Amsar gaisuwar Hafsatu wadda anan gidan Binta ta zauna tana dafama su shu'aibu abinci Har zuwa Lokacin da Cikinta ya shiga wata na tara sai ta koma gidanta a wannan Lokacin Malam makama Jikinshi yayi zafi dan sai an kwantar dashi an tayar dashi.


Ranar wata juma'a da asubah Binta ta soma ciwon naƙuda ranga ranga aka kaita asibiti wanda suna  zuwa asibitin ana ƙoƙarin shiga da ita ɗakin Haihuwa Binta ta haifo Ɗanta Namiji sankacece mai kama da Ita sak haka suka shigo Mota suka yo Gida tunda ta riga ta haihun ma Kai tsaye Gidan mahaifanta suka wuce da ita Masha Allah tabarakallah Duk wanda ya kalli jaririn Binta baya son ɗauke idanu akanshi sabida yadda Allah yayi masa halitta mai kyau fari jajir kamar mahaifiyar shi Kuma Abin farin cikin yadda Binta ta haihu da Cikakkiyar Lafiyarta.


A gidansu ta cigaba da Wankan ta har zuwa ranar Suna wanda Ali ya kawo manyan ragunan shi Guda Biyu Shu'aibu ne yazo dasu Gidan Yaro yaci Sunan Mahaifin Binta AHMAD wanda tsabar farin ciki ya cika zuciyar Malam modibbo yay ta wa Ali Godiya na takwaran da yayi mashi Binta sai da ta cika kwanaki arba'in sannan ta koma gidanta yaronta Yayi Girma yayi ɓul ɓul wanda sai ka rantse yakai wata Uku a lokacin.


Ahmad yana watanni Uku Allah ya amshi ran Kakan shi Mahaifin Binta Malam Modibbo daga mura yana kwanciya sai gawa tsananin ruɗewar da Malam makama yayi da jin Mutuwar Aminin nashi sai ta baka mamaki Kuka yake yana cewa akai shi wajan Abokin shi Ali faɗa yahau yi yana cewa su Shu'aibu mai yasa suka gayawa Babansu Mutuwar.


Haka akai sadakar bakwai ta malam modibbo aka gama kowa ya watse Sai Jikin Malam makama daya ƙi daɗi har takai da sai da aka basu gado a asibiti Kwanan shi uku a asibitin Rai yayi halinshi Allah ya amshi ranshi haka aka gama karɓar gaisuwar shi gidan ya koma sai ƴan mazan kawai Da Ali yaso su dawo gidan shi sai Wani ɗan uwan malam makama ya hana yace baze yuwu yarinya ƙarama a haɗata da ƙartin maza ba hakan yasa sukai zaman su agidan mahaifan su.


Rayuwa na tafiya Komai yana tafiya yadda ya kamata Tun Suna kukan rashin mahaifansu har Kuma rashin ya zama Jiki agaresu Kwanci tashi Ahmad ya shekara ɗaya yana Gudun sa Ko ina ga Shi Ƙato yana da Girman Jiki da bala'in wayo wanda ba zaka ce masa ɗan fari ba, Ita ko Binta tai wata Irin rama Ƙirjinta har ciwo yake sabida ɗaukar Ahmad Dole Innar ta tasa ta yaye shi yana shekara ɗaya da wata Huɗu ta ɗauke shi ya koma hannunta wannan tasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Innah da Ahmad dan ko Binta da yake ce mata ( Mama ) baya yarda ta ɗauke shi masifar ƙiwa baya yarda da kowa sai Innah sam bai shaƙu da Mama da Ali ba sai Innah yana sheƙara Biyu Allah ya tunkuɗo wa da Ali wani irin arziƙi wanda Tuni ya sa ma'aikata suka soma yiwa ƙannen shi gininsu dan yafi son yaga kowanne a kusa dashi a shekarar ya biya musu Hajji shida Binta suka je suka sauke farali Bayan dawowar su Ginin daya sa ake ma ƙannen shi har an gama da yake da Kuɗi sanda su shu'aibu suka je kowa yaga nashi Ɓarin har kuka sukai dan daɗi A lokacin yace Kowanne ya samu yayi aure.


Shu'aibu Lokacin ya gama karatunsa yana ƙoƙarin Neman aiki Yusufa shima ya gama amman takardunsa basu fitoba sai yake zuwa shagon Ali wanda suke ce masa ( Alhaji ) haka suma su Bello da Muhammadu nan dai shagon suke zuwa suma Shu'abu ne kaɗai yake ta faman fafutukar Neman aiki.Allah cikin Ikon sa shu'aibu ya sami aiki a wani banki yayi Murna sosai Haka ya soma aikin shi cike da Nasibi sai dai Babu batun aure a gabanshi Sun sha faɗa da Ali ( Alhaji ) akan maganar ya fitar da matar aure amman yaƙi tun Alhaji na ma shu'aibu faɗa har ya tattara shi ya watsar.


Kwanci tashi Ahmad yana da shekara bakwai amman har Lokacin Binta bata sake haihuwa ba Tuni an saka shi a makarantar primary mai suna Army day dake janguza Bokabo Barrack wadda makaranta ce ta ƴaƴan sojoji masu son suyi aikin soja dama sauran yara masu sha'awar aikin na soja, makarantar haɗe take da Primary da secondry Ahmad na son yayi soja har cewa yake sai ya zama soja wannan tasa Alhaji ya sama mashi wannan makaranta Innah ke  kai abinta ta kuma ɗauko shi, Dan lokacin Ƙannen Binta duk sunyi aure wanda Alhaji ne ke musu kayan ɗaki sannan shike ɗawainiya da Innah Haka kuma ƙannen Maman Kowacce Gidan Hutu take aure Shiyasa innah bata da matsalar Komai Musamman ta ɓangaren Alhaji mahaifin Ahmad ya tsaya mata sosai Musamman yadda yaga tana Son ɗanshi wanda ko zuwa sukai Ahmad baya zuwa wajansu yana maƙale da Innah.


Ahmad nada shekara Goma cif a duniya Mama ta sami Ciki wannan karon ba wani laulayi haka ta haifi ƴarta mace kyakykyawar Gaske Ranar Suna yarinya taci Suna Aysha Wannan yarinya ita ta zamewa Mama abar Hira hakannan ta ɗauki son Duniya ta ɗora ma Aysha sabida ita gani take Ahmad ba nata bane shiyasa Ko jansa ajiki bata yi Shima kuma Baya shige mata.

Duk inda yaje bakin sa akan Innah itama innah bakinta akan Mijinta mai gidanta Amadu.


Aysha nada wata tara Mama ta sami wani Cikin Haka tacigaba da rainon cikin da shayar da Aysha dan sai da ta haihu sannan ta yaye Aysha Saudatu ƙanwar Mama taso tafiya da Aysha amman mama taƙi sabida Soyuwar Aysha aranta Ranar Suna Yaro yaci Suna Kamal.


Ahmad ya shiga  secondry School   Jss one duk dai a wannan makaranta army day lokacin yana da shekaru Goma sha Uku A wannan Lokacin ya sauke alkur'ani mai girma

Yaron yana da Basira sosai abu ɗaya zaka gaya masa ya ɗauke shi a ƙwaƙwalwarshi Yana da wani irin kyau mai fisgar hankali Miskiline tun yana yaro baya da son magana bamai Iya ma halinshi sai Innah don In yaje Gidansu Hutu ma faɗa suke da Mama.


Suma su Aysha da Kamal sun shiga makaranta anan rijiyar zaki Lokacin Mama ta haifi Hafsatu wadda tsiransu da Kamal shekara Biyu dan shi kamal nada shekara Uku Aysha nada Huɗu Ahmad nada Shekaru Goma sha Huɗu a lokacin.

Mama ta kuma haifar mace Fatimah daga kan fatima Kuma taɗan tsaya da haihuwar tata Lokacin Shu'aibu ya soma neman aure wata yarinya Hadiza anan Ƙofar na'isa take Ƴar Babban ɗan kasuwa ce hadiza babanta yana da Kuɗi a wannan Lokacin wannan tasa Ƴaƴan gidansu Suke cikin wadata Sunyi Karatun Boko dana addini daidai misali Sun haɗu da shu'aibu Taje bankinsu gyara account Ɗinta anan soyayya ta Ƙullu Hadiza tana da son Tai gayu tana da Son ta fantama tai sabga da ƴaƴan masu da shi Tana son shu'aibu shima yana sonta sosai wannan tasa suka ƙulla maganar aure a tsakaninsu kowa daya ji batun auren Hadiza da shu'aibu yayi mamaki sabida yadda akasan ta dason Namiji mai kuɗi dan ita tace da wuya ta kasheta gwara daɗi ya kasheta tana da Mugun kwaɗayi da son abin Duniyar tsiya Mahaifiyarta har Tsiya take mata tana ce mata Hadiza inda ba agidan wadata kika taso ba da ban san yadda zaki ba sai ta kada baki tace Baba kenan ai dama ganin Kuna dashi ne yasa naji bana ƙaunar talaka shima shu'aibu dan dai kawai ina son shine Kuma naji ance masu aikin banki suna da albashi mai tsoka wayake son talaka a halin yanzu ai se Dole.

Hadiza mace ce mai hangen na sama da ita mai shegen burin tsiya sai dai ita bata da Munafuruci In ka cire son Kuɗinta bata da wani hali a rayuwarta wannan Kuma halittarta ce haka Itace babba agidansu a mata sai wanta Guda ɗaya ƙannenta mata ƴan Biyu sun taso Cikin gata da soyayyar Iyayensu mahaifinsu nada hannu da shuni shiyasa da maganar auren tama ta taso ba'a ɗauki Lokaci ba aka ɗaura mata aure da shu'aibu bayan shatara ta arziƙin da mahaifanta suka lafta mata a ɗakinta.


Zaman Hadiza da Mama agida ɗaya Zama ne na Girmama juna Hadiza na Ƙoƙarin Bin Mama musamman data ga Mijinta yana da shi ba zata taku ba Kamar wasa shima shu'aibu yana auren Hadiza aka soma masa ƙarin Girma nan da nan yayi Kuɗi sai Hadiza ta soma fantamawa Cikin danginta Komai suka kwaso ita zata yi musu Shekararta Guda Gidan Shu'aibu itama mahaifanta duka suka rasu a hanyar bauchi sakamakon hatsarin Mota Kuka hadiza tasha kamar babu Gobe haka ta ɗebo ƙannenta mata su Biyu ne daman dan namiji yayanta ne ya girma yama isa aure.

Ƴan uwan mahaifansu sun so ta basu ƴan Biyu su riƙe amman taƙi Ita ta aurar dasu alokacin tana shekara Uku agidan shu'aibu dan har Lokacin itama bata haihu ba.


Lokacinne kuma mama ta kuma samun Ciki kamar wasa Mama ta haifo ƴaƴanta mata Guda Biyu Naja'atu da Surayyah wanda aka Ɓoye Musu Hassana da Hussainar daga kansu mama tace In Allah ya yarda tayi autoci Hadiza ce take kula da su Naja ita ke musu Komai dan ita har Lokacin Allah bai bata haihuwar ba mai ɗa aka ce wawa Jan ƴaƴan mama ajiki da Hadiza keyi yasa mama ta sallamawa hadiza Komai nata sukai wata irin shaƙuwa zaman amana da Mutunta Juna ya ƙara Girma a tsakaninsu.


A wannan Lokaci yayan Hadiza yayi aure ya tare agidan mahaifinsu Shima Kuma ya faɗa kasuwanci irin na mahaifinsu.

A shekarar Alhaji ya cewa Yusuf ya fito da matar aure.


Lami

Anan Cikin Ɗiso gidansu yake basu da Uba dan ya rasu Sai babarsu da take riƙe dasu Matane Su Huɗu ƴaƴan babar tasu Ko wacce Tana Sana'ar Cikin Gida don ta ciyar da kanta domin alokacin Babarsu tace ta gaji da Ciyar dasu kowacce ta girma ba Mijin aure dan wani Irin nauyin Jinine dasu dan sa'annin Lami kaɗai sun aurar da ƴaƴa kusan Ɗaiɗai amman ita har Lokacin Allah bai kawo mata ba, gasu mugayen ƙazamai da ƙyar Yaya Babbar yarsu ta sami wani makaho anan gwangwazo ta aura Yana da mata Uku da tarin ƴaƴa haka ta samu ta lalaɓa ta aura itama mai bin yayar tasu ta auri wani bakanine anan yakasai sauran lami da ƙanwarta a haka itama lami taga yusuf taje siyan Hoda shagonsu ta Liƙe masa dan ta girmeshi sosai Amman haka ta Nace da kwarkwasa da Kirsa ta janyo Yusuf har Gidansu.


Domin Lami bata ɗauki Kirsa da kwarkwasa a ƙasa ba gadon babarta tayi wadda jama'a ke mata laƙani da Habi kirsa tafi malam, Habi babarsu Lami mace ce mai masifar kirsa da jarabar Munafurci wanda sai da ta raba Mijinta marigayi da matansa baki ɗaya macece makira Muguwar gaske sai dai ita tace malami baze ci Kuɗinta ba da baiwar Kirsa kaɗai ta raba Mijinta da Kishiyoyinta wanda Mutanen Unguwa ke cewa haƙƙin Kishiyoyinta ne ke Bibiyarta ita da ƴaƴanta da kowacce ta auru da ƙyar!


Lokacin da Alhaji yaji batun auren Yusuf da Lami Yayi Murna ƙwarai Haka suka soma shirin Biki wanda Duk ƴan ƙananun maganganun da Mutane ke kawowa Alhaji akan lami bai yarda ba har akai aure lami ta tare agidanta nan dai Rijiyar zaki Kusa da sashin Hadiza Lami ta tare A farkon zaman nasu gwanin daɗi Lami na tsakiyarsu tana Musu Biyayya sai dai yadda taga mazajen su na fantamawa sai ta ɗauki Baƙin ciki da ƙyashi ta ɗorama ranta a farko sai ta soma zuga Yusuf akan shi baze sami abin da zai tsaya da ƙafarsa ba sai a ƙarƙashin yayansa sai da Yusuf yayi mata kaa! yace bata isa ta rabashi da ƴan uwansa ba daga lokacin ya taka mata Burki bata Kuma gigin gaya masa wata magana akan Ƴan uwan shiba.


Mama bata fiye shiga Hurumin Lami ba sabida bata da yawan magana ita sosai wannan tasa Lami ta koma ɓarin Hadiza tana ƴan kai mata Ƴar Gulmar mama akan ta cika Izza da sauransu sai Hadiza ta taka mata Burki tace ita bata son Munafurci Ganin wannan sai lami ta Ja baya dasu ta Koma rayuwarta ita kaɗai Ga takaicin Samun su Alhaji da yayi mata tsaye aranta.

Duk suna da Kuɗi Mijinta ne a baya.

Lokacin tana shekara ɗaya ta soma laulayin Ciki ashe itama Hadiza tana da nata Cikin a maƙale bata sani ba sai da ya fito sannan ta kula Murna wajan shu'aibu kamar yayi Me.

Cikin Lami da Hadiza yana Girma Har zuwa Lokacin haihuwar su yayi wanda a daran da Hadiza zata haihu Allah ya amshi ran Innah babar mama Tashin hankali ba'a saka maka rana Haka mama ta tafi Galadanci a wannan dare batare data sanar da Matan Gidan ba sabida tsabar ruɗewar data yi.

Naƙuda ce mai wahala ta kama Hadiza wadda Harta kai data fita a hayyacinta ga shu'aibu baya nan a ranar yayi tafiya. Lami da ƙaton Cikinta dake gabda fita ita ke ɗawainiya da Hadiza Cikin Daran Yusufa ke cewa Lami babar mama ce ta rasu lokacin tazo ɗaukar Fitila zata koma Sashin Hadiza ta haska ɗakinta don da Duhu ga ba wuta kuma Injinsu ya Mutu.


Ta kaɗa kai tana cewa Allah ya jiƙan rai.

Koda taje ɗakin Hadiza ta Rungume Hadiza tana ce wa.

"Nikam Babu abin da ya ɗaure Min Kai kamar yadda Mama tai Buris dake kina naƙuda nafa je na gaya mata amman tace kada na takurata ita bacci zatai"

Hadiza ta ɗago cikin tsananin azaba tana cewa Lami.

"Nidai ku kaini asibiti nagaji rabu da ita bata tata nake ba fatana na rabu da abin da ke cikina lafiya"

Haka Lami taita Ɗawainiya da Hadiza cikin son gwaninta har asubah Lokacin Hadiza ta haifo sankaceciyar Ƴarta fara tas mai kama da babanta Ko kallon ƴar bata iyaba sabida azaba Lami ce ta gyara ta tas taima jaririyar wanka sannan ta koma sashinta.

Tai wanka ta tafi Gidansu Mama gaisuwa Lokacin da mama taga Lami tai mamaki har tana cewa mai yasa tazo ita da take da Tsohon Ciki.


Buɗar bakin lami sai tace ai ya zama dole Ne ko ina naƙuda mahaifiyarki ta Mutu ai dole nazo gaisuwa nayi ma da Hadiza tazo mu tawo tare tace Itama ta kanta take ai ba akanki aka soma rashi ba.

Mama taji zafin abun amman bata nuna ba sannan ta Jinjina Halin girma irin na lami.

Har yamma lami tana wajan zaman makokin ana amsar gaisuwa da ita bata cewa Mama Hadiza ta haihu ba haka ta dawo Gida.


Lokacin sashin hadiza ya cika da ƴan uwanta ƴan barka nan ma bata cewa Hadiza Gidan gaisuwa taje ba sai ce  mata tayi asibiti taje dan Taji Cikinta yana juyawa Ƙannen Hadiza suna ta wa Lami Godiya akan Hidimar data yi mata Har Lokacin Ita ma hadiza bata san mama bata nan ba Sai ma Ƙullatar mama da tai aranta tare da Ɗora cewa mama bata ƙaunarta Fuska Lami ta samu wajan ƙannen Hadiza nan take basu labarin Yadda sukai da mama ajiya wanda ƙannen Hadiza sukai ta masifa suna cewa Hadiza sai ta Kula mama bata ƙaunarta Tunda ta kasa zuwar mata tana naƙuda.


A taƙaice Hadiza bata ji Mutuwar babar mama ba sai da Shu'aibu ya dawo koda ya gaya mata ma bata wani ɗauki abun da Girma ba dan bata zata A Daran naƙudarta mama ta bar Gidan ba.

Itama mama da mamakin Hadiza ta dawo wanda sai da takai zuciya nesa taje tai wa Hadiza barka wadda anan Itama Hadizan tai mata gaisuwar Rasuwar da aka mata ɗin.


Yarinya taci Suna Amina.

Amman ana ce mata Amatullahi.

Tun daga wannan kuma sai amincin mama da Hadiza yay baya mama na ƙullatar Hadiza akan bata je mata gaisuwar mutuwar uwarta ba duk da tai mata uzirin Ciki amman yaci ace data dawo taje sashin ta tai mata gaisuwar kamar yadda lami har babarta da yayinta ta kawo sukai mata gaisuwa amman duk yadda take da Hadiza bata samu wannan ba to itama haka hadiza ta ƙullaci mama akan Yadda tai Burus da ita a lokacin naƙudarta da take neman taimako Amman ga yadda ta gayawa lami kada ta dame ta.

Itama lamin har Mahaifiyarta da yayinta takai suka ma Hadiza barka amman ga mamakin Hadiza mama ko ƴaƴanta bata bari sun zo ganin Amatullahi ba.

Wannan shine masomin rashin jituwar mama da Hadiza wanda lami munafuka ita ta haɗa su.

Da wannan damar Kuma lami ta sami Hanyar Shiga Jikin Hadiza dan itace yarinya ta dinga aibata mama tana cewa mama baƙin Ciki take wa Hadiza shiyasa ma taƙi tsaya mata wajan haihuwa Wanda hakan ya ƙara Tunzura hadiza wajan Tsanar Mama acikin zuciyarta wanda gaba ɗaya ma ta daina shiga Hurumin maman.


Amatullah nada wata Lami ta haifo Ameera baƙa mai kama da ita sak.


Lokacin tuni Ahmad ya dawo Wajan mama sabida Gidan Innah ma an kulle shi mutuwar Innace musabbabin dawowar Ahmad Gidan su wanda yake shekarar ƙarshe a secondry baya shiga harkar kowa agidan yana ɗaki Kullum yana tunanin Innar shi Haka rayuwar tashi ta cigaba a gidansu har tsayin wata Guda.

Ranar da lami ta haifi ameerah ranar Hadiza ta riƙo Amatullah a hannu zata shiga sashin lami daga bayanta taji ance.

"Lahh Ji beby mai kyau Umma ki bani ita inyi wasa ina son ta............

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.