Bakon Lamari 15


                   *15*


Da ƙyar Amatullah take ɗaga ƙafafunta waɗanda suke mata tsami da zugi, Tana Bin bayan su mama kamar wadda ƙwai ya fashe mata aciki.

Naja'atu ce ta amshi Iman cike da tausaya wa take cewa.

"Kiyi sauri Amatullah mu wuce part Ɗinmu in sha Allah ba zaki Kuma zaman part ɗin kuba"

Haka suka jera zuwa part ɗin Mama.

A falo mama ta zauna ta rafka tagumi Tunda take Bata taɓa ji ko ganin uwa irin Ummah ba mace mai son zuciya da son abin duniyar tsiya ta mayar da ƴar Cikinta kamar ba ƴarta ba sabida ƙwaɗayin Abin duniya.


Cikin mutuwar jiki Amatullah ta zauna a ƙasan carpet tana mai Cusa kanta a tsakanin Cinyoyinta tana cigaba da kuka abin tausayi sai Iman ma ta soma kukan wadda take hannun Naja'atu haka ta miƙa mata Iman ɗin ta rugumeta suka cigaba da kukan nasu.


Surayyah Naja'atu Mama Sai da sukai hawayen tausayawa Amatullah.


Cikin tattausan kalami tare da kwantar da hankali mama tace mata.

"Kiyi haƙuri Amatuh haƙiƙa Allah Nasa yake jarrabta Ta yiwu akwai abin da ya ɓoye a rayuwarki Na ɗaukaka In sha Allah wahalarki tana gab da yankewa"

A hankali ta share hawayenta ta ɗago kanta ta zubawa Mama idanu kafin tace.


"Anya mama kuwa zan fita daga cikin wannan bala'i Nagama na gidan Miji na dawo Gida ma ban tsira ba Mama babu wanda ya tambayeni dalilin zuwana gida bare na sami gatan da za'a ɗaukar min ƴanci agidan Imran Ummah data fi kowa kusanci dani tana Guduna tana ƙyamata wallahi ko Iman bata taɓa ɗauka ba Mama mai nayi ne da kowa yake ƙina ji nake kamar zuciyata tai Bindiga na mutu na huta Cikin kwana Biyun nan naji gwara Mutuwa ta da rayuwa ta"


Ta faɗa tana rushewa da wani Irin Kuka mai tsuma Zuciya.


Alhaji dake Namiji ne da sauri ya miƙe ya nufi ɗaki Mama kuka Naja kuka surayyah kam Kuka harda majina sabida tausayin Amatullah duk dauriyar mama da yakana da tawakkali wallahi kasa jure danne tausayin Amatullah tayi kuka take sosai na halin da yarinya ƙarama ta shiga acikin rayuwarta duka kuma sanadin gurɓatacciyar uwa wato shiyasa akace Idan kai dacen uwa tagari ka gama dace aduniya da lahira domin uwa itace garkuwan ɗanta.


Falon ya ɗauki ɗif babu wanda ya iya magana sai tashin Kukan su dana Iman daya cika falon ta danna mata Nonon ma taƙi karɓa Sabida babu ruwa sai fata sabida rashin samun wadataccen abinci da bata yi.


Mama ta dube ta tana mai janyota Jikinta.


"Kiyi haƙuri Amatu! dukan mu ba dan bama sonki muka zuba Miki idanu ba a,a kowa yana gudun zubewar Mutunci ne wajan mahaifiyar ki da bata ganin Ƙimar kowa akan auren ki, Kada ki manta tace su Alhaji Ba sune suka haifeki ba dan haka kada su ƙara saka mata baki akan sabgar auren ki, To kinga duk mai son Jan girman sa baze kai kanshi Inda za'a taka shi ba"


Mama taja fasali kana ta ɗora.

"Amman kowa acikinmu yana jimanta halin da kike Ciki ace Da ɗanyen Jego Miji ya koroki gida amman har yau ba'aji komai daga gare shiba Dan Allah Amtuh Ki kwantar da hankalin ki Ni zan riƙe ki kamar yadda zan Riƙe su Naja ki zaman ki anan Inda hali ma ki koma makarantar Ki yanzu tashi Kije ku kwanta dare yayi Bana son ki tashi hankalin ki"


Miƙewa tai bakinta yayi mata nauyi ta furta wa Mama cewar Imran bai sake taba cewa yayi ta dawo Gida Haka ta bi su Naja sukai Cikin ɗakin baccin su.


A gadon Surayyah ta kwanta su kuma suka Kwanta a gadon naja taja Iman jikinta tana shafa kanta Kowa yay bacci a ɗakin amman ban da Amatullah data Rintse idanu Hoton Hussaini ƙaninta take kallo yana dukanta Ƙaninta fa Hussaini ya manta Hatta Kayansu na makaranta itake wanke musu ada takan Iya haƙura da abinci a makaranta ta basu suci nata, ada sanda tana amarya idan tazo haka zata basu kuɗi suna nan nan da ita amman yau sabida Bata da shi kuma Allah ya ɗora mata ƙaddarar dawowa gida Shine takai da har ya ɗauki Waya ya naɗa yana dukanta kuma abin takaicin Abisa umarnin mahaifiyarta.


Yawan Kukan data yi shine ya haifar mata da zazzafan zazzaɓi ga Jikinta duka ya fashe abinka da farar fata duk Jikinta yayi jajir da ƙyar baccin azaba yayi gaba da ita.

***********************


Sai ƙarfe Sha biyun dare Anty ta sauka a ƙofar Gida Ta sallami mai napep sannan ta tura Gate ta shiga Cikin Gidan kai tsaye sashinsu ta nufa ta Buɗe Ƙofa. 

Ta shiga ciki Baffa na kaiwa da Komowa a tsakar Gidan ya ɗago ya dubi Anty wadda tai sak da ganin shi dan batayi zato ba.

"Lami daga ina kike?"

Ya faɗi maganar babu alamun wasa.

Ta shiga sosa kai tare da cewa.

"Lah Ameerah bata gaya maka ba? Yaya ce bata da lafiya shine aka Mun kiran afujajan to kasan dole na tafi Tunda babu ran Hajiya yanzu yaya ce uwar tamu nace wa Ameerah ta gaya maka inaga ta manta amman kai haƙuri"

Ta faɗa da sauri tana wuce wa cikin Ɗakinta.


Baffa ya girgiza kai tare da shiga ɗakinsa.


Anty na shiga ɗaki Ameerah ta miƙe zurum tana faman sosa kai.

"Au baki bacci ba? na ɗauka ai duka kunyi bacci ina can bakin rai bakin fama ashe auren Ahmad sati mai zuwa shida waccan ƴar mai kuɗin sai Ɗazu da muka je wajan Malam Yaya tasa ya Binciko mana"


Anty ta faɗa tana aje Wata baƙar Leda a ƙasa.

"Hmm Anty ina zanyi bacci ina tunanin ki Tun safe Kika fita baki dawo ba sai yanzu"

A masifance ta ɗago tana ce mata.

"Akan uban wa na fita in ba Akanki ba maza ɗauki waccan baƙar ledar Kije Ki wanka da ruwan maganin Cikinta tabbas kamar Kin shiga Gidan Ahmad Ne kin gama"

Anty ta faɗa tana mai yaƙinin cewa kamar Ameerah ta shiga Gidan Ahmad Ne ta gama kamar yadda Malaminsu ya basu tabbaci.


Jikin Ameerah yana rawa abin ka da wadda take Jiran Ƙiris akan soyayyar Ahmad data rufe mata idanu haka ta ɗauki Ledar ta shige Bayi Mintuna kaɗan ta fito tana cewa.

"Anty na gama ai anty yau munga tashin hankali Yaya fa ɗazu ya kusa kisan kai Akan Hussaini ya doki Amatullah shine ya rufe shi da duka baji ba gani"

Anty taja tsaki tana ƙara Jin tsanar Amatullah aranta kafin tace.


"Dama yabar hussainin ya karya shegiyar banza Nifa na tsani wannan yarinya da idanu kamar Gurjiya"


Ameerah bata cewa Anty Komai ba tayi saman gado ta kwanta tana jin yadda Jikinta ke mata ƙaiƙayi sai dai ta saka aranta indai buƙatarta zata Biya babu wani abu.

Haka itama Antyn tabi bayan Ameerah nan da nan bacci yayi awon gaba dasu.


***************


Ahmad ya rasa abin da ke masa daɗi a wannan dare haka ya kwana ya tashi da asubah ya zira jallabiya Brown colour ya nufi masallaci anan ya zauna har zuwa ƙarfe Shiddan safe sannan ya Miƙe Ya nufi Gida sai da yasha Coffee mai zafi a ɗakinsa sannan ya wuce Sashin Mamah.


Ya sameta a ɗaki a zaune tana lazumi Bayan sun gaisa shuru ya Biyo baya batare daya mata maganar Jiya ba itama bata masa ba.


Har zuwa Takwas Na safe suna tare a ɗakin Lokacin Naja'atu ta shigo Gyarawa Mama ɗaki.


Ta zube ta gaishe dashi.

Ya amsa mata a kame.

"Yaya Amatu ta tashi?"

Cewar Mama.


Sai Lokacin ma ya tuna ashe tana sashin Maman.

"A,a mama ta dai farka amman tana kwancen Naga kamar tana rawar ɗari zazzaɓi yana damunta"


Naja ta faɗi tana wucewa wajan wardrobe domin ta gyarawa mama kayan Ciki.


"Kai jama'a wannan yarinya tana ganin taskun rayuwa"

Mama ta faɗa cikin damuwar Jin zazzaɓin Amatullah Ɗin.


Kafin ta dubi Ahmad tana mai cewa.

"Ka daure kaje kaga Jikin nata mana ko asibiti za'a kaita?"

Ya shafa saman kanshi kamar Koda yaushe Tare da Miƙewa ya fita daga ɗakin Maman.

Kai tsaye Ɗakin daya san tana Ciki ya nufa ɗakin su Naja kenan ya saka hannu ya Murɗa handle Ɗin Ƙofar ya shiga cikin Ɗakin tare da mayar da Ƙofar ya rufe Ɗakin Babu kowa Sai ita kaɗai daya hango saman gado ta nannaɗe Jikinta Cikin Bargo wanda bama zaka tantance a ina ta Aje jaririyar tata ba tattaki yake a hankali har ya ƙarasa Gaban gadon da take kwancen..........*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.