Bakon Lamari 18


 *BƘNLMR018*

"Kada ka mini haka Yayah Ahmad kada ka ɗauki Hukunci Cikin sauri, Tun asali baka taɓa min tambaya akan hakan ba ni kuma tsoran ka ya hanani na shaida maka ainihin Gaskiya ta"

Ta faɗi maganar cikin tsananin Kuka gaba ɗaya ta Cakume shi tama Ƙi bashi damar Yin magana sabida yadda ta Cure ajikinsa.


Duk yadda Iman ke uban kuka bai saka ta Ɗauketa ba ita dai Burinta ya saurareta tana hango tsantsar Tashin hankali acikin Idanun shi wanda yake ƙara sanya gabanta faɗuwa.


A hankali yake rage sautin Gudun Motar shi yana gangarawa gefen Titi har ya ƙarasa Gefe ɗaya wanda  ya kashe Motar ya Sunkuyar da kanshi Ajikin sitiyarin Motar Jikinsa yayi sanyi sosai Jinsa yake kamar marar lafiya ba tada da zaɓin da ya wuce na kwanciya a saman bayansa tana cigaba da Kuka wanda hawayen ta ke Ɗiga har saman Fuskar Ahmad.


Ya rintse Idanu da sauri ya Janyeta ajikin sa Yana mai sake matsawa can Gefe Guda.

Ya tsareta da girman Idanunshi.

Yana mai ƙara Gyara Nutsuwar shi kamar bashi ya gama hauka ɗazu ba.


"Nayi Miki Uzirin hakan Amatuhh na kuma yarda muna da laifi ni zan saurare ki bani labari mai ya haɗa ki da Mijin ki inda dama zan mayar dake har Wajan sa in naji Kece baki da gaskiya"

Ya faɗi maganar cikin dauriya tare da ƙarfin hali.


Ta goge hawayen ta a hankali ta janyo Iman Jikinta, Ya saka hannu ya amshi Iman ya ɗora ta saman kafaɗun sa yana Jijjigata daga ita har Mahaifiyarta ababan tausayine yaji ya tsani kanshi akan tsawar da yayi mata ɗazu Amatuhh bata dace da tsawa ba.


"Ka daina fushi dani to yaya?"

Ta faɗa tana Goge hawayen ta.

Subuhanallah! ya faɗa cikin ransa yana mai Jinjina mata kai.


Tiryan tiryan amatuh take bawa Ahmad labarin halin da ta shiga agidan Imran sai dai ko kaɗan taji bakin ta ya kasa faɗa ma Ahmad Imran na ƙoƙarin Nemanta ta baya taji tana son rufa mashi asiri Kodan Iman.


Ya girgiza kai batare da damuwa ba yace mata.

"To ya kike so ayi yanzu Inna fahimce ki bakki san koman Gidanshi ko?"

Haushin yadda ya nuna mata Ko in kula akan maganarta taji dan haka ta ƙi ce masa Komai shima da yake yana cikin damuwa ne yasa Yay mata banza yaja Motar ya Nufi Komawa gida Domin ada yayi niyyar Yin nesa da ita ne har sai Ummah ta gane kuren ta sai dai yadda ta bashi Labarin Gidan Mijin nata shi baiga abin zafi ba kawai zai mayar da ita gidane ta koma ɗakinta shiya fi alkhairi.


ta cigaba da haƙuri ko wacce mace dama akwai kalar tata jarrabawar agidan aurenta.


Sunkuyar da kanta tayi tana dana sani akan Yadda ta rufewa Ahmad Matsalar Gidan Imran har suka ɗauki hanyar shiga unguwar su Bata kuma cewa komai ba.

*******

Hayaniyyar mutane da surutu acikin masallaci shine ya Cigaba da tashi har zuwa Lokacin da wata haɗaɗɗiyar baƙar Mota tai Parking a bakin masallacin wani dattijon Mutum mai nagarta fari tas ya Fito daga Motar ya shigo Cikin masallacin Lokacin jama'a sun soma watsewa saura ya rage Alhaji Kawu baffa da Liman.


Sallamar dattijon ita ta sanya Alhaji ɗagowa Bayan dogon Tunani da mamakin daya shiga Tun bayan ɗaura auren ɗan nashi.


"Kuyi haƙuri sai Yanzu na shigo can ma jama'a sunyi yawa ne dafatan kun aiwatar da abun da na sanya ku?"


Cewar dattijon yana kallon Baffa Ƙanin alhaji.

Baffa ya damƙo alawa da Goro ya miƙa ma dattijon tare da cewa.

"In sha Allah, Tuni Mun aiwatar ai tunda naga saƙon ka ta cikin akwatun Shigowar saƙon wayata kawai sai na raɗama kawu shi kuma ya raɗama Liman Muka zartar da Hukuncin naka kamar yadda ka Umarta"

Dattijon yayi dariya Irin tasu ta manya yana cigaba da cewa.


"Idan ban da abin idiris kai zaka bi maganar yara ne kana namiji Dan yarinya ta kawo Mutum tace tana so an duba nagartar shi Anga ya dace a aure shi kawai dan shirme da hauka ta dawo tace bata so kai kuma kabi ka yarda harda shaidawa mahaifin yaro dan Rashin kirki kuma ka rasa ranar da zaka sanar sai ranar ɗaurin aure haba sam wannan ba daidai bane wannan tasa nace ni a matsayina na yayan shi da Muke uwa ɗaya Uba ɗaya Kuma Nine waliyin zainab Na turo Maka saƙo da cewa Ku wakilta ɗayanku ya zama madadina kafin na ƙaraso ku ɗaura auren batare da Kun bari hatta shi mahaifin yaron yasan da zainab Ɗin za'a ɗaura ba Gudun kada ya hana dama ai ni kuka sani waya amshi Kuɗin aurenta bani ba wa kuka sani akan auren ai nine sabida haka Zainab matar Amadu ce halak malak kota ƙi ko taso In yaso in taje gidansa ta kashe kan nata sakaran banza Dan tsabar so kuna ji kuna gani ku tafka kuskure"

Dattijon ya faɗa yana Tauna jan goron da baffa ya bashi.


Kafin baffa ya Dubi Alhaji da har yanzu bai gama dawowa daidai ba sabida mamaki yace masa.


"Yaya Lokacin da ka ɗauki wayar Mahaifin ita zainab Ɗin Nima Lokacin shi wannan yayan mahaifin nata ya turo Min da saƙo akan Da Allah Mu sami mutum Guda ya zama waliyin zainab daga ɓangaran mu Idan yaso Mu ɗaura auren kada Mu fasa dan son zuciyar mahaifinta da ita kanta Ni kuma ganin hakan ba haram bane Tunda hatta kana wata ƙasar ma ana iya ɗaura maka aure Muddin da shaidu Ko in kaje wani garin ka sami matar aure kana iya wakilta wani a matsayin waliyinka ya karɓa maka auren shine yasa Ni na zama waliyin Ahmad dama da sadakin sa a hannuna kai Kuma ka zama waliyin zainab shaidu suka shaida Muka ɗaura Musu aure abisa Yarda da amincewar shaƙiƙinta yaya ga mahaifinta wanda dama Tun asali da mukaje Neman auren ta Gidansa Mahaifin zainab ya tura mu shi muka sani a matsayin waliyinta Kuma shiya wakilta mu abin da yasa Kaji Liman yace anfsa zuwa can za'a ɗaura da ƴar uwarsa Duk dan Mu ɓatar da tunanin kane Gudun zaka iya cewa a haƙuran kawai a fasa Ɗin kamar yadda mahaifinta yace maka wannan tasa Lokacin da Liman zai shaila ya faɗi haka amman da aka zo ɗaura aure Kasan da zainab dai aka ɗaura masa"


Baffa ya kai maganar yana miƙawa Yayan mahaifin Zainab sadakin Zainab Ɗin.


Washe baki dattijon yayi tare da zira Kuɗin Cikin aljihun Rigar shi yana mai cewa.

"Nafa Gode muku ni daman ban san duk iya shegen da suka shirya ba sai da naje Gidan yau yake gayan cewar Sun fasa bawa zainab Amadu Nai masa bakam har ya gama surutansa na son zuciya Agabansa nayo maka Massage tunda dama Ina da Numberka Gudun kada ma Nai Lattin zuwa nan a watse shine yasa nace Ku ɗaura danna san kafewar Idi yanzu ma Sai nai da gaske zai amshi sadakin ƴar Amman Ku bani kwana Biyu in sha Allah zata tare a ɗakinta"


Alhaji yabi dattijon da kallo wanda da wuya a sami Mutum jajurtacce Irinsa Sai kawai tunanin Amatullah ya faɗo masa suma mai yasa Basu tsaya mata Irin haka ba, wannan ma ya ishe su ishara uban ƴar yaƙi Aminta da aurenta itama.ƴar haka amman yayan mahaifinta yayi dubara har aka ɗaura auren dan kawai ya hango mata alkairi a auren nata da Ahmad Ɗin wanda daga ita har mahaifinta suka gaza gano hakan.

Sun fahimci juna sosai bayan gama tattaunawa suka Yiwa ma'auratan addu'a da fatan zaman lafiya mai ɗorewa sannan Suka raka yayan mahaifin Zainab Alhaji Iliya mai kwano Mota Suma suka yi Cikin Gida.


Lokacin da Alhaji Ilya yaje Gidan ƙaninsa ba wata shakka ya fito masa da sadakin zainab wanda a ɗayan Biyu dama yaje masa kowa ya amince ko yace babu shi babu shi muddin bai yarda ba.

A mamakin Alhaji Ilya sai Alhaji idi ya fashe da kuka yana cewa.

"Yaya samun ɗan uwa kamar ka akwai wuya wallahi Nima na kasa komai Sabida yadda nake takaicin zainab ta rasa nagartaccen Miji ɗan mafuta ashe kai kana can ma kana mana ƙoƙari yaya koda ba'a ɗaura aurenta acan bama wallahi Ka kawo shi nan bazance komai ba domin ka isa kai hakanne daga ni har Abin da na haifa bamu isa Mun maka Musu akan Hukuncin kaba Yaya Bani da uwa da Uba a yanzu Kai kaɗai ka rage Min a rayuwata, dama Tun Jiya na kasa Nutsuwa to ɗan yau ne ka haife shi amman baka haifi halin shiba, Wallahi yanzu har Kunyar mahaifin yaron ta kamani"

Alhaji Ilya yayi Murmushi tare da Jin daɗin Yadda Ƙanin nashi ya amshi maganar shi batare da Musu ba.


"Kira min zainabun da mahaifiyarta"

Cewar Alhaji Cikin bada Umarni.

Da sauri Alhaji idiris ya fita zuwa Cikin Gidan shi wanda ya cika da ƴan uwa ana ta hidima domin har zuwa Lokacin basu fasa Zancen fasa auren Zainab Ɗin ba.


Ɗakin Matar shi Hajiya Zahra ya shiga ya tarar da ita ta zabga tagumi daga gani abin duniya ne yayi mata yawa.

Ya tsaya akanta ya dube ta da kyau kafin yace mata.

"Kizo babban falona ki zo da zainab yanzu"

Hajiya zahra ta Share hawayen data ke Ɓoyewa wanda Kuka take tun daran Jiya ta riga ta narka Kuɗinta wajan Siyayyar aure tare da gayyatar dangi da Ƙawayenta tama kasa Tunkarar Kowa da batun cewar zainab ta fasa auren da za'a mata Haka tabi Umarnin Mijinta wajan zuwa Ɗakin Zainab ɗin.


Bayan Fitar Dady daga gaya mata saƙon.

Alhaji Ilya.

Ta shiga ɗakin Ta tarar da Zainab Duk ta Cure Jikinta Cikin Bargo Babu abin da take sai Kuka sai yanzu taji wutar Son Ahmad Da kishin sa sun kamata Sosai da gyar take Numfashi.


Da sauri Hajiya ta ƙarasa Kan gadon ta Janyota Jikinta tana ce mata.

"Subuhanallahi Zainab kashe kanki zakiyi ina aure ne an fasa Shi dan Allah Ki kwantar da hankalinki babu mai Miki auren Dole duk son da Mukewa Ahmad Mun haƙura tunda bakya son shi"

Kuka ne mai ƙarfi ya kuma kama zainab ta Rungume Hajiya tana cewa.

"Hajiya Ni sai yanzu ma na kuma Jin Ina son Ahmad Please na janye batun fasa auren zan aure shi a haka Tawa ƙaddarar Kenan Son wanda baya ta tawa In da yana sona baze share ni ba amman Jiba ko waya bai Min ba"

Ta faɗi Muryarta a dashe.


Hajiya ta shafa kanta tausayin ta na narka zuciyarta kafin tace.

"Share hawayen ki ƴar dady taso Muje Yayan mahaifinki na neman mu kada Mu jima yayi faɗa"

Haka Zainab ta wanko fuskarta bayan ta saka hijabi tabi bayan Hajiya Duk inda suka ratsa Dangi na buɗa suna tsokanarta babban falon Dady suka Shiga gaban zainab sai faɗuwa yake haka suka zauna Sosai Alhaji Ilya yayi mata faɗa tas ya ƙara da cewa.

"Idan Kuma Kika Bijire to babu ruwana ta yuwu wannan ce damar Ki ta ƙarshe shekara kusan talatin da hauri Kina zaune ba aure wace ni'ima ce Allah bai Miki ba? ya baki rai da lafiya ya raya ki cikin mahaifa masu Kuɗi masu son ki da ƙaunarki Kina aikin gwamnati kina da Mota To Danya jarabce ki da Namiji Miskili shine duk zaki ɗaga hankali kika san halaƙar shi da yarinyar ta yuwu ma Ko Ƴar uwar shice ba yabon Kai ba Nina nasan Amadu ba mazinaci bane kada Ki kuma faɗin wannan kalmar a yanzu don kada Ki Ɓata auren ku da zargi dan haramunne"

A lokacin Kuka Zainab take tana yabawa Baba Ilya na yadda ya jaddada martabar Zumunci Murya a dashe take masa Godiya Ita ko Hajiya bakinta yaƙi Rufuwa Sai Murna take tana yabawa mazan ƙwarai Waɗanda suke tsayawa akan Zumunci Domin Allah tabbas bada ban Baba Ilya ba da tuni anfsa auren zainab.


Sai da Dady ya raka Baba Ilya har mota sukai sallama ya tafi sannan Ya koma yana sanar da abokan sa cewar an ɗaura aure acan masallacin Unguwar su angon Haka yayta waya a wannan wunin Daga Cikin Gida Kuwa shiri yaci uban na da don Hajiya ta tura ƴan uwanta can Gidan su Ahmad dan a basu makullin Gida nan da anjima zasu tafi jere sannan akwai Dinner Anjima da daddare Gobe Kuma zatai wuni sai a miƙa amarya ɗakinta.


Wata Irin Nutsuwa Zainab taji Tun lokacin da Baba Ilya ya sanar da Ita auren ta da Masoyinta Ahmad tana fatan wannan aure ya ɗauru har Su Mutu babu rabuwa tana fatan ita kaɗai zatai rayuwa agidanta babu Kishiya Haka Ta tara ƙawayenta a ɗakinta ana ta Hira ga mai Dilka tana Faman gyara mata Jikinta.


****

Koda wasa su Alhaji Basu sanar da matansu yadda ta kaya da Batun auren Ahmad a masallaci ba kasancewar maza daman basu Fiye faɗin maganganu marasa daɗi ba Kowa yaja bakin sa yayi Shuru Haka anan Gidan su Ahmad aka cigaba da sabgar Biki wanda Tuni Gida ya cika da dangi Kowa sabgar gaban shi yake Idan ka cire Maman Ameerah data Fice Tun safe tai ƙaryar Yayarta dai Jikin nata ne yayi zafi.

**********************

Da sauri Take Ƙoƙarin Buɗe Murfin Motar dan ta fita Lokacin dayayi parking a bakin Ƙofar Gidansu wanda ya cika da jama'ar Biki wasu tabarma ma suka Shinfiɗa a saman dakali suna shan Iska.


"Amatuhhh"

Ya kira sunanta a kasalance...........

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850**Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.