Bakon Lamari 10

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *10*


Cikin shigar Kakin sa na sojojin Nigeria Army green yake saukowa daga step ɗin Jirgin, Idanun shi manne da ƙaton baƙin glass sai ƴar ƙaramar jakar dake hannun shi a nutse yake saukowa fuskar shi babu yabo babu fallasa kamar koda yaushe.


Tattaki yake a tsakanin filin jirgin wayar shi daya Kunna yanzu ya ɗauko yana Kiran Kamal wanda tuni sun iso Domin ɗaukar shi daman jiran saukar Jirgin suke yi.


"Kamal nafa sauka kana ina ne?"

Sanin rashin haƙurin Yayan nasu ya sanya Kamal Fitowa daga cikin Mota da sauri da wayar a hannun shi yana Cewa.

"Muna wajan ai Yaya Tun ɗazu Muka iso"

Juyawa yayi batare da yay magana ba suka haɗa idanu da Kamal wanda ya tawo da sauri ya Zube a ƙasa yana gaisar da Yayan nashi kana ya amshi jakar Hannun shi suka Nufi Mota.


Gidan Gaba Kusa da driver ya buɗe ya shiga Bakin sa ɗauke da Bisimillah ya zauna yana mai zare Glass ɗin dake Manne a idanunshi.

"Yaya Barka da dawowa ya hanya?"

Muryoyin Naja da surayya da Ameerah ne suka cika Kunnen shi Cikin Mamaki yaɗan Juyo yana kallon su ta cikin madubin motar.


"Daku yazo kenan lafiya?"

Ya faɗi a taƙaice.

"Yaya wallahi Mama ce tace a zo dasu"

Cewar Kamal.

Bai kuma magana ba ya jingine kanshi da jikin seater Motar ya lumshe Idanun shi gaba ɗaya Jikinsa ciwo yake masa Tsananin gajiya ce Cike a jikin nashi.


Har Kamal yaja motar Bai kuma cewa komai ba kuma daman Tun fil azal shiba mai yawan maganar Bane ba.


Ameerah ta kafe shi da idanu ta cikin madubin Motar gaba ɗaya ya tafi da dukkan Imanin zuciyarta Tsananin son shi na kuma fisgarta Jitake kamar ta dauwama a haka tana ta kallon shi Jinta take tana yawo acikin Duniyar gajimare Wata biyar Ɗin da yayi bai zo gida ba Taga yaƙara cika da kyau Hutu ya kuma ratsa shi kamar ba soja ba.


Tana jin ko a mace ta Huɗu ce zata zo masa Indai zai aure ta bata Biyu ba.


Duk hirar da su Naja keyi Ameerah bata Jinsu sai ma ƙara Tsira masa idanu da tayi tana kallon shi jita ke kamar ta Cinye shi ɗanye.

Dama Zuciyarta zata bar jin tsoron sa data tunkare shi da kalmar so! sai dai tsananin Tsoron da take yi masa yasa Ko haɗa idanu bata iyayi dashi Inda Allah ma ya temake ta Antyn ta taiwa Mama maganar ta wanda Mamar tai musu alƙawarin Ahmad dole ya aure ta bayan ya auri Matar shi ta farko.


Tuna wannan Batu yasa ta sada kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta daya sha jan lalle wanda tayi shi Jiya don Ahmad ya gani.


A haka suka ƙarasa Gida Ko parking bai bari Kamal ya daidaita ba ya Ɓalle marufin Motar ya fita yana Jan tsaki ƙasa ƙasa.

Ya kula Yarinyar dake kusa dasu Naja ta kafe shi da idanu wadda bai ma gane kowa ce ba sabida yaga yaran Gidan nasu nada yawa Baya son raini ko kaɗan ya lura yaran Yanzu Idanun su ya buɗe da Son maza.


Kamal ne yabi shi da jakar shi bayan ya kashe motar Suma Su Naja haka suka fito daga motar bayan sun tashi Ameerah wanda a zaton su duk bacci take Yi wanda ita ba baccin take ba tsabar Tunanin soyayyarta ne yayi mata yawa.


Haka suka ƙarasa gida da sauri tai ɓarin su har tana haɗawa da Gudu tana kiran Anty mahaifiyarta da ƙarfi.


Cikin sauri Anty ta fito tana Kama Ameera tana cewa.

"Ke lafiyar ki? kika shigo min gida haka kamar wata sakarai?"

Janyo Anty tai Cikin falon su suka zauna sannan ta dube ta.

"Anty yaya ya ƙara kyau daga gani yana cikin kwanciyar hankali Anty dan Allah ki ƙara min ƙoƙari akan shi Anty tunda na tashi da soyayyar yaya na taso a rayuwata kina kallo bana kula kowani namiji sabida shi dan Allah kiwa Baffa magana akan shi koze sami Alhaji da maganar mu"

Ta ƙarasa maganar tana jan Numfashi mai ƙarfi.


Tsananin tausayin yarinyar ne ya kama Anty Ameerah ƴarta ce ta fari wadda tafi soyuwa fiye da dukkan ƴaƴanta acikin zuciyarta dan haka dole ta Bawa ƴarta abinda take so koda zata rasa komai nata ne a rayuwa.

"Ki ƙaran haƙuri Ami, munyi magana da uwarsa ki bari muga auran nashi daga nan sai muga gudun ruwan su, Babanki kuma kinsan baze magana ba kinsan haƙurin su yayi yawa dukkan su sanyi gare su dan haka kada ki damu nai miki alƙawari Ahmad Sai ya aure ki koda tsiya koda tsiya tsiya! dan na fahimci kamar da rainin hankali a wajan uwarsa kawai ta faɗan hakanne dan tasa hankalina ya kwanta, Shima kuma Ahmad bawai Ganin girma na yake ba Dan na fahimci Duk sanda zaizo Ko kallon sashin nan bayay bare yazo ya gaishe ni sai dai ya tari Baffan sa a waje su gaisa Duk yadda nake wa uwarsa baya gani Inma ya ganni a wajan uwarsa haɗe rai yake yayta janta da hira su barni zaune ni kaɗai"


Ameerah ta lumshe idanu tare da cewa.

"To Anty kawai idan tai niyya tasa ya haɗe mu rana ɗaya mana?"

Anty tace.

"Barni da Hajiya Binta, dani take maganar ta ɗauka yadda nake mata a fuska har zuciyata haka yake? to sai da na laluba nagano zamu kwashi dukiya wajan ɗanta sannan nai mata kwanton ɓauna na shiga Jikinta Burina Ahmad ya aureki koda baki ce kina son shiba dama da niyyar na haɗaku bare da bakinki kince kina son sa sabida haka ki kwantar da hankalinki Ahmad Mijin kine Uban ƴaƴanki ki aure shi ki hayayyafa Komai nasa ya dawo namu Hatta uwar tasa ma sai yadda kika ce zai mata Sabida a rayuwa ina baƙin Cikin Mutum Biyu Hadiza da Binta sun fini komai Ita hadiza mijin ƴarta daya tsaya mata wannan abu na ƙona Mini rai Shiyasa jiya danaji labarin auren ta ya Mutu yau sai da nai sadaƙa sabida Murna ita kuma Binta Duba kiga kaf ƴaƴanta mata Uku dake ɗaki bamai auren talaka Shima Ahmad jibi yadda Allah ya ɗaukaka shi a aikin shi Lokaci ɗaya ga kuma kasuwancin sa wanda naji ashe ƙatuwar plaza ya saya ya zuba kayayyaki kuma ance kayan ma daga ƙasar waje ake shigo dasu ya damƙawa kamal a hannunsa yake kula masa da komai na ɓangaren plazar,sannan ya sami yarinyar dazai aura ƴar manyan Mutane, Binta a yanzu tafi ƙarfin Komai a rayuwa Hutu da jin daɗi kullum ƙara Huda ta yake shiyasa Sai da nai yadda nai da Gulma da Kirsa na rabasu da Hadiza don Muddin Suka haɗa kai ni tawa ta ƙare Sannan Kuma nasan yadda nai nake amshe saƙon matan gidannan Wanda take bani tace a raba musu na wajan Ahmad nake riƙewa nakuma toshe hanyar da zataji Duk dan tai baƙin jini acikin su to Alhamdulillahi wannan tarkon nawa ya kama domin kuwa yanzu duk matan gidannan haushin Binta suke ji suna ɗaukarta mace mai son kanta da izza Yanzu tarkona na gaba ki Auri ɗanta daga nan kuma ta kaɗe har ganyenta wallahi"

Zare idanu Ameerah tayi har zufa na keto mata.

"Haba Anty dan Allah ki bar yin haka wallahi babu kyau ko kaɗan Sabida bakisan ranar mutuwar kiba"


wata dariya Anty ta kwashe da ita kafin tace.

"Ke yarinya ce Ameerah baki san dawan garin ba ada can ma kafin a haifeku Mijin Binta Nada kuɗi Mijin Hadiza nada kuɗi kafin ya kwanta ciwo Ni kuma mijina baya cas bare as suke mana komai har Allah ya bashi malamin makaranta Kina kallo fa daga Alhaji sai Sha'aibu sai babanki sai sauran ƙannen shi Biyu su waɗannan bana ta tasu dan basa gabana amman waɗannan faccalolin nawa guda Biyu sun tsayan araina yadda bakya zato bafa zasu fini da Miji ba sannan suzo su fini da ƴaƴa Ina sam Ita waccan suruki ita waccan ƴaƴa musamman ma Ɗanta mai son ta mai kashe mata Kuɗi wallahi sai ma kin shiga gidan shi daga yau ki ɗau ɗammarar kota kwana"

Anty ta faɗa har idanunta na sauya kala zuwa ja.

Ameerah tabi ta da kallo sam bata fahimci me take Nufi ba akan waɗancan maganganun nata.


"Kuma sannan ba waccan matsiyaciyar ta dawo ba ki dinga janyon ita wallahi bazan ɗauka ba Ki tattara ki watsar da ita ke Budurwa ce ita bazzawara sabida haka hanyar Jirgi daban ta mota daban wallahi bana ƙaunar Amatullah ko kaɗan a duniya"

Ameerah tai saurin tashi daga wajan tayi ɗaki dan aduniya Ameerah bata son taji Anty na zagin Amatullah sabida ƙaunar da take mata Shaƙuwace tun ta yarinta zama suke na so da ƙaunar Juna ada Ko bacci baya rabasu duk da iyayen nasu mata basa shiri haka koda Amatullah tai aure Ameerah bata haura kwana biyu bata je ta ganta ba wannan shaƙuwa tasu har tai yawa basa Ɓoyewa Junansu sirrin Juna musamman ma Ameera data fi Amatullah yawan magana.

**************


Ahmad Ɗakin shi dake daidai Ƙofar Fita daga sashin su ya karɓi Key wajan Kamal ya Buɗe ya shiga ciki, Ko ina na ɗakin Need babu datti sabida gyaran da yake sha wajan su Naja dan kullum sai sun Buɗe ɗakin sun share sun Goge kayan wutar dake Ciki wannan yasa ɗakin babu datti ko tarkace.

A falon daya sha manyan kujeru masu tsananin kyau da ƙatuwar Tv da Shinfiɗaɗɗan carpet kamal ya aje masa Jakar Shikuma Ahmad ya wuce Bedroom Domin yayi wanka nan ma a gyare yake tsaf dan hatta Bedshirt An sauya shi da wani fari tas mai kyan gaske Taka Luntsumemen carpet ɗin dake Bedroom Ɗin yayi zuwa gaban gado yana shaƙar ƙamshin turaren daya kama ɗakin ya sami muhalli aciki tare da soma Cire Botiran gaban rigar kakinsa.............

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

*Assalamu alaikum yan uwamata :muna farincikin sake gabatar muku BINTU* *-SPA-ND-MORE.. inda zaku sami  ingantaccen garin maganinmu,na zallar magungunan gargajiya daya hada da hakukuwa,ganyaye,kauci,huda,sassake da hatsi kala kala wadanda basuda illah  ko kadan ajikin Dan adam.wannan maganin an hadashi ne bisa yarda da amincewa da da hannun gwanaye kuma masanan* *magungunan gargajiya nagarin kano.wannan magani yana gyara nono wanda ya yamushe,ko wanda ya kwanta,ko wanda ya tartare,ko wanda akeso ya cicciko,ya daga, ya mike,yayi kyau.*

*Ina masu kananan nono?*

*Ina masu yaye?*

*Ina yammata da ake shirin aure?*

*Ina matan gida masuson gyara?*

*Ina zawarawa masu shirin aure ko gyara don zawarci?*

*Ina ramammum mata dasukeso suyi kiba su murmure?*

*Wannan gari shine kuke bukata.yana* *tadakomada,yana da kiba,yana ciko nono,yana sawa mace tayi* *mulmul,tayi dumimi,tayi kyau tayi* *haske,sheki,sulbi da santsi kamar kinyi gyaran jikin yan* *maiduguri.koina ze cike Tatar data yamushe zata mike tayi fes kamar sabuwar amarya.*💯💯💯🔥🔥🔥 *A BINTUS-SPA-ND-MORE  muna gyaranjiki* *gangariya,inda za a gyara Amarya ko  uwargida  ciki da waje kifita fes ga kamshi ba a magana.Akawai turarukan wuta, na daki,na jiki,na tsuguno, na kaya ,humrori.Akwai zafafan kuma gangarinyan* *magungunan mata sha yanzu magani yanzu da yardar Allah,Akwai ingantatun supplements na nono,hips skin,na kiba,na saukar da niima da dai* *sauransu.kayanmu guarantee ne,babu cuta babu cutarwa.muna aikawa koina a Nigeria cikin aminci.yar uwa kada ayi babuke,kada abaki labari.sai angwada akansan na kwarai takenmu shine gaskiya da amana.*


BINTUS-SPA-ND-MORE... na nan a mandawari nagoda street daidai asibitin yara na marmara @kano.Zaku samu BINTUS-SPA-ND-MORE  @CALL\WHATSAPP 07067338694/ 08136259679

IG Bintus-spa-nd-more..

No comments

Powered by Blogger.