Bakon Lamari 14


                  *14*


Cikin dakakkiyar Muryar shi mai cike da amo! ya furta.

"Daga Ina kike dan baki da Tunani shine zaki wani kwaye Cinya a waje kina tsallaka Titi bakya ko tunanin wani yaga Jikin ki a yadda kike?"

Ya faɗa yana mai zuba mata Girman Idanun sa ya kafe ta dasu yana jiran Amsarta.

Shuru tayi Bata iya bashi amsa ba Wanda hakan ya Kuma bawa cikin motar damar Yin tsit babu abin da ke tashi sai sautin wa'azin daya kunna acikin motar tashi sai Kuma ƙamshi da sanyin Ac.


Rintse idanunta tayi ta Kulle su gam tana sauke ƙaƙƙarfan Numfashi tana jin yadda idanunsa ke yawo a saman fuskarta.

Ba zata iya ba, bazata iya Jure wannan yanayin ba kallon sa gareta yana jefa zuciyarta Cikin wani yanayi wanda ya shuɗe ada!.

"Amatuhh!!"

Yaja sunan cikin wani yanayi mai wuyar a fasalta shi.

Hawaye ne mai zafi ya soma gangaro mata a saman fuskarta yana Jiƙa gaban rigarta.

Dama zata iya dama hakan ba haramun Bane data raɓu da jikin Yayah Ahmad a wannan Lokacin ko hakan zai zama garkuwa gareta Ko hakan zai saka taji salama acikin zuciyarta yaya zatai wadda tafi kowa kusanci gareta UWA! Ta juya mata baya ta mayar da ita abokiyar gabarta Akan Kuɗi!


Ta kama Ledar Abincin dake hannunta ta matse gam ta mayar da Jikinta waje ɗaya ta cure ta cigaba da zubar da hawaye mai zafi wanda zuwa wani Lokacin Kuka mai sauti ya soma fitowa daga gareta Kuka take mai ƙarfi wanda ya cika Ilahirin Motar.

Ahmad ya rintse idanunsa nan da nan Jijiyar dake kanshi ta Miƙe Ya fesar da zazzafan Huci Duk wasu makaman faɗan sa daya yi Niyyar Sauke mata akan Bar masa yarinyarta datai Jiya ta kwana yaji ya zubar dasu.


Yana da rauni matiƙa Ga Jin kukan Mace macen ma....

Ya kasa ƙarasa faɗin hakan a zuciyarsa.

A raunane ya juyo gareta rauni wanda ya jima baiji shi gare shiba.

"Meye na kukan Amatuh gaya min matsalolin ki Please kada ki Ɓoyen Komai Ki fitar da duk wani abu aranki Ni yayan kine Zan share dukkan hawayen Ki"

Ya faɗi hakan muryar shi can ƙasan maƙoshin sa yana danne zafi da raɗaɗin da yake Ji acikin zuciyar shi.


A hankali ta ɗago da idanunta dayay wani Mugun jaaa ya ƙara girma Fuskarta tai wani Irin kumburi ta tashi abin ka da farar fata.


Da sauri yay gefe da kanshi Don ganinta a haka zai iya saka shi cikin wani yanayi da Baya son yaji shi.


"Idan na gaya maka matsala ta mai zaka yi UMMAH  data fi kowa sona aduniya ta rufe idanunta akan Imran ta firfita shi akaina bani da wani sauran Jin daɗi yayah ina addu'ar Allah ya ɗauki rayuwata In mutu In shiga aljannah in huta"


Ta faɗa tana cigaba da kukan ta.

Ya bita da kallo Amatuh yarinya ce har yanzu bata gama sanin kan rayuwa ba to meye take fatan Mutuwa wadda ko bata Nema ba da Lokaci yayi zata tafi.


"Sai aka gaya miki Nima kamar ita nake? zan saurare ki in da shawara sai na baki"

Ya faɗa yana Janyo wayar shi da zainab keta kira ya katse Kiran ya kuma Zubawa Amatuh ido yana binta da kallo.

"Tun ina cikin matsala agidan nai maka waya amman sai kace Ni matar aure ce Kada na kuma kiran ka ay"

Ta faɗi tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.


Ya saki Murmushi kaɗan.

"Amatuh kinyi auren soyayyah da Mijinki Zaɓin kine fa keda mahaifiyar ki to mai zai sa na Shiga Hurumin abin da bai shafeni ba?"

Ya faɗi yana ɗage mata Girar shi guda.

Hawaye ne ya shiga zubo mata ta kafe shi da ido a wannan karon bata da ta cewa bakin ta yayi nauyi.


"Dama haka ne ya dace da masu kwaɗayi Irin ku! a wan can karon Kin manta irin rashin Kunyar da kika Dinga Yi akan shi zaɓin naki?"

A wannan karon ya fitar da maganar da tsananin Ɓacin ran daya ke Ƙoƙarin Ɓoye wa 

Hannunta ya hau rawa jikinta yahau rawa.

"Ina gudun ranar nadama Ina gudun abin Kunya Ina jin kunyar mutane masu daraja Musamman kai Yayah ka kasance Mutum nagartacce amman sai da nasan ya zuciyarka rawa dan girman zatin Allah Yayah kayi haƙuri Dukkan abin da yafa ru ba laifi na bane wallahi Ummah ce tai min barazanar tsinuwa A yanzu ma Dana dawo Ɗin babu wani canji hantara kyara wulaƙanci Daidai da ƙanne basu raga min ba kamar ba Jinin suba narasa wazan Tunkara akaf ahalina sabida kowa shakkar Cin Mutuncin Ummah yake na shiga yawo don na tsare Martabata  a kwana Biyu tak naji gwara rayuwar Gidan Imran akan wannan yawon da nake yi wallahi"

Ta ƙarashe maganar tana sakin wani marayan Kuka!


Sunkuyar da kanshi yayi a ƙasa Yaƙi ɗagowa hartai kukan mai isarta.

"Ba zan hanaki kuka ba Amatuhh ta yuwu idan kikai kukan zakiji salama cikin zuciyar ki rayuwarki tana Buƙatar tallafi tana buƙatar Jigo don in aka barki a haka tabbas akwai matsala naso na tausaya Miki sai dai tsananin dafin dake zuciyata ya tauye Dukkan wani tausayi acikin ta"

Ya faɗi hakan yana mai zuba mata Idanun sa dasu ka rine suka sauya kala nan take.


Ta ƙara komawa ƴar firit ta rame tai Duhu babu komai ajikinta sai girman idanunta wannan wani irin rayuwa ne yarinya ƙarama ta faɗa Cikin matsaloli masu yawa.


A hankali ta ɗora hannunta akan Mabuɗin Ƙofar Motar ta juyo ta dube shi sau ɗaya tak tare da Buɗe Murfin motar ta zira ƙafafun ta zata fita.


Da sauri ya damƙi Hannunta ya damƙa mata kuɗi masu yawan da bai san adadin suba ya kuma sakin Hannun nata da sauri.


Girgiza kai tayi tare da zube masa kuɗin a saman jikin sa ta buɗe Motar da saurin ta tafita batare data ɗauki shinkafar ta dake Cikin ledar ba.Ahmad ya shafo saman kanshi dake saisaye babu suma ko ɗaya Ya Lumshe idanunshi Zuciyarshi na rawa.

A hankali ya ƙureta da idanunshi harta ɓacewa Ganin shi.


Jikin sane yayi sanyi Lokacin daya kai Duba saman ledar data bari wani irin tausayi yarinyar ta bashi wanda ya zubar masa da dukkan wani zafi nata daya Ƙunsa.


Har Lokacin daya je gidan su Zainab bai dawo daidai ba yasha tambaya wajan Zainab akan meya ke damun shi haka ta saka shi agaba kamar zata masa Kuka sai da ya ware sannan ta saki Jikinta.

A daddafe yayi mata sallama duk ta dame shi akan zancen Event ɗin da za'ai abikinsu sabida ɗazu su Baffa sunzo wajan Dadyn ta an tsaida maganar auren su tunda su dama a shirye suke.


A wani super market ya tsaya yayi uwar siyayya wadda sai da taso tafi ƙarfin Boot ɗin motar shi yabiya Kuɗin siyayyar sannan ya Nufi Gida sai da ya tsaya a masallaci Yayi sallar Isha'i sannan ya wuce Gida a bakin Gate ya tsaya ya sami Yaran kawu ya basu umarni akan su kai kayan Ɓangaren su Amatuhh.


Lokacin da yaran suka Shiga Ɓangaren Su Amatullah na tsakar Gida hasken ƙwan nepa ya haska Gidan abin tausayi ita tana daga can Gefe tana bawa Iman Nono dan tun dawo warta gida Mama ta aiko mata da Iman tace ta bata Nono kada ɗaukar hakkin yayi yawa. Ummah da nana suna zaune a bakin Ƙofa nana na saman Cinyar Ummah tana zuba shagwaɓa.

Ummah sai ƙananun maganganu take faɗi tana cewa.

"Dan uban mutum daya kaso auren shi yunwar Cikin sa ma ta ishe shi gashi ga gidan nan ya zauna bani ɗaya yaywa asara ba"

Nana nata Sheƙa dariyar shaƙiyanci wanda sarai Amatullah tasan da ita suke Dan haka taja bakinta tai shuru Tana gudun tai magana tata tai zafi.


Sallamar yaran ce ta katsewa Ummah Maganarta bakinta a buɗe tana kallon sha tara ta arziƙin da suke ta shigowa dashi.


Bakinta yaƙi rufuwa duk zaton ta ma ko Imran ne sai dai ganin Ahmad a tsakar gidan ya sa ta koma ta zauna Jiki duk a mace dan yana mugun yi mata ƙwarjini.


Ya Rissuna yana gaishe da ita kafin ya leƙa ɗakin Baba ya duba shi kana ya fito ya Dubi ummah.


"Dan Allah Ummah kiɗan sassauta ma Amatuh bai dace daga Haihuwar taba tana fita waje neman abinci Ga kayan abinci nan duk wata za'a dinga kawo Muku amman Please ta zauna agida don Allah"

Ya faɗa Lokacin daya ƙarasa wajan Amatullah wadda tai saurin gyara rigarta tana mayar da Mamanta Cikin Riga.

Taɓe baki yayi yana ɗaga Iman sama Yana mata wasa.

Tashi tai sum sum tabar masa wajan sai da yayi mata wasa ya gaji sannan ya bawa nana ita shi kuma ya Nufi nasu ɓangaran bai sami damar Leƙawa wajan Mama ba Yayi shirin kwanciya.


Bayan nana ta miƙa mata Iman taja Yarinyarta Jikinta tana addu'ar kwanciya bacci don Baccine Cikin Idanunta sai dai me kamar da wasa taji saukar wayar wuta ajikinta kafin tai Yunƙuri ɗagawa taji Muryar Ummah tana cewa.


"Hussaini zane min mitsiyaciya wato yawo kike dani kina cewa na hanaki abinci? baƙar munafuka to wannan ma abincin daya kawo babu rabon ki Muddin kina son ganin farin ciki a rayuwarki ki koma gidan Mijinki dan nai masa waya na bashi haƙuri yace baya gari amman koda yaushe zaki iya ganin shi yazo tafiya dake"


Wani tsalle Amatullah tayi ta bangaje Hussaini ta rungume ƴarta ta fita Tsakar Gida da Gudu tana Ihu Abin mamaki Hussaini ya Biyota yana kuma Jibgarta dan tsabar jahilci ina kataɓa ganin ƙani yana zane yayar shi Baba yana ɗaki yana kuka yana cewa 

"Amatullah baiwar Allah ina ma ina da ƙafa da na fito na tare Miki"

Hanyar Ƙofar Gida ta Nufa agigice duk hankalinta ya bar Jikinta.


Cin karo tayi da Mutum agabanta wanda batai wata wataba ta faɗa saman sa tana Rungume shi Tana mai fashewa da marayan kuka!

Ahmad da tun soma Kukan Amatullah ya farka daga baccin da yake da sauri ya saka riga ya Fito zuwa sashin nasu Cin karo yayi da ita tana Ƙoƙarin fitowa babu abin da ya bashi mamaki sai sanda yaga Hussaini na Ƙoƙarin kawo mata wani Dukan.


Da wani zafin nama ya Mayar da ita bayanshi ya saka Hannu ya wanke Hussaini da mari! ya kuma saka wani ya ƙara bashi kafin ya Rufe shi da duka bakajin komai na tashi agidan sai muryar ummah data Hussaini Ummah tana cewa .

"Jama'a ku kawon ɗauki zai kashe Min ɗa"

Hussaini yana Ihu yana cewa.

"Yaya tsautsayi ne bazan ƙara ba"

Ahmad Baya ji baya gani sai da Amatullah ta Rungume shi ta baya tana Ihu tana cewa 

"Kada ka kashe Shi wallahi Na yafe da baka taɓa shi ba"

Kafin wani Lokaci mutan gidan sun cika Ɓangaren da ƙyar su Alhaji suka ƙwaci Hussaini a hannun Ahmad wanda Jikinsa yake ta faman Ɓari da alamu allurar sojan ce ta motsa.


Idanu Jajir ya Dubi Mama data zuba masa Idanu tana salati.

"Mama kuje da Amatuh part Ɗinki kada ki barta a wajan waɗannan azzaluman"

Daga haka bai Kuma cewa komai ba yabar wajan duk surutun dake tashi na Mutan gidan bai sanya ya tsaya ba.


Rufe kanshi yayi aɗaki yana buƙatar kaɗai cewa.


Surutai da ƙananun maganganu ke tashi tare da Kukan Ummah data ke ta zage zage tana Cin alwashi akan Amatullah kamar ba ƴar Cikinta ba Alhaji ne yace kowa yaje ya kwanta Cikin tausayawa Mama ta riƙe Hannunta tare da cewa.

"Mu tafi ciki Amatu"...................

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.