Bakon Lamari 13

 


                  *13*


Cikin mutuwar Jiki take sanya kaya ajikinta gaba ɗaya tunaninta ya tsaya cak, Yaushe ya dawo Gida Ina zai kai mata Iman ita bata son duk wata alaƙa da zata Haɗa ta dashi Dan haka Koma Ina ya nufa da Iman dole ya

dawo mata da yarinyarta Tafaɗa tana Danno Bakinta gaba kamar Yana kallon ta.

Tana kammala shiri ta Fita tsakar Gida ta zauna Yayyafin ruwan sama na Dukan Jikinta Idanunta Lumshe Tana shaƙar Mayen Ƙamshin Turaren shi daya bari a tsakar Gidan Tun tana Zaune harta Gaji ta Miƙe ta fita harabar Gidan Ƙofar Gida a rufe Haka nan Gate Ɗin ma a rufe Jingina tayi da Bango Hawaye yana zubo mata Wa zata Tunkara da Batun Ahmad ya ɗaukar Mata Iman ya fita?


Haka ta koma cikin Gida gaba ɗaya Jikinta yayi mata sanyi ɗaki ta wuce a wannan dare Bacci Ɓarowa shine yayi awon Gaba da ita daman Ga jikinta Duk ta gaji.

Wajan Asubah zazzaɓi Duk ya rufe mata Jikinta ga Nononta ya samƙame Ya ciko sabida Rashin sha da Iman batai ba zuwa asubahi kanta ya soma yi mata azababban Ciwo a daddafe ta Fita tsakar Gida tayo alwala ta dawo ta zauna tana azkar Ta jingina kanta Jikin itace wajan shiddan safe ta Fita ɗakin Baba ta gyara shi sannan ta koma ɗaki ta kuma zama ji take Kamar tai tsuntsu ta ganta a gaban Iman bata san tana son yarinyar taba sai da ya nisanta ta da ita.


Kuka take a wannan Lokacin domin ta kasa jure rashin Iman.

"Amatullah Lafiyar ki, kike kuka?"

Taji Muryar Ameerah a saman kanta wadda sam bata ji Sallamar da Ameerah ke mata a ɗakin ba.

Ta ɗago jajayen idanunta ta zubawa Ameerah Tare da cewa.

"Ba komai Idona ke min Ciwo"


Da sauri Ameerah ta aje kwanon abincin data shigo mata da shi a gabanta tare da zubewa a kusa da Amatullah Ɗin tace mata.

"Yaya naga Kina kuka da idanuna sannan Kice Idanun ki na maki ciwo Ina Iman ban ganta ba?"

Sai Amatullah ta kuma fashewa da kuka tana cewa.


"Tun jiya ya tafar Min da Ƴata ko ina ruwan shi dani Oho dan rashin Imani ya tafar Min da ƴata bai dawo Min da ita ba"

Da sauri Ameerah tace.

"Waye Imran? garin yaya?"

Tura baki Amatullah tayi tare da cewa.

"Yayah Ahmad Mana"

Jimm ameerah tayi Batai magana ba har tsayin wasu Lokuta Kafin tace.

"Meye Ya haɗa ki da shi da har ya Ɗauki IMAN ɗin?"

Cike da Mamaki Ameerah ta faɗi maganar.

"Oho mai"

Amatullah ta faɗa tana mai cigaba da kukanta.

Ameerah Danne abin da ke taso mata a zuciya tayi kafin ta shiga rarrashin Amatullah tana yi tana kawar da sharrin shaiɗan a zuciyarta.

Da Ƙyar ta Lallaɓa ta taci Indomie da ƙwan da ta da fo mata sannan Suka fita Ameerah na ce mata tazo suje wajan Mama ta gaya mata Ita kuma Amatullah taƙi tace yaje ya kwaɗanta Iman ɗin ya cinye.

Ranta Babu Daɗi ta fita daga Gidan tayi gidan sabuwa koda taje can ma sabuwa taita tambayarta meye ya kumbura mata idanu tace ba Komai Haka suka tattara don tafiya Gidan aikin nata.

***************

Da Gudu Ameerah ta shiga Cikin Gida tana yada kwanon tana kiran Anty wani azababban Kishin Ahmad na cin ranta.

Da sauri Anty dake haɗa ma Ƙanin Ameerah abinci ta fito tsakar Gida Tana cewa "Ke! Nifa nagaji da wannan ɗagamin Hankalin da kike jiya kin shigo min gida a firgice yau ma haka Uban me aka kuma yi Miki?"

Rungume Anty tayi tana cewa.

"Anty zuciyata raguwa ce na kasa lafawa duk wanda zai Raɓi Yaya Ahmad Anty zuciyata zata Buga Jina ke kamar zan Mutu in ban sami Yayah ba"

Anty ta shiga shafa kan Ameerah tana jin Raɗaɗi acikin zuciyarta na yadda da ranta da lafiyarta ƴarta ke neman rasa Nutsuwarta akan ɗa namiji.

"Ki shuru Ameerah kada Mutan gida suji me muke ciki wuce Muje Ɗaki maza"

Jikin Anty har yana rawa tama mance da wani Abincin da take zubawa suka nufi ɗaki suka zauna a saman Kujera Ameerah ta ɗago Fuskarta datai jage jage da hawaye tace.

"Anty jiya fa ƴar Amatullah a wajan sa ta kwana Fisabilillah meye haɗin sa da ita yanzu naje na tarar tana ta Kuka Da ƙyar na danne zuciyata na Dawo gida Anty Nifa bana son naga yana kula ko wace mace idan bani ba duk da nasan Amatullah ba zata ci Amanata ba domin tasan yadda nake son shi"

Anty ta zunduma wata irin ashar tana miƙewa tsaye.

"Dama kece Wawiya waya gaya Miki yanzu akwai amana ai wanda ka yarda dashi shiyake fara cin amanarka dama ni fa wannan tsinanniyar yarinyar bana ƙaunar ta bana son ta wato Har yanzu bai haƙura da ita ba kenan?"

Da sauri Ameerah ta Rufewa Anty Baki tana cewa.

"Nifa Anty bana zargin Amatullah kawai Kishin Abin naji acikin zuciyata amman wallahi kamar yadda yaya baya ranta itama haka bata na shi ran"

Anty Tayi juyi tana cewa

"Dama Yaya sai da tace min sai na tashi tsaye akan Ahmad sannan haƙar mu zata cimma ruwa sabida haka bana jin Ko ita waccan Ƴar mai kuɗin zan bari ya aura dan haka daga yau ki soma shiri Cikin ko wani yanayi zaki iya jin An ɗaura auren ki da Ahmad Ina shine Burin ki to kisa aranki wannan Buri naki cikakken Buri ne sai kin aure shi ita kanta uwarsa sai dai ta koma ƴar kallo"

Anty tana faɗin haka ta ɗauki wayarta ta shiga kiran Yayarta a waya ta shige ɗaki tabar Ameerah da nazarin maganar tata. 

Mintuna kaɗan ta fito da mayafi tana cewa ameerah ta kula da gida zata Fita anguwa.


Amman taji zuciyarta tayi sanyi tana Jin Ahmad shine rabin rayuwarta ta yarda ta kowace hanya mahaifiyarta tabi Idan har Burinta zai cika ta sami Muradin zuciyarta.

*********************

Ya tashi da tsananin mamaki acikin Zuciyarsa na yadda Amatu tai ko in kula da ƴar Cikinta haka ya shirya ya fita yayi sallar asubahi ya dawo ɗaki Lokacin Iman ta tashi tana ta tsala Ihu Jin Kukan yake na juyar masa da kanshi da sauri ya ɗauketa da madararta yayi Falon Mama yana Kiran Naja'atu wadda ta fito da Hijabin sallah a jikinta ta zube tana gaisar dashi ya Miƙa mata Iman yana cewa ta bata madara ta Goyata.

Amsar Yarinyar tayi cike da Bin Umarninsa haka ta Juya ɗaki shikuma ya Nufi Ɗakin Alhaji Domin su gaisa.


Zaune ya tarar da Mama da Alhaji suna hira a ɗaki yayi sallama suka amsa ya zauna a ƙasan carpet yana gaishe dasu Bayan sun gaisa Alhaji ya dube shi Cike da kulawa yana cewa.

"Ɗazu muka gama maganarka da kawunan ka Ina ganin yau zasu je Gidan su yarinyar nan kawai zamu kai Lefe Jibi idan muna raye tunda Lefan ka daman yana ƙasa Idan yaso nan da  wani satin in suna shirye a ɗaura aure matarka ta tare agidan ka dake Bayan layi abin da baka ƙarasa ba sai ka Ƙarasa Da wuri Tunda zaka jima anan Ɗin gwara ka zauna da matarka"

Tunda Alhaji ya soma maganar yayi ƙasa da kanshi Jin maganar yake daga sama Sam baze iya musu da maganar Alhaji ba amman yaso an ɗan ɗaga Bikin an barshi kamar yadda yake ada sabida yana da shirin da ze a ƙasa amman Tunda Alhaji yace ayi Ɗin hakan za'ai babu ja.


"Baka ce Komai ba Babana ko kana ganin abar shi kamar yadda yake? ni abin da yasa nace ayi Yanzu sabida naga ka sami Lokaci ka dawo Kano Komai zai zo maka da sauƙi"

Cewar Alhaji wanda yake maganar Cikin dattako.

"Alhaji ba wani abu abar shi hakan Allah ya ƙara Girma"

Daga haka yaja Bakinshi yayi shuru Mama ta bishi da kallo tana yaba tsananin Biyayyarsa.

Duk Yadda baya son abu idan suka umarce shi dayi baya Musu tana addu'ar Shima Allah ya bashi masu yi masa Biyayya kamar yadda yake Yi musu.

"Binta ke baki ce Komai ba?"

Cewar Alhaji.

Mama tayi dariya Ta kauda kanta Gefe.

Alhaji yayi dariyar shima yana mamakin wannan alkunya da Mama kewa Ahmad.

Ya jima suna ɗan tattaunawa da Ahmad ɗin kafin Suyi sallama ya wuce Ɗakin sa.


Alhaji ya kalli mama yace mata.

"Kinga yaron nan naki badai zurfin Ciki ba koda abu bai masa ba baze Fito fili ya faɗa ba sai yace to"

Mama batai magana ba ta miƙe ta fita waje dan ita a tsarinta taso abar Ahmad yay Bikinsa anutse amman Tunda Alhaji yace ayi a yanzun hakan za'ai babu ja.


Da Naja taci karo tana Faman damben bawa Jaririya Madara.

Mama ta dube ta tana cewa.

"To farin shiga kada ki shaƙawa ƴar mutane madara a hanci Ina kika samo ƴa da wannan safiyar?"

Naja tai dariya tana ɗaga Iman tana Cillawa tana cewa.

"Wallahi Yaya ne ya kawon ita tun ɗazu Nima ban san A ina ya samo Ƴar nan ba mai kyau da ita"

Cikin ɗunbin mamaki Mama ta saka Hannu ta karɓi yarinyar tana kallonta.

"Ai wannan ƴar Gidan Amatu ce haka ta Girma Ma sha Allah"

Mama ta faɗa tana Ƙurawa Iman Idanu.

"Lah Dama ƴar gidan Amatullah ce ƙwarai kuwa sabida Naji ameerah tace tana Gida Tun ɗazu Yaya ya kawon Ita yace na kula da ita"

Mama ta riƙe haɓa bayan ta ɗora Iman kan cinyarta tana cewa.


"To in ban da abin sa ya za'ai ya rabo Ƴar da take shan Nono da mamanta fisabilillahi zaizo ya same nine"

Mama ta faɗi bayan ta tashi riƙe da Iman a hannunta tayi Cikin Bedroom Da ita.

Ahmad wuni yayi a ɗakin sa bai fita ko Ina ba Sai da akai la'asar sannan yayi wanka cikin wata Blue shadda ya shirya kansa ya fita.

Kai tsaye sashin su Amatullah ya nufa domin ya duba Jikin baba.

Yadda ya sami Baba abin ya ɗaga masa hankali Waya yay ma wani likita abokinsa akan zai kawo baba ya duba shi abokin nashi yace baya kano amman zai dawo Next week Bayan sunyi sallama ya kuma yiwa baba Sannu ya tashi ya fita A tsakar Gida suka haɗu da Umma wadda ganin Ahmad yasa ta daburce taƙi ma haɗa idanu dashi Shiko ya saki Jiki da ita sosai suka gaisa.

Sannan ya kama hanya ya fita part ɗinsu ya koma Kai tsaye yayi falon mama wadda tun kafin ya zauna ta rufe shi da faɗa tana cewa ya ɗauki Ƴar Amatu ya kai mata kayarta.


Ya saki ƙayataccen Murmushi tare da cewa.

"Mama ai ta bar min tunda Taƙi zuwa ta karɓe ta"

Daga haka yayi mata sallama ya Nufi Mota domin zuwa gidan su zainab wadda ta ishe shi da waya.


Tafe yake yana tuƙi yana sauraran Wa'azi acikin Motar tashi Karaf kamar ance ya ɗaga kanshi ya hangeta ta tattare zani zata tsallaka titin daze Shigo da ita layin.


Amatullah dawowarsu kenan ita da sabuwa daga wannan Gidan dai na Jiya wanda yau ma sun daki Gurbi dan da suka je wai Matar Gidan ta fita bata nan haka sabuwa taita Mita daga nan ƴan shige shigensu sukai Gidajen masu kuɗi wanda anan Amatullah ta samo Abinci wanda ta ɗaure a leda ta tawo dashi Gida bayan sun rabu da sabuwa a bakin babban titi.


Sakin zanin Jikinta tayi bayan ta tsallako Tana mai dafe ledar abincin tana tafe kamar iska zata kwasheta dan tsananin Sauri Burinta taje ta amso Iman dan haƙurinta ya ƙare a wannan Lokaci.


Caraf taji an damƙi Tsintsiyar hannunta da ƙarfi Juyawar da zatai domin tai magana taga Ahmad Ne Riƙe da Hannun nata kafin ya soma janta har zuwa bakin Motar shi ya Buɗe Gidan gaba ya shigar da ita ciki kafin ya rufo ta ya koma mazaunin Driver ya zauna Fuskarnan tashi babu alamun Dariya........

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.