Bakar Inuwa 54
*_Episode 54_*
..........Koda suka kammala falon suka sake dawowa, ya kuma ɗaure fuska yanda bazata roƙesa fitar ba. Dole ta kama kanta dan kuwa koda ya zaunar da itama karshen 3seater sai ya kwanta shi ya ɗaura kansa a cinyarta. Ya kuma kamo hannayenta duk biyu ya ɗora a sumarsa sannan ya canja musu tasha.
Raudha babu bakin magana, tun tana cuna baki gaba har laushin sumar da takema kallon zatai ƙarfi saboda yanayinta na irin tamu ada ya fisgeta ta tura yatsunta a ciki a hankanli. Lumshe idanu Ramadhan yayi da sauke numfashi a hankali dan hakan abune da yake matuƙar so a rayuwarsa shima.
A hankali ta cigaba da wasa da yataunta cikin sumar cike da shauƙi harta shagala ta manta dawa take tare. Haka ta cigaba da wasa da sumar kansa cikin shagala tana kallon film, yayinda shi nashi idon ke'a lumshe ya lula duniyar tunani.
★Kowa bai damu da rashin ganinsu a gidan ba har yamma, sai gimbiya Su'adah ce data cika tai fam da takaici, dan har Muneera ta aiko tai mata cid ɗinsu ta koma ta sanar mata ai duk yau ma bata tunanin Raudha taga rana. Gara Ramadhan kan fita yayo salla. Dama kuma shi yaje ya gaisheta da safe ma.. Har lunch ta shirya masa da kanta da maganin da Adda Asmah ta kawo waina fidda son Raudha a ransane ya tsaneta. Har sai ya mata korar kare a government house. Sai dai abinda bata sani ba na tsananin jan ra'ayinsa da mallakar zuciyarsane akan Ayna'u, malamin daya bata ya tabbatar mata Ramadhan yaci maganin nan sai ya manta har gimbiya Su'adah ɗin ma da kaf Taura family ya koma ƙarƙashin ikon ƴarta Ayna'u, hatta da mulkin ƙasar NAYA Aynah ce zata koma mai tsarawa da zartar da yanda za'ayi.
Sai dai kuma Ramadhan ya kwafsa mata baije sashen da rana ba. Washe garima babu wanda ya gansu, sai randa suka cika kwana uku yaje sashen nata shi da Raudha da rana. Hakan baisa ta gaza tanadin na dare ba a cikin gasashshiyar kazar da taji kayan haɗi na ban mamaki aka aika masa har sashen Anne da kunun madara da yasha zuma a ciki a wannan rana. Ita kanta Raudha basu ƙyaleta ba. A baki Bilkisu sukaji abinda tafi so, amma kasancewar guri ya ƙure aka haɗa mata zoɓo mai sauƙi aka barbaɗe da magani sanin Ramadhan baya shan zoɓo shi kuma.
Tunda Lubnah ta nufi sashen Anne da abinci sai kuma zuciyar gimbiya Su'adah ta shiga ƙunci, rasa mike mata daɗi tayi tanata faman kaikawo a bedroom ɗinta. Gaba ɗaya zuciyarta na nuna mata ƙiyayya da abinda ta aikata akan ɗan data haifa saboda tsanar matarsa. Sai dai kiyayyar da takeji akan Raudha nata ƙoƙarin danne gaskiyar dake son bayyana kanta ga kuskuren da idonta ya rufe ta kasa fahimta...
Sam Anne bata kawo komai a ranta ba ta haɗa kayan wajen gimbiya Su'adah a cikin dinner ɗin su Ramadhan. Taya ma zatai tunanin za'ai amfani da uwa wajen cutar da ɗanta? Ita bama ta taɓa kawoma ranta wani cikin surukan nata na bin malamai koda akan Pa ba. Tama shedesu akan hakan ɗari bisa ɗari dan bata taɓa ganiba gaskiya. Ita kuma mutumce da bata yanke hukunci akan abinda bata ganiba sam.
Raudha yarinyace mai tsarta, haka kawai taji gabanta na faɗuwa lokacin da sukai zaman cin abincin. ALLAH ta shiga ambato a zuciyarta, yayinda Ramadhan gashin kaza ya ruɗesa ya ɗan ɗiba da cokali mai yatsu ya kai bakinsa yana ambaton “uhhm”. Kallonsa tai kawai batare data iya cewa komai ba. Sai da zai kai lauma ta biyu ne ALLAH ya bashi ikon ambaton Bismillah. Ƙaramar ajiyar zuciya ta sauke, koda yace suci kazan catai ta ƙoshi, dan itakam idan tace zatai irin cin namansa ai matsala za'a samu. Bai wani ci da yawa ba ya tashi akan zaije wajen meeting idan an tashi yazo yaci. Amma ta tabbatar taci abinci inba hakaba ya dawo ɗura zai mata da kansa.
Gimbiya Su'adah ce ƙarshen shigowa. Ramadhan ya gaidata cike da kunyar tun safe bai koma sashenta ba. Koda yake Anne ma da suke tare sai ya fito salla take ganinsa. Ya ɗanyi mamakin yanda ta amsa masa a sake, ta kuma gaida su Anne itama. Kowa zaune yake a kujera har su Yafendo, shine kaɗai zaune ƙasan lallausan carpet ɗin falon domin girmamawa ga iyayensa.
Ba Ramadhan ɗin kaɗai ba, hatta su Pa sakewar gimbiya Su'adah ya basu mamaki, duk da suna danganta hakan da abinda ta kawo take ganin zataci nasara. Su dai babu ruwansu, idan Ramadhan ya amince ya karɓa zasu tayasa so, idan baya so kam bazasu masa dole ba tunda yay musu biyayya akan Raudha kar su cika shiga hakkinsa.
Bayan an buɗe taro da addu'a Bappi ya bama Gimbiya su'adah damar faɗin abinda tazo musu da shi kafin yau. Tunda ta fara bayani Ramadhan ya ɗago a rikice yana duban mahaifiyar tasa. Fara'ar fuskarsa kuwa tuni ta ɓace sai dai komai baice ba harta kammala. Bappi ya jinjina kansa da maida hankalinsa ga Ramadhan da ya maida kansa ƙasa.
“Ramadhan kaji abinda mahaifiyarka tace. Tana buƙatar ka auri ɗiyar ƴar uwarta domin likita ya sanar matarka bazata sake haihuwa ba saboda ciki data zubar a kwanaki”.
Ramadhan daketa jera kalmomin innalillahi a zuciya ya nisa da ƙyar. Abinda Maah bata sani ba ya daɗe da kammala bincike akan yanda Raudha tasha magani, sai dai takamaimai wanda ya bama su Muneera maganin suka zuba mata dama yake nema ruwa a jallo. Sai gashi a cikin sauƙi ta tabbatar masa da itace, domin inba itace ɗinba taya tasan mahaifar Raudha zata lalace harta gagara haihuwa....?
“Ramadhan!”.
Inna dake gefensa ta kira sunansa. Numfashi ya furzar da ɗago idanunsa da suka kaɗa ya kalleta. Sai kuma ya maida kansa kasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.
“Kiyi haƙuri Maah bazan bijirema umarninki dan baki isaba. Sai dai zanyi hakane tare da tabbatar miki wannan BAƘAR INUWAr da kike hangemin gwara ranar da kike gudanmin da ita. Ban musa miki wasu a dangin Ameenatu nada tabo na ƙaddarar rayuwa ba, amma ina son ki sani wlhy Ameenatu yarinyace kamila mai addini. Sannan ta kawomin mu..tuncin...ta har gida. Idan zan faɗa miki wacece wadda kikema kallon mutuniyar kirkin a yanzu zakisha mamakin hakan. Maah laifin wani baya shafar wani ko'a wajen UBANGIJI. Sannan ALLAH na fidda rayayye a cikin matacce. yana kuma fidda matacce a cikin rayayye. Hauhuwa kuwa ta ALLAH ce, amma insha ALLAH akoda yaushe zaki iya ganin zuri'ata basai na auri wata ba”.
Dukkanin wata fara'a dake a fuskar gimbiya Su'adah ta ɓace ɓat, baka ganin komai sai ɗunbin ɓacin rai da azabar masifa. Gasu Pa kuwa gaba ɗaya murmushi ne kwance a fuskokinsu, bana bijirema gimbiya Su'adah da Ramadhan yayi bane. Na yabo da tabbatar da ingancin tarbiyyar Raudha da sukajine daga bakinsa. Wanda su sanin kansune Ramadhan baya iya boye abu inhar bai masa daɗi ba zai faɗa, hakama idan yayi masa zai yaba koda da murmushi ne. Koba komai hankalinsu ya sake kwanciya da yarinyar da suka jima suna kyautatama zato.
Babu wanda ya sake cewa komai har ita. sai Inna ce tai musu nasiha da gaba ɗaya take nufin da gimbiya Su'adah take amma sai ta haɗa kowa da kowa a ciki. Daga haka taron ya tashi babu wani armashi. Dan ko bikin yaran gidan da sukaso tattaunawa a yau ɗin shima bai yuwu ba dole aka barsa sai wani lokacin dan ana jiran sauran gidajen angunan su kawo kuɗi ne. Ƴammata kusan shidda za'a aurar a gidan nasu Ramadhan. Ciki harda Lubnah da Bilkisu kuwa. Sai Sumayya, Rufaidah, Ai'sha da Ummita. Dukansu sunyi karatu wasunsu ma na aiki, Ummita ce kawai take kan karatun saboda manemin nata ya takurane yasa za'a haɗa da ita amma sa'ar Muneera ce ma. Koda yake ita kanta Muneera ɗin ta isa auren ai kawai dai dan akwai yayuntane.
Babu wata walwala Ramadhan ya koma wajen Raudha, dan yasan ma'anar shirun mahaifiyarsa. Tuni ita har tayima shirin barci. Tana zaune ne a kan gadon tana assignment ɗin makaranta da aka basu na cikin hutu, sai dai sanye take da hijjab a saman kayan barcin nata. A kallo guda ta fahimci ransa a ɓace yake, cikin dauriya ta masa sannu. Bai amsa ba sai dai ya kwanta a gadon tare da ɗoro kansa saman cinyarta bayan ya ture takardun gabanta gefe.
“K dole kin zama ƴar boko ko?”.
Ɗan murmushi tayi kawai dan yanda yay maganar kamar mai son huce haushinsa akan bokon nata ne. Cikin san kauda masa damuwarta tace, “Harka tunamin Abbanmu. Idan mukai masa laifi koya tashi baida ko sisi sai ya hana kowa zuwa makarantar boko ranar. Ya ringa faɗin, “Anma fasa bokon, daga yau bazaku sake zuwa ba, bandama shegantaka irin ta bature yabi duk ya katantane duniya ya hana kowa zaman lafiya, komai bazaka samesa yanda kake muradi ba sai kayi wani abu shege a.b.c.d kai nifa shiyyasa ma ana kaini ina tserowa a makaranta da ƙyar na haɗa sakandire ɗin ma”.
A bazata dariya ta ƙwace masa. Har haƙoransa na bayyana baki ɗaya sai dai ya kai hannu yana karewa. “ALLAH na lura Abba ɗan darune?”. Ganin yanda ya karɓi zancen ya saka Raudha dake nata ƴar dariyar itama faɗin, “Tab damma baka sanshi bane. Wlhy duk randa darun Abba ya tashi gidan nan ranar kowa sai yaji a jikinsa. Ko ruwa ka cika kofi zakasha sai yace ka ƙara masa talauci kana baƙin cikin ya zama mai kuɗi”.
Yanzu kam sosai yake dariya. Raudha da farin ciki ya cikata itama ta tura yatsunta duka a cikin gashinsa tana masa susa. Nan ta shiga bashi labarin M. Dauda sai dai na hankali wanda tasan mutuncinsa bazai zube a garesa ba. Cikin amincin ALLAH sai gashi ƙaunar mahaifinta ta sauka masa a rai har yanajin sassaucin takaicin halayyarsa tada da bincike yazo da ita.
“Ya kamata ma muje mu gaishe da Abba Hutawa gaskiya”.
Cak Raudha ta dakata da susan da take masa a cikin gashi ta tsurama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ido idanunsa a lumshe suke yayin da hannayensa duka ke harɗe a ƙirjinsa yana kwance rigingine. Yanda ya nutsu zai baka tabbacin susar da take masa cikin gashi na masa daɗi. Ya buɗe lumsassun idanunsa da suka canja launi a hankali ya zuba mata su. Gira yaɗan ɗaga mata yana sassanyan murmushi. “Yadai naji kinyi shiru Ustazah?”.
Hawayen da suka ɗan cika mata ido ta haɗiye, cikin ƙaƙaro murmushin itama tace, “Nagode da karamcinka”.
“Cmon johre. An gaya miki Abban nakine ke kaɗai banson iyayi”.
Yay maganar yana dungure mata hanci da ƙoƙarin miƙewa zaune. Toilet ya shiga, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya da hawaye lokaci guda. Wani abu mai muhimmanci na sukar ranta. Koda ya fito wanka cayay ta kawo masa sauran namansa. Dan bacin ran daya shigo da shi ta riga ta gusar da shi. Kawo masa tai harda kunun, yako ci abinsa yay ƙat sannan ya koma bayin yayo brush, koda ya dawo assignment ɗin ta nuna masa inda bata gane ba.
“Ustazah! Kibar batun Assignment ɗin nan nima inada nawa Assignment ɗin mai kawo lada ma.”
“Please Ya Ramadhan dafa an koma hutu idan ALLAH ya kaimu zamuyi submitting”.
Gadon ya hawo yana ɗaure igiyar rigar barcinsa. Ya zare mata hijjab ɗin jikinta sannan ya ɗauka takardar data rubuta questions ɗin da amsar data rubuta daban na wanda ta gane. “Yarinyar nan kanki fa naja”.
Ya faɗa cikin ɗage mata gira. Murmushi kawai tayi da maida kanta ƙasa. Shima hankalinsa ya sake maidawa ga takardun yana faɗin, “Ai gyaran ma kaɗanne”. Bayani ya shiga mata dalla-dalla harma akan abinda bata tambayesa ba, dan shima yayi course ɗin sanda yana jami'a. Sosai taji daɗin bayaninsa har tana sake zaƙulo masa wasu tambayoyin. Sai dai taƙi sakewa da jikinta sai faman karewa take da hannu kamar mai jin sanyi. Tsaf yana lure da ita amma yay kamar bai gani ba. Zata sake jeho masa wata tambayar ya turo kayan karatun nata ƙasa da jawota jikinsa yana faɗin, “K ni na gaji da aikin bautar bature zo kiji wata magana”.
Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss's..........✍
Leave a Comment