Bakon Lamari 12

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *12*


Lokacin daya fito daga Palon mama kusan ƙarfe taran Dare ne, sabida haka alwala yayi ya wuce masallacin dake kallon ƙofar Gidansu yayi sallar Isha'in daya rasa Yana

fitowa daga Masallacin suka haɗu da Kamal wanda yake Buɗe Gate zai shigar da Motar Shi daya kai masa wanki Tun jiya sabida Haka dakata wa yayi Kamal har ya shigar da Motar Cikin Harabar Gidan sannan ya Miƙo masa Keyn Motar.

Amsar Keyn yayi sukai sallama da Kamal ya Nufi Cikin Gida shi kuma Kamal ya Juya da tashi Motar dan ya kaita gareji sabida Harabar Gidan bazai ci mota Biyu ba dan haka iya ta Ahmad ce kaɗai ta sami wuri a harabar Gidan.


Hadari ne keta haɗowa a garin sabida yanayin na damuna ne iska mai ƙarfi tana Kaɗawa wanda ya bawa Ahmad damar Ƙara sauri wajan shiga Gida sabida baya son ruwa ya taɓa shi Gudun zazzaɓin daya ke haifar masa Kuma ya lura Hadarin dab yake da zubar da ruwan sama.


Kukan Jariri ke tashi cikin kunnen shi Lokacin daya kai ƙofar shiga sashin su A hankali yake ƙara matsar da Kunnen shi zuwa Inda yake Jin sautin fitar Kukan Jaririn Tabbas ba Gizo Kunnen shi ke yi masa ba Ƙofar Sashin Kawun sa Sha'aibu anan yake Jiyo Kukan jaririn wanda har takai ga jaririn ya sarƙe yana tari Kukan yaƙi Fita ta daɗi.


Da sauri ya ƙarasa Cikin sashin Abin mamaki harya tura Ƙofar da aka karo ya shiga tsakar Gidan amman babu wanda ya fito daga ɗaki bare yasa ran sallamar daya ke yi za'a amsa masa.

A hankali yake Bin sahun Inda yake Jin kukan jaririn Bai sha mamaki ba sai da ya tsinci kansa a Ɗakin daya haɗu da tarkacen Itace Duhu Dumɗun acikin ɗakin babu alamar Haske Hannunsa har rawa yake wajan Ɗauko wayar shi dake aljihun jallabiyar shi.


Yana mai kunnata ya Haska ɗakin da fitilar wayar tashi


Wanda idanunshi yakai masa Duba wajan Jaririyar Yarinya ɗanyar haihuwa yashe a ƙasan wani ƙaramin zani sai Kuka take Duk ta ɓata Jikinta da Dattin Sumuntin Ɗakin.

Cikin zafin nama ya ɗauke Jaririyar yana jijjigata ajikinsa har Lokacin bata daina Kuka ba sai cilla ƙafafu take.

A hankali ya saka mata harshen sa Cikin bakinta wanda ta kama tana mamula kamar ta sami Nono sai Kukan ya tsaya ta kama ajiyar Zuciya.

Haska yarinyar yayi sosai yana ƙare mata kallo tausayi da Soyayyarta a take suka Kama masa Zuciyarsa.


Hannunta ya kama wanda aka saka mata ƙaramar azurfa a ɗan ƙaramin yatsarta Da sauri ta saki harshen nasa ta canyara Kuka Har tana ƙwarewa.


Ya Kuma Ɗorata a kafaɗarsa Kallo ɗaya yayiwa hannun yaga Ya kumbura har yaja Ruwa.

Ya zaro idanunsa waje yana mamakin Rashin Imanin uwar yarinyar da bata san ya rayuwa take Ciki ba amman an barta cikin tsananin azabar Ciwo a hannu ba tare da an kula ba.


Amatullah.

Tunda suka fita da Sabuwa bata dawo gida ba sai da akai Sallar isha'i Lokacin da suka je Gidan Alhaji Idris mai kwano masu gadi suka hanasu shiga sabuwa taita Kiran Number Hajiya Zahra bata same taba sabida Haka sai kawai suka Juya Koda suka juya Ɗin a hanya Amatullah ta sanya wa Sabuwa Kuka akan cewar bata da Daidai da Kuɗin Maganin sauro bare abin da zata ci Ruwan Nono ya kawo Yarinyar ta tasamu Tsananin tausayin ta ya kama sabuwa sabida haka sai kawai tai Rijiyar Zaki cikin tasha Da Ita wajan Wata Hajiya Balki mai Abinci akan ta ɗan yi mata aiki ko naira Ɗari biyar ta bata Cikin Ikon Allah suna zuwa tashar ma Hajiya Zahran ta Kira sabuwa Sai dai ganin Magariba ta kawo kai yasa sabuwa tace mata Gobe 

Zasu dawo Basu ma sami Hajiya Balki ba sai yaranta dan haka sai suka Juya Gida to sai sabuwan tace wa Amatullah ta Bita Gidanta taci abincin dare sai ta koma Gida Sabida Sabuwa tana jin tausayin Amatullah sosai.

Hakan akai Suka Nufi Gidan sabuwa Anan taci Abinci har akai isha'i sannan tayo Gida Bayan sunyi sallama da sabuwa.

Koda ta Koma gidan Bata sami tarbar arziƙi a wajan Ummah ba bare ta sami Darajar tace mata daga ina take sai ma ɓacin rai data riska dan Nana ta ɗaukar mata kayanta Kala ɗaya takai gidan Ɗinki an rage mata ta sanya su ajikinta Koda tai magana Nana tahau Gaya mata baƙar magana Hussaini Ƙaninta shine mai cewa sai ya ɓallata ya ɓalla banza sai da ƙyar Hassan ya riƙe Hussaini Amatullah tasha Kuka a ɗaki Sannan ta aje Iman a saman zaninta ta Ɗebi ruwan sanyi a rijiya ta shiga Banɗaki domin tai wanka Duk da ba Omo bare sabulu amman tasan Ruwan sanyi zai mata Maganin zafin daya Isheta.


Tajima tana kallon Gefen cikinta wanda tsargiyar ɗinkin da akai mata na C's Ta cire tsaf wajan yayi Kyau babu alamun wata matsala Jan ajiyar zuciya tai aranta tana Godiya ga Allah daya sa wajan bai sami wata matsala ba ya warke ras.


Duk Budirin Kukan da Iman take sam bata jiba sabida Bayin yaɗan shiga Loko Haka ta gama wankan ta ɗauro zani ta Fito kanta Ko ɗan kwali babu.


Sai dai koda da fito Ɗin Ta tsinci kanta da tsananin faɗuwar Gaba sakamakon wanda ta gani a tsaye Riƙe da Iman A hannun shi yana jijjigata Tsananin tsoro da faɗuwar gaba ne suka Kuma ƙaruwa acikin zuciyarta Ko shekaru nawa zatai bata gan shiba bazata mance Kamannin saba YAYA AHMAD.

Ta faɗa aranta da sauri Kuma ta raɓe shi tai ɗaki har tana Bugewa da bango.


Da kallo ya bita yana mamakin Ramewar da yarinyar tayi tome ke damunta?Ya girgiza kan shi yana mai juyawa Ya fita da Iman A hannunshi Wajan motar shi ya nufa ya Buɗe tare da aje Iman aciki ya zagaya ya buɗe Gate sannan ya koma ya fitar da Motar Sannan ya dawo ya rufe Gate Ɗin ya Koma Cikin Mota yayi mata key yaja ya bar layin.

Kai tsaye wani ƙaramin Private Clinic ya kaita wanda Nurse suka karɓi Iman domin su duba Hannun ta kamar yadda yayi Musu Bayani Rintse Idanu yayi yana jin zafin yadda Ƴar ƙaramar yarinyar Keta tsala Kuka Lokacin da Nurse ke gyara mata Hannun nata wanda tace masa Buguwa ne tayi bayan an gyara aka shafa mata magani a wajan Ya biya Kuɗi sannan ya Shiga Mota sai da ya biya ta wani super market ya sayi madara ta Jarirai ya tambayi yadda ake haɗawa tare dasu pampers dasu Pida sannan ya ƙara Saya mata Riguna masu kyau sai yayo Gida.


Lokacin daya ƙaraso Gida tuni an soma ruwa da sauri ya shigar da Motar ya Kulle Gida sannan ya fito da Iman da kayan daya siya yayi ɗakinsa da Gudu gudu, Batare daya Bi takan Amatullah ba bare ya kai mata yarinyarta so yake yaga Gudun ruwan Haukanta........

Bayan ya shiga ɗakin ya rufo ƙofar shi ruwan zafi ya haɗa yay wanka ya Rage daga shi sai Guntun wando da singlet Itama Iman Tawul ya Jiƙa da ruwan Ɗumi ya goge mata Jikinta tas sannan ya sauya mata kaya wajan saka pampers ne yaci wahala dan har Gumi sai da ya haɗa yana gama shiryata ya Haɗa mata madara a pida da ruwan Ɗumi ya ɗaga kanta yana bata Cafkewa tai tana sha tana ajiyar Zuciya Har ƙwallar tausayin yarinyar ce ta tarar masa a idanunsa tas ta shanye Madarar dake ƙatuwar Pidar Ya kwantar da Ita saman Ƙirjinsa yana shafa kanta mai cike da suma Kafin wani Lokaci tayi gyatsa ba jimawa Bacci yay awon gaba da ita sai Fitar Numfashi mai ɗumi take.


Anan ƙasan Carpet yaja Pillow ya kwantar da kanshi Shima da yake Gajiya na Cin Jikinsa bai Minti Biyar ba bacci mai Daɗi ya kwashe Shi Batare daya yi Tunanin kaiwa Amatullah Yarinyarta ba......... 


Amatullah.


*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*
*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.