Bakar Inuwa 9


 *_Episode 9_*

..............*_GOVERNMENT HOUSE_*


        Sosai jam'iyya mai mulki ke shirin kamawa da wuta a wannan ɗan tsukun a dalilin shirun party Chairman da shugaban ƙasa game da batun ɗan takara. Bakajin komai sai tsugunne-tsugunne da kace nace. Dan a wannan gaɓar ba wai jinta bakin su party Chairman ne kawai keda amfani ga jamiyya ba. Hatta manyan jam'iyar an zuba musu na muzurune game da kaiwa da kawowa da suketa famanyi cikin duhun dare.

      Wasu a cikinsu na goyon bayan shugaban ƙasa ne kai tsaye, yayinda wasu ke kaiwa da komowane akan nasu ƴan takarar da suke fatan a tsaida domin cancanta ko wani burinsu na daban tamkar yanda shima shugaban ƙasa keda tasa manufar shi da muƙarabbansa na bayan fage, harma da wanda suke a cikin tafiyar mulkin tsundum.



*_01:32am_*


         Agogo ya nuna a sirrintaccen falon dake fadar shugaban ƙasa ke ganawa da shaƙiƙansa na siyasa masu faɗa aji a bayan fage dama a zahiri ga jam'iyyar. A zahiri su ɗin manyane na ƙasa da ko kwatancen arziƙi sukai da kai idan da rabo sai ka haye. Da taimakonsu shugaban ƙasa ke mulki bayan UBANGIJI ya ƙaddara hakan, duk da dai akwai wasu gwasaken ɓoyayyu. Inda yay biyayya ga dukan tsarinsu ya mora suka mora. Daɗin hakan yasa basa buƙatar kuɓucewar mulkin a hannunsu, gudun kar wanda zai faɗa a hannunsa ya gagara zama ƙarƙashin mulkin mallakarsu da faɗa aji. Hakan yasa su yanke shawarar sake ɗora wanda zai iya binsu sau da ƙafa, sai dai sun hanga sun hango matsalolin dake cikin hakan ga dukkan waɗanda suka hasaso ɗin kai tsaye. Da ga ƙarshe bayan wasu dalilai suka yanke shawarar bama tsohon Alƙali kuma shahararren ɗan kasuwa Alhaji Hameed Taura takarar, da shirin bayan anyi komai an gama mulki ya samu zasu salwantar da rayuwarsa wanda zasu bama mataimakinsa ya maye gurbinsa. Sunyi wannan tunanin duk da cewa Alhaji Hameed Taura ɗayane da ga cikinsu, sai dai sam baisan akwai wata alaƙa a tsakaninsu su huɗu da suka killace kansu da itaba wadda babu shi. Sannan baisan ɓoyayyar manufarsu mummuna akansa ba tun shekaru masu yawa da sukasha auna rayuwarsa ba'a dace ba, saboda kwanansa basu ƙareba dan a hannun ALLAH suke. Babban dalilin zaɓarsa domin sake kawo kujerar shugaban ƙasa yanada alaƙa da farin jinin da ALLAH yay masa ga al'umma saboda ɗunbin ƙyautatawarsa ga talaka. Bashi da ƙyashi balle wulaƙanci. Ya cicciɓa mutane da yawa talakawa da sukai arziƙi a ƙarƙashin dukiyar da ALLAH ya mallaka masa. Bashi da girman kai, bashi da izza. Sannan baya ɗaukar raini ga dukkan wani maiji da kansa koda ace ya fisa arziƙi ne. Bai taka kowa bai yarda a takashiba shima.

      Su kansu kusan kaso biyu bisa ukun dukiyoyinsu kaso biyu na Alhaji Hameed Taura ne. Wannan yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da yasa zukatansu suke jin tsoron kar wataran ya amsa su koma baya. Shiyyasa suka sha auna halaka rayuwarsa amma ALLAH baisa sun dace ba. Hatta ɗansa *Basheer Hameed Taura* sunsha kai masa hare-hare ALLAH na kareshi. Rashin nasarar hakan ta sakasu komawa kan jikansa namiji tilo shima guda ɗaya a cikin ƴaƴa goma sha shidda da ɗan nasa Basheer Hameed Taura ya haifa mai suna *_RAMADHAN B. HAMEED TAURA_*. Sun so tsunduma rayuwar Ramadhan a harkar shaye-shaye tun yana secondary school ALLAH ya tsallakar dashi. Dan kuwa bai jima da farawaba ALLAH ya fargar da Uwargida kuma amarya ga Alhaji Hameed Taura, *Hajiya Firdausi Amin Taura* kenan. Mace ce jajirtacciya kuma tsayayya akan ahalinta. Sam bata da wasa koda akan fuskane. Mace ce mai addini matuƙa da son taimako. A hannunta Ramadhan ya girma tun daga yaye, duk da kuwa suna gida ɗaya mahaifiyarsa sam bataso hakan ba, musamman da taga bayanshi bata sake haihuwar wani ɗa namijinba a cikin ƴaƴa shidda mata data sake haihuwa da Basheer Hameed Taura. Bama itaba kaf sauran matan Alhaji Basheer Hameed Taura ɗin guda biyu duk basu da ƴaƴa maza sai mata. Sai dai babu yanda ta'iya, dan sam Anne ba sakarar uwar miji bace da matar ɗa zata taka koda da kirsane. Babu ruwanta da rayuwarsu bare harkarsu, dan bata taɓa sakama matan ɗan nata idoba balle damuwa da mi suke ciki. Dan da ace ita ɗin sakaraice da tasha matuƙar wahala a hannun Gimbiya Su'adah.  

        Gimbiya Su'adah mace ce mai izza da tsananin taƙama kasancewarta ɗiyace ga sarkin jihar Bina. Sannan ƴar gata kuma sangartacciya mai ji da mulkin gidansu. Mace ce mai shegen girman kai da ƙyamar talaka, dan sam bata biyo ƙyawawan halayar mahaifinta ba. A ƙasar amuruka suka haɗu da Alhaji Basheer Hameed Taura yayin karatu, inda soyayya mai ƙarfi ta ƙullu harta kaisu ga aure kasancewar su ƴaƴan ƙwarya tabi ƙwarya.    

        Bayan ceto rayuwar Ramadhan da Anne tayi daga faɗawa shaye-shaye suka sake harar rayuwarsa akan neman mata. Sai dai anan ALLAH ya karesa, dan baima saka matan a gabansaba balle su damesa. Musamman daya kasance yanada ƙananun shekarune dama a wancan lokacin. Abokan banza suka ƙirƙirar masa da sukaso fara jansa yawon dare, tunda ya farga da halayensu ya janye jikinsa. Dan Ramadhan mutumne daya gado halayen iyayen nasa ta ɓangarori biyu. Akwai halin mulki na ɓangaren mahaifiyarsa tattare dashi. Akwai kuma halin dattako na ɓangaren kakansa dake yawo a jikinsa. Hakanne ya sakashi zama mai murɗaɗɗen hali tun daga yarinta har girma. Bazamu ce dashi miskili ba. sai dai zamu kirasa mutum mai tsananin girman kai da ɗagawa. Ba komai yake so ba, ba komai ake saka yaso ba, sai idan shine yaso a karan kansa. Da yawan lokuta Anne ce kawai ke iya tanƙwarashi ta ƙarfin tsiya saboda itama tanada zafi sosai.

       Su *Alhaji Wali Bajau* basu daina bibiyar rayuwar iyalan Alhaji Hameed Taura ba musamman Ramadhan da suke kallo matsayin zuciyar gidan har yakai girma. Da tsiya-tsiya da makirci Alhaji Haladu Gwandu ya ƙulla soyayyar ɗiyarsa da Ramadhan har takaisu ga aure a shekarar daya kammala karatunsa akan lauya. *Amnah* yariyace ƙyaƙyƙyawa kuma ƴar gayu kamar yanda Ramadhan ke buƙata. A shekaru kaɗan ya ɗarata hakan ma dai-dai da ra'ayinsa ne, dan sam baison auren yarinya ƙarama yace sun cika shirme da ƙuruciya wa miji. Soyayya ce ta haɗa Amnah da Ramadhan a zahiri, a baɗini kuwa su Alhaji Gwandu sun shirya hakanne da manufa, dan ta bayan fage suka dinga amfani da Amnah suna cutar da Ramadhan. Burin Ramadhan aikinsa na lauya, tare da faɗaɗa karatunsa na Addini dan tun yana shekara sha bakwai ya sauke alkur'ani mai girma ya fara hadda, saboda Anne bata da wasa, ga shi ALLAH ya bashi ƙwalwar karatun shima. Sai dai burin mahaifiyar Ramadhan gimbiya Su'adah ba haka bane. Burinta duk dukiyar Taura Family ta dawo hannun Ramadhan ne, dan haka taita ƙoƙarin jan hankalin mijinta harya amince da jawo Ramadhan ɗin cikin babban kamfanin (company) na taura aka ɗaurasa matsayin oga kwata-kwata. badan ya so ba ya amsa, dan shi hakan baya cikin burinsa. Amma nasihar tsoho Hameed Taura ya sakashi amincewa akan tilas ya fara musu aiki. Lokaci-lokaci kuma yana taɓa aikinsa na lauyanci a ɓoyo dan gudun ɓacin ran mahaifiyarsa mai zafin zuciya da son nuna gadara ga kowa.

        Suna shekar ta uku da aure Amnah ta haihu ƴarta mace, sai dai kuma an haifeta sikila ne tamkar uwar tata data kasance sikilar ce dama. Ko kusa hakan baisa ubanta ƙin son kayarsa ba duk da sam gimbiya Su'adah basan auren takeba. Amma kasancewar itama uban Amnah ɗin ba koma baya bane akan juya kuɗi ya sata ɓoye ƙiyayyar auren a ƙasan zuciyarta, sai idan abin nata ya motsane taita azabar masifa.

     Hawan Ramadhan MD a Taura company matsaloli sukaita faruwa na ɓatan kuɗaɗe da wasu asarori da aka rasa musabbabinsu. Tun su Alhaji Hameed na kawaici hartakai shida mahaifin Ramadhan Alhaji Basheer Taura sun zaunar dashi sun masa ƙorafi da tambayar mike faruwane haka company keta baya maimakon gaban da suke fita da nasarori?.

     Amsa ɗaya ce shima baida masaniya. Amma yana kan bincike da ƙoƙarin daƙile komai. Tun ana tattaunawa iya su uku harta kai Anne ta shigo tafiyar, hakama sauran matan gidan sun sani. Kowa yana ɗaura zarginsa akan Ramadhan da tunanin ko yana wata harkar banza ne ta kuɗi a ɓoye?.

    A ranar da su Alhaji Balarabe Gizo suka shirya kai rayuwar Ramadhan ƙasa yayi dai-dai da ranar birthday ɗin ƴarsa Haseenah ƴar shekara biyu cif a duniya. An shirya liyafa ta gani ta faɗa tare da gayyata ta mutanen arziƙi Alhaji Haladu Gwandu ya baiwa Amnah ruwan addu'a da aka gauraya da guba akan ya amso ma Ramadhan ɗinne saboda ciwonsa na diabetis, Ramadhan nada diabetis  sakamakon ya zame musu tamkar gado ne. Alhaji Hameed Taura nada shi, hakama Alhaji Basheer Taura, shima Ramadhan ɗin haka da wasu daga cikin yara matan gidan. Sam Amnah batai tunanin mahaifinta zai iya cutar da Ramadhan ɗinta ba. Dan haka ta ɗauka ruwan addu'a da ƙyaƙyƙyawar zuciya takai masa. Sai dai an samu akasi bayan gama birthday party lafiya an watse ta buɗe fridge a gajiya ta ɗauka goran da ruwan addu'ar yake da tunanin ruwa ne saboda fitilar kitchen dake a kashe saita falo data ɗan hasko kaɗan ta sha. Tana sha Haseenah najan hannunta da mata gwarancin ruwa ruwa. Sai da tasha sosai sannan ta bata tasha itama.

      Wannan magani da Amnah tasha da ƴarsu Haseenah ya zama sanadin barinsu duniya. Dan kuwa azababben ciwon ciki ne ya baibayesu ita da ɗiyar har sai da aka kaisu asibiti, inda tunkan suje ma Haseenah ta rasu saboda ƙarfin gubar, Amnah kuwa sai kusan asuba itama tace ga garinku nan. Likita ya tabbatar musu hanjinsu ya kakkatsene ita da ɗiyarta saboda ƙarfin gubar da suka sha.

       Kwatanta irin tashin hankalin da Ramadhan ya shiga a wannan lokaci ɓata bakine. Bama shiba kowama da ke da alaƙa dasu wannan al'amari ya taɓa masa zuciya. Dan kowa dai ya fahimci guba aka ajiye musu. Sai dai ba'asan kowa ya ajiyeba saboda Amnah ita babanta yaba hannu da hannu batare da kowa ya sani ba. Ya kuma jaddada mata maganin diabetis ne kar Ramadhan yasha sai randa yake aiki musamman motsa jikinsa. Ita kuma ALLAH baisa ta bashi maganin ya sha da rana ba ta bari sai an tashi a birthday ɗin Haseenah. Ashe da rabon ajalinsune a ciki.

     Sosai Ramadhan ya fita a hayyacinsa. Dan yana mayuƙar son matarsa da ƴarsa duk da lalurar dake tare da su ta sikila. Iya bincike anyi a gidan babu wani bakin zare da aka samu sai tunanin cikin masu zuwa birthday ne suka ajiye gubar kawai. Tsabar yanda Ramadhan ya tada hankalinsa akan son gano wanda ya aikata ya saka su Alhaji Haladu Gwandu da abin yay matuƙar taɓawa da tunzurawa sakawa aka kai Ramadhan ƙasar Ukraine wai ganin likita. Sune suka tsarama likita ƙaryar da yace kar a sake yarda Ramadhan yay zaman NAYA sai bayan wasu shekaru harya manta da abinda ya faru. Sunyi hakanne domin su nisantashi daga bincike ko bibiyar ainahin gaskiyar lamarin da suka san reshe ya juye da mujiyane. Dan haukane kawai Alhaji Haladu Gwandu baiyiba a dalilin rasuwar shalelensa data bar duniya a dalilinsu.

    Ƙura ta lafa, abubuwa sun canja, shekaru sunyi gudu har kusan biyar da faruwar komai. Ramadhan yayi jiyyar zuciya data gangar jiki harya warke, amma anyi-anyi ya dawo NAYA yaƙi. An kaɗa dambu da takiya yace shi da NAYA har abada. Babu irin roƙo da lallaɓa da basu masaba musamman gimbiya Su'adah da take kasa ɓoye ɗunbin soyayyar da take masa koda a idanu ne amma ya kafe akan bakansa. Da ga ƙarshe ma sai ya koma U.S da zama. Kafiyarsa da murɗin hali yasaka kakansa Alhaji Hameed Taura yin fushi yace su barsa ya dawwama acan dan ALLAH karya dawo. Ya kuma saka sharaɗin koda wasa kar wanda ya sake zuwa dubashi har Mahaifinsa da gimbiya Su'adahn. Inko ba hakaba zai saɓama mutum a gidan.

    Wannan shine dalilin da yasa Alhaji Hameed Taura baya son ko maganar Ramadhan ai masa a gidan, duk da yana tsananin kewarsa a kusa da shi da begensa shima. Dan shi kaɗai ke zuwa dubashi a ɓoye batare da shi kansa Ramadhan ɗin ya sani ba.

     Yayinda Ramadhan kuma har yanzu zuciyarsa ke cike da burin binciko koma wanene da alhakin kashe masa iyalinsa, dan haka a tsahon shekarun nan babu abinda yake saƙawa da kwancewa bayan kasuwancinsa daya maida hankali dayi shi kaɗai sai hanyar dazai yi binciken yanda rayuwar matarsa da ƴarsa ta salwanta. A cikin wannan halin kuma Anne ta kawo shawarar Ramadhan B. Hameed Taura ya maye gurbin kakansa a kujerar shugaban ƙasa da akai masa tayi. Inda dudu shekarun Ramadhan B. Taura 36 a duniya. Ya rasa iyalansa yanada shekaru 31. Yanada ashirin da bakwai yay aure. A yanzu shekaru 5 cif da faruwar komai kuma.

     A hasashe ba'a taɓa samun wani shugaban ƙasa mai adadin shekarunsa na ƙuruciya ba a ƙasar ta *NAYA* ba sam.


        “Kana nufin dole kenan mu amince da zancen Alhaji Hameed Taura indai muna buƙatar cikar burinmu Your Excellency?”.

     Monday Mazier ya faɗa a ɗan hasale.

     Shugaban ƙasa da Alhaji yaro glass suka kalli juna suna murmushi mai kama da takaici suma. Yayinda Alhaji Haladu Gwandu ya dafa kafaɗar Monday Mazier ɗin yana faɗin. “Mr MM cool down abeg. Muma duk irin zafin da kakeji munjisa a lokacin daya tabbatar mana ya amsa tayinmu, amma kuma jikansa ne zaiyi bashi ba. Ƙwarai da gaske ya shammacemu, shammata maiban mamaki. Dan yayi hakane dan mu janye buƙatarmu kodan kasancewar jikan nasa yaro, tunda yana ganin ba'a taɓa shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsa ba a wannan ƙasa ta NAYA. Sai dai kodana zauna nai zari sai banji komai ba, domin Ramadhan baida maraba da hoton bango da kowa zaizo ya kalla ya wuce manne a falo batare daya amfana masa komaiba. Shine surikina da yarinyata ta rasa ranta a dalilinsa, yana can U.S tsahon shekaru biyar tamkar zararre. A ganina wannan damace a garemu mai sauƙi, duk da naji a raina Taura yayi hakane danya dawo da hankalin yaron gida kamar yanda sukaita fata a shekarun baya yaƙi hakan. Amma idan Taura yasan wata ai baisan wataba, Idan muka fitar da yaron matsayin ɗan takara zamu kawo wani sabon abu a ƙasar nan da ba'a taɓa yiba, sannan matasa zasu yarda da gaske muna tare da su. Babu tantama mulki zai cigaba da kasancewa a hannunmu ne”.

        “Woow exactly my man”.

Mr MM ya faɗa yana bama Alhaji Haladu Gwandu hannu suka tafa bakinsa washe da dariya tamkar yanda shugaban ƙasa da Alhaji Yaro glass da Alhaji Balarabe Andu keyi suma alamar hankalinsu yaɗan fara dawowa jikinsu.

     Alhaji Yaro glass ya gyara zama da faɗin, “Tabbas nima sai yanzu na fahimci manufar Taura na yarda cikin sauƙi, kuma hakan yamin daɗi, dan mu idan bai saniba wata damace ta ɗaukar fansa sau biyu akan abu guda. Ramadhan zai hau mulki na tsahon shekaru biyu kacal, sannan zai mutu sau biyu......”

      “Sau biyu kuma?”.

Shugaban ƙasa ya katse Alhaji Yaro glass cikin rashin fahimta.

     Alhaji Yaro dake murmushi yace “Ƙwarai kuwa sau biyu, dan dole ne mu ɗauka fansar Amnah data mutu dominsa, sannan mu kashesa adalilin taurin ran kakansa da ubansa. Na farko zai kasance cikin nasararsa da jin daɗin mulki a shekarar farko, a shekara ta biyu zai fara ciwo a dalilin guba da zata zagaya jininsa zuwa ɓargo da jiki. A shekara ta uku muyi bikin mutuwarsa da biznesa vice president ya hau kujera ya shekara biyu biyar cif kenan. Shekar ta ƙarshe a sake sabon zaɓe wannan shine amsar mutuwa biyu”.

     Ya ƙare maganar yana ƙyalƙyalewa da dariya, suma sauran suna tayasa kamar wasu zararru. Sai da sukai mai isarsu kafin suyi shiru suka koma shan shayi da cigaba da ƙulla tsiyatakunsu........✍



🤔🤔Hummm wani lokacin ma rasa abun magana ake.


No comments

Powered by Blogger.