Bakon Lamari 16


 *BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *16*


Cikin nutsuwa ya tsugunna a gaban Gadon irin Yadda Ƴan wasan ƙwallon Ƙafa suke Tsugunnon su.

Ya saka hannu a saman Bargon data Rufe jikinta dashi Yaja shi kaɗan da sauri Kuma ya saki yana mai yarfe Hannun shi.

A hankali Cikin Sautin Muryar shi mai Amoh! yake ce mata.

"Amatuh! Amatuh!! Amatuhh!!!"

Can ƙasan Maƙoshi ya furta Kiran Sunan nata tamkar wanda Ke yi mata raɗa.


Cikin Baccin azabar daya ɗauketa Taji sautin Muryar shi yana Kiran Sunanta.

A hankali take Buɗe idanunta Waɗan da suka Kumbura suka tasa Sukai wani irin Jajir, Ta yaye Bargon dake Jikinta agarin ta Miƙe ta zauna ta zamo da Iman Da wani irin zafin Nama ya tare ta yana Ɗago idanunsa ya zuba mata yana mai kallonta wanda yake Nuni da kallo ne irin na gargadi.

Tayi ƙasa da kanta tana mai ƙara jan Bargon ta rufe rabin Jikinta dashi.


Ya ɗora Iman akan Cinyar shi ya saka yatsan shi guda yana mata wasa nan da nan ta soma ɗaga ƙafa tana cillawa tana dariya.

Shima Biye mata yayi yana dariyar kamar ba shiba.

Ta ƙasan Ido ta saci kallon shi tana mamakin son da yakewa Ɗiyar tata.


"Meke damun ki yanzu?"

Ya jefa mata tambayar batare daya dubi saitin taba.

"Bana jin komai"

Ta bashi amsa Muryarta a dashe.


"Wai kukan ne har yau baki daina ba? lallai kin sami aiki"

Ya faɗi maganar batare daya kalleta ba.

Hawaye ta share wani bin kamar mai Juju idan yana jefa mata magana a fakaice kamar baƙar magana yake gaya mata wani Bin kuma ya rarrasheta ta rasa wani Irin mutum ne shi wani irin murɗaɗɗan Hali gare shi.


"Kin zo kin kwanta ke baki tashi ba Bare ki Break ko Yarinyar nan ta sami Abincin ta"

Ya faɗi maganar kai tsaye.

Kunya ce ta kama Amatullah wadda ta Kuma Jan jikinta ta maƙure kamar mai Jin bacci.


Shuru ne ya biyo baya a ɗakin Kafin ya Miƙe tsaye da Iman a kafaɗar shi.

"Nifa bana son gardama Ba zaki tashi ba"

Ya faɗi maganar a tsawace.

Da sauri ta yaye Bargon ta dira ƙafafunta a ƙasan Gado.

Yabi Santala santalan fararen ƙafafun nata da kallo yana rintse Idanunshi sabida shatin dukan duk ya fita ruɗu ruɗu a ƙafafun nata.


Ya fita tsayi sosai hakan yasa ta koma ƴar Firit a gaban shi yayi gaba tabi bayan shi zuwa falon Mama.


Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun falon yana kiran Surayyah Da sauri tazo ta zube agabanshi Umarni ya bata akan ta haɗo ma Amatullah Tea da dankali sannan ya mayar da kallon shi wajan Amatullah datai tsaye akan shi batare data zauna ba.


"Kina tsaye min akai na kamar Dogari malama nema wurin zama"

Jikinta a matiƙar mace ta zauna  A daidai saitin Ƙafafun shi Tana kare fuskarta da hannunta.


Ta kula sai kallonta yake sabida yadda taji Idanunshi yana yawo a jikinta har surayya ta kawo mata kayan karin bai ɗauke Idanunshi akanta ba.


Haka taja plate Ɗin dankalin tana ci tana haɗawa da shayin ba don tana soba dan cikinta ya tushe sai dan Gudun faɗan shi.


Ta ci kaɗan ta ture sauran gefe.


"Ki ɗauka kici duka Baze yuwu kina zama da yunwa ba"

Tai raurau da idanunta yaushe rabon da wani ya tirsasa ta taci abinci to wama ya damu da jin yunwar tata ma.

"Yaya da gaske na ƙoshi"

Ta shi yayi Tsaye Ya fice daga falon.

"Ki saman a mota"

Ta tsinci Muryarshi daga bakin falon.


Ta fahimci yana da saurin fusata abu kaɗan ne yake saka shi yayi fushi ta Lura baya son gardama tana ɗaya daga cikin abin da ke sanya shi yay watsi da Mutum.


Jikinta a mace ta ɗauki Kayan karin takai Kicin sannan tabi bayan shi tunda da mayafi ajikinta.


Harya fitar da Motar ƙofar Gida ya shiga ya kunna Jikinta har rawa yake Wajan wucewa dan bata son wani acikin ƴan Gidansu ya ganta.


Ta Tsaya a bakin Motar batare data shiga ba.


Yay mata banza sai ma horn daya danna wanda ya cika Gurin wanda yake mata nuni dashi baze iya mata magana ba sai dai ita ta shiga dan kanta.


Haka ta buɗe Gidan gaba kusa da driver ta shiga ta zauna.


A zafafe yaja motar yana sheƙa gudu a saman titi wanda yake mata nuni da ta mugun ɓata mishi rai.


"Dan Allah yaya kayi haƙuri kada ka zubar damu"

Ta faɗi kamar zatai kuka!

Can bakin wani  Maryam collection ya dataka ya fita Mintina kaɗan ya dawo hannun shi da manyan ledoji.


Ya zuba a bayan motar yaja suka Nufi Hanyar Gida a bakin gate ya tsaya yana mai ce mata.

"Ki ɗauki kayan can Kije ki dinga wanka kina sanyawa Fitar min a mota"

Sai ta kasa Fita kuma ta kasa yi masa godiya.

Sai ta soma Kuka tana haɗa hannaye tana share hawayenta.


Sunkuyar da kanshi yayi ƙasa ya rasa Yaya zaiwa yarinyar nan so take ta haɗa mai zafi da wannan Koke koken nata.

"To yanzu ya kike so ayi miki? ko kinfi son komawa wajan Ummah ko Kina son a mayar da auren naki ne?"

Duka ya jefa mata tambayoyin masu rikita da zuciya.


Shima kenan ya ɗauka Auren tane ya Mutu kamar yadda kowa agidan ya ɗauka auren nata ne ya Mutu.


"Ni fa naga kana fushi dani"

Bakinta ya faɗi maganar wadda da sauri Kuma tai shuru tana istigifari da auren wani akanta take gayawa wani ƙaton maganar nuna kulawa, Koda yake ya zama dole ta damu da damuwar shi kamar yadda ya nuna damuwar shi gareta.


"Amtuh yaya zan miki Kukan ki yayi yawa kowa da kika gani akwai tashi kalar jarrabawar Addu'a ita ce mafita Dole kiga na damu ina ganin kamar ina takura ki babu yadda zance ga abu nan take Kiyi shi nace ki sha tea da yawa Kinƙi ni wannan yarinyar kawai nake tausayawa Tunda kika hau mota kike kuka sai kace ance zan cinye kine"


Ya faɗi yana Jan huci mai zafi.

"Kayi haƙuri na dena"

Ta faɗi a hankali.

Ya bita da kallon tausayawa dan baya so ko Ɗaga murya ya dinga yi mata yarinyar abar tausayi ce Sam baya jin ɗigon riƙonta aran shi saima tsananin tausayin ta wanda ya hanashi sukuni.


Ya miƙo mata Iman wadda tai bacci sannan ya fita ya fito mata da kayan da kanshi ya kai mata har bakin sashin Mama sannan ya koma mota yaja ya nufi barrack Ɗin da aka turo su wanda yau suke son haɗa Team ɗinsu gobe da sassafe zasu wuce.


Da sauri ta kwashe kayan ta nufi falon mama tana masa fatan alheri acikin zuciyarta.


Koda ta nuna wa mama kayan Waɗanda suke dogayen riguna ne ɗinkakku da manyan hijabai mama tai Mata Murna tai masa fatan alheri.


Haka suka wuni suna hira da mama bayan tai wanka ta sauya kaya su Surayya kuwa Iman tana hannun su.


Tsayin sati Guda tai a sashin mama Kuma zamansu sai son barka domin babu takura Mama na janta sosai ajiki Kuma ta dage tana gyara mata Jikinta Domin mama kewa Iman wanka Tuni ma ta dawo ɗakin mama da kwana Sai a yanzu take yaba halin Girma na mama da karamcin ta.


Tun daga ranar da suka fitan nan  kuma bata sake ganin Ahmad ba sai ji tai wai ashe ya Tafi wajan aikin da aka tura shi sai dai Kusan duk dare yana kiran mama su gaisa bai taɓa cewa a bata ba itama bata taɓa Gigin cewa a bata su gaisa ba.


Ranar Litinin aka kai Lefen Ahmad wanda ranar ƴaƴan mama dake ɗaki suka cika gidan da yaransu Sai janta suke har Aysha mai bin Ahmad nacewa tazo suje gidanta dake Hotoro ta taya ta zama mama tace Ku rabani da faɗan Yayanku Kullum sai ya tambayen ina ajiyar sa babu ruwana.


Sai lokacin tasan ashe yana tambayarta tsabar miskilanci ne ya hana ya na cewa a bata wayar.


Su baffa sun kai lefe lafiya an saka ranar Biki asabar mai zuwa wadda itace ranar ɗaurin aure sun dawo da shatara ta arziƙin tukwici.

Sashin mama har dare dangi na shigowa wanda daga ciki harda Anty wadda rabon da ta shigo wajan mama tun ranar da Amatullah ta dawo koda tazo Ɗinma a tsaye tai wa mama Fatan alheri ta juya mama bata kawo komai aranta ba tunda kowa uzirin gabanshi ya ishe shi haka ta cigaba da amsar Baƙi ƴan taya Murnar tasowar auren Yaya Ahmad.


Washe gari da sassafe Anty ta nufi Sashin Ummah cikin Kirsa da Munafurci a ɗage Ummah ta watsa mata kallon banza dama Umma cike take da kowa agidan.

"Hadiza dama nazo Miki da magana ne akan yarinyar ki yanzu Kina ji kina kallo Binta ta ɗauke miki ita tana can tana mata bauta Ke ko oho? wato yanzu Dai Binta so take ta mamaye gidan nan ta juya kowa"

Ummah ta ɗagawa anty hannu.

"Ke Lami dakata bana son munafurci ba bakin ku ɗaya da Bintar ba shine zaki zagayo nan kina gayan maganar banza ko kin zata ban san kowa ce bace Ke wuce ki bani gu kona Tona miki asiri"

Zage zagen Borin kunya anty tahau yi kafin ta kama hanya ta fita burinta bai cika ba dan taso ta haɗa gagarumar Masifa ne a tsakanin Ummah da Mamah.

Ita kuwa Ummah abin da yasa batai wa Anty wata maganar arziƙi ba sabida sun gama magana da Imran Ne wanda ta shawo kansa da ƙyar Yace mata ranar Juma'a zai shigo kano asabar Idan ya huta zai Shigo wajan safiya ya ɗauki matar shi wannan tasa ta zubawa su Mama ido bata wani ɗaga hankalinta ba dama tashin hankalinta Akan Imran ne to kuma ya dawo dan bada ban kayan abincin da Ahmad ya kawo mata ba da Tuni ta shiga tasku.


Ko wani ɓangare shirin Biki ake Sosai domin tuni dangin mama na nesa dana kusa da dangin su Alhaji sun soma cika gidan.

Haka zalika daga Ɓangaren Amarya zainab suma shirinsu har yafi  nasu mama.

Daga ɓangaren Anty ma Kullum sai ta fita sun ɗauki hanyar Ɓata ita da Yayah wanda Har ta rame sabida jarabar rashin Hutu.

Sun sami nasarar zuwa wajan wani Boka wanda ya basu tabbacin duk wani aiki da zasu yi akan Ahmad basu da nasara sai dai akan Ita amaryar tashi wadda zasu haɗata da Jinnun da zai hau kanta ta Tubure tace ta fasa auren Ahmad Ɗin da wannan Murnar su anty suka dawo Gida suna Zuba idanun ganin yadda auren Ahmad zai Juye ya koma kan Ameerah.

  

Abin mamaki itama Ameerah tun da Amatullah ta koma sashin mama shikenan ta daina zuwa dan rabonta da Ameerah harta manta.


Yau ta kama Alhamis wanda su Amatullah suka je Kitso daga nan suka wuce Gidan Ƙunshi ita da Naja da Surayyah tun safe mama take kiran layin naja bata samu ba har akai magariba Lokacin ne suka shigo Gida sai dai Sun bar Amatu acan Tace zata tawo komai dare dan bata cin lalle da wuri mama tai faɗan barin tan da sukai har ta Ce sai sun koma sun tawo da ita.


Saukar Ahmad kenan agidan Yayi shiri Cikin Royal Blue Boyal mai yankan sugari ya ɗora Hula kalar Ɗinkin Jikinsa yayi masifar Kyau sai baza ƙamshi yake Zeje Gidansu Zainab ne shida wasu Abokan shi wanda zasu ɗauki amarya su wuce wajan Kamun da ake yau wanda Zainab ɗin ta adda ba masa da waya akan dan Allah yazo badan yaso ba ya sauka ayau wanda ko mama bata sani ba sai da ya shigo yanzun.


Ya duba agogon hannun shi.


"Mama sai mun dawo akwai abokai na dake Jirana a waje"

Mama tai masa fatan alheri har yakai Bakin Ƙofar fita ya dawo kamar yayi mantuwa.

"Ina Amatu?"

Kamar mama na jira ta hau gaya masa ai su naja sun baro ta gidan lalle.

"What lallen me kuma? dan basu da hankali zasu bar ta da yarinya a wani waje"

Ya shiga Kiran surayya wadda tana zuwa yahau yi mata faɗa kamar zai daketa Sannan yace ta bashi numbern mai lallen.

Jiki na rawa ta karanto masa ko mama baiwa magana ba ya fita wajan motar shi ya shiga yabar Layin da wani irin gudu batare daya bi takan abokan shi dake tsaye zaman Jiran shi ba.


Yana tafe yana kiran Numbern mai lallen wadda tai masa kwatance nan Rafin ɗan nana ne Haka ya dinga bin kwatancen har ya Samu ya ƙarasa ƙofar Gidan.

"Ki ce ma Amatu ta fito ko ba a gama lallan ba"

Daga haka ya katse kiran.


Mai lallan ta dubi Amatullah tana  mai sakin dariya.

"Au ashe baban iman keta min waya tun ɗazu to yana ƙofar Gida"

Da yake suna ta hira ne da Amatullah harta gaya mata sunan Iman ɗin.

Duk wayar da Ahmad kewa mai lallan ta ɗauka ko matarsa zai kawo dan suna haka da mutane sai da yazo yace mata ta kira masa Amatu.


Jikin Amatullah yay sanyi ko kamawa na ƙafar bai yi ba ta cire ta Goya Iman ta fita waje tana raba idanun waye yazo ɗaukarta ita dai tasan IMRAN bai san tazo lalle ba to ko mama ce ta turo yaya kamal ya ɗauketa.


Da haka ta ƙarasa Ƙofar gidan ta tsaya tana waigen inda zata hangi wanda yazo ɗaukar nata..............*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.